Sashe 112
Sakar Makafi Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read
..........Cikin son kauda kukan nan na Nimrah dake cizon zuciyarsa ya kauda zancen ta hanyar ɗaukar wayarsa ya turama Daddy Imran saƙo. Koda ya duba yaga mi Dadan ya turo sai yay gyaran murya da katse yanayin. Dan yanzu ma su Mammah da Kulu kuka suke sosai ba Nimrah kawai ba. Shima Kawu Tanimu dake lallashin Nimrah data ɗora kanta a kan ƙafarsa ya turama saƙo.
Saƙo na shigo ma Kawu Tanimu waya ya ɗauka ya duba sai yaga Daddy Imran ne. Ɗan kwallon inda yake yayi, sai suka haɗa ido. Kansa ya jinjina masa tare da gyara zama yayi gyaran murya.
Cike da girmamawa Kawu Tanimu ya maida hankalinsa kansu shima yana murmurshin ƙarfin hali ga su Mammah.
“Mammah kuyi haƙuri kuka ba shine magani ba. Komai ya riga ya faru, hakan kuma ƙaddararmu ce babu abinda zai canja. Yanzu zaku ji kuma dalilin kasancewar Maijiddah ko nace Kulu a tare da ku”.
A take suka shiga share hawaye su. Suka maida hankalinsu ga Kawu Tanimu har su Daddy Imran ma a yanzu. Duk da shi Dadah bazaka taɓa gane yanayinsa ba ma. Sai dai rabin kallonsa nakan Nimrah da har yanzu ke sharar hawaye.
“Aiki ne ya kai Kulu gidanku ba cutarwa ba. Tunda yanzu kun san duk abinda ya faru da ƙauyenmu a shekarun baya. Mun rasa da yawa wasu har yanzu bamu san duniyar da suke ba. Dan duk da a shekarun da suka gabata wasu sun koma garin, har yanzu dai wasu shiru. Zan iya ce miki ina cikin wanda basu koma ba har yanzu, ba komai kuma ya hanani komawa ba sai rasa zuri'ar gidanmu da mukai kusan gaba ɗaya kamar yanda kuka ji. Idan ma da wanda suka rage har yanzu bamu san ina suke ba. Hatta ni basu san ina raye ba. Haka ma Nimrah babu wanda yasan tana raye. A yanzu haka ni jami'in ɗan sandan farin kaya ne. Hakama Maijiddah.....”
“Yan sanda kuma?”.
Gwaggo Khadijah ta faɗa cikin waro idanu. Hakama Nimrah sosai take kallon Kawun nata. Mammah kam sai tayi murmushi. Duk da abin ya daketa ita mace ce mai ɗabi'ar riƙe kai. Kawu Tanimu dake murmushi ya ce,
“Hakane Gwaggo ƴan sanda. Kamar kuma yanda na faɗa aiki ne ya kawo Kulu gidan. Dan lokacin da Boss baya a tare daku mun tabbatar kowa zai iya shigowa jikinku da mugun ƙudurin cutarwa. Wannan ne dalilin da yasa Alhaji Nasiru zuwa wajen IG domin a bashi ƴan sandan farin kaya ƙwararru mata da zasu zauna da ku......”
Yanzu kam hatta Dadah da Daddy Imran sai da suka kalli Kawu Tanimu.
Cigaba yay da faɗin, “A wannan lokacin ni da Maijiddah dake matsayin ɗiya a gare shi mun kammala karatun da mukaje yi, wanda acan na haɗu da ita har muka fara soyayya. Mahaifinta mutum ne mai sauƙin kai, duk da kuwa yana da babban matsayi na kankat a girma a hukumar ƴan sandan farin kaya bai ƙyamace ni ba ko kallona a talaka baƙauye. Tana sanar masa ni take so yay addu'a, sai dai yayi bincike a kaina kafin ya bani ita. To mun gama hutun amarci kenan mun koma kan aiki Alhaji Nasirun yazo masa da wannan buƙatar. Ni kuma lokacin ina tare da shi. Shine nai caraf nace zan yi. Har ma abin ya basu mamaki. Na dai samu na basar dan karsu gane. Saboda a lokacin ko ita Maijiddah bata san ina da wani abu dake da alaƙa da gidan ba. A lokacin Alhaji Nasiru sai yace nayi haƙuri mace suke so. Amma sai IG yay murmushi da faɗin. “Babu damuwa, akwai yarinyarta Hauwa'u, kuma matarsa ce zata iya aikin, kana da girma a wajena da bazan iya baka gama gari ba sai wanda na yarda da shi, sannan Haysam yaron kirki ne da zamu iyama hidima koda yana a ɓoye. Amma za'a samo wata su zama biyu. Sai dai su duka babu wanda zai san aikin ɗan uwansa. Sannan zasuyi aiki a fannin abinci dan shine mafi haɗari da za'a iya cutar da mutanen gidan” cikin gamsuwa yayi godiya. Har yana ƴar tsokana ta. Wannan shine sanadin fara aikin Maijiddah da Hanne. Sai dai su kansu basu san suna da alaƙa ba sai kwanaki. Alaƙata da Nimrah kuwa ta fara saninta a shekara ɗaya data gabata, na ajiye hotunan dana ɗauki Nimrah kamar yanda na saba batare data sani ba, nazo da su na ajiye a ɗaki na manta shaf zata zo weekend a satin, tazo tana gyara min ɗaki ta gani. Ita da farko ma ta ɗauka wani alaƙa ne tsakanin mu. Kun san kishin mata. Ina dawowa ta birkice min. Ni kuma kawai naga banda wata mafita na zaunar da ita na mata bayanin komai da alaƙarta da Nimrah ɗin. Abin ya girgizata, ya kuma bata tsoro da mamaki. Tayi kuka tayi dariya. Daga nan ne take sake bani labarin rashin jinsu ita da Ruƙayya. Tun daga nan kuma nake ƙara samun duk wani information ɗin ta a wajen Maijiddah.”
Ba Nimrah ba hatta Mammah sai da ta share hawaye, ƙaunar Uncle Nasiru na sake shiga zuciyarta. Wannan shine asalin ɗan uwa na amana. Mai hidima domin ALLAH batare da sanin ɗan uwa ba.
Kulu ta taso zuwa gaban Mammah ta durƙusa. Cike da girmamawa ta ce, “Mammah ki gafarce ni. Ban aikata komai gareku dan yaudara ba, aikinmu ne ya gaji haka. Wlhy har cikin raina nake jin ƙaunarki a zaman da mukai. Hakama kaf zuri'arki ina jinsu har cikin raina. Ban taɓa koda sha'awar cutar daku ba balle kwatantawa....”
Hawaye suka zubo mata. Mammah tayi murmushi, tare da kamo hannunta. “Daina kuka Hauwa'u. ALLAH yay miki albarka. Na fahimce ku ƙwarai da gaske. ALLAH kuma shine shaida ban taɓa kamaki da wani abu saɓanin alkairi ba daga ke har Hanne. Shiyyasa nake jinku har cikin raina, na kuma samu nutsuwa da yarda da ku. Muma kuma munji daɗin zama dake daga ke har Hannatu. Ciwon da zanji kawai a zuciyata a yanzu shine na rabuwa da ku”. Mammah ta sake share hawaye...
Kawu Tanimu ne yay murmushi da faɗin, “Kiyi haƙuri Mammah ki daina kuka, in sha ALLAHU kuma aikinsu bai ƙare ba tukunna, da sauran lokaci”.
Cikin farin ciki bakin Mammah ya washe. Nimrah kuwa matsowa tai ta rungume Kulu tana murna. Yanda tayi ɗin har sai da ya saka kowa dariya banda Dadah da kallonta kawai yake a kaikaice.
Daddy Imran dake murmushi ya ce, “Lallai kun mamaye mu da yawa. Amma Alhamdullah tunda bata hanyar cutarwa bace sai muce ALLAH ya saka da alkairi. Sannan muma mu baku haƙuri game da aurar da Daughter batare da kowa a danginta ba. A lokacin bamu da wata mafita ne, abin kuma yazo a bazata bisa hukuncin UBANGIJI....”
“Baƙwa buƙatar bamu haƙuri Sir, mune ma ya kamata muyi muku godiya anan. Sannan muyi farin ciki da kasancewar samun nagartaccen miji da Nimrah tayi. Sai dai kamar dai ya kamata na saka rigima sai na sake mata sabon biki nima tunda a ƴan gayyata naje wancan”.
Yanda ya ƙare maganar da tsokana ya saka kowa dariya a falon. Nimrah kuwa ta ɓoye kanta a jikin Gwaggo Khadijah. Dadah dai fuskarsa ta motsa kaɗan, sai dai bazaka ce murmurshin yayi ba ko saɓanin haka. Babban burin Nimrah sake dogon hira da Kawun ta da matarsa musamman akan yaya garinsu yake a yanzu. Amma bazata iya tambaya a gaban Mammah da su Dadah ba. Dan kar suga kamar bata gamsu ba da wanda suka ji tare. Amma tana fatan su barta anan ta kwana. Dan abubuwa da yawa take son ji gaskiya. Tunaninta ya katse sakamakon sabon labarin da Kawu Tanimu ke bama Mammah game da Nimrah. Ƙuruciyarta da yanda take fitinanniya uwar daba a faɗa. Su Mammah sun sha dariya sosai. Ita ko tana faman ɓoye fuska.
Sosai wannan zama ko muce ziyara ta haifar da nishaɗi da sabuwar zumunta da gina alaƙa. Dan sun tattauna abubuwa da yawa. Daga ƙarshe Dadah ya miƙama Imran wata jakka. Shi kuma ya miƙama Kawu Tanimu.
“Documents na Nimrah ne a ciki. An samar da su kuma ne ta hanyar luɗin sadakinta. Dan kuɗin an saka mata hannun jari da su kamar yanda Mammah ta bada shawara a kamfanin mu da su Ma'aruff ke tafi da shi ya hanyar kasuwanci. Kasonta da ake bata duk shekara sai aka dinga saya mata kaddarori da su. Sai kuma abinda ba'a rasa ba da sauransu. Wannan kuma basai anyi wani bayani ba ai. Akwai account da aka buɗe da sunanta da kuɗaɗe kuma a ciki, sai dai itama bata san da su ba. Dama mun bar komai ne har sai zuwa lokacin data mallaki hankalinta. Tunda yanzu ka bayyana Kuma muna ganin ya dace ka sani mun damƙa su a hannunka matsayin uba.”
Kawu Tanimu da yay kasare yana kallonsu da jinjina al'amarin waɗan mutane ya sauke ajiyar zuciya mai ƙarfi. Jakar ya ɗauka ya maida gaban Dadah. “Bani na cancanci riƙewa ba kai ne Sir. Dan koba komai kana da ƙarfin ikon da yafi namu a yanzu ga Nimrah. Ko babu alaƙar aure bata da iyayen da suka wuce ku a yanzu. Mu sai dai ta kiramu a suna ai”.
“Kunfi ƙarfin a suna kuwa.”
Daddy Imran ya faɗa yana murmushi. Sai shima Dadahn ya ɗan murmusa kaɗan a karo na farko. Sannan kuma yay magana a karo na farko idonsa akan Nimrah..........✍️
127