Sashe 29
Sakar Makafi Part 3 Complete Hausa Novel · about 7 min read
Ana idar da sallar azhar aka fara kwasar mutane zuwa wajen walimar.
Amare kam sai wajen biyu saura ma. Dan tare aka zo ɗaukar su tare da Mammah. Bilal zai jasu, dan haka Ammar ya maƙale a kusa da shi. Aiko tunda suka fito ƙamshin su ya buɗaɗe compound ɗin. Ji Ammar yay kamar yaje ya rungume Ruƙayya, ya dai daure ya cije da ƙyar. Mammah na lure da shi, ta girgiza kai kawai. Shima Bilal sai ya zungureshi yana nuna masa Mammah ɗin. Ammar ya ɗan waro idanu yana shafa ƙeya. Bilal ya kauda kai yana dariya ciki-ciki. Tun daga nan Ammar ya kama kanshi. Amma harga ALLAH daga shi har Bilal ɗin kamshin turaren su Ruƙayyan ɗaga musu hankali yake.
Sai da suka fara tafiya su Nimrah suka gaishe su. Bilal dake kallonsu ta mirrorn gaba ya ce, “Wai ya naga duk kunyi laushi ne? Mammah yaranki ko basu da lafiya ne?”.
Ƙaramar dariya Mammah tayi, yayinda Nimrah da Ruky suka ƙara lafewa jikinta. Sai Biebah ce ta ce, “Yaya bazaka gane ba”.
“Ganar da ni Auta. Dan ke gani nai ma kin rame min a ido fiye da su”.
Hawaye suka zubo mata. Sai kawai Ammar ya hau dariya da faɗin, “Wai kuka kike?”.
Kanta ta sake duƙarwa, da lafiya-lafiya ne sai ta rama. Dan shi da Aunty Mimi sam bata raga musu kasancewar su sakonta. Bilal bai ƙara magana ba, sai idanunsa da suka kaɗe. Shi kansa Ammar ɗin dauriya ce kawai amma har ya fara jin kewarta tunma da aka fara bikin nan. Motar tai shiru dan suma su Nimrah sun koma jikin Biebah suna hawayen ne. A haka suka iso wajen.........✍️
Kuyi hakuri da jina shiru jiya. Rasuwa akai mana😭🙏46
........Sosai wajen yayi ƙyau, komai kuma a nutse a tsare. Ɓangaren mata daban na maza daban. Kasancewar itama Asma'u sun iso aka dawo da ita wajen su Biebah. A motar aka barsu Mammah ta shige. Sun kai kusan mintina goma sannan Aunty Mommy tazo tafiya da su. Wajen yayi tsitt kamar yanda aka buƙaci shirun domin fara addu'a. Dan haka hankalin kowa ya dawo kan amare da suka shigo. Sai dai fuskokinsu rufe da hular alƙyabba su duka huɗun, Dada yaji daɗin yanda akai musu shigar mutunci kuwa. Har wajen da aka tanada domin su akai kaisu. Kujeru huɗu daga gefe ta ɓangaren mata.
Dai-dai lokacin kuma ake isar da batun zuwan shugaban ƙasa da kansa ba saƙo ba. Tare da iyalansa gaba ɗaya. Mutane sun ƙara tabbatar da lallai akwai alaƙa mai ƙarfi tsakanin su Dada da Shugaban ƙasa a yau, dan haka ƙus-ƙus ya fara tashi a wajen har sai da aka buƙaci shiru. Sosai tsaro ya ƙaru a wajen, bayan sun zauna akai addu'a sannan Imam ya fito yay karatun Alkur'ani. Sosai zukata suka ƙara nutsuwa, kafin a fara gudanar da wa'azi daga bakin manyan malamai musulinci daya sake sanyaya jikin mutane. Ya kuma saka amare ƙara shiga hankalinsu dan kai tsaye akan rayuwar aure a musulinci taken lectures ɗin suka gudana. Lokacin sallar la'asar yay aka dakata. Sai da aka yo salla aka ɗora wata sabuwar lecture ɗin kuma dai, zuwa 5 akai addu'a aka fara liyafar cin abinci kuma.
Alhamdullahi komai ya gudana cikin nutsuwa da dattako. Dan sosai manyan mutane sun halarci wannan walima. Gashi an nuna a gidajen tv live. Banda masu posting a wayoyi kuma. Sai dai a karo na farko hotunan su Nimrah sun fita. In da mutane suketa ka-ce-na-ce akan wai Zak-Shadow ya auri yarinya ƙarama. Mata suka fara faɗin matarsa tai masa halaccin jiransa shekara takwas ya dawo ya saka mata da kishiya. Mutane basu san gaskiyar magana ba amma sun iya tsara zance da girmamashi. Ga batun zuwan shugaban ƙasa wajen shima sunata yan-yan, akai. Oho shi wanda suke yi dan shi ɗin ma babu alamar yana da lokacin su.....
Ana dawowa gida sallar magriba akayi aka kuma fara shirin dinner. Ana idar da isha'i aka fara wucewa da mutane nan ma. Yayinda amare ke can ana tsara musu ado da kwalliya na amaren girma. Kai daga gani kasan fitar ta musamman ce. Babu wanda ya saka ran zuwan Dada wajen nan da Faro. Dan haka ma akace ayi angunan bogi. Wai Ma'aruff ya zauna tare da Biebah. Nimrah kuma Ja'afar.
Mammah naji ta ce, “Babu ruwanta su da Muhammad, gara su fara kiransa su sanar masa idan ya amince to. Aiko sunata darurar kiran nasa suka dai daure. Sai da wayar ta kusa tsinkewa ya ɗaga. A lokacin fitowarsa a wanka kenan ma. Cikin kame-kame da in inar rashin dalili Ma'aruff ya sanar masa. Yay shiru kamar bazai amsa ba. Hakan yasa Ma'aruff fahimtar sun taro match. Amma ya daure dai bai kashe wayar ba.
Dada yay gyaran murya, sannan ya furta, “Ku kun zama manyan banza kenan ko Ma'aruff? Kunsa Mammah ta takura na barku kuyi shine kuma zaku sake kawo wani abun..”
“Dada kayi haƙuri mun tuba. Kawai mun san ko munce kazo bazaka zo bane. Kuma Yaya Haydar ma idan baka zo ba shima nasan bazai zo ba......”
“Shi ke nan su Bilal ɗin basai suyi ba ya wadatar”. Dada ya faɗa cikin katse shi, yana gama faɗa kuma ya yanke wayarsa.
Ja'afar ya ce, “Hummm dama bana faɗa maka ba Twiny, Dada fa wlhy kishin tsiya ne da shi. Da zakuji ta tawa suma su Bilal su haƙura. Amaren kawai su zauna ba dole sai da anguna ba. Idan ba hakaba kaɗan daga aikinsa yace kada ma aje da Ninah wajen”.
“Wlhy Dada daya gama damu”.
Cewar Bilal kamar zai kuka. Dariya su Ja'afar ɗin suka sanya kuwa. Ma'aruff ya ce, “To inaga kawai abi shawarar Twiny ALLAH. Dama da yaya ya amince ayi dinnar ɗin nan. Kada mu ƙureshi kuma kun san dai Dada ƙaniyarmu zamu ci a ƙarshe”.
Hakan yafi basu masalaha, dan haka duk suka amince. Suka kira su Aunty Ummi suka sanar mata. Itama ta gamsu, dan wlhy tasan badan Mammah ta saka baki ba ma bazai bari ba. Daga haka aka kwashi amare zuwa wajen dinner daya gama cika ya tumbatsa. Ga uban tsaro har ba'a magana.
Received at 14:59Reactions:Yanda aka tsara amaren ma kawai babu angwaye sai ya kawo wani sabon salo daya burge mutane. Gashi sun sha ƙyau har sun gaji. Gaba ɗayansu material ne a jikinsu dogayen riguna, sai dai kowacce da kalar nata da kuma irin ɗinkin da take so.
Kasancewar an tsara wajen da iya adadin mutanen da ake buƙata komai a nutse. Bayan addu'a ƙawayen su Nimrah da suka shirya kalolin rawa suka fara gudanar data farko tare da su Mu'azz. Ba ƙaramin ƙayatarwa abin yayi ba. Sai kuma mawaƙan da sukai waƙoƙin biki suma suka fara baje kolinsu. Sannan ƙawayen Asma'u suka gudanar da tasu rawar. Su dai na Biebah sun ɗauki girma. Su Feddo sun sake yin rawa ta biyu, kafin ai taƙarshe harda amare. Sosai abin ya ƙayatar da jama'a. Su Uncle Ja'afar sai liƙe yaransu suke da kuɗi. Bilal yana fakar ido ya rungume Ma'u, Ammar na ƙyalla ido ya gani yace, “Wlhy nima bazaka barni a baya ba. Haba ai nayi haƙuri jama'a”. Shima ya kama Rukyn sa ya kanainaye. Mi su Lailah zasuyi ba dariya ba. Sai da Ma'aruff yay musu ƙulli a baya kowa ɗai-ɗai suka sake su. Nimrah nama Ruky dariya da shaƙiyanci ita ko ba baki. Dan gaba ɗaya jikinta yayi sanyi tun lectures ɗin ɗazun. Ita kanta Nimrah ɗin ƙarfin hali ne kawai. Asma'u kam ai bama a magana, kodan ita da Biebah zasu bar gida ne zuwa wasu gidajen. Garama Asma'u gida za'a kaita dan bayan gidan Baffa basu da wani gida abin alfahari sama da gidan Mammah.
Sosai dinner ta ƙayatar itama sai sambarka. Kamar yanda Dada ya saka doka ƙarfe sha biyu a aka tashi. Dan sha biyun ma na cika sai ga kiransa a wayar Aunty Mommy. Cikin rikicewa ta ce, “Dada ALLAH mun tashi, dan yanzu haka ma su Yaya Ma'aruff sun wuce da su Ninah gida. Muma muna ƙarasa sallamar baƙi ne kawai. Ajiyar zuciya ya sauke yana ajiye wayar. Faro da Imran suka kallesa sukai murmushi. Dama tun ɗazun sai ƙananun tsaki yake musu....
___