← Book details Sakar Makafi Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 110 OF 113

Sashe 110

Sakar Makafi Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read

.........Abu kamar wasa akaita tafka rikici Kawun mu dai yaƙi ƙara aure. Daga ƙarshe ma ya lallaɓa ya saida babbar gonar kakanmu batare da sanin kowa ba ya ɗauke matarsa suka gudu, har yanzu kuma ba'a sake jin ɗiriyar su ba. Duk da anyi nema sosai a lokacin amma dole aka haƙura. Daga ƙarshe wannan shine sanadin rasuwar kakanmu. Itama matarsa da muke kira Inno kakarmu kenan tabi bayansa.
      Tabbas gida ya faɗi, duk da mahaifinmu na tsaye tsayin daka wajen ganin ya haɗa kan sauran ƙannesa uku. Amma abu ya gagara, sai ma rikicin gado daya shigo musu. Ba komai ya kawo hakan ba kuma sai munafunce-munafuncen matansu. Ƙarshe dai sai a gidan maigari aka raba musu wannan gado. Bayan an raba gado hankula suka ɗan kwanta, kowa ya koma cin gashin kansa, daga nan ne mahaifinmu ya fara sana'ar kifi. Yana saida ɗanye, sannan duk ranar kasuwa Inna kan soya a gida ya fita da shi. A wannan yanayin akai auren su Yayana su kusan bakwai. Dan harda ƴaƴan kawunan mu. Yayana ya auri Hassatu, ƴa ɗaya tilo mace a wajen babba malamin garinmu. Mutumin kirki mai tarin cikar kamala da kwarjini. Yana da tarin iyalai shima sai dai duk maza ne Hassatu ce kawai mace. Ba ƴaƴansa kawai ba har ƴaƴan dangi da marayu yana riƙewa. Sannan yana da makaranta da duk daga can muke fara karatun allo. Idan ka tasa sai ya damƙa ka ga wani almajirinsa dake wani gari bisa ga al'adar mutanen yankinmu da kowa ya sani.
       Hassatu yarinya ce mai nutsuwa da ilimin mahammadiyya. Soyayya ce kuma ta haɗasu da Yayana. Na samu gata a wajenta sosai tun kan ta shigo gidanmu. Wannan shine sanadin shaƙuwar dake tsakaninmu. Babu jimawa abokan auren Yaya Hassatu duk suka haihu a gidan, amma ita shiru kake ji.
        A lokacin ni ina makarantar allo ne, dan bikinsu babu jimawa aka kaini makaranta. Ban kuma tashi dawowa ba sai lokacin rasuwar Babanmu. Bayan komai ya lafa Inna ma tayi takaba sai akace bazan koma ba. Yayana ya cigaba da sana'ar mahaifinmu ni kuma na maida hankali akan noma da abinda baza'a a rasa ba. A kwana a tashi har lokacin da na isa aure nima, har lokacin kuma dai Yaya Hassatu bata haihu ba. Abinda ya faru da Kawun mu yasa kowa yaji shakkar ƙin yin magana akan rashin haihuwar Yaya Hassatu, dan kowa na tsoron a sake maimaita ƴar jiya musamman yanzu da bamu da mahaifi. Bayan auren mu da matata da ni na zaɓa da kaina babu jimawa ta haihu.
        An fara ƴan ƙananun magana a ɓoye sai ga Yaya Hassatu da ciki. Farin cikin da akai bashi da misalin kwatance, dan kowa tattalinta yake. Kowa burinsa aga abinda zata haifa. Itama dai hakan ne balle ni kuma ai ba'a magana. Yanda kasan banyi aure na haihu ba haka nake zumuɗin wannan ciki. Har hakan yasa muka fara samun saɓani da matata. Ban biye mata ba, dan harga ALLAH nidai ina matuƙar so da burin ganin jinin Yayana da Yaya Hassatu. Yanda nake bata labarin sojoji a birni da aikinsu yasa ta ƙwallafa rai da fatan son ta haifi namiji ya zama soja. Kowa kan mata dariya akan wannan buri nata har Yayana, amma ni na saka a raina indai ina raye zan cika mata shi. Dan haka nake ta ƙara ƙaimi wajen sanar da ita duk abinda ya shafi aikin soja. Gab da zata haihu akai bikin wata ƙanwarmu aka kaita wani ƙauye maƙwaftanmu. Kwatsam randa suka kai kayan jere suka dawo basai gasu da labarin haɗuwa da sojoji ba. Uban gudun da suka ci, jarumtar da Yaya Hassatu ta nuna har hirarta da sojoji nan da labari ya gagara ƙarewa, dan hatta ruwan roba da suka bata ta adana robar kamar abin ado. Kowa ɗaukar al'amarinta yake shirme, amma ni na saka a raina da kaina sai na nema wannan soja bayan ta haihu yaro ya tasa. Sai dai labarin ya canja a lokacin da Yaya Hassatu ta haihu bayan kwanakin da basu gaza goma ba da haɗuwar su da sojoji. Saɓanin namiji data ƙwallafa rai dan ya zama soja mace aka samu. Hakan bai rage komai na farin cikinmu ba. Akai shagali sosai ran Yaya Hassatu cike da burin son sake haɗuwa da wannan soja ta masa bayani sai ta sake haihuwa zata bashi. Sai dai UBANGIJI bai ƙaddara ba har Naja'atu da taci sunan Inna na mata laƙani da Nimrah ta fara tasawa. Duk da kuwa sunan dana saka mata ya zama anta surutu wai na saka mata sunan aljanu. Oho bamu kula ba daga ni har Yaya Hassatu tunda ya mana. Inna da Yayana kuwa babu ruwansu daman.
        Zakanayar Kawu Tanimu ta girma a Zakanyarta, dan kuwa ita yarinya ce mai shegen ƙiriniya. Faɗa kona uban waye zata saya da kuɗinta a buga koda zataci duka. Kai fitina zan ce muku babu irin wadda batayi ba yarinyar nan. Abun na damun su Yaya Hassatu nikam ko'a jikina. Hasalima daɗi nake ji Zakanyata mai ƙarfi ce. Wlhy iya gaskiyata ina son Nimrah da wani irin so daga ALLAH NA da ko ƴaƴana bana jinsu haka a raina. Shiyyasa komai na gani ita take fara zuwa min arai. Gashi dama ni nawa yaran duk maza ne su uku, banda mace, ko hakan ne ya sake ɗaga darajar soyayyar tata a raina ban sani ba. Mun sha samun saɓani da iyalina akan hakan, har yaji tayi gidansu, har kalmar zargi ta jefeni da ita akan Nimrah amma hakan bai sauya komai ba.
       Muna tsaka da farin cikin rayuwarmu, da kwanciyar hankali duk da abubuwa sun faffaru a ƙauyukan gefenmu shine ma dalilin ajiye sojojin nan kwatsam sai ga sabon iftila'i ya saukar mana. Iftila'in daya rusa komai, ya ruguza kowa, ya maida mana gari kufai. Wannan iftila'in kuma shine sanadin shigowar sojoji garin mu. Ba su kowa bane kuma sai su Oga gasu nan......”
        Hawaye Nimrah ta share dan anzo inda take son ji.
    “Kawu Tanimu ya cigaba da faɗin, abubuwa da yawa sun faru musamman a gidanmu da Nimrah ta zama sanadin buɗe wani sirri da babu wanda yasan da shi. An samu makamai da suka tayar da hankali. Wanda a dalilin su ne aka samu har a wasu gidaje bama gidan namu kawai ba. Ni a lokacin ina wajen neman kuɗi na. Bamu san hawa ba bamu san sauka ba sai ga sojoji har garin da muke kasuwanci sun zo sunyi ram da mu. A lokacin ne na fara ganin mutumin da inda karatu ne zance na haddace shi daga bakin Yaya Hassatu. Ba kowa bane kuma sai Oga. Ya kalla inda Dadah yake...”
        Ba Nimrah kawai ba, hatta su Mammah sai da suka sha mamaki. Nimrah ta ce, “Dama shine yaga Umma da ciki?”.
       “Kwarai shine Zakanyata”.
    Nimrah ta zubama Dadah idanunta tana wani ƙyaƙyƙyafta su. Shi ko a kallo ɗaya ya janye nasa cike da basarwar daya iya. Dan ya fahimci so take yayi magana. Daddy Imran daya fahimci Nimrah ɗin sai yay murmurshi. A maimakon Dadah shi sai ya fara bata labarin. Tun daga randa suka haɗu da su Ummanta, fara yaƙin daya kaisu ƙauyensu, dan bai san shi Dadah na mafarki akan haihuwarta ba. Har zuwa rikicewar komai da yanda ta nuna musu makamai a gidansu da labarin fatalwoyin bayan gida. Har zuwa kama su Kawu Tanimu da suka saka aka kamo. Binciken su har rikicewar abubuwa a wannan daren a gidan kakanta daya haifi Umma, dama garin gaba ɗaya. Harbin Ummanta, da makircin da aka shirya. Amanarta da Umman ta damƙa a hannun Dadah. Da fiddota da sukai a cikin kwalla da kakarta ta ɓoye. Dawowar su gida, da abinda ya biyo baya na makirce-makirce daga gidan soji da munafukan bayan fage. Aurenta da Dadah, da kuma kama Dadahn da yanda hankula suka tashi. Har zuwa rufe shi, da shima kamun da akai masa. Dalilin su na ɓoye musu akan yana ƙasar waje....
      Wani kalar Kuka Nimrah take yi mai ban tausayi. Hakama Kulu. Gwaggo Khadijah da Mammah ma sai share hawaye suke yi. Cikin shiɗewa da sharɓe majina ta ce, “Dan ALLAH ku gaya min gaskiya a yau Daddy, kenan ba Dadah bane ya kashe min Umma na?”.
      Shiru falon ya ɗauka na wasu sakanni. Dadah kam ya wani kafe Nimrah da idanunsa da suka sauya kala. Duk da ya san wani yanki na sirrin nata a kwanakin da suka gabata a Dubai. Daga nan ya fara bincikenta batare data sani ba...
     Daddy Imran ya katse shirun da faɗin, “Tabbas ba shi bane Nimrah. Duk wanda kuma ya gaya miki shine ya yaudare ki ne. Sannan ya zalunce shi. Hasalima akwai wata manufa a tare da shi. Haysam kariya ya bama ahalinki da mahaifiyarki. Sannan da hannunta ta ɗauki amanarki ta bashi. A gabana akayi wlhy! Wlhy. Kin dai ji na rantse miki. Idan ma wani yayi amfani da video nan dana gaya muku anyi editing ɗinsa ne wajen gurɓata tunaninki wannan zaluncinsa ne. Sai dai muna fatan UBANGIJI ya bayyana gaskiyar lamarin nan kafin wani a cikinmu ya koma ga ALLAH...”
       “Ni shaida ne ma akan abinda ka faɗa. Sannan a gabana komai ya faru batare da sanin ku ba”.
      Nimrah ta juya a firgice tana kallon Kawunta da yay maganar. Hakama Dadah da Imran da su Mammah.........✍️
125
Chapter 110 · 0% Book details