← Book details Sakar Makafi Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 104 OF 113

Sashe 104

Sakar Makafi Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read

.........Yana shirin shiga wanka Nabeeha data biyo shi ɗakin tai sallama ta shigo. Bai ko nuna ya san da shigowarta ba balle amsa sallamar tata ba yay shigewarsa bayin. Sororo ta tsaya tana kallon ƙofar bayin, zuciyarta na mata zafi dan har yanzu ranta a ɓace yake. Tsabar yau yanda take jin sai ta sauke masa abinda ke cikinta tas ko zama ta kasa yi. Tsaye tai a bakin ƙofar bayin tamkar bodyguard tana jiransa. Shi mutum ne mai jimawa a wanka, dan haka har ƙafafunta suka fara mata dayi bai fito ba, amma haka ta daure ta cigaba da tsaiwar.
         Yana buɗe bayin da ita ya fara cin karo tsaye ta riƙe ƙugu da hannayenta. Baima sanda ya ayyana a ransa (Dambe zamu fara kenan) ba. A zahiri kam fuska ya sake tamkewa ya ɗauke kansa. Ganin zai raɓata ya wuce tai saurin shan gabansa.
      “Haysam wlhy sai ka saurare ni. Duk ma wacce zamuyi yau sai munyi.”
     Cikin ɗan zuba mata ido da motsa lips kaɗan ya furta, “Dawa zakiyin?”.
         “Da kai, wlhy da kai zamuyi Haysam akan wannan shegiyar yarinyar ƴar tsintuwa mai kama da kazar mayu. Yanda baka ji kunyar tuɓewa a gabanta ta ganka a Haysam ɗinka ba, nima bazan ji kunyar cin ubanta ta gane ni ba sa'arta bace. Karuwancin t.......”
       Ruff taji an matse mata baki kafin ma ta ƙarasa faɗa. Azaba ta sakata zazzaro idanunta waje tana kai hannu tana kokawar ture nashi. Ko gezau dan mazan rainon SOJA ne fa. Cike da baƙar mugunta irin ta sojoji yake murza lips ɗinta daya matse a tsakanin yatsunsa biyu. Sai kuma ya kai ɗayan hannun ya damƙe kunnenta na dama shima. Wata kalar zabura Nabeeha tayi sai ga hawaye ɓul-ɓul. Jikinta karkarwar azaba yake yi.
       Tafiya ya fara yi da ita a haka har gaban gadonsa. Jikinta ya ƙara ƙarfin rawa, dan tasan muguntarsa ta bala'i a wannan fanin musamman idan tai masa laifi. Ƙarfin buge-bugenta ne ya ƙaru. Dan bazata yarda ta hau gadon nan ba. Sai dai itama ta sani, bata da ko kwatar wannan ƙarfi a yana farin ciki ma ballantana fushi. Yakushi da mintsini ta fara kai masa masu azabar zafi amma a banza wai an tsikari kakkausa. Yana kaita gaban gadon yasa ƙafa ya taɗe ƙafafunta ta zube akai wanwar. Da yake su Dadah an ƙware da iya mugunta har lokacin bai saki kunnenta da lips ɗin nata ba kuwa....

   ....Sam kukan ma ta kasa yin mai ƙarfi. A haka Dadah ya sake fitowa a bayi yana nason ruwa alamar sabon wanka yayi. Ko kallon inda gadon yake baiyi ba duk da yanda shashshekar kukanta ta cika ɗakin. Tsaf yay shirin fitarsa. Yana tashin ƙamshinsa da taku ɗai-ɗai ya ƙarasa kusa da gadon a bedside drawer ya ɗauka agogonsa. Ya ɗaura sannan ya ɗora ƙafarsa ɗaya dake nan tas-tas kamar ka lashe a saman gadon. Cikin kaushin murya ya fara maganar data saka Nabeeha runtse idanunta.
          “Wannan kaɗan nai miki idan kika cigaba da bijirema gargaɗina akan ɗaga muryarki a kaina musamman a gaban yarinyar nan. Yanda zata rainaki kuma ki cigaba da koya mata kada ki fasa dan ALLAH. Duk kuma randa kika zo da batun ta fara maida miki murtani zan baki mamaki. Ina miki gargaɗin da kiyi tsakanin ni da ke kawai duk zan iya ɗauka amma kada ki fanɗarar min da yarinya ta fara ɗauka abin arziƙi kike yi ta koya. Sannan fita babu neman izini daga yau na yanke ta. Idan ba haka ba, wlhy! Wlhy! Wlhy kinga uku kenan. Idan kika ƙara zan baki mamaki. Duk da wannan baya cikin tsarina. Idan kunne yaji, jiki ya tsira. Ki kuma tashi ki gyara min ɗaki tas. Abu na ƙarshe kowacce ku zata dinga kwana biyu da ni. Daga huɗu na la'ar duk wadda take dani zata ajiye duty ƴar uwarta ta amsa a ranar cika kwana biyu kenan..”
      Yana gama faɗa ya sauke ƙafarsa. Ko kallonta bai sake yi ba duk da yanda ta fashe da kuka ya kaɗa kansa yay tafiyarsa. Itama Nimrah ɗin ko kallon sashenta baiyi ba ya kaɗa kansa ya fice. Ya zata ma zai sameta a sashen Mammah. Sai ya samu sai su Shariffa kawai. Sai Hanoon da tunda ya shigo ta zuba masa idanu kamar tsohuwar mayya. Shi ko duk da ya ganta uffan baice akanta ba. Bai ma nuna a fuska yasan da ita ba.
        Bai jima ba ya fito, sai dai a ransa yayi mamakin rashin ganin Ruky da Nimrah a sashen. Hakan na nufin koma ina suke suna tare. Kwarai kuwa Dadah suna tare. Dan tun da tabar sashensa kitchen kawai taje ta ajiye basket ɗin kayan da yaci abinci ta ɗauki ƙaramin hijjab data ajiye a falo tai ficewarta. Sai da ta fara zuwa ta gaida su Mammah sannan ta gudu sashen Ruƙayyan. Suna can abinsu suna hira, dan Ammar ya fita a gidan uzirinsa tun ɗazun.....

       ÷×÷×÷×÷×÷×÷×÷

    Su Dabo dai sunyi ram da su Malam Almu. Sai dai kuma ganin wanda ke tare da Malam Almu ɗin ya sake rikita lissafinsu. Musamman ma Faro dan Dabo da Yusuf da T-Dalha duk basu sanshi ba su kam.
       Kaf gidan sai da suka bincike. Amma babu komai daya shafi ta'addanci. Hasali ma zuwa kawai ake a kwana a cikinsa. Idan ma da wani abu mai amfani sai dai wanda baza'a rasa ba. ALLAH sarki Malam Almu duk ya rikice. Sai sharar hawaye yake da rantsuwar shi ba mutumin banza bane. Ogan nasu kuwa babu alamar damuwa a tare da shi, sai dai ya kasa haɗa ido da Faro daya tsare shi da idanu.
        A UNIT ZERO suka samu Daddy Imran na jiransu. Shi ma Imran ya girgiza da ganin Ogan su Malam Almu. Dan cikin kasa ɓoye mamakinsa har sai da ya furta, “Musbahu! Dama kana raye?”.
          Kansa ya risinar kawai hawaye na cika masa idanu. Sai kuma a hankali ya jinjina kan. Daddy Imran ma sai ya kasa sake cewa komai. Ƙarshe ma yay shigewarsa falon gidan kawai dan gaba ɗaya ya gama shiga ruɗani. Su ko su Dabo suka tisa ƙeyarsu zuwa ɓangaren da ake ajiye irinsu.

      Sai da sukai kusan awa ɗaya da rabi da shigowa sannan Dadah ya iso gidan a ƙaton sabon mashin ɗinsa. Yanda komai nasa ke a rufe yasa shi kasancewa a ɓadda kama. Guri ya samu ya kafe mashin ɗin, kafin ya fara cire hular kansa. Hakan yayi dai-dai da isowar Dabo wajen da sauri. Hular ya amsa yana masa sannu da zuwa. Ya jinjina masa kai kawai yana ƙoƙarin barin wajen. Dabo ya take masa baya. Kaida ka gansu kaga cikakken Boss da yaronsa na amana.
      Tun a yanda ya samu Faro da Imran jigum-jigum yasha jinin jikinsa. Bai dai ce komai ba ya kai zaune. T-Dalha ya fara gaishe shi da girmamawa. Kai ya jinjina masa kawai. Faro da Yusuf ma suka miƙa gaisuwa. Imran kam sannu da zuwa kawai ya masa. Dan gaisuwa kam babu kalar wacce basuyi ba da ga safiya zuwa yanzu.
          “Mike faruwa?”.
     A karo na farko Dadah ya faɗa da murya mai zurfi.
      Imran ya ce, “Humm miye na bai faru ba. Wai kasan dawa muka samu Malam Almu?”.
      Dadah baiyi magana ba, amma yanda ya zubama Imran ido zaka gane shi yake saurare. Imran ɗin ma sai ya cigaba da faɗin, “Musbahu fa!”.
         Da alama ma dai Dadah ya mance waye Musbahu. Dan haka kai tsaye ya furta, “Waye haka?”.
       “Musbahu Shanshani aminin Garba na NDA dai daka sani”.
      Dadah ya wani ɗan ƙanƙance idanu. Dan kai tsaye ya gane Musbahu ɗin saboda yana ɗaya daga cikin mutanen da bazai manta ba a rayuwarsa. Ba saboda ya riƙe su bane akan abinda suka aikata masa a baya. Sai saboda yana kallonsu a matsayin tubali na biyu na nasarar rayuwarsa bayan dangin mahaifinsa. Dan shi Dadah duk wanda ya zaluncesa ko cutar da shi, yana masa kallon tsanin da ya dinga takawa ne step by step na isowa wannan lokacin. Saboda babu babban gishirin zaman duniya irin maƙiyi. Masoyi kullum haskenka yake gani, sannan farin ciki yake ƙawata rayuwarka da ita. Shi ko maƙiyi zaluncinsa ƙara ɗaga darajar ka yake, dan wani ma a dalilin wannan ƙiyayyar yake fara sanin waye kai har ya fara sonka shima...
      Ya furzar da numfashi mai nauyi. Dan tabbas a wannan ɓangaren an sake bashi ƙafa. Dama duk baiwarka UBANGIJI na baka ikon sanin abinda yake son ka sani ne kawai. Sai ya ɓoye maka wasu domin ya sake tabbatar maka kai fa ɗan Adam ne, sannan bawansa mai rauni....
           “Ku kawo min Malam Alamu”.
     Ya faɗa cikin kawar da tunaninsa kawai. T-Dalha da Dabo ne suka miƙe. Babu jimawa suka dawo da Malam Almu da ya gama fita a hayyacinsa. Yana kuma cin karo da Dadah ya sake gigicewa. Dan a take ya fara rawar mazari tamkar wanda yay gamo da wani Dodo ko mayuncin zaki mai haɗari a dokar jejin daba gida gaba babu baya. Dadah kuwa ya kafe shi da idanunsa masu ladantar da kowane shege. Idan ma baiwa ce tabbas ALLAH ya bashi a cikin idanu. Dan hatta Daddy Imran idan ya tsare shi dasu yakan ce, (Malam daina kallona da idanun nan naka masu kama dana kumurcin maciji). Dadah kan hararesa ko ya ɗauke idanun kamar bai jishi ba............✍️
119
Chapter 104 · 0% Book details