← Book details Sakar Makafi Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 106 OF 113

Sashe 106

Sakar Makafi Part 3 Complete Hausa Novel · about 7 min read

.........Karo na farko Dadah yay magana idonsa akan Malam Almu.
     “Yanzu zaka koma ka cigaba da aikinka a gidan. Dan ina son ka cigaba da tirke min Malam Buba”.
      T-Dalha ya kalli Dadah da sauri. Kuma sarai Dadah ya ganshi. Shi ko Malam Almu na son tambayar dalili amma babu fuska. Dan wargi ma wuri yaka samu. Dadan ma na gama faɗa ya miƙe bayan ya kalli agogon dake hanunsa. Bai kuma sake cewa kowa komai ba ya nufi hanyar fita. Miƙewa Imran yayi ya bishi. Kusan tare suka iso jinkin mashin ɗinsa.
          Dadah da tun da ya fito yake jin takun tafiyarsa a bayansa ya ɗan juyo ya kallesa. Sai kuma ya ɗauke kansa ya maida gefe.
      Cikin sauke numfashi Daddy Imran ya ce, “Nazata shima Musbahu ɗin zakayi magana da shi ne?”.
     “Ba yau ba.”
Dadah ya faɗa a taƙaice.
Imran ya ce, “Okay shike nan. Amma mika fahimta da sunan Baba shima daya ambata?.”
        “Humm bamma san mizan ce ba. Amma ko waye bawan ALLAHn nan ya shigar min rayuwa da yawa a kwanakin nan da suka gabata. Nama rasa ina zan ajiye tunani na a kansa”.
      “Bakai kaɗai ba Zak.. daga ni har Faro mun kasa hutawa da hasashe-hasashe da bincike. Amma komai bamu iya samowa ba, ga box kace har yanzu ka kasa gane kansa. Yanzu dai alaƙar Musbahu da Baba na nufin maganar T-Dalha ta bayyana, dama yace mutane da yawa ke masa aiki. Kuma ba lallai susan juna ba sai wanda baban yaso in ya haɗasu aiki. Gaskiya mutumin nan hatsabibin kansa ne. Shiyyasa nake jin zumuɗin son jin ta bakin shi kuma Musbahu ya akai yasan Baban? Miye alaƙar su? Sannan yaya akai Musbahu ya canja daga mutumin banza?. Dan in har dai yanda T-Dalha ya tabbatar mana Baba mutumin kirki ne alaƙarsu da mutum irin Musbahu zata zama abin mamaki, duk da rabonmu da Musbahu tun a NDA bayan kammalawarsu. Bamu sani ba ko har yanzu yana da alaƙa da Garba.”
        “Wannan shine dalilin da yasa bazan yi magana da shi ba a yau. Dan ina son mu fara bincike yaya alaƙarsa da Garba ɗin bayan barin NDA. Sannan ina aka fara posting ɗinsa aiki? Yanzu kuma a ina yake?”.
      “Yes tunani mai ƙyau. Bari na kira Hassan, nasan in sha ALLAHU yanzu zai cika mana aiki. Idan kuma shima Dabo yayi to?”.
       “No. Hassan ɗin ya wadatar”.
   “Okay ba damuwa. Amma kaga yanayin T-Dalha kuwa daka ambaci Malam Buba?”.
       “Na gani, ai shi a tunaninsa har yanzu bamu san waye shi ba. Kamar yana neman ta inda zai sanar mana ne yana shakka”.
     Murmurshi sosai Imran yayi, tare da faɗin, “Lallai kam har yanzu bai gama sanin waye Zak-Shadow ba”.
     Ƙaramar Harara Dadah yay masa. Daddy Imran yayi dariya. Daga haka yay kiran Hassan. Yana ɗagawa suka gaisa.
         “Hassan aiki muke so na gaggawa. Daga nan zuwa safiya muna son bayanin wani Musbahu Kabir Billiri. Tun daga shigarsa NDA har zuwa matsayinsa na yanzu a soja.”
       “An gama Oga. In sha ALLAHU kafin safiya zan ajiye maka komai”.
     “Na yarda da kai”.
   Murmurshi Hassan yayi daga can har Dadah dake saurarensu na ji. Dan a hans free Daddy Imran ya saka wayar. Suna yin sallama ya furta. “Miye next?”.
           Kallon agogon hannunsa yayi. Sai kuma cikin ɗan taɓe lips ya ce, “Muje kawai muyi shiri. Dan bazan iya cigaba da ɗaukar rigimar ƴarka ba”.
       Dariya sosai Imran ya sanya. Shi dai Dadah bai sake magana ba ya haye mashin ɗinsa tare da saka hular kwanon ya burga abinsa yay gaba.....

       ()/()/()/()/()/()/()/()

     “Aunty wai lafiya har yanzu baki dawo ba. Daga cewa zaki je wanka kizo ki karɓemu muma mu samu muyi amma shiru. Ga Aunty Jiddah ma da tace har girki zatayi ta kira cewar gata nan taho wa.”
       Nabeeha da idonta ya cika da hawaye da ƙyar ta iya motsa lips ɗinta dake kumbure sunɗum saboda muguntar da Dadah yay musu ta bama Ismat amsa.
        “Idan Jiddan tazo kuzo kawai kuyi wankan”.
      “To ke kuma fa? Ba zaki dawo bane? Ni sai nake jin ma kamar da ƙyar kike magana, ko baki da lafiya ne?”.
    Kasa magana Nabeeha tayi saboda kukan dake ƙoƙarin kufce mata. Sai kawai ta yanke wayar tama kashe ta gaba ɗaya. Bargo ta ƙara ja ta rufama jikinta saboda mugun zazzaɓin da take ji. A zuciyarta kuwa babu kalar sunan mugaye da azzalumi da bata kira Dadah ba. Ji take da zata iya abinda zatai masa yau sai ya sha mamaki. Sai dai ina, kura ma tasan gidan mai babbar sanda. Duk da yanda ya wajiga rayuwarta hatta umarninsa na gyaran sashensa bata tsallake ba sai da tayi. Dama tasan duk wannan iya shegen nata yaga damar ƙyaleta ne kawai badan baida hanyar maganinta ba. Kawai dai shi dama haka yake. Mutum ne mai basar da abu, sai lokacin daya gadamar kulawa sannan. Ai ta rantse bazata yafe ba wannan muguntar da yay mata ba. Kaf jikinta babu inda baya ciwo, ta shiga ruwan zafi yafi sau uku a banza. Ga baki ya haye. Kunenta yay jazur shima abinka da mai hasken fata....

{{=}}{==}{{=}}

             Madam Nimrah kam bama tasan bidirin da akai ba. Har yanzu tana a sashen Ruky suna sabgarsu. Dan ma barci ya hanata sukuni. Sai dai data fara Ruky da Mu'azz ke tada ta. Haka dai ake hirar. Kayan kwaɗayi kuwa suci wannan suci wannan. Ruky da Mu'azz har sun gaji amma ita bata gaji ba. Har Ruƙayya sai da tai magana akan hakan. Ita dai Nimrah tace oho kawai ita komai so take. Ji take ma idan bata ci ba kamar akwai matsala.
      Da mamaki Mu'azz ya ce, “Matsala kuma? Sai kace mayya”.
     Harara ta ballara masa da faɗin, “In ni mayyace kaima ai haka tunda dangi muke”.
        Ruky ta sanya musu dariya. Dan daga nan suka kaure abinda suka saba wato faɗa. Hirar kuma ta baro sashen Ruky suka koma na Mammah. Dama takaicin ganin Hanoon ne ya hana su zama can. Hatta Small Mom sun kira sun ma gulmar dawowar Hanoon ɗin. Ganin Asr ta gabato Mammah tace Nimrah taje ta shirya zasu je anguwa ne. Ruky da Mu'azz suka marairaice. Amma Mammah ta ce, “Babu ruwanta ta tambayi mijinta. Itama Nimrah ɗin Dadah ne yace. Jin haka Ruky tace itama zata sanarma Dadahn to. Su Shariffa na mata dariya Gwaggo Khadijah tace ai wannan ba hurumin Dadah bane. Tunda ya aurar da ita shi yanzu bashi da iko akan irin wannan abubuwan sai mijinta. Daga ita har Nimrah sai abin ya tsaya musu arai. Har takai suna kallon juna ma. Asma'u da Lailah mi zasuyi in ba dariya ba. Gaskiya Autocin Mammah na buƙatar saiti...

        Koda Nimrah tazo dan cika umarnin Mammah sam hankalinta bai bata wani zancen amsar girki ba. Dan ita fa ba sanin yanda akeyi tayi ba. Ba zama da kishiya ta taɓa gani ba a zahirance. Tunda kaf iyayen nasu babu mai ita. Su kuma ba wani mu'amular mutane suke ba sosai balle bin gidan ƙawaye. Dama dangin su Daddy Imran ne dai suke shiga, suma kasancewarsu ƴan boko masu mata fiye da ɗaya ɗai-ɗai ne. Ba kuma wajen da suke dogon zama bane. A dai nasihar da akai mata tana jin anata ambaton ranar girkinki ranar girkinki. Yaya ranar girkin take shi ne fa bata fahimta ba balle ta sakata a jadawalin tsarikanta. Ko zancen Nabeeha na ɗazun ya bata haushi ya kuma bata dariya, shiyyasa ko Ruky bata bama labari ba ma..
        Jin sashen shiru bai sa ta maida hankali da cewar basa nan ba. Dan ta wuto Nanah a babban falo tana mopping. Bata kulata ba kuma dan ko gaisuwar datai mata bata amsa ba. Haka kawai Nanah ke mata zubin munafukai.
     Wanka ta fara yi da alwala. Koda ta fito sai tai zaman shafa mai tunda lokaci bai ƙarasa ba. Nimrah da Ruky akwai son kwalliya, dan haka bataji gandar yi ba. Sannan ta shirya tsaff cikin wani lass da yay mata shegen ƙyau. Skirt ne da half bubu. Bata ɗaura ɗan kwalin ba tace sai tayi salla. Bayan ta idar ta fara tsara ɗauri. Sosai tayi ƙyau Masha ALLAH. Dai-dai nan kira ya shigo wayar nan da har yanzu ke ajiye cikin drawer ɗin mirror ɗinta. Sai da ta kusa tsinkewa ta ɗakko cikin yatsina fuska. Haka kawai yanzu haushinsa take ji, ta dai daure ta ɗaga. Bata wani gaishe shi ba, tadai yi sallama daga haka tai shiru.
       “Nimrah ba gaisuwa?”.
   Cikin yamutsa fuska kamar tana gabansa tace, “Ka faɗi abinda zaka faɗi ina uzuri ne”.
       “Hummm” kawai yace. Sai kuma ya cigaba da faɗin. “Ga saƙo nan zan bama Malam Buba ya baki. Ki tabbatar kin yi yanda nace. Yin kuskure na nufin sake yin nesa da Ummanki ko rasa wasu abubuwa masu muhimmanci.”
         “Naji”.
   Ta faɗa itama tana yanke wayar. Kamar jira tana ajiyeta ta ɗauki ɗan kunne zata saka Dadah ya turo ƙofar ɗakin da sallama ya shigo. Wani kalar tsargawa zuciyarta tayi, ta dai dake, cikin fakaitar idanunsa ta tura wayar ƙarƙashin hoda dake buɗe. Kafin cikin sanyin murya ta ce, “Dadah sannu da dawowa”. Dan har yanzu fuskarsa a tsume take...........✍️

       121
Chapter 106 · 0% Book details