Sashe 92
Sakar Makafi Part 3 Complete Hausa Novel · about 7 min read
Cike yake da buƙatar yin wanka. Dan gaba ɗaya kayan jikinsa sun gama takura masa. Ga gajiya da hayaniyar da yasha yau. Bai wani saka al'amarin Nabeeha a ransa ba dan yasan halin kayansa. Ya zare kaya kawai ya shiga wanka bayan ya gama ganin abinda Nimrah ɗin tayi a wuyansa, dan Nabeeha bata goge duka ba. Ya ɗan jima kafin ya fito. Bai yi mamakin samun Nabeeha ta shigo ba. Sai dai yanda ta cika tai fam ya sashi yin murmushi yana kauda kansa.
Sanin zai koma wajen Mammah ya sa ya saka jallabiya a maimakon kayan barci. Kafin ya iso inda Nabeeha take a bakin gado ya zauna kusa da ita. Kai tsaye ya ce, “Bani ruwa”.
Batare data kallesa ba ta ce, “Ka muje falo ga abinci”.
“Kin san bana cin abinci da dare ai. Ki bani ruwan sai ki bani green Apple kawai”.
Miƙewa tai batare da tayi magana ba taje fright ɗin dake ɗakin ta ɗakko masa ruwan da cup ɗaya ta dawo.
Ruwan kawai ya amsa ya barta da cup ɗin. Da yake a buƙace yake da son sha bai ma fahimci a buɗe ruwan yake ba ya cire murfin kawai ya kai bakinsa. Sai da yay bismillah kamar yanda ɗabi'arsa take sannan ya fara sha. Tas kuwa ya shanye shi ya miƙa mata robar kamar ba yanzu yasha ruwa a wajen Nimrah ba.
Koda yake shi mutum ne mai son ruwa sosai. Shi kansa bai san irin adadin ruwan da yake sha ba a rana. Idanunsa a rufe ya dafe jijiyoyin kansa dake harbawa da duka hannayensa. Sai da yay kamar mintuna biyu a haka sannan ya buɗe idanun nasa ya ɗauki wayarsa dake a bed side drawer da tai motsi alamar shigowar saƙo. Waya ce ta aiki mai muhimmanci, kuma yana saka ran su Faro ne, dan haka ya kalla Nabeeha da nufi sakata aikin da zata bashi waje... Sai dai me? Yana motsa lip kansa yay wani ɗan sarawa, hannu ya sake kaiwa yana ƙoƙarin dafe shi saboda nauyin da yake neman fara masa.
Ita ko Nabeeha dama bata lura ba ta miƙe ne kawai ta nufi ƙofa ɗauka masa Apple da yace.
Ganin haka ya sashi yunƙurin sake ɗaukar wayar. Abu kamar wasa yana ƙoƙarin fara duba saƙon da aka turo masa idonsa ya fara juyewa dishi-dishi....
Mamaki ne ya fara kama shi kam, ya shafa idanun tare da buga kan nasa kaɗan amma ina. Karo na farko ya ambaci sunan ALLAH a bayyane. Hakan ne ya saka Nabeeha dake shigowa ta ƙaraso gabansa da sassarfa ta zube tana kama masa kan itama da faɗin, “D. Miya faru? Kanka ke ciwo ne?”.
Kai ya girgiza mata da ƙyar, ya motsa lips da nufin mata bayani amma yay masa nauyi. Sai kawai ya yamutse fuska yana lumshe idanu. Miƙewa tai ƙoƙarin yi zuciyarta na tuna mata batun Nimrah sai dai cikin rashin sa'a yay baya zai zube a gadon shi kuma. Kasancewar tana a jikinsa kawai suka tafi gaba ɗaya.
Duk da a tsorace take da wahalar da tasha ɗazun a hannunsa da safe, ga yanayin da yake ciki. Jinta kwance a jikin nashi ga fuskarta akan tashi tana shaƙar ƙamshin mayen turarentasa na barci da ko'a baya yana da matuƙar tasiri a gareta balle a yanzu kawai ta samu kanta da rungune shi sosai. Duk da kanshi ya fara juyewa irin na wanda yasha ƙwaya saƙon Nabeeha bai gagara tasiri a jikinsa ba, har takai ma ya riƙota shima da irin riƙo na sallamawa. Sai dai ƙarfinsa ya fara rauni. Amma hakan bai hanashi son biyama gangar jikinsa da zuciyarsa muraddinsu ba.....
÷÷÷÷÷÷÷÷÷÷÷÷÷
Faro daya tabbatar idan Dadah yaga saƙonsa zai kira ya ƙara jujjuya wayar cike da ƙosawa. Tun yana ƙirgen sakanni har ya koma mintina. Ganin fa kamar wasa wankin hula zai kaisu dare kawai ya danna masa kira. Ina harta tsinke babu amsa. Ya sake gwadawa a karo na biyu. Amma nan ma ba'a ɗaga ba.
(Mike faruwa. Yasan Haysam akan aiki. Kuma ɗazun yayi waya da Imran akan yau zasu kama Ojo. Ya kuma san Imran zai sanar masa) Akalar kiran ya maida kan Imran. Cikin sa'a bugu ɗaya ya ɗauka. Faro ya sauke ajiyar zuciya. Ko gaisuwa basu tsaya yi ba ya ce,
“Imran halan ka manta baka faɗama Boss muna bakin aiki ba?”.
“Ah. Na faɗa masa mana. Miya faru?”.
“He didn’t pick my calls seven times.”
“Oh my God. Inaga ciwon kan ne. Dan babu jimawa muka rabu da shi. Yan zu wani abu ya faru ne?”.
“ALLAH ya bashi lafiya, akwai matsala kam gaskiya. Dan guy ɗin nan fa baya gidan nan. Sai wasu mata da muka samu. Sun tabbatar mana kuma ya kai sati biyu ma baya nan”.
“Mata! Su kuma su waye to?”.
“Humm garkuwa yayi da su. Sunce kuma ana fita da wasu ma. Sannan ana shigowa da wasu. Sai dai basu san ina ake kaisu ba.”
“Lallai akwai matsala. Yanzu dai idan kuka bar yaran nan da nufin masa tarko bamu sani ba ko ya gane ana bibiyarsa ne ya bada ƙafa. Idan aka kwaso su kuma nan ma akwai matsala. Tunda zata iya yiwuwa bai sani ba kaga mun bashi haske. Zaɓi ɗaya ne damu yanzu. Idan akwai maɓoya wasu a yaran su nema a dakaci zuwansa. Mu kuma nan ka dawo mu kafa sabon binciken sanin ina yake a yanzu”.
Baza'a rasa mafaka ba, duk da itama zata iya zama mai haɗari. Dan tunda yazo ya kafa wannan gidan a jeji babu yanda za'ai ace bai san sirrin wajen ba. Sai dai bamu da zaɓin daya wuce hakan.”
“In sha ALLAHU mune da nasara”.
“ALLAH yasa. Sai ka jini”.
Daga haka Faro ya yanke kiran.
Imran da zancen Dadah ya tsaya masa a rai shima layin nasa ya fara kira. Dan yasan ƙarfe tara da wani abu baza'a ce dai ya kwanta ba. Dole akwai dalili. Family layinsa ya kira. Ga shi dai tana shiga amma ba'a ɗaga ba shima har sau uku. Sai yaga kawai bari su bashi lokaci zuwa anjima koma safiya....
★___________★
Kuka sosai Nimrah tayi bayan wucewar Dadah. Dan wani irin nauyi taji zuciyarta ta mata. Ga ƙunci daya mamayeta. A sati biyu ya saba mata da abubuwa da yawa da take jin shaƙuwarsu ƙololuwa. A yanzu bata ƙi su yini tare su kwana tare ba tana ganinsa a kusa da ita. Sai dai tasan hakan yaudarar kanta take. Dan dole ta raba shi da wata. Dole akwai ƙa'idar da zata ganshi yanzu. Wataran ma ƙila ta kwana ta yini bata ganshi ɗin ba.
Tabbas ta jinjina ma mata masu abokan zama. Dan yanzu ta fahimci abinda ake kira da kishin. Sai ma ta ɗan ji zata iya sassautama Nabeeha dan wlhy tayi namijin ƙoƙari. Sai dai hakan ba yana nufin zata bar mata Dadahn bane. Dole ne su zuba mai sa'a ya ɗauki kambu. Amma in har bata shiga huruminta ba itama zata kauda kanta ta barta da halinta kawai. Idan kuma har ta kasa riƙe girmanta ko tace zata cigaba da raina musu Mammah to anan fa ne tsakaninsu babu ragi babu ragowa. Dan an taɓa abinda bazata iya kauda kai ba............✍️
107
........Yana shigowa sashensa da fuskar Nabeeha da ke zaune tana lissafin mintuna ta cika fam ya fara cin karo. Shi abin ma sai yaso bashi dariya. Bai dai yi ba, sai ma a ransa ayyanawa yake (Dole maza masu mata da yawa su samu hawan jin.....)
Tunanin nasa ya yanke, sakamakon isowar Nabeeha inda yake. Da farko kamar zata rungumesa sai kuma ta tsaya cak. Yanda ta buɗe hanci tana shinshinarsa kamar wata mage dake son gano inda kifi yake yasa shi fahimtar ta. Sai dai kafin ma yay magana idonta ya ciko da ƙwalla. “Amma kana ganin hakan adalci ne? Ni ce da kai kaje kana kasancewa da wata?”.
Shi dai kallonta kawai yake, sai kuma ya kawar da kansa yana kallon agogon hannunsa. Kafin ya sake maido idanun nasa kanta. Sai kuma ya ɗan duƙo kansa saitin kunnenta. “Ita wadda ta kawo miki gulmar bata haɗa miki da lokacin shigowata bane?”.
Cike da takaici ta ce, “Koma dai miye ai sai ka dinga jin tsoron ALLAH. Kun je kunyi sati biyu bance komai ba. Kun dawo ɗin ma nawa lokacin da ita zaka raba”.
Fuuu tai shirin barin wajen. Hannunta ya riƙo ya maido ta gabansa. Batare da yayi magana ba kawai ya rungumeta. Zazzamewa ta shiga yi da sake faɗin, “Ni sake ni. Kaje ka gama rungume wata banza zaka zo ka samin wannan ƙazamin turaren nata a jiki.”
Sakin nata kuwa yayi, bai kuma sake cewa komai ba ya raɓata zai wuce. Karaf kuwa sai idonta akan wuyansa dake zane da shatin lips ɗin janbakin Nimrah. Saukar hannunta kawai yaji akan wuyan nashi, ta shafo jambakin tana nuna masa. Da rawar murya ta ce, “Oh har saƙo ta baka kazo min da shi?”.
Dadah ya kai hannunsa saman goshi ya murza da ƙarfi. Shi bai san tsakanin Nimrah da Nabeeha ɗin ma wake son maida shi mahaukaci ba kam. Rashin abin faɗa ya sashi zagayeta kawai ya cigaba da tafiyar sa.....