Sashe 68
Sakar Makafi Part 3 Complete Hausa Novel · about 7 min read
..........“Uhmm lallai, kice ɗan mutan Kobi zai shiga one chance...”
Cikin sake ɗaga murya Nabeeha ta sanya dariya, kafin ta ce, “Fiye da wanda ka shiga kuwa a shekarun baya. Ai kai shalelena ne. Yanzu kuwa ɗan shagwaɓa zaka koma”.
Nimrah ta cije lips, batare da zato ko tsammani ba kawai ta ɗago fuskarta tana kallon Dadah. Ido suka haɗa, ta wani juya masa su cike da salon da ita kanta bata san tama iya ba. Ya wani ɗan ɗage gira alamar ni ɗin. Sai ta ɗan murguɗa baki. Mitsitsin murmushi ya suɓuce masa. Idanunsa ya janye tare da motsa lips da nufin bama Nabeeha amsa kawai yaji saukar lips ɗin Nimrah akan haɓarsa ta sakar masa sumba mai sauti a tattausan gashin gemunsa. Dan ɗiɗɗishe tayi ma saboda tsabar neman magana harta kai dan ya fita tsaho. Ido ta rufe ta sake ɗiɗɗishen da ƙyau tana kuma sauke lips ɗin akan nashi tai musu wani kalar sha ɗaya ta janye da sauri.....
Cak kuwa bakinsa ya kasa motsi saboda mamakinta. Alamar yama fara mance waya yake sai ya fara ɗan takawa ya matsa inda take. Dan tana bashi sumbatar ta wani ja jikinta baya ta raba jikinsu ita a dole kunya take ji. Dan kanta ta duƙar ƙasa, itama bayan ta sake ja, ya sake matsawa ya bita, sai da ta dangane da jikin gilashin shi kuma ya ɗora hannunsa a jiki tare da matse mata waje sosai sannan ya furta, “Ki saka wayanki a caji zan kira can”.
Kafin Nabeeha tace wani abu ya yanke wayar, cikin aljihu ya tura wayar ya kamo haɓarta ya ɗago fuskarta. Tuni ƴar tsuntsuwa mai neman magana taji zuciyarta na gudun ceton rai irin na ɓarawon da aka tarfa za'a kama a cikin ƙirjinta.
“Duk yunwar ce za'a cinye min lips?”.
Idanunta dake a rufe ta ɗan matse. Kunya mai tsanani ta mamayeta. Dadah ya hura mata iska akan idanun ta yanda dole ta buɗesu. Idanun na shiga cikin nashi ta sa hannu zata rufe fuskar. Hannunwan ya riƙe. Ta re da faɗin, “Ba wannan maganar Little Tiger. Dole ki ƙarasa abinda kika fara. Dan Haysam Abdul-rasheed Shehu Kobi bai san tsokana ba. Karatun farawa da gamawa har ƙarshe kawai ya sani”.
Nimrah gaba ɗaya zuciyarta ta karye. Da ƙyar ta iya ɗaga ƙafafunta da sukai mata nauyi ta gyara tsaiwarta. Cikin rawar murya da ƙunƙuni, ta sami kanta tana furta, “Ni Dadah banyi komai ba fa, sai dai in aljanu na ne suka zo”.
Da ƙyar ya danne murmurshin dake neman suɓuce masa, ya tsaya yana kallonta da mamaki idanunsa masu ɗauke da ƙarfin iko da kulawa na sake narke mata da silale sauran ƙamshinta. Ya ɗan karkatar da kansa kaɗan, ya ƙara shanye girman idanun a kantan dai. A hankali, ya furta, “Humm aljanun nan zasu sa na ajiye tausayi ashe, na yi ma waɗan nan gasassun ƴan shilar da daɗinsu ke saka aci har ƙashi haɗiya irin ta mayunwacin zaki.”
“Lah ai sun fita ma yanzu”.
Ta faɗa fuska a shagwaɓe tana wani kif-kif da idanu.
“Are you sure…?”
Ta jinjina kai a hankali.
Idanunsa suka tafi kamar zasu lumshe, sai kuma ya buɗesu yana mai sake kai fuskarsa gab da tata. A wani irin hankali ya sauke lips ɗinsa a kan nata. Kamar yanda tai masa yayi, sai kuma ya janye yana ɗora goshinsa akan nata. Cikin raɗa ya ce, “Wannan ya isa yau…?”
Hannu tasa ta sake rufe fuska tana jinjina masa kanta alamar (Eh).
Bakin nasa ya matsar kan kunenta. Da murya mai bala'in shigewa maƙoshi ya furta,
“Ni kuma ya mun kaɗan dan ina jin yunwar ƴar shila sosai”.
Siririyar dariyar da bata shirya ba ta saki. Har yanzu hannunta nakan fuskarta ta furta, “Ai ba abinci bane”.
Hannunsa ya sauka a ƙugunta. Ya matsota da manneta da jikinsa sosai dan har sai da taja numfashi da sassarfa.
“Da abinci ne da kaf zan cinye batare dana rage ko kaɗan ba saboda daɗinsa. Amma shi ɗin ma ina gama buɗe masa ido sai na.....” ya ƙarasa faɗa a cikin kunnenta da raɗar da nima Bilynku ban jiyo ba.
“Wayyo Dadah ni dai karka kurumta ni”.
Ta faɗa tana fisge jikinta da gudu tabar wajen. Shi kansa baima san ya saki ƙaramar dariya ba yana sauke hannunsa kan gilas ɗin kansa a duƙe.
“Ga tsoro ga jan faɗa”..
Ya faɗa akan lips yana barin wajen....
✓✓✓✓✓✓✓✓✓
Zufa ta lulluɓe Nabeeha da furucin Dadah mai kama da bugun guduma. Sautin sumbatar da Nimrah tai masa ya shiga maimaita kansa a cikin kunne da zuciyarta tamkar ƙarar nakiya mai saka ƙasa girgiza. Yanda haƙoranta ke neman fara gab-gab na rawa dole ta fisgi ɗan kwali ta tura cikin bakin. A maimakon ihun dake neman kufce mata sai hawaye. Wayar ta wurgar tare da tashi da gudu ta nufi bayi. Dai-dai kuma nan Ismat da taji shirun yayi yawa kusan mintina arba'in ga Mu'azz na jira ta biyota. Mamaki ya kamata ganin bata a ɗakin. Sai kuma cike da ƙunƙuni ta ɗauka wayar kawai ta fita.
Mu'azz dake tsaye a inda yake tun ɗazu ta miƙama wayar tana godiya. Shi dai kansa kawai ya jinjina ya juya ya fita. Dan a wuya yake da abinda Rayhana da Amimah suke masa tun ɗazun. Da ƙyar ya iya kai zuciyarsa nesa bai bubbuge shegu ba duk da sun girmesa. Kai a haihuwar kaji ma sun haifesa. Dan tsoffin guzumaye ne kawai ba aure sai yawon clubs.
Yana fita Ismat ta hau yi musu masifar abinda sukai ma Mu'azz ɗin. Suma suka hayayyaƙo mata, a take faɗan daya sake tunzura Nabeeha ya ɓarke a tsakaninsu. Sai ko gata a fusace ta fito a ɗakin. Dukkan takaicin da Nimrah ta zuba mata da ƙaiƙayi koma kan masheƙiya daya sameta ta hau juyewa a kansu. Dan haukace musu tai su shirya su barmata gida suna damunta.
Ismat da Amimah dai shiru sukai, sai Rayhana ce ta yaɓa mata baƙar magana cike da rashin kunya.
“Humm lallai Aunty, mune yau kuma kike kora a gidan da kema baki da wani power ɗin zamansa? Da dai kin barmu koba komai muna ɗebe miki kewa kafin ƴan Dubai su gama cin amarci su dawo....”
Ai batama rufe baki ba Nabeeha ta kai ma wuyanta shaƙa. Ta turata kuma ta matse da bango. Hankalin su Amimah ya tashi matuƙa. Dan lokaci ƙanƙani idannunta suka juye jikinta ya hau rawa. Ba ƙaramar shaƙar ta Nabeeha da alamu suka nuna bata cikin hayyacinta tayi ba. Da ƙyar da haɗuwa su uku harda Nanah da ihunsu ya sata shigowa a guje suka ɓanɓare Rayhana a hannun Nabeeha. Aiko kamar wadda ta suma sai gata yaraf a ƙasa jiki na rawa. Dan Rayhana irin muguwar siririyar nan ce dai masha ALLAH. Sannan bakin ne kawai babu ƙarfi.
Ruwa Nanah ta kawo mata. Da ƙyar suka samu ta sha tana fidda numfashi da sassarfa hannunta a wuya. Sai da ta ɗan dawo hayyacinta Amimah taja Nabeeha zuwa ɗaki ita kuma Ismat na ma Rayhana fifita Nanah ta zare jikinta ta fice. Da ɗan gudu-gudu tana waugen bayanta ta shige cikin ɗakinta. Jikinta har ɓari yake ta ɗauka waya tai kiran First Lady tana labarta mata komai daya faru.......
^°^°^°^°^°^°^
Tunda Dadah ya dawo ya zauna Nimrah bata yarda ta kallesa ba. Tama wani basar idonta a television. A kujerar da dai suka tashin take, kuma inda take a da kafin taje neman magana.
Shima inda ya tashi ya zauna. Sai dai yanayin nashi zaman ya canja a yanzu. Dan ya zauna ne ƙafarsa ɗaya a kujerar ya miƙe, ɗayar kuma a ƙasa ajiye. “Zo ga abincin”.
Ya faɗa cikin rashin wasa dan bai so tai gardama. Duk da yasan da wuyama hakan ta kasance. Bako tayin ba kamar yanda yay hasashe, dan tsam ta miƙe da filon data rungume a jikinta.
“Dadah ka fara kira min Rukyn sannan to Please”.
Kallonta yay cikin ido. Ta taɓe baki da turashi tana ƙiƙƙifta idanu. Sai kuma ta fara ɗan bubbuga ƙafafu kaɗan-kaɗan ta ce, “Dadah Please kai ne fa kayi alƙawari. ALLAH ina jin kewarta sosai. Idan banyi magana da ita ba hawan ruwa zai kama ni”.
“Ina da maganin sauke shi ai.” ya faɗa yana kamo hannunta ta zaunar a kujerar a gabansa bayanta na jingina da ƙirjinsa. Bata nuna zata tashi ba, shima sai ya cigaba da faɗin, “Ko kin manta ni likitan Nimrah ne”.
“Ba wani likitan Nimrah. Ni wlhy Dadah ma baka ji dani yanzu. Kawai ka maida ni wajen Mammah mai shagwaɓani, mai gatantani. Mai riritani. Mai.....”
Wani kalar juyo da ita yayi kafin ta kai ƙarshe, kawai ya haɗe lips ɗinsu ya shiga bata wata azababbiyar, zazzafar sumbatar data saka jikinta rawa kar-kar-kar. Sosai ya sake manneta da jikinsa ta yanda bazata suɓuce masa ba.
Komai ya tsaya cak, ta yanda zukatan guda biyu ke gudu a cikin ƙiraza. Musamman ga Nimrah da komai ke zuwa mata a farin shiga. Farin shigar ma irin ta sabon ɗalibi a ranar farko ta zuwa makaranta. A hankali ta fara jin jikinta yana saki sannu-sannu. Zuciyarta dake cinkushe a mintuna kaɗan ɗazu ta fara warwarewa kamar an cire mata wani nauyi da bata san tana ɗauke da shi ba...........✍️
84