← Book details Sakar Makafi Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 94 OF 113

Sashe 94

Sakar Makafi Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read

       Ba ƙaramin tashi hankalin Daddy Imran yayi da ganin halin da Dada ke ciki ba. A rikice ya shiga jera masa tambayoyi. Sai dai bai samu amsa ko ɗaya ba dan hannunsa ma na riƙe da kansa ne. Imran da yaga babu wani abun kaico da Doctor zai iya gani sai kawai ya koma ya masa iso cikin ɗakin..
     Shima kansa doctor yanayin Dadan ya bashi tsoro. Musamman daya san halinsa na jarumta akan ciwo. Babu zancen ɓata lokaci kawai ya shiga dubashi yanda ya dace da jera masa tambayoyi. Ganin bashi da niyyar kula doctor ɗin Imran ya shiga roƙonsa da magiya. Dole ya daure ya amsa masa a dunƙule kuma a takaice. Cikin zargi doctor ya sake masa sabon bincike bayan na ainahin matsalar da yake shan magani a kanta. Sai dai abinda ya gano ɗin ya rikitashi, bai daiyi magana ba. Treating ɗinsa ya fara yi yanda ya kamata. Dan wasu allurai ya haɗa a cikin drip ya saka masa. Sai da ya tabbatar komai yana tafiya yanda ya kamata sannan suka fito shi da Imran ɗin saboda Dada ya fara barci mai nauyi....
        “Doctor akwai wani matsala ne?”.
   “Tabbas akwai matsala Sir, amma in sha ALLAHU komai zai zo da sauƙi. Sai dai a sanin da naima Yallaɓai baya shan komai na maye, ban san yaya akai haka ba”.
      “Maye kuma? Ai ko sigari zan iya rantsewa Haysam bai taɓa kwatanta sha ba balle ma shan”.
     “Shiyyasa na shiga ruɗani ai. Dan gaskiya matsala biyu ce ta haɗe masa shi ya kawo masa wannan matsanancin ciwon kan da badan anyi gaggawa ba komai zai iya faruwa. Kuma ko yanzu na san da wahala in baiyi jiyyar kwana biyu ba. Damma yana da jini mai ƙarfin gaske, dan wannan kwayoyin zasu iya sakashi barcin sati guda wlhy koma su masa illa a brain”.
        “Doctor kanata min magana a juye fa...”
    “I'm sorry Sir. Yallaɓai yasha ƙwayoyi ne masu ƙarfin gaske. Sai kuma matsalar da kasan yana shan magani a kanta. Sai kuma ƴar gajiyar jiki data kawo ciwon kan tun fil azal...”
    “Kwaya kuma?”.
“Tabbas kwaya ta shaye-shaye ma”.
“No! No! Ba Haysam ɗina ba. Akwai dai abinda yake ɓoye daya kamata mu sani. Yanzu komai daya dace ka masa?”.
          “In sha ALLAHU. Sai dai zai iya tashi da zazzaɓi mai zafi. Idan hakan ya kasance za'a iya masa amfani da ruwan sanyi a jiki. Bayan kamar awa ɗaya idan bai sauka ba dole zan dawo na sake masa sabon treatment. Sai kuma ciwon ciki, duk da na masa allurar saurin daƙile hakan amma bamu san abinda ALLAH zai yi ba, dan wannan daga waccan matsalar ne”.
     Godiya Imran yay masa, tare da rakashi har compound. Hakan yay dai-dai da fitowar Mole daga bayi. Ai da uban gudu ya koma ciki zuciyarsa na duka da sauri-sauri. Tabbas yau ALLAH ya kiyaye da shida Imran dole ai kiciɓus na zahirance.....

(★)-(★)-(★)-(★)-(★)

        Cikin sa'a kuwa barcin ya ɗauki Nimrah. Sai dai gaba ɗayansa mafarkin kiran wannan waya da bata ɗaga ba ya kasance.
    Sai kusan tara da wasu mintina ta tashi da ƙyar. Sam bata wani ji daɗin barcin ba. Sai ma ji take kanta ya mata nauyi kamar zai yi ciwo. Ga yanda jikinta yay mata nauyi wanka kawai take buƙata. Dan haka ta gyara gadon kamar ba'a kwanta ba sannan ta nufi bayi. Can ma sai da ta gyara sannan tayo wankan. Ta fito kenan kira ke shigowa wayarta. Sai da gabanta ya faɗi, sai kuma fahimtar wayarta ce bata ɗazun ba ya sa ta sauke a jiyar zuciya. Sai ta share wayar kawai ta shiga shiryawa. Sai da ta kammala tsaff cikin doguwar rigar abaya baƙa datai mata ƙyau sannan ta ɗauki wayar tana shafa ciki dan yunwa take ji. Sosai ta waro idanu waje ganin Daddy Imran ne ashe ya kirata. Da sauri ta kira shi back.
       Daga can Imran ya amsa sallamarta da gaisuwa da tai masa a tare. Daga ƙarshe yace tazo yanzu ta same shi a sashen Dadan su yana jiranta. Bata kawo komai a ranta ba tace to. Kamar jira ake ta yanke wayar waccan ta fara ringing itama.
      Ji tai wani kalar takaici ya kamata. A fusace ta nufi wayar dan ɗazun a saman sofar ɗin ɗakin ta wullar da ita. Ɗauka tai a zafafe ta ɗaga kiran....

       {==}{===}{===}{==}

       “Lafiya kuwa gidan nan yake Aunty?”.
     Shiru Nabeeha bata motsa ba, balle Amima tasan taji maganar tata. Cikin mamaki ta ƙaraso inda take jikin mirror tsaye da waya a hannu. Itama zama tai a stool ɗin mirrorn sannan ta taɓata. Firgigit Nabeeha ta dawo hayyacinta. Dan ita ko motsin shigowarta ma bata ji ba, ranta a ɓace yake sosai da abinda take ganin Dadah ya mata da gangan.
        “Aunty kina lafiya kuwa?. Inata magana amma shiru kamar wadda ta suma a tsaye”.
    Gajeren tsaki Nabeeha taja, sai kuma ta sauke numfashi tana ajiye wayar a kan mirror ɗin. “Bamma san kin shigo ba sam wlhy. Hankalina ya tafi wani tunani can daban”.
      “Hummm Aunty kenan. Ya kamata dai ki kwantar da hankalinki, idan ma har yanzu waccan banzar yarinyar lamarinta ke damunki. Ba gashi har sun dawo sun sameki ba cikin ƙoshin lafiya. Miya gwaguyeki? Ita kuma mi ta fiki da shi? Tana tafiya kamar zata tsinke duk da nasan ba finta nai ba.
         Shiru Nabeeha batace komai ba, sai dai tayi ɗan murmurshin takaici da jan tsaki. Sakin zancen itama Amimah tayi, ta koma na farko data shigo da shi.
          “Uhm dama fa naga wannan Imran yake ko mi a gidan da wani baƙo sun nufi sashen Yaya Haysam, shine nace lafiya kuwa?”.
     Sosai ƙirjin Nabeeha ya buga, tadai yi ƙarfin halin dannewa. Abinda ya faru ne daren jiya ya shiga dawo mata, duk da da safen nan abinda yay mata yasa bata tsaya tambayarsa yaya kan nashi ba. Duk da kuwa a gaban idonta tana gani da ƙyar ya iya kai kansa banɗaki tamkar wanda ke cikin maye, da alama ma akwai sabo na jiki da ya sashi farkawar. Haushin kiranta da wannan suna yasa ta baro masa ɗakin masa ɗakin batare data jira shi ba. Anan ɗakinta tai wanka tai sallar asuba. Ba kuma ta sake bi takansa ba tai zaman yin waya da Momyn su da taga tai mata kira har kusan biyar da daddar.....
        “Aunty baki bani amsa ba kin sake tafiya tunanin”.
     “Mtsoww! Ƙyale ni Amimah kinji. Idan na gama abinda nake zan fito”
   “Amma Aunty dakin duba ko wani abu ne dai...”
    “Nace ki barni. Zuwan Imran ɗin ne baƙonki a nan gidan ko mi? Kin san dai yanda kullum yake nane da shi ko matar aurensa sai haka. Mtsoww ba zuwa da sassafe ba yama dawo nan gidan shima a bashi ɗaki, kinga mu zama matansa uku ke nan”.
        Fahimtar ranta a ɓace yake yasa Amimah bata sake magana ba ta fito.........✍️
109

..........Cike da tsiwa Nimrah ta ɗaga wayar. Dama gashi zuciyarta a kusa take.
      “Nikam wai ko kana bina bashi ne malam? Ka takurama rayuwata fa. Tunda ka faɗi abinda kake son faɗa a baya ba sai ka ƙyale ni ba”.
      “Ba kici bashi na ba, amma kina da abu mai muhimmanci a wajena Nimrah. Sannan ni da alkairi nake binki. Na jima ina neman hanyar dazan sameki amma na rasa. Sai a kwanan nan nake samun labarin kinyi aure. Auren ma wai maƙiyinki kika aura, wanda yay yunƙurin kashe mahaifiyarki. Anya kuwa Nimrah baƙya ganin akwai kuskure a yin hakan. Amma na miki uziri, dan na fahimci har yanzu baki gama sanin waye Zak-Shadow ba. Makirin mutum daya iya taku da bada ƙafa kenan. Shi ɗin ƙuli-ƙuli ne da ba'a gane masa gaba balle baya.....”
       “Nifa gaskiya kana sakani a ruɗani. Kana raba min hankali da yawa. Saboda ko abubuwan daka gaya min a kansa a baya ni ba haka nake gani daga garesa ba a yanzu. Amma zan baka dama guda ɗaya tak, idan har ka gaza zaka sha mamaki na. ”
     Da sauri Mr Specter yay ma Dagger alamar yace ya yarda. Dan haka Dagger ya sake kwantar da murya ya ce, “Na yarda da duk sharaɗin ki Nimrah. Sannan a wannan karon na miki alƙawarin sai na tabbatar miki da ɓoyayyar fuskar Zak-Shadow da baki sani ba. Sai na bankaɗo miki munanan ayyukansa. Sannan zan haɗaki da mahaifiyarki dake ɓoye kanta saboda shi”.
         Nimrah ta ɗanyi shiru kamar mai nazari. Sai kuma a hankali ajiyar zuciya mai nauyi ta suɓuce mata. Ta kai zaune a bakin gadon karo na farko. Tabbas tana son ganin Ummanta, tana kwaɗayin hakan kodan ta tabbatar da gaskiyar nan akan Dadah...
      “Kin amince?”.
Dagger ya katse mata tunani.
Kamar tana a gabansa ta jinjina kanta a hankali. “Na amince. Sai dai ina sake tabbatar maka idan naga daɓanin abinda ka faɗa zan baka mamaki. Dan kai ma baka san wacece ZAKANYAR KAWU TANIMU ba. Nimrah kawai ka sani”.
      Dagger yay ƙaramar dariya. “Niko nasan Zakanyar Kawu Tanimu. Amma bazaki san na sani ba sai nan gaba idan kika gama sanin wanen ni. Na barki lafiya. Sai dai nan da kwana kaɗan saƙona zai riske ki. Idan kin aiwatar yanda ya kamata ki fara shirin haɗuwa da Ummanki. Kije ga mijinki dan yau kaɗan ya rage kishiyarki ta halaka shi da ƙwaya...”
     Ɗiff wayar ta katse. Ƙirjin Nimrah ya buga, sakamakon kalaman ƙarshe.
  “Kwaya?”.
  Ta maimaita kalmar da tafi tsaya mata a ƙofar zuciya. Ai ba shiri ta watsar da wayar ta miƙe jiki na ɓari ta fita....
Chapter 94 · 0% Book details