← Book details Sakar Makafi Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 105 OF 113

Sashe 105

Sakar Makafi Part 3 Complete Hausa Novel · about 7 min read

..........Kusan kwatankwacin tambayar da Dadah yay ma Sanda a jiya itace ya maimaitama Malam almu a yau. Sai dai saɓanin Sanda Malam Almu kai tsaye ya bada tashi amsar da iya gaskiyarsa kuma.
       “Sunana Yunusa. Asalin ɗan ƙauyen Manku. Can aka haifeni can na girma. Rashin mahaifiya yasa mu shiga ƙuncin rayuwa a hannun matar uban ni da ƴar uwata. Duk da ana tausaya mana mun gagara samun taimakon kowa daga dangin iyayenmu harma da abokan arziƙi na gari saboda tsoron masifar Zinaru. Mahaifin mu kuwa Uhmm ma bashi da ƙarfin ikon furtawa akansa ma balle mu dake amsa sunan ƴaƴa. Ɗaukin mutum ɗaya muke samu matar maƙocin mu. Itama sai ta faki idon Zinaru. Sai wani da ake kira Babba. Babba hatsabibi ne sosai a ƙauyen mu, kowa tsoronsa yake ji dan cikakken ɗan tauri ne kuma ɗan farauta. Alaƙata da shi a dalilin ɗansa ne da muke abota. Rashin mai kwaɓa min yasa Rabe samun nasarar jan ra'ayina ga harkar farauta, sannu a hankali na zama riƙaƙƙe a harkar, idan kana son shaida waye Almu na Babba ƙarfe bashi ratsa jininka. Guduma mai fasa kan tantiri to ka taɓa min ƙanwa. Anan ne fa zaka sha mamaki. Dan hatta da Zinaru yanzu kam tsorona take, dan akwai randa naje gida na tadda ƙanwata na kuka wai ta mareta, humm ai bamma san na dasa mata wuƙa daga farkon cinya zuwa ƙarshenta na tsargata ba. Atake ta sume saboda azaba. Ni kuma na tsallaketa na bar gidan. Duk fa abin nan da nake sam bana shaye-shaye, iyakata shan magungunan ƙarfe da ƴan dabaru irin na ƴan farauta da ƴan tauri. Ba ruwana da Babana, dan haushinsa nake ji saboda yanda ya kasa kula damu. Wannan yanka da naima Zinaru yasa daga ranar ko kallon inda ƙanwata take bata iya yi, dan tasha jiyya kusan ta shekara ɗaya kamar ƙafarta zata ruɓe.
      Dalilin baro garinmu faɗane ya haɗamu na farauta da wasu mafarauta dake makwaftan ƙauyen mu. Wannan faɗa kuma yasa aka zubar da jini sosai a tsakanin mu da su, sai dai babu wanda ya mutu sai dai nakasa. A wanda aka nakasa kuwa harda shugaban tawaga Babba. Dan an tsayayar masa ido ɗaya. Nan fa muka tabbatar da sai mun rama da mafi munin ramako. Muka dinga binsu ɗaya bayan ɗaya muna caccake musu ido ɗaya. Kwana biyu tsakani suka shigo garinmu muma dan ɗaukar fansa. Sai dai maimakon su farmake mu sai suka farmaki ƴan uwanmu. Duk duniya ban haɗa al'amarin ƙanwata dana kowa ba, dan haka na tattarota muka baro garin cikin dare. A niyyata na samu inda zan maƙalata na koma a cigaba da yaƙi, sai dai aka samu akasin lissafi. Munzo zamu tsallaka titi Oga ya bugeni da mota.
     Naji ciwo sosai, dan ban tashi farkawa ba sai bayan kwanaki. Samun ƙanwata a kusa da ni yasa naji sassauci. Oga na kula da komai na asibitina, ƙanwata kuwa na jiyyata. Watana biyu na samu lafiya. Oga ya ɗebemu zuwa gidan shi, acewarsa muje mu ƙara hutawa jikina ya ƙara sauƙi sosai. Banyi gaddama ba, dan ba komai alkairinsa bamai guguwa bane a garemu, duk da ya zama sanadin kwanciyata jiyya harta watanni. Ganin ƙanwata na cikin aminci a gidan, dan tana taya matar gidan yan ayyuka, ni kuma maigadi ya zama tamkar abokona sai na sulale a wani dare dan zuwa ƙauyenmu naga yaya abubuwa ke tafiya.
         Na iske mummunan labari, dan kuwa dai da kungiyar mu, da kungiyar wancan ƙauyen sun kusa haddasa rikicin faɗa daya saka aka zo aka tattaresu zuwa binni. Sun zo neman ƙanwata kuma domin yin ramuwar gayya kamar yanda sukai ga sauran ƴan uwan abokaina, sai dai sun samu bata nan dan haka suka huce akan Zinaru da babana. Wannan shine sanadin rasa mahaifina. Naji babu daɗi, sannan nayi kuka sosai, dan duk da yanda nake nuna ban damu da babana na da yanda shima bai damu da al'amarinmu ba ina sonshi. Ban kwana ba a ranar na dawo gidan Oga, na kuma yima kaina alƙawarin nabar harkar farauta har abada tunda na rasa mahaifina a dalilinta.
      Muna a wata na biyar Oga yazo min da tayin aiki, sai dai yace min ba'a nan gidansa bane. Sannan yace min zan samu alkairi mai yawa da zan inganta rayuwar yar uwata. Tunda mace take, yau da gobe bazai yiwu ta cigaba da zama a gabana ba. Jin haka yasa banyi musu ba na amince. Shi ya bani shawarar barinta a gidanshi, ni kuma aminta da shi yasa na barta, dan itama tace ba komai na barta ɗin tana jin daɗin zama wajen hajiyar.
       Wannan ne maƙasudin fara aiki a gidan. Da farko aikin namun daɗi, musamman yanda nake samun karramawa da alkairi daga Hajiya Babba. Hakama su Ma'aruff. Ga kuma drivern gidan da muka zama kamar ƴan uwa, duk da ya girmeni sosai a haihuwa. Watanni na kusan uku naga na tara kuɗi sosai sai naita murna, abunka da wanda bai taɓa ganin ko dubu goma a dunƙule matsayin tashi ba, biɗi-biɗi na shirya nazo gidan Oga nace masa nifa zan aje aiki, dan yanzu haka ina da kuɗi kusan dubu ɗari uku. Sun ishe mu rayuwa. Dariya Ogan yayi a lokacin, sai da yayi mai isarsa sannan yace dani ai yanzu ne ma zan fara aikin daya kaini.
     Mamaki ya kamani, cikin tabbatar wa yace, “Kwarai da gaske Almu, yanzu ne zaka koma ainihin aikin da muka kaika gidan domin shi. Dan kuwa BABA ya gama aminta da dukkan motsinka”.
       Babu wanda sunan Baba bai daka ba a zuciya, idan ka cire Dabo da Yusuf da basu san da zancen ba. Sai dai babu wanda yayi magana suka bar Malam Almu ya cigaba da maganarsa.
     Cikin kasa haƙuri na ce, “Waye Baba?”.
     “Karka damu sanin Baba, bashi da wani amfani a gareka Almu. Abinda zan faɗa maka yanzu shine mai amfanin. Dan haka ka nutsu ka saurareni”.
        Zama na gyara na bashi hankalina gaba ɗaya batare da nayi magana ba.
    “Ba wani aiki bane mai wahala Almu. Muna son ka dinga sanar damu duk wani motsin mutanen dake gidan nan koda jariri ne. Kai hatta baƙi dake shigowa ma muna son musan shiga da fitar kowa. Lambar mota idan da motar suke, ko lambar mashin. Kai idan nace maka komai, komai da komai nake nufi. A baya akwai wanda muka saka aiki sai dai sakarai ne. Shiyyasa kai muke ganin zaka iya. Idan kuma har kayi yanda muke so duk wata kanada albashi naira dubu ɗari bayan wanda ake biyanka acan gidan”.
    Na fara murna yace, “Ba shike nan ba ma. Kana da ƙyautar gida ƙarami bayan ka kammala. Sai dai da sharaɗi”.
       “Kowane sharaɗi ne zan iya Oga”.
Na faɗa tun kafin ya rufe baki. Murmurshi yayi mai yalwa da faɗin, “Ka tabbatar?”.
      Na ce, “Kwarai ma kuwa.”
“Sharaɗin shine ƙanwarka zata cigaba da zama a wajena har sai ka kammala aikin. Sannan bazaka dinga ganinta ba har sai na tabbatar da kwazonka zan dinga gaya maka lokacin da zakuna gaisawa. Sharaɗi na biyu komi ka gani kada ka tambayeni dalilin sakaka yinsa a wannan gidan. Sharaɗi na uku idan ka bari wani yasan mi kaje yi a gidan kaida sake ganin ƙanwarka har abada ”.
     Hankalina ya tashi nace masa na fasa. Kawai zan ɗauki ƙanwata na wuce. Yace ina ai na makaro. Tun tuni aiki ya faɗa ma”.
     Hankalina ya tashi sosai, nai masa kuka nai roƙo amma yaƙi. Sai ma nuna min bindiga da yayi, da tabbatar min shi SOJA ne. Idan na damesa zai ma kashe ƙanwar tawa ne ni kuma ya kamani tunda dama mai laifi ne. Idan ina son na tsira, ƙanwata ta dawo hannuna naje nai aikina kawai. Ya bani waya, tare da umarnin sanar min komai daya lissafa min. Dan an buɗe min wani abu WhatsApp, ya nuna min yanda zan dinga naɗe magana ina tura masa. Ya gargaɗeni na adana wayar sosai. Sannan ya kawo ƙarama ya bani. Wannan shine dalilin zuwana gidan wlhy”.
       Shiru kamar kowa ya kasa magana a falon. Sai zuwa can T-Dalha yay ƙarfin halin katse shirun. Babu wanda ya hana shi, dan indai harkar bincike ce a barma jam'ian farin kaya kayansu.. cikin nisawa ya ce, “Yanzu ina ƙanwarka?”.
       “Tana hannun Oga har yanzu. Sai lokaci-lokaci yake barina naje har gidan na ganta. Sai dai ana jimawa sosai”.
      “Waye Sanda?”.
   “Ban sanshi ba. Oga ne kawai ya haɗani da shi a shekarar data gabata, akan zai tayani aiki. Shine aka kaishi matsayin mai bayin fulawa. Wanda yake yi kuma yazo yace ya ajiye aiki”.
        “Shi Buba miye alaƙar ku?”.
    “Bamu da wata alaƙa gaskiya. Dan ganinsa kawai mukai yazo a madadin direba. Yama ce mana shine ya turo shi kuma da sanin su Alhaji Ja'afar ne”.
      Yanzu kam da Mamaki Imran ya ce, “Su Ja'afar kuma?!”.
      “Eh tabbas haka ya faɗa”.
  Daddy Imran ya ce, “Okay na tuna. Sun min bayani kan zuwansu duba shi tsohon driver da yay accident, suka kuma buƙaci ya samar musu da wani ta hanyarsa”.
     ALLAH sarki Dadah sai da yaji iskar da ta tsaya masa cak ta kaɗa da ƙarfi. Dan harga ALLAH sai da yaji yuuu a ƙasan zuciyarsa da yaji sunan su Ja'afar ɗin...........✍️
120
Chapter 105 · 0% Book details