Sashe 20
Sakar Makafi Part 3 Complete Hausa Novel · about 7 min read
Tun kafin ta iso falon ƙamshinta ya iso hancinsa. Turaren nan nata na rikita masa lissafi tun ba yanzu ba. Yana dakewa ne kawai kada ai abin kunya. Amma yau sai yake jin kamar ma bazai iya hakan ba. Biebah da bata san yanayi ba tai sallama a ƙofar falon. Koda ya amsa da bata iznin shiga kanta a ƙasa ta shigo.
In dai haƙuri ne da rashin son hayaniya shi shaida ne akan Biebah ɗinsa. Ta ɗakko halayya da yawa na Mammah. Rashin kamaninta da su Haysam baisa ya taɓa kawoma ransa ba mahaifinsu ɗaya ba. Sai a jiya da Haysam ɗin yay masa bayani da kansa. Ya kuma tabbatar masa mahaifin Biebah ɗin na nan a raye. Hasalima ya ƙara bunƙasa da dukiya, kuma bai ƙara samun haihuwa ba har yanzu. Wannan abu ya ɗaure kan sa sosai, dan shima ana faɗar sunan ya sanshi. Dan mutum ne daba ɓoyayye ba. Lallai akwai baban al'amari a tsakanin wannan ɗiya da mahaifinta, ga shi kuma wani ikon ALLAH tana bala'in kama da shi, ya tabbatar koshi yaga Biebah a yanzu ba asiri ba komi ke kansa sai zuciyarsa ta girgiza. Dan kamanin bana wasa bane ba fa....
“Yaya sannu da zuwa. Kayi haƙuri na saka jira”.
Furucin Biebah ya katse masa tunani. Ajiyar zuciya ya ɗan sauke da sakin murmurshi. “Ba komai, ai amarya bata laifi”.
Bata wani kawo komai a ranta ba tunda tasan dai bai wuce akan saka rana ba. Sai tai ɗan murmurshi kawai tana sunkuyar da kai. “Ina Baby na?”. Ta faɗa cikin son ture wancan zancen. Ɗiyarsa take kira Babynta. Wannan kuma yana cikin abinda ya saye zuciyarsa da shi sosai. Ya nisa kaɗan yana gyara zama. “Babyn ki na lafiya. Duk da yau kwana biyu banje na gansu ba nima.
Received at 6:24 AM
Aiki yamin yawa sosai. Amma koda nake fitowa ɗin nan munyi waya”.
Tai murmurshi tana jinjina masa kai. “Masha ALLAH. Ya jikin Hajiya?”.
“Alhamdulillah da sauƙi itama.”
Ruwan data zuba ta miƙa masa. Ya haɗa da hannun nata ya riƙe. Hakan ya sata daburcewa dan bai taɓa mata hakan ba koda da kwatance. Kallonsa ta ɗan yi ta janye idanunta dan haka yay murmurshi da faɗin, “Kowa kin tambayi ya yike amma ni banda ni. Anya akwai amana a wannan sabgar Biebalo.”
Kanta a sunkuye tana murmurshi ta ce, “Ai kai na ganka kana lafiya”.
“Tab sama-sama dai. Bakiga duk ma na rame ba”.
Ɗagowa tai ta kallesa fuskarta na nuna damuwa. Ta ce, “Miya same ka?”.
“Ƙaunar Biebalo da tsananin buƙatar ta a kusa dani mana”.
Ya faɗa kansa tsaye yana ja mata hanci. Wata muguwar kunya data rufeta bata ma san ta furta, “Kai Yaya na banu”.
Dariya yayi sosai. Dan yanda tai ɗin dole ta baka dariya. Sai da yasha ruwan ya ajiye kofin sannan ya gyara zamansa da faɗin. “Da gaske nake fa. Shiyyasa ma kikaga inata dojema zuwa gidan nan. Dan nasan bazan iya kauda idanu na ba.”
Ita dai yau gaba ɗaya yana neman rikitata da kalamansa. Abinci ta buƙaci zuba masa. Yace ta barshi sai yaje salla ya dawo magriba ta kusa. Ta jinjina kai tana miƙewa ta koma kujerar nesa da shi kaɗan kamar yanda ta saba. Bai hanata ba ya cigaba da janta da hira har aka kira sallar magriba sannan ya miƙe ya shiga bayin cikin falon ɗaura alwala...........✍️
Received at 6:24 AM
3 people reactedKIƊA A RUWA 3
38
........Dada ya fito Faro ya fito suka haɗu a compound. Cike da shaƙiyanci Faro ya furta, “Alhajin ALLAH ai nazata ma sallar a ciki zakayi yau?”.
Cikin rashin fahimta Dada ya harareshi. Faro yay dariya da faɗin, “Miye na hararata daga faɗar gaskiya. Na shiga ciki akace zuciyarka na ɗakinka tare da kai. Amma bawan ALLAH ko kunyar Mammah baka ji ne?”.
Yanzu kam Dada ya gane sarai. Dan haka ya girgiza kansa da faɗin, “Bani da lokacin ka. Ka cigaba ina da maganinka a hannu Haydar”.
“A'a tsaya mi kake nufi?”.
Gaba Dada yay abinsa batare daya sake tanka masa ba...
Bayan an idar da salla sun fito Faro kema Dada bayanin yaran nan duk sun zo hannu fa. Sannan ya fara aiki akan Garba.
Dada ya jinjina kansa yana ɗan furzar da iska. “In dai Garba ya faɗa tarkonmu Ojo ya gama zuwa hannu Haydar. Yanzu damuwata musan ta yanda zasu rarraba kayan nan da yaran suka ce”.
“Nima hakan na damuna sosai. Amma akwai wani jami'in farin kaya na yarda da aikinsa gaskiya. Ko zamu shigo da shi tawagar nan ne?”.
“Hakan ba laifi bane in dai ka yarda da shi.”
“A, na yarda da shi gaskiya sosai. Amma in kana da lokaci yau da sai yazo ku haɗu”.
“In dai ka yarda da shi basai na ganshi ba. Dan satin nan zan yi busy da yawa. Bana jin ma zan shigo UNIT ZERO gaskiya.”
“Yaran nan fa? Ya kamata dai ka shigo”.
“Ku cigaba da kula da su. Amma kar ku haɗasu da waɗan can tunda su an fara treating ɗin su. Driver nan ma Bilal nake so ya dawo dan yayi tafiya”.
“Ba Ammar na nan ba?”.
“No, Ammar baya ji, zai iya ƙwaɓa aikin. Karka damu Bilal ɗin ya kusa dawowa”.
“Na gane. ALLAH ya dawo da shi lafiya ya bamu sa'a”....
Isowar Nabeeha wajen ya saka Dada yay shiru. Faro da bai san dawan garin ba ya fara tsokanarta da kalmar, “Uwargida sarautar mata”..
“Hummm!”.
Kawai tace masa. A take ya fahimci ya ɗebo da girma. Sai kawai yayma Dada sallama ya wuce masaukinsa. Nabeeha bata gaida shi ba, dan haka bai sake bi takanta ba. Sai da ya wuce Dada da yaƙi kallonta da alamar ɗaci a muryarsa ya ce, “Ke baki iya gaisuwa wa mutane ba ko?”.
Duk da yanda take son dinga danne yanayinta sai da ta ɓata fuska, muryarta na fita da takaici ta ce, “Miyasa zai kirani da wani Uwargida”.
Idanu ya zuba mata a karo na farko. Abu biyu ya saukar mata a lokaci ɗaya. Tsigar jikinta ta tashi, sannan wani shakkarsa ta tsarga mata. Ta sani shi baya son raini, ba'a kansa kawai ba. Ko ga wani kayi, wanin daya tabbatar ya girmeka sai ya nuna maka ɓacin rai. Sai dai idan wancan ɗin ya zubar da nasa girman ne...
“Kayi haƙuri ina son muyi magana ne”.
Nabeeha ta faɗa muryarta na rawa. Tamkar Dada bai jita ba, yay ƙoƙarin barin wajen. Da sassarfa ta tari gabansa, cikin danne shakkarsa dake son rinjayarta da aro jarumtar dole kawai ta rungumesa ta sakar masa kuka.
Kasa motsawa Dada yayi, sai dai yabi compound ɗin da kallo dan son tabbatar da babu mai ganinsu. Ita ko wani bugawa ƙirjinta yayi, saboda jin ƙamshin turaren da tunda ta dawo take jinsa a jikin Nimrah da Ruƙayya. Tabbas turaren SHUWA INCENSE AND MORE +234 704 229 3387. Duniya ne. Suna da turare wuta da khumra kaloli har uku: black humra, white humra, brown humra. Akwai oil perfume da kullacham da genine da Turare kabasa kaloli uku shima. white, black, and brown. Akwai man kitso, da kayan gyaran jiki masu gyara fata da sanyata laushi da santsi kiyita glowing abinki hajjaju. Tsagaitawa tai da kukan nata, ta ƙara zuƙar numfashi da ƙyau. Jin tabbacin ƙamshin ne fa ya sata saurin jan jikinta baya. Ya bita da kallo, itama nata idanun ta ɗago tana kallonsa, zuciyarta na tafasa a cikin ƙirjinta. Tana da kishi mai zafi, kuma ko yaya ya taso mata bata iya haɗiyewa.
Tsaf ya karance wutar bala'in da ke ci a cikin idannunta. Sai dai bai san akan miye ba. Bai kuma yi magana ba har sai da ta buɗe nata bakin ita tayi.
Received at 6:24 AM “Saboda kana samun biyan buƙatar ka a wajen tatsitsiyar yarinyar da ka haifi wadda ta fita ma kake wulaƙantani Haysam. Ka kasa sauke nawa hakkin amma ita kana tare da ita ko kunyar ƙannenka baka ji? Kaƙi taka inda nake duk da halaccin da nai maka na jiranka tsahon shekarun da bani da tabbas na dawowarka. Kana zaton bazan iya barinka ba saboda ina sonka ko?......”
Kuka ya sarƙeta ta kasa ci-gaba da magana. Sai jiri da take ji kamar zata faɗi. Kanta ta dafe, da jan ƙafa tabar wajen ganin yaƙi yay magana. Wani irin zafin tsanarsa take ji a ranta. Tana son mijinta, tana masa kishi mai tsananin gaske da ita kanta har tsoron kanta take ji. ALLAH wani lokacin har ji take kamar garama ace ya mutu idan ta tuna yarinyar nan matarsa ce...
Koda ta wuce Dada ya kai mintuna biyu a wajen kafin ya wuce ciki dan kalamanta sun masa zafi. Bai samu kowa a falon ba sai su Afrah. Hankalinsu kuma na kallon cartoon har ya wuce basu ganshi ba.