Sashe 65
Sakar Makafi Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read
.........Sosai Asma'u ta jikatar da har ta bama Bilal tsoro. Dan babu arziki suna idar da sallar asuba sai da ya nemo doctor. Bai dai sanarma kowa ba har su Shariffa dake a sashen nasu. Dan gaskiya shi kunya ma yake ji asan hakan ta faru. A dubawar farko doctor ta shiga salati, dan ciwo ne sosai yaji mata har sai anyi ɗinki. Baya a ɗakin dan haka ta fito inda ta barshi a falo tana sanar masa sai da an mata ɗinki.
Sosai hankalin Bilal ɗin ya ƙara tashi, dan baiyi zaton abin zai girma har hakan ba. Amma harga ALLAH laifin Asma'u ne da taso yi masa gardama a gaɓar da shi kuma bazai iya haƙure mata ba. Ya tabbatar a lokacin ne aka samu matsalar. Dan ihun kukan data fasa masa har sai da ya rufe mata baki. Yaso shiga wajen Asma'un doctor ta hana shi, ta dai ce abu zai amso mata kawai a asibitin su dan babu kayan aikin ɗinki a tare da ita tunda ta zata zazzaɓi ne kawai.
Bayan ta kira wadda zata bashi kayan ta mata bayani ya fita. Ita kuma ta koma ta cigaba da lallashin Asma'u dake ta nishin wahala. Ga zazzaɓi a jikinsa sosai. Ruwa ta sake haɗa mata ta kaita ta shiga. Suna cikin hakanne Bilal ɗin ya dawo. Sai bin Asma'u da Doctor ta riƙo suka fito a bayi yake da kallo, ita ko taƙi yarda ta kalla inda yake sam. Tausayinta ya kama shi, ganin yanda take tafiya ma kasan akwai matsala. Jiki a sanyaye ya fita a ɗakin ya sake basu waje.
Duk dauriya irin ta Asma'u da shiru-shiru tasha kuka a ɗinkin nan. Haka dai aka gama sannan doctor tai mata allurai bayan ta saka Bilal ya haɗo tea ta bata tasha da ƙyar. Daga haka ta kwanta sai barci. Har cikin barci sai sakin ajiyar zuciya take a jere. Bilal na nane da ita yini guda. Dan Mammah kawai ya fita gayarwa ya samu basa nan sunje duba Nabeeha asibiti. Daga nan ya dawo kawai abinsa. Daga ƙarshe sai bayan anyi sallar Azhar yaje gaishe da su Mammah. Anan ne yake ƙara jin ciwon Nabeeha ɗin, har su Lailah suka bashi labarin abinda Hajiya Hasiba tai musu.
Ana cikin hirar Ruƙayya da Ammar suka shigo. Fuska kumbure Ruƙayya ta gaida su Shariffa ta wuce ɗakin Mammah. Ita a dole wai fushi take dasu. Dan Lailah dake binta da kallo ce ta maida dubanta kan Ammar da faɗin, “Yaya Ammar kai kuma abinda matar taka ta koyo kenan?”.
Zama yay yana dariya. Ya ce, “Fushi take da ku ne”.
“Da mukai mi?”.
Cewar Shariffa. Nan ma dariya Ammar yay har Bilal na taya shi.
“A'a Aunty ai bai kamata na faɗa ba, idan mun huce zamu kawo kammu”.
Bilal ya kwashe da dariya. Cikin ɓata fuska Ammar ya ce, “Haba Yaya yada haka. Kai da zaka sasanta”.
“Abin ne ya bani dariya Auta. Banda shirmen ƴar Mammah ana fushi da iyaye ne?”.
“Ita kam ai gashi tana yi. Sai ma Twinyn nata ta dawo sai su haɗu su biyu”
Lailah ta bashi amsa. Daga haka suka shiga hirar Nimrah kuma. Sai lokacin Bilal da Ammar suka san Dadah da Nimrah basa gidan. Mamaki yay matuƙar kamasu. Sabon shaƙiyanci ya tashi....
Acan ɗakin Mammah kuwa Ruƙayya ta rungumeta. Sai ga hawaye. Dariya Gwaggo Khadijah ta sanya musu. Mammah dai ta hau lallashi. Sai da ƙyar ta samu tayi shiru. Daga nan ta koma nasiha, dan bata tambayeta miya sakata kuka ba kar ta mata ɓaranɓarama. Bata saki jikinta ba sai da ta tambayi Nimrah Mammah tace mata basa nan. Babu abinda yazo ma Ruƙayya a rai sai Nabeeha. Sai kawai ta kwashe da dariya tana tambayar Aunty Nabeeha fa?. Mammah bata fahimci shaƙiyanci Ruky ba, kai tsaye ta bata amsa da tana asibiti anjima zatama su Ammar magana ma suma suje har da su su dubata.
A gaban Mammah Ruky ta nuna jimami. Tana fitowa falo ta shiga kwasar dariya. Sai lokacin ta je wajen su Lailah dake tambayarta ƙalau take?. Abinda take ma dariyar ta sanar musu. Ammar dake kallonta yana jin kamar ya haɗiyeta ya janye idanunsa ya na tambayar mike faruwa?. Labari shima su Shariffa suke bashi. Mamaki ya kama shi. Caraf Ruky ta ce, “ALLAH wannan ciwon nata dan Dadah ya tafi da Ninah ne.”
Cike da mamaki duk suka dubeta. Su Lailah na shinshino gaskiya a maganar ta. Dan su sam basu kawo hakan a ransu ba. Bilal ya ce, “Zancen Ruky fa nakan hanya. Amma inta tabbata haka ne na sake raina wayon matar nan ma”.
“Haɗa da ni nan Yaya. Ai dole ne ma anjima muje dubiya dan ba'ayi babu mu ba”.
“Kai Auta banda gulma”.
Dariya Ammar ya saki. Ruky kuma ta ce, “Dan ALLAH Uncle Billa muje.”
“Ki naɗarma Ninah gulma ko”.
“A'a ai bama zan faɗa mata ba.”
“ALLAH yasa, da dai ban san hali ba kenan...”
============
Su Ammar basu sami zuwa duba Nabeeha ba sai washe gari saboda yanayin jikin Asma'u. Ganin da sauƙi washe gari suka shirya wajen goma da safe suka tafi. Ita Mammah har tana jin daɗi sunfi su Ma'aruff yin abin arziƙi. Bata san gulma sukaje yi ba. Itama Asma'u daba komai ta sani a halayen Nabeeha ba sai wanda ake ɗan faɗa sama-sama bata fahimci komai ba.
Sun ma samu Nabeehar ta takura sai an sallame ta. Momyn su nata faɗa saboda tace mata bazata bita gidanta ba ɗakinta zata koma. Basu kuma ko kai gaisawa ba sai ga Ummu da Uncle Nasiru har da su Bintu. Maimoon ce kawai babu tana makaranta. Ganin baƙin bai saka Hajiya Hasiba daina tujara ba. Sai ma ƙarawa da tai dan su dukansu batai maraba da ganin kowanne ba. Uncle Nasiru daya fahimci komai sai bai nuna yama san da zamanta a ɗakin ba. Suma su Bilal sai sukai kara saboda Uncle Nasiru ɗin.
Yanda kuma Nabeeha ta gaida mahaifin nata a yau cikin girmamawa ya bama kowa mamaki. Sannan ya fusata Hajiya Hasiba. Fuuuu ta fice a ɗakin tana jaddadama Nabeeha tunda ita zata nunama bata da muhimmanci karta sake tunawa da ita matsayin uwarta. Rayhana da Amimah suka bita suna bata haƙuri. Ismat kuwa sai kuka. Dan a yanzu al'amarin iyayen nata na damunta. Bataƙi ace Momy ta haƙura ta koma gidan Abbansu ba.
Duk da Nabeeha bata gaida Ummu ba Ummun ce ta bada shawarar tunda an sallame ta su Bilal su wuce da ita gida kawai. Uncle Nasiru ya gamsu da hakan. Dan haka Ismat ta hau tattara kaya Asma'u na tayata. Ruky da Bintu kuwa suka ƙi tayata dan ƴan banzan ma sun haɗe kai ne sunata ƙus-ƙus kamar abinda ke faruwar bai damesu ba..
Badan su Ammar sun so ba suka ɗakko Nabeeba. Itama bata so ta bisu ba, gashi ita da Ruky da Asma'u da Ismat duk suka shiga baya. Har suka iso gidan tana ƙananun tsaki. Babu kuma wanda ya kulata, sai Asma'u dake mamaki, Ismat kuma na mata alamar ta bari dan ALLAH. Amma sai Nabeehar ke watsa mata harara.......
>>>>>%<<<<<
Mammah batai zaton Dadah bai san Nabeeha bata da lafiya ba. Sai a yau da Nimrah ta takura masa da magiyar ya kira mata Mammah ɗin ne sannan. Sai da suka gaisa ya bata wayar dan duk ta ƙagu. Sun gama gaisawa cikin hirar tasu Nimrah ke tambayar Ruky. Mammah tace sunje asibiti dubiya. “Mammah waye baida lafiya?”.
Mammah ta ce, “Auntynku mana. Mijinki bai gaya miki ba kin mata sannu”.
Kalmar nan ta miji na mata nauyi, amma dai ta danne taɗan kalla inda Dadah yake zaune da laptop gabansa yana aiki. Sai kawai ta ce, “Ƙila ya manta ne Mammah”.
Mammah bata ji daɗi ba. Dan sam bata son Muhammad ya tafi da matansa a bauɗe. Amma sai batace ma Nimrah ɗin komai ba suka cigaba da fira. Sai da sukai sallama Nimrah ta kaima Dadah wayar kamar yanda Mammah tace mata ta bashi zata faɗa masa saƙo data manta. Koda ya amsa ɗin ganin Mammah bata yanke ba ya kai wayar kunnensa, cike da girmamawa ya ce, “Kun haɗa kai da ƴarki an ware ni Mammah”.
Mammah tai murmurshi har yana iya jiyo sautinsa. “To Muhammad mai uwa a bakin murhu ai baya cin tuwonsa gaya ko”.
“Naga shaida yanzu kam ai”. Yay maganar yana murmurshi. Mammah ta sake yin murmurshin itama. Sai kuma ta jeho masa tambayar da saka shi yin tsamm.
“Muhammad bana son ka fara da tafi da gidanka haka. Karka manta Nimrah yarinya ce a tsakanin ku. Duk abinda kuka koya mata shi zata tashi dashi. Kuma a ƙarshe kune da shan wahala. Dan in ta koya sai ta fiku iyawa.”
“Mammah wani abu ya faru ne”.
“Eh ina magana ne akan Nabeeha. Miyasa baka haɗasu a waya ta mata yaya jiki ba?”.
“Yaya jiki? Bata da lafiya ne?”.
“Wace irin tambaya ce wannan?”.
Miƙewa yay tsam a inda ya ke ya koma can jikin window nesa da Nimrah. Sannan ya bama Mammah amsa da, “Ni wlhy Mammah ban san bata da lafiya ba. Dan tun randa muka iso dana kirata har 3 times taƙi ɗagawa sai kuma wayarta a rufe.”
Mamaki sosai ya kama Mammah. A ranta tana jinjina rashin hankalin waɗan nan mutane. Ta ce, “Shike nan ALLAH ya ƙyauta.” daga haka ta saki zancen. Tama yi masa sallama abinta. Dama ya san bazata gaya masa yanda akai ba. Koda ta yanke layin Nabeeha ya sake gwadawa. Sai dai har yanzu wayar switch up take...........✍️
81