← Book details Sakar Makafi Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 12 OF 113

Sashe 12

Sakar Makafi Part 3 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Ga Ruky kuma za'a fara aikin lada🤣. Bari muga ya za'a kwashe🥱. A barku haka ko a ƙara biyun🏃🏼‍♀️💃?.
Received at 3:05........Dai-dai lokacin Nimrah ke shigowa falon goye da Naseer dake barci. Afrah biye da ita da ƙatuwar robar ice-cream a hannu. Itama Nimrah ɗin da ledoji a hannunta.
        Da sauri Ruky ta nufi saman tana faɗin, “Kai bari nai sauri na dawo. Irin wannan kayan daɗi haka waya kawo mana?”.
        “Kwaɗayayayya ki kalla gabanki dai kar ki faɗi”. Cewar Nimrah tana harararta. Ruky bata kulata ba ta cigaba da haura staircase ɗin. Hankalinta kwance tai knocking ƙofar bedroom ɗin nasa. Ammar dake kwance daga shi sai shot da vest yana kallon Film a laptop a tunaninsa Mu'azz ne kai tsaye yace, “Come in”.
        Kai tsaye Ruky ta tura ƙofar ta shiga abinta, dan hankalinta ma nakan ta koma wajen su Nimrah ne. Sallamarta ta saka Ammar ɗagowa da sauri. Yay bala'in waro idanu waje, gashi ya kasa tashi kamar wanda yay sumar zaune. Sumar ma irin ta tsuntsu daga sama gasashshe ɗin nan. Itama Ruky cak ta tsaya lokacin da take juyowa idannunta suka sauka a kansa. Kanta ta duƙar da sauri tana kif-kif da idanu. Dan Uncle's ɗinsu ko 3quarter na wando da wahalar gaske ka gansu da shi a falo balle shot da vest. Ganin hannunta na neman kifar masa da abinci baima san ya diro a gadon ya iso gabanta ba. Sai jin hucinsa tai a kusa da ita. Yana kama tray ɗin ta sakar masa zata gudu. Hannunta ya cafko kuwa da ɗayan hannunsa, ɗayan yana rungume da tray ɗin.
       Da sauri ta furta, “Uncle Mammah na jirana”.
     “Idan kin amsa min tambayoyina kenan”.
     Ya bata amsa yana jan hannun nata. A haka suka isa gaban gadon nashi ya ajiye tray ɗin. Sosai Ruky ta rikice da mamakinsa da tsoro. Ai tana ganin ya saki hannun nata yana gyara tray ɗin tai hanyar ƙofa da sauri. Taku biyu ya iskota. Ƙafa ya saka mata. Dan haka ta tafi zata faɗi ya sake riƙota da hannunsa. Ruky tai tsirmai-tsirmai da idanu. Gaba ɗaya lamarin Ammar ya gama firgitata.
        “Uncle kana lafiya kuwa?”.
    “Da sauƙi dai kam Babie”.
“Babie”.
Ruky ta maimaita sunan tana waro idanu, sai dai ta kasa kallonsa, ga jikinta jini na gudu saboda yanda yake tsaye a kusa da ita sosai. Har kamar ma yana neman haɗe jikinsu sai da ta matsa baya. A mamakinta shima sai ya matso. Ta sake matsawa. Ya sake matsota har suka dangane da bango. Yanda ta maƙure lips ɗinta na rawa yaso bashi dariya. Ya dogara hannunsa da bango yana gyara tsaiwarsa...
        “Uncle dan ALLAH kayi haƙuri idan laifi na maka”.
      Yanda tai maganar murya na rawa ya sashi kai hannu kamar zai taɓa lips ɗin nata sai kuma ya tuna gargaɗin Dada. (Kar kaga na saka an ɗaura auren nan ka zata dami a kala ka samu Ammar. Kaje ka nema soyayyar yarinyata kafin tarewarku. Domin Bilal ma soyayyar Asma'u ya nema harta amince masa. Kaima na baka wannan damar dan in har baka samo zuciyarta ba sai wata shekarar zata tare ita kam......)
      Fasawa yayi, ya ɗan haɗiyi yawu yana cije nashi lips ɗin. Cikin wayancewa ya furta, “Yaushe na zama abin wasan ki a gidan nan? Jiya kece mai faɗin aji tausayina a aura min budur-bazar ne ko miye ma kika ce maimaita?”.
       Ɓoyayyar ajiyar zuciya ta sauke. Sai kuma tai ƴar dariya da tura baki. “Uncle to miye laifina anan. Bama godiya ya kamata kamun ba na damu da kai. Naga ne yanzu kowa yayi aure kai ko budurwa baka da ita....”
          “Ke waya faɗa miki banda budurwa? Ina da ita mana”.. 
     “Lah! Da gaske dan ALLAH Uncle?”.
    Kai ya jinjina mata.
Ta ce, “Wooow dan ALLAH wacece?”.
“Gata nan a gaba na”.
Ya bata amsa kai tsaye. Tsabar rashin man kai sai ta fara waige-waige a zuciyarta tana tunanin to wacece? Sai kuma ta zubama laptop ɗinsa dake saman gado idanu. “Dan ALLAH ka nuna min hotonta ALLAH bazan faɗama kowa ba har Ninah.”
       “Hummm haba Ruky ni zaki yaudara, ai ko rantsuwa kikai akan Ninah bazata ji ba nasan sai kin faɗa. Faɗa min miye budur-bazar?”.
    Dariya ta ƙyalƙyale da ita, sai kuma ta ɗan tura lips da faɗin, “Shike nan tunda baka yarda ba. Uncle kai kamar ba bahaushe ba. Budur-bazar ne baka sani ba?”
Received at 4:41 PM      “Naji ba bahaushe bane ni. Faɗa min?”.
“Sakin wawa fa ake nufi?”.
“ALLAH ya shiryeki miye sakin wawa kuma?”.
Tai dariyar da ke saka tsigar jikinsa tashi. Kanta tsaye ta ce, “Irin wadda ba'a daɗe da aure ɗin nan ba mana a sake su, sai kagansu kamar ƴan mata amma sun yaɓa aure”.
“Gaskiya kin raina ni. Ni sabuwa dal a leda garan. Sweet sixteen”.
Bakin ta ɗan tura masa da faɗin, “Uhmmm”.
“Dan ALLAH ki tausaya min ki bar tura min lips ɗin nan. Na rantse a matse nake”.
     Da mamaki da ƴar rikicewa ta ce, “Na shiga uku Uncle kamar ya?”.
   Maimakon bata amsa sai ya bar wajen. Kai tsaye inda jallabiyarsa take yaje ya ɗauka ya sanya dan kar taga gobarar data haɗa. Ita ko duk yanda take son basar da kalamansa sun fara sakata a ruɗani. Dan gaba ɗaya a yanda yake mata maganar ma yau salon na daban ne. Sum-sum ta nufi ƙofa, sai jin rufewarta Ammar yayi, ya zaburo zai yi magana ina harta gudu. Cikin dafe kai ya furta, “Ya ALLAH ka taimaki marayan ALLAH kar yay aika-aika a gaban Dada da Mammah”....

      Ashe Ruky tana ruwa🥱🤣🤏.

«««««««»»»»»»»

        “Ruky lafiyarki kuwa?”.
  Nimrah ta faɗa cikin raɗa tana ƙara tsatstsare Ruƙayya da ido. Sashen da Mammah take Ruky ta ɗan saci kallo. Ganin hankalinta akan bama su Afrah abinci a baki yake ta kama hannun Nimrah kamar zasu yi wani abu a kitchen. Suna shiga ta leƙa ƙofar baya dan tabbatar da su Kulu basa kusa sannan ta dawo kusa da Nimrah.
        “Ninah wlhy Uncle Ammar ne ya firgitani. Wai kinga yanda yake min magana kuwa.”
     Sosai Nimrah ta waro idanunta da faɗin, “Ke kodai dan kina ruɗe ne”.
    “Ba wani ruɗe wlhy. Sai kace wata ƴar ƙwaya..........”
    Tsaf ta kwashe labari ta sanar mata. Nimrah akai zugum tana tuno Dada. Yayinda zuciyarta ke ayyana mata (To mike damun iyayen nasu? Ko itama Rukyn an ɗaura mata aure da Ammar ɗin......)
     Zungurinta da Ruky tai ya sata kawo numfashi. “Wai tunanin mi kike yi?”.
        “Uhmm Ruky anya kuwa kema ba'a ɗaura miki aure da Uncle Ammar ba? Ya kamata hankalinmu ya dawo jikinmu. A baya bamu gane abinda yasa Mammah ke saka mana dokokin rufe jiki da nasiha akan maza ba. Amma tunda abin nan ya faru na batun video ɗin nan nake ta nazari abubuwan da suka shuɗe a baya.....”
       “Na shiga uku Nimrah aure kuma? Kada ki haukatani dan ALLAH. Wlhy kin fini ƙarfin zuciyar ɗaukar abu”.
       Karo na farko Nimrah tai ƴar dariya da faɗin, “Kema ɗauka zakiyi yarinya. Ni wlhy yanzu ma na ƙara yarda bamu da hankali. Kammu baya gane komai. Inyeee kaga ta Uncle Auta. Har naji sanyi a raina tunda yanzu bani kaɗai bace”.
      Harararta Ruky tayi idanunta na tara hawaye. Ta ce, “Dan ALLAH Ninah yi shiru. Wlhy zuciyata bugawa take. Kinga mu koma falo”.
        “Miye na wani bugawar zuciya. Mammah tace sai ɗan gata akema irin wannan auren fa. Dan haka dalla malama manta da wani bugun zuciya mu ALLAH ya tabbatar haka ɗin ne ma. Muna kusa da Mammah ɗinmu, kuma muna tare na har abada. Dama ALLAH ya bamu na cigaba da jin daɗinmu da masoyiya Mammah har mutuwa.”
    Murmurshi Ruky tayi itama. Dan harga ALLAH zukatansu na ƙaunar Mammah kamar yanda Nimrah ta faɗa....

     Mammah najin motsin zasu fito tabar wajen tana murmurshi. Dan tunda suka taho ta biyosu, dan a yanda suka bar falon sai tai tunanin wani rashin jin zasu aikata. Dan tun jiya ta tsargu da yanda suke kallon su Afeef suna dariya. Tasan halin yaran nata ƴan ƙunar baƙin wake ne. Dama kuma ta tabbatar bazasu bar Afeef akan laifinsa ba. Haka kawai hirar tasu ta dinga bata dariya a zuciya. Dan ta fahimci autocinta sun fara hankali......

[×××][××××][×××]
Chapter 12 · 0% Book details