← Book details Sakar Makafi Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 76 OF 113

Sashe 76

Sakar Makafi Part 3 Complete Hausa Novel · about 7 min read

.........Nima ban canja daga wannan tsarin ba. Nabi ayarin ƴan uwana matasa zuwan kudancin ƙasar neman na kaina. Duk da yayana yayi-yayi nai irin sana'arsa ta suyar kifi da saida ɗanye daya gada shima ga mahaifinmu naƙi. Ba komai ya saka naƙi ba sai dan ina son shiga duniya na ilimantu da karatun ta. Badan Iya da Yayana sun so suka barni ba, na tafi neman nan. Sai dai Alhmdllh tun a farko na samo alkairi, sannan kuma kwaɗayin kawo wa ƙauyenmu cigaba ya ƙara faɗaɗa a zuciyata. A komawata ta biyu BABA yazo gareni. Daga lokacin sabuwar tafiyarmu ta fara. Duk da dai da farko ban gane sa ba, bai kuma ce min komai game da shi ba, yakan zo dai kullum ya sayi kayan sana'ata. Sannu a hankali shaƙuwa irin ta mai haja da mai saye ta shiga tsakaninmu, har takai yana zama muyi ƴar hira kafin ya wuce.
        A wani zuwa da zanyi ganin gida ne ya bani tarin alkairi yace na kaima Iya. Mamaki ya kamani, musamman yanda kai tsaye ya kira sunanta Naja'atu. Ban iya daurewa ba na nuna tsorata, sai yay dariya da dafa ni yace na kwantar da hankalina zai min bayani. Badan na samu nutsuwa ba nace ina sauraren sa, hotuna ya bani, wanda suka sake rikitani. Domin kuwa ni da shi ne da mahaifinmu a jiki, a cikin ɗakinsa na bukka a wancan lokacin. Kai tsaye na ce, “Baba kai ne dama?”.
        Yay ƙaramar dariya, tare da faɗin, “Yaro mai basira. Tabbas kana da banbanci da shi, dama na daɗe da jin hakan a raina”.
     Ban ɓoye masa mamakina ba na ce, “Waye na banbanta da shi?”.
     Kai tsaye ya ce, “Ɗan uwanka. Na gwada shi tun a shekarun baya amma ya kasa, zuciyarsa nada zafafawa, duk da a zahirinsa mai sauƙi ne.”
        Na sake shiga ruɗani, dan haka na kasa haɗiyewa na roƙesa ya buɗe min dan na gane. Ya nuna min ba'a nan ba, sannan ba a lokacin ba. Naje gida na dawo. Sannan karna bama kowa labarinsa bayan Iya. Badan hankalina ya kwanta ba nabi zancensa. Sai dai a daddafe nai hutun kwanakin nan. Koda na bama Iya labarinsa kuma sai ta nuna kamar bata fahimta ba, sannan ta min gargaɗin na rabu da shi, kai nama canja garin da nake zuwa neman kuɗin. A gabanta na amsa da zanyi hakan, amma na kasa samun nutsuwar yin biyayya. Dan ina ji a raina akwai abinda ke tsakaninsu da Baba. Haka na shirya na koma batare da ta sani ba, shi ko Yayana dama bance da shi komai ba, kuma na roƙeta akan kada ta sanar masa, sai ta nuna min koda ban roƙeta ba dama bazata sanar masa ba.
     Na koma ga Baba, dan bama nace sana'ata ba, saboda a lokacin nafi ƙaguwa da shi. Sai dai me, Baba ya ɓace min ɓat, gashi ban taɓa sanin a ina yake ba. Hankalina ya tashi, kuma raina ya ɓaci, haka dai na gama takaicina na haƙura, badan ya fita a raina ba na cigaba da sabgogina. Sai a ranar da nake cika wata guda sai gashi kwatsam. Naso nuna masa fushi na, amma sai ya fara da bani haƙuri duk da zai iya haifaita, ya kuma min bayanin wani aiki ne na gaggawa ya taso masa, bai samu kammala shi ba kuma sai a jiya. Yanzu haka bai ko ƙarasa gida ba wajena ya fara zuwa. Fushina ya sauka, na kuma bashi haƙuri nima. Ya nuna min ba komai, amma na kasance cikin shiri, sannan ya bani wani address yace idan na tashi naje wajen na tsaya zai zo.
      Hakan kuwa akayi, naje inda yace, ya kuma zo ya same ni. Daga nan yay min jagora wani tsohon gida da bazaka taɓa ɗauka akwai mutum mai rayuwa a cikinsa ba. Sai da na shiga kuma naga abin mamaki. A ciki komai a tsare yake, sannan a tsaftace. Lura da yanda nake kallon gidan ya sashi yin murmushi. Ya ce, “Karka damu da duk abinda zaka gani a tare da ni, ka bani hankalinka kawai shine mafi mahimmanci.” kaina na jinjina masa kawai. Ya cigaba da faɗin, “Da farko zan fara da baka haƙuri, sannan ta'azziyar mahaifinku daya rasa rayuwarsa a dalilina”. Cikin zabura nace “Iyeee”. Ya ce, “Kwantar da hankalinka, zan maka bayanin komai”. Badan hankalin nawa ya kwanta ba na zauna. Ya ciga da mun bayani. “Ba ina nufin na kashe mahaifinka bane da hannuna. A'a an samu kuskure ne an kawo min hari tsautsayi ya faɗa kansa. Saboda a lokacin ni bana nan, na tafi can cikin garinku sanar masa halin da nake ciki da kuma shirin barin inda nake a wannan daren, sai muka samu saɓani ya tafi kai min abinci shi kuma. Su kuma kawai suna zuwa suka same shi cikin bukkar suka farmake shi, yayi ƙoƙarin guduwa suka kashe shi. Sai da kwanansa bai ƙareba a lokacin,  ALLAH yasa wani ya gani shine ya ɗauke shi ya kaisa gida. A lokacin da labari ya karaɗe gari duk da riskin da nake ciki ban bar garin ba sai da na je na gansa, a lokacin ne na fara ganin ɗan uwanka da mahaifiyarku. Da farko sun ce bazasu saurareni ba, dan da haɗin bakina akai masa haka. Sai da ALLAH ya bashi ikon yin magana ya sanar musu bani bane ba sannan, da yin wannan magana da komawarsa ga UBANGIJI bai wuce mintuna goma ba. Hankalina ya tashi, musamman ganin yanda ɗan uwanka ya ɗaga nashi hankalin da alwashin ɗaukar fansa ga kosu wanene. Naso ya fahimta mutanen nan masu haɗari ne amma bai saurareni ba. Gashi bani da isasshen lokaci, amma duk da haka sai da na kwana biyu a garin cikin ɓoye-boye dan kawai ya saurare ni, sai dai banci nasara ba, dole na haƙura na taho na barshi da burika da yawa a kanka, abinda yasa ban tunkareka ba kayi ƙanƙanta, sannan ya tabbatar min idan na faɗa maka ga yanda mahaifinku ya rasu ka shiga wani hali sai ya tona min asiri. Na barka badan naso ba, amma na cigaba da bibiyarka. Hatta zuwanka garin nan nine na saka abokinka Ƙasimu ya jawoka. Tunkan kazo na samar maka da wannan wajen da kake zaune. Ina sake roƙonka ka yafe min, ka kuma fahimceni karka zama irin yayanka. Alkairine ya haɗani da mahaifinku, kuma har abada bazan taɓa na mata ba.”
        Nayi kuka sosai a wannan lokacin, amma na fahimce shi fiyema da yanda yake so. Saboda ni Baba na zuwa dani wajensa ba kamar Yayana ba. Daga wannan lokacin labarina ya fara tsakanina da BABAH. Ya fara ɗorani akan hanyoyin samarwa ƙauyena cigaba, kafin wasu ayyukan sirri da ni kaina ban san manufarsu ba. Sannan ya saka ni makarantar yaƙi da jahilci ta dare, a cikinta nayi har sakandire. Ina kammala Sakandire babu jimawa abinda ya faru ya faru a yankinmu, aka rasa wasu, wasu suka tarwatse, sannan kuka ceci wasu a matsayinku na sojoji. Kisan Yaya Hassatu ne ya fara sanya min son shiga aikin tsaro. Dan haka ina komawa na tunkari Baba da batun. Yayi farin ciki, amma ya bani shawarar na zama ɗan sandan sirri ba soja ba. Domin yanzu ina baƙatar ɓuya ne saboda bama garina kariya daga waɗan can munafukan. Banyi masa musu ba, da taimakonsa na samu aikin ɗan sandan farin kaya, sannan kuma ya saka na koma karatu, wannan karatu na shekara biyar shine sanadin kaini matsayin da nake a yanzu tare da tsayawar UBANGIJI da taimakon Baba da kuma nuna jajircewa.”
         “Tirƙashi” cewar Imran. Sai kuma cikin nisawa ya cigaba da faɗin, “Kenan idan na fahimta shi Baba ya jima a ɓoye, sannan akwai wasu mutane da suke bibiyarsa shiyyasa yake ɓuyan. Amma abinda ban gane ba anan, kai kaɗai ne ke masa aikin?”.
      “Tabbas haka ne Sir, akwai abinda ya faru da shi, amma bai taɓa gaya min ba duk da nasha masa tanbaya. Sannan bani kaɗai nake masa aiki ba, sai dai babu wanda yasan wani a cikinmu. Ta yanda muke gane bamu kaɗai bane idan wani aiki ya taso, zai iya aikaka ka kai abu waje kaza, ko yi masa bincike a waje kaza, ta haka ne muke fahimtar juna”.
       “Har yanzu yana a wajen?”.
    Dadah yay tambayar a yanzu.
Amsa Kawu Tanimu ya bashi da, “Sir ai inaga shekara ɗaya tak na sanshi a wannan gidan ya canja waje, daga nan ma bai sake bari mun haɗu a cikin gida ba.”
        Cikin mamaki Faro ya ce, “Sai a ina kenan?”.
     “Inda yaso. Dan shi ba'a nemansa, sai dai shi ya nema. Sannan ba'a ganinsa kai tsaye, sai dai shi idan yaso ganinka duk inda kake zai zo”.
        “Tab ɗi. Lallai wannan ƙwaro ne?”.
     Kawu Tanimu yay murmurshi da jin furucin na Faro. “Ai bazaka san hakan ba ma sai ka mu'amulance sa. Yana da abubuwan ban mamaki sosai.”
          Dadah ya miƙe a hankali, inda suke ya bari zuwa jikin ƙarfen jirgin, ya dafe shi da duka hannayensa yana kallon yanda duhu ya mamaye ruwan. Iska ya ɗan furzar, batare da ya juyo ba ya ce, “Ina buƙatar ganinsa. Da gaggawa”............✍️

   92
Chapter 76 · 0% Book details