Sashe 102
Sakar Makafi Part 3 Complete Hausa Novel · about 4 min read
...Nimrah ta fara girkinta mai sauƙi da zai mata sauri kuma kiran Dadah ya shigo mata. Murmurshi tayi tare da ɗaukar wayar ta fito a kitchen ɗin saboda ta riga ta kunna gas. Kujerar dining taja ta zauna tana kai wayar kunenta..
“Assalamu alaikum”.
Dadah da ransa yake a jagule ya amsa murya a maƙoshi. Nimrah sarkin wayo, kai tsaye ta fahimci wannan asalin Dadah ne ba mijin Nimrah ba. Nitsuwa ta yafama kanta. Cikin tsantseni ta gaishe shi.
Nan ma a taƙaice ya amsa mata, shiru na sakan biyu sai kuma ya ce, “Sai yanzu kika tashi?”.
“A'a tun ɗazun, kusan awa ɗaya da rabi. Ina kitchen ne ma yanzu?”.
“Mi kike dafawa?”.
“Ɗan waken fulawa”.
“Harkar kwaɗayi ko?”.
Ta ɗan sosa gefen wuyanta tana murmurshi kamar tana a gabansa. Shima jin tayi shiru sai sautin murmurshi ta kawai yake ji ya ce, “Shike nan, ince abin arziƙi ne ki haɗa dani. Bari na kira Mammah su nasan basa rasa abinci....”
Da sauri Nimrah ta ce, “A'a dan ALLAH Dadah karka kirata. Indai zaka ci ne bari na canja, ruwa kawai nasa a wuta”.
“No yi abinki”.
Cikin shagwaɓa kamar zatai kuka ta ce, “To dan ALLAH na maka wani abu? Wlhy dama na gaji da zama ba aiki”.
Shiru kamar bazai amsa ba. Sai kuma a dake yace, “Kiyi mara nauyi.” daga haka ya yanke wayarsa. Baki ta tura kamar yana gabanta. A zuciyarta tana faɗin (Dadah zuma ga zaƙi ga harbi) da wannan tunanin ta tashi ta wuce kitchen ɗin. Sai da tai ɗan nazarin miya dace ta masa tunda yace mara nauyi sannan ta ɗora. Tare da kwaɓa garin ɗanwakenta shima kaɗan ta saka. Kasancewar aikin nata bamai yawa bane bai jata lokaci ba ta kammala. Duk da yunwar da take ji har jikinta na ƴar rawa-rawa haka ta daure ta haɗa masa komai, tunanin kawai ta tafi da nata ɗanwaken ya sata haɗawa a ƙaramin kwano ta wuce a haka batare da tunanin canja kaya Ko saka gyale ba....
::::::::::::::::::::★
Dariya sosai irin ta mugunta First Lady keyi da ganin kaf dukiyar Hajiya Hasiba a hannunta. Tare da documents ɗin nata kaddarorin data jima tana bata ajiya saboda irin wannan ranar. Ita ko wawiya tana murna da tunanin tsabar yarda ce hakan. Sai wayarta da itama tasa Adeel ya ƙwamuso mata. Dan duk abinda yayo tamkar umarni ne daga gare ta sakamako gubar asiri data gama turare masa jiki da ita. Sannan aka bashi wata ya sha a lemo. Banda Wadda aka dinga aika masa tuni daga bokayenta kala-kala. Dan babu arziƙi ya baro harkokin business ɗin sa dan zuwa cika umarnin ta.
Cike da kissa da kisisina duk da abinda tasa ta masa ta gyara zama da faɗin, “Ranka ya daɗe yanzu ya batun naka dukiyar? Musamman gidan daka bata a Dubai”.
Adeel da idonsa ke rufe da asiri kai tsaye ya ce, “Ki riƙe na baki”.
“Woow da gaske?”.
Kansa ya jinjina mata. Aiko ta sheƙe da dariyar daya sashi zuba mata ido. Gashi yana jin wani nauyi da zafi a zuciyarsa yanda take control ɗin sa amma a zahiri ya kasa iya koda nuna fushi. Haka ta sashi a gaba ta gama shaƙiyancinta sannan ta ce, “Shike nan aikinka ya ƙare yallaɓai. Zaka iya komawa inda ka fito. Sai kuma mun haɗe a fannin business”.
Tamkar wani soko ya jinjina mata kai. Sai kuma ya miƙe suƙuy-suƙuy kamar tsohon raƙumi ya fice. Ai ko ta sake kwashewa da dariya. Sai kuma ta ɗauka waya tai kiran Mamawo. Mamawo dake asibiti dole ta lallaɓa ta samu waje ta laɓe sannan ta ɗaga.
“Humm ranki ya daɗe muna asibiti ne fa mutuniyarki ba lafiya. Da alama abinda Adeel yaje ya aikata ne ya gigitata.”
Dariya First Lady ta sanya. Cike da isa ta ce, “Wa yace dani ba ni ba, nima nace da shi ba shi ba.”
Mamawo tace, “Humm” tana murmurshin yaƙe. First Lady da bata san tanayi ba ta cigaba da faɗin, “Zaki iya zuwa ki amshi naki documents ɗin, tare da tukuycin aikin ki”.
“Ina godiya ranki ya daɗe. Sai zuwa anjima dai dan yanzu kar yara su ji babu daɗi idan na taho. Shi kuma zancen Adeel ɗin fa ranki ya daɗe? A taimaka dan ALLAH mana. Wlhy yanzu duk duniya babu abinda nafi so kamar naga ya auri Rayhana..”
Murmurshin basawa First Lady tayi. Cike da isa ta ce, “Tukunna dai bamu zo wannan matakin ba. Sai kin cika sauran aikin ki”.
“Baki da matsa maa. Ki bani kwanaki kaɗan”.
“Yayi”..........✍️
117