Sashe 88
Sakar Makafi Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read
..........Anan kuwa sashen Mammah farin ciki da murna ce ta kaure. Dan Nimrah na shiga da gudu ta wuce inda Mammah take ta rungumeta tana sakin kuka. Yayinda ita kuma Ruky ta haɗasu su biyun ta rungume.
Su Ma'aruff ma sai abin ya basu dariya. Da ƙyar da ƙyar Mammah ta lallashi kafi Autocin nata. Kowa kallon Nimrah da mamakin yanda tai fresh yake. Cike da shaƙiyanci su Mimi da su Aunty Ummi kema juna sigina.
Bayan Nimrah ta gaida Mammah da Gwaggo Khadijah suna riƙe da hannun juna ita da Ruky kamar masu tsoron a rabasu taje ta gaida Uncle Ma'aruff da Uncle Ja'afar. Sun amasa mata da kulawa. Suma dai ransu fal gulma sai dai babu damar yi saboda matsayinsu na iyaye maza. Haka su masu Aunty Mommy ɗaya bayan ɗaya Nimrah ta gaishe su. Ana cikin hakan sai ga Biebah. Da gudu da gudu Ruky da Nimrah sukaje suka naƙaleta.
Nan fa falon ya ƙara rikicewa. Ƴaƴan Mammah sun haɗu. Yunwa ta fara isar Nimrah. Ta dafe ciki tana yamutsa fuska. Ruky data lura ta ce, “Yunwa?”.
Kai ta jinjina mata. Tashi tai ta kawo mata wainar fulawa data soya mata. Cike da farin ciki Nimrah ta rungumeta da faɗin, “Wayyo my rabin jiki”.
Dariya kowa ya sanya. Nimrah dai ta fara ci kamar wadda take a yinwace su Mu'azz na mata surutu. Yanda tayi ɗin sai da ya saka kusan kowa kallonta a falon, sai dai babu wanda yayi magana. Sai da taci tayi nak ta godema ALLAH sannan takai kwance a jikin Small Mom tana faɗin, “Wayyo Small Mom na ƙoshi da yawa”.
“To irin wannan cin yunwa da kikama waunar nan Ninah”.
“ALLAH nayi kewarta ne. Yanzu ma kawai cikina ya cika ne amma bakina bai ƙoshi ba.”
Shigowar Ammar ta hana kowa bata amsa. Sai kuma ga Bilal kai kace tare suke. Shi ko dai bai iya shiru ba. Sai da ya ce, “Iyeee kunga ƴar Mammah kuwa? Irin wannan Fresh mi Dadah ke baki haka?”.
Ba shiri Nimrah ta ɓoye fuskarta a jikin Ruky. Sai dai batace komai ba. Shima kuma bai sake maimaitawa ba illa dariya da yayi kamar kowa. Nimrah ta gaida su shi da Bilal. Suka amsa mata da kulawa. Dole hirar ta tsaya saboda shirin massalaci. Kowacce mijinta ya janyeta a kaikaice suka gudu. Sai su Mimi suka rage da Nimrah dake dariyar gulmar Ruky a zuciya. Dan tana ganin abinda Uncle Ammar yay mata kafin su fita....
(★)★(★)★(★)
A yau da kwanaki bakwai ke cika da fara case ɗin Jush rikici ya ɓarke tsakanin jami'an ƙasar sa dama ƙasar Dubai. Dan sun ce basu yarda ba da haɗin kan ƙasar budurwar tasa tai komai, dan aikin baiyi kama dana mutumin ɗaya ba musamman yanda suka kasa gane kan gubar da aka zuba masa. A gefe ga ƙyamariro tako ina a gidan amma ace basu naɗi komai daya faru ba. Wannan yafi ƙarfin yarinyar ita kaɗai.
Tofa babbar magana, dan wannan rikici shine ya fiddo maganar kisan Jush ɗin kai tsaye ma duniya. Saɓanin farko da kawai ana nuna batun kisan batare da sunan wanda aka kashe ba. Sai a yau ne sunan ya bayyana ɓaro-ɓaro tare da hotonsa. Kafin kace mi manyan gidajen yaɗa labarai na duniya sun shiga haskawa da kace nace. Hukumomin Dubai sukai zaman farko a teburin tattaunawa...
Wannan fa shi ake kira da sunan babbar magana, wai ɗan sanda yaga gawar soja. Labari da ɗumi-ɗumi mai kekketa zuciya da sanyata bugun fanfalaƙe ya riski kunnuwar ƴan ƙungiyar duhu. Koma muce sun gani da idanunsu, duk da a ranar farko sunga labarin. Kasancewar ba suna ba hoton wanda akai mawa ɗin yasa basu maida hankali ba balle ma abin ya dame su.
Sannan kaf ɗinsu babu wanda ya taɓa sanin ma Oga Jush ɗin nada gidan sirri a Dubai balle budurwar. A matuƙar gigice kiran wayoyi ya fara kai-kawo a tsakaninsu. Hatta wanda basa ƙasar suka fara haɗo kayan dawowa. Dan wannan al'amari ne daya wuce misalin tunaninsu.
Tuni waɗanda ke cikin ƙasa kam sun haɗa gangamin meeting na gaggawa. Duk da a babu shiri ne sai ga kusan mutum goma sun hallara. Duk da ma a hakan zaman iya na manya ne. Sauran ƙananun Members na can an barsu da ruɗani da tashin hankalin zuciya. To Oga ya mutu su ina suka kama?.
....★“Mike faruwa ne? Mi yake shirin faruwa?!!!”.
Mr Specter ya faɗa cikin ƙaraji da gigitar ruɗani jikinsa na karkarwa.
“Akwai abinda ya kamata mu sani ƙwarai da gaske. Dan duk da anyi kisan a inda ba ƙasarmu ba, bama yankin mu ba bazamu sakankance da tunanin babu saka hannun maƙiyanmu ba. Ashe shiyyasa muketa neman Oga kwana da kwanaki babu labarinsa. Wannan wane irin al'amari ne mai ruɗar da kai?”.
“Wannan ya wuce ruɗar da kai, harda ruɗanin zuciya. Ni gaba ɗaya ma ji nake tamkar hawan jini na na sama.”.
“Ni ko ina ganin ba ruɗar da kanmu ya kama muyi ba. A wannan gaɓar nutsuwa mukafi buƙata. Sannan a samar da sabon shugaba. A kuma jira su Viper su iso a sake sabon zama. Sannan fa ba lallai ace abinda ya faru ya farun ne daga ɓangaren mu ba. Dan Oga na harƙalloli daban-daban a kasashe da ban da ban. Ku duba fa mu dukanmu yau ne muka fara ganin wannan gidan nashi na Dubai. Ita kanta wannan yarinyar gashi masana sunce bincike ya nuna ta jima tare da shi tun tana da ƙarancin shekaru a duniya. Amma mu bamu taɓa sanin ta balle labarinta. Hakan na nufin akwai abubuwa da yawan gaske da suka shafi oga da bamu taɓa sani ba. Ba kuma dama ya zama lallai mu sani ɗin ba tunda yana aikinsa yanda ya kamata matsayin shugaba akan abinda ya shafe mu”.
“Haka ne. Scythe yazo da magana ta hankali kuma wadda ya kamata mu duba. Mu kuma kalleta a matakin nutsuwa hakan zai sama mana kwanciyar hankali da yin nazari yanda ya kamata. Koba komai zamuyi abinda ya dace daga namu ɓangaren. Dan ni dai zuciyata tana raya min akwai hannun maƙiyanmu a wannan al'amarin. Duk da na rasa ina zan kalla ko kamawa daga ɓangarorin maƙiyan namu. Saboda wannan aikin duk inda ya fito ya fito ne daga masu ƙarfin iko da ɗaurin ƙugu”.
“A wannan gaɓar ba'a raina maƙiyi. Dan duk maƙiyi sunansa dai maƙiyi. Dama ɗaya yake jira ta halaka. Abu mafi damuna anan yanda komai na ƙungiya ya tsaya tsahon wata ɗaya kenan. Gashi Oga ya rushe dukkan tsoffin tsarikanmu da shirin gina wasu. Da yanzu nan da kwanaki biyu zai iso domin ƙaddamar da su. Wannan nan babban ƙalubalene a garemu. A gefe idan ma maƙiyanmu basu da hannu a wannan kisan, a yanzu sun samu lasisin farmakarmu. Dan tsohon Janar ɗin nan shegen kansa ne. Balle ya tattara akalar mulkin ya danƙa a hannun tsinannen nan Zak-Shadow. Na rasa wane irin mutum ne mutumin nan. Munbi duk wata hanyar kauda shi amma kamar munayi a banza. Gubar nan ta ƙarshe da muke da yaƙini a kanta ma shiru kake ji gashi nan ma ya cigaba da harkokinsa kamar komai bai faru ba”.
Shiru ɗakin ya ɗauka. Zantukan da suka tattauna na ratsa su. Musamman ma na ƙarshen nan da suka fi komai shigar su. Dan tabbas da gaske akwai babban ƙalubale a gabansu a wannan gaɓar. Dole ne kuma ɗayan biyu ta kasance a kansu. Ko su miƙe da shirin sabon yaƙi. Ko ayi nasara a kansu ta hanyar da basuyi zato da tsammani ba......
+++++++++++
“Amma ke dai baki da zuciya wlhy. Yanzu kina nufin komawa zakiyi?. Ke ko kishin kanki baƙyayi da Dad. Duba fa tunda kika baro gidan uwarsu ta kira taji nan kika zo babu wanda ya sake kiran mu har ita”.
“Ni dai babu ruwan ka. In ma bani da zuciyar ai tawa ce ko. Kai ko bance zan koma ba ai kace na koma. Jiba fa inda muke a ɗakin hotel guda ɗaya jal mu huɗu. Ni kaɗai mace a cikinku. Duk da kuke ƴan uwana idan son zuciya ya raya muku cutar da ni fa, tunda Dad ma ba kullum muke ganinsa ba.”
“Amma Hanoon baki da hankali. A cikinmu ubanwa ya taɓa yi miki wani abu mara ƙyau?”.
“Idan bakuy min ba ai wataran zakuyi min. Ince kai randa nazo a bayi na sameka da yarinyar mai aikinmu ta da. Ka iya zama ka lallaɓeta ta kawo maka kanta shegiya ko sisi bata samu sai wahala. Ƙarshe ma itace ke baka kuɗin. Sannan gashi nan abinci ma sai mu yini bamu ci ba muna wahala. Ko ɗakin Hotel ɗin badan Dad ya jima da biyan maƙudan kuɗi ba a kansa mun isa mu zauna?. Ai har ku ɗin dole ku koma can. Dan haka ni dai ba zan zauna ba. Gara na koma.”
“Humm munafuka, kedai kice zaki koma saboda wannan tsohon dattijon da girman jikinsa ke kwasar ki”.
“In ma dan haka ɗin ne ina ruwanka. Kaji da taka damuwar”.
“To wa zai baki kuɗin jirgi?”.
“Ina ruwanka koma wazai bani tunda banzo nace kai ka bani ba”.
Hanoon ta faɗa tana jan akwatinta ta fice ta bar su Afeef da Dayyan da kallon juna baki sake..........✍️
104
...........Har masu tafiya massalaci suka gama shiryowa suka fito tare da yara da aka ɗakko school babu Dadah babu labarinsa. Nimrah dai nata dannewa, bata yarda kowa ya lura da halin da take ciki kan son ganin ta ina zai ɓullo ba. Sannan ta hana zuciyarsa yin dogon tunanin hasaso mata yana tare da matarsa ne. Da hakan yazo mata a rai sai tai a'uziyya ta ture gurɓataccen tunanin da faɗin (Inama ruwana idan haka ne?).
Sai da taga har su Uncle Ma'aruff na shirin wucewa massalaci ta kasa daurewa ta ɗauki wayarta. Gajeren saƙo ta tura masa kamar haka.
(Kowa ya tafi massalaci amma banda Dadah na. Idan Babyna ya rasa sallar juma'a naga Boni). Daga haka ta ajiye wayar suka wuce kitchen ita da su Ruky. Dan dole a haɗa abinci mai yawa kamar yanda sauka saba duk irin wannan ranar ta juma'a da dama su Aunty Mimi ke yini gidan..
.....★★