Sashe 113
Sakar Makafi Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read
.........“Naja'atu yau gaki ga Kawun ki. Baƙya buƙatar a sabunta miki matsayinsa ko darajarsa a gareki. Hakama soyayyarsa dan kin tabbatar mana da ita kika girma Alhamdullah. Ina da buruka masu yawa game da ahalinki. Ga ɗaya a ciki na fara cikawa. Kuma in sha ALLAHU wanda zasu biyo baya ma zan cika su. Duk wanda suke anan suna da muhimmanci a gareki, dan haka zan faɗa a gabansu. Ke AMANA ce a gareni, kuma in sha ALLAHU zan kamanta riƙewa gwargwadon iko na. Nasan na tauyeki kwarai da gaske a shekarunki ba miji irina kike buƙata ba. Mai irin shekarunki ne, dan haka ina baki haƙuri, ina kuma bama Kawunki akan tauyeki da nayi. Banyi haka domin zalunci ba, UBANGIJI ya ƙaddara hakanne kawai....”
Cike da wauta da suɓutar baki Nimrah dake share hawaye tace, “Nidai Dadah ba wani zalunci. Kai nake SO ba wani yaro ba hu'umm”.
Bata fahimci tsiyar data tafka ba sai da takai ƙarshen maganar tata. Ganin yanda Mammah ta kauda kai tana murmurshi. Haka ma Kawu da Daddy Imran. Dadah ko tsareta yay da idanu. Sai Gwaggo Khadijah da Kulu ne ke dariya ƙasa-ƙasa.
“Wayyo na banu”.
Nimrah ta faɗa tana miƙewa da gudu ta bar falon zuwa kitchen. Mikwa zasuyi in ba dariya ba. Hatta shi kansa Dadahn sai da ya murmusa yanzu kam har yana sauke ɓoyayyar ajiyar zuciya.
Bayan sun tsagaita Kawu Tanimu ya ce, “Boss babu wani tauye Nimrah da kayi harga ALLAH. Kai da ba wani takwarkwashashshen tsoho ba balle ace. Sannan kaji ma Zakanyata tace ita kai take so ba wani yaro ba. Kuma gaskiya ne kai kafi dacewa da ita fiye da kowa. Sai dai mu cigaba da muku addu'a da fatan alkairi kuma.”
“Wannan haka yake. Banda ma abin Haysam shi ɗin ma nawa yake. Yo ko babansa Jameel ai ya ɗauki ƴar budurwa yanzu ko”. Gwaggo Khadijah ce mai maganar. Dan haka Dadah ya murmusa kansa a ƙasa. Daga nan suka ɗan sake tattaunawa dai irin ta manya. Dan Kulu ma ta miƙe tabi bayan Nimrah....
Da ƙyar suka yarda sukai sallar magriba a anguwar, Kawu Tanimu kuma ya dinga roƙonsu sai sun ci abincin da aka shirya musun. Haka dole suka cin, sai dai Dadah da bai cin ba. Ba kuma wai abincin ne bai masa ba. Kawai shi tsarinsa ne ba ko ina yake cin abinci ba. Kai in dai ma ba tafiya yayi ba zai rantse daga abincin gidan Mammah sai na Imran da Uncle Nasiru, sai ko gidan Baffa. Daga ba nan ba ko sai UNIT ZERO ko idan yayi tafiyar data zama ta kwana ko kwanaki. Koda kuma zai ci sai ya keɓance. Kulu data jima da fahimtar haka sai ta shirya nasa a kwando mai ƙyau..
Bayan sun kammala zasu wuce ne kuma Nimrah ta sanya rigima ita anan zata kwana. Mammah ta nuna mata Dadah da ido. Shi ko da sarai yaga abinda Mammah tayi kafin ma Nimrah ta iso kansa yay ficewarsa yana ƙoƙarin ɗaga kiran Nabeeha dake shigo masa.
Murmurshi Kawu Tanimu yayi kawai, cikin lallashi yace tayi shiru ya tabbatar wataran Dadah zai barta tazo ta kwana. Amma yanzu yayi wuri ai duka tarewanta kwana nawa ne....
Shi ma dai Daddy Imran da Gwaggo Khadijah sun shiga cikin ƴan lallashi. Har Daddy Imran na mata alƙawarin da kansa ma zai kawotan. Da haka dai akaci kanta ta haƙura. Sai dai har suka bar gidan tana sharar hawaye. Shi kuma Dadah dake driving ɗin yayi kamar bai ma san tanayi ba. Sai abin ya ƙara bata haushi..
Mammah data san halinsa tace su biya asibiti, dan ta tabbatar idan ba haka tai masa ba bazai taɓa zuwa duba sutukar tashi ba. Aiko yanzu ma sai da ya ɗago ya kalleta ta cikin mirror. Sai ta kauda kanta kamar bata ganshi ba. Ta tabbatar bazai yi musu ba, dan ba halinsa bane ta bashi umarni ya tsallake. Sannan kodan Nimrah dake wajen nan ma zai matse koda ransa bai so ba.
Aiko kamar Mammah ta sani, ba ƙaramin ɗaurin goro tai masa ba. Amma bazaka taɓa gane hakan a fuskarsa ba. Sai ma tambayar wane asibiti ne da yayi. Mammah ta ɗauka waya ta kira Uncle Nasiru. Shine ya sanar musu asibitin, yace ai baima san zasu zo ba shima yanzu suka wuce gida da Ummu.
Sun iso asibiti na kuɗi mai ƙyan gaske. Nimrah da barci ya ɗauketa daga kuka ya ɗan kalla bayan yayi parking. Kamar zaiyi magana sai kuma yay shiru. Sai kuma su Mammah na buɗe murfi ta buɗe idanu. Dadahn ta kalla, suna haɗa ido ta tunzura baki gaba. Shi ya fara janye idanunsa yana buɗe nasa ɓangaren ya fita. Itama sai ta fita. Jikin Mammah taje ta maƙale tana tambayar miyasa suka zo asibiti?.
Mammah dake goge mata fuska da hawaye suka ɗan bushe ta ce, “Mara lafiya zamu duba”.
Kai Nimrah ta gyaɗa kawai. Mammah ta gyara mata har ɗan kwali da mayafi. Dadah ma sai suka bashi dariya. Sai dai wannan soyayya ta Mammah da su Nimrah na sakashi nishaɗi. Har suka fara tafiya bashi da alamar binsu. Sai da Mammah ta juyo tana faɗin, “Ya kuma ka tsaya Muhammad”.
Magana ta ALLAH ba ƙaramin kamu a wuya Mammah tai masa ba yau. Cikin sake tsumewa da kamewa ya saka wayarsa aljihu yabi bayansu. Da kwatancen Uncle Nasiru suka iso ɗakin. Koda suka tura ƙofar suka shiga sun sami duk su Jiddah zagaye da ita. Harda Nabeeha da bata jima da isowa ba ita da Nanah. Dan kiran datai masa suna gidan Kawu Tanimu izinin zuwa asibitin ta nema. Shi kuma ganin taji gargaɗinsa na ɗazun sai babu musu yace sai ta dawo. Shine ta ɗakko Nanah suka taho saboda abincin da zasu zo da shi.
Su Rayhana ma duk suna nan, dan tuni sun dawo. Hakama Mamawo. Sai mijin Jiddah da yaranta uku daya kawo dan su duba Hajiya Hasiba ɗin. Ɗakin ya ɗanyi shiru ganin su Mammah ɗin a bazata. Sai ma Jiddah ce ta katse shirun cikin fara'a tana musu barka da zuwa. Nabeeha kuwa tunda taga Nimrah ce tare da Mammah ɗin sai ta ɗauke kai tana sake haɗe fuska.
Hajiya Hasiba an farka tun kusan biyar na yamma. Sai dai ko zama bata iya yi. Yanzu haka ma idanunta a rufe suke yaran na fama da ita ta tashi tasha ko tea ne dan samun ƙarfin jiki. Amma ta ƙi sai hawaye da take zubarwa. Cikin rawar jiki Ismat ta tashi tana jawo kujerar da take kai ta bama Mammah, ta sake tada Amimah a ɗayar kujerar ta bama Gwaggo Khadijah. Sai lokacin Mammah ta lura Dadah bai shigo ba. Kallon Nimrah da Jiddah ta riƙe ma hannu tai da faɗin, “Ina Dadan ku?”.
“Mammah bai shigo ba”.
Nimrah ta bata amsa tana kallon ƙofar itama. Sai kuma ta nufi ƙofar ta leƙa. Tsaye ta ganshi yana waya. Sunan Imran kuma da taji ya sata gane da shi ne. A ranta tana mamakin wannan ƙauna. Kalla fa yanzu-yanzu suka rabu amma har an kira wayar juna. Abinda Nimrah bata sani ba kuma Daddy Imran ya kirane yana sanar ma Dadah cewar Hassan ya turo bayanan Musbahu yanzu haka.
Batai magana ba duk da ya ɗago ido ya kalleta tunda ta fito. Sai da ya sauke wayar cikin shagwaɓa da kauda kai gefe ita a dole tana fushi ta ce, “Dadah Mammah tace ka shigo”.
Idanunsa ya ɗan zuba mata. Sai kuma ya ɗan motsa. A zatonta kamata zai yi sai ta koma ciki da ɗan gudu. Mamakinta ya sashi binta da kallo. Sai kuma ya girgiza kai kawai. A ciki ma yanda ta shigo ɗin yasa duk suka kalleta. Banda Mammah dake amsa gaisuwar mijin Jiddah.
Jiddah dai bata munana zato ba. Amma Nabeeha da su Rayhana duk yanayinsu ya canja. Haka kawai sheɗan ya ayyana musu saɓanin tunani. Dan Nimrah ɗin na shigowa da abinda baifi mintina biyu ba Dadah ya shigo. Hatta Mamawo sai da taji ta yarda da abinda ranta ya ayyana. Sai dai abin mamaki kowannensu shigowar Dadan sai da ya nutsu. Mammah da Gwaggo Khadijah ce kawai hankalinsu ke kan Hajiya Hasiba data buɗe ido da ƙyar tana amsa musu gaisuwa da kai saboda tsabar takaici. A ganinta miya kawo maƙiyarta dubata haka da sauri. Dan tasan Hajiya A'isha na cikin wanda zasu fara farin ciki da abinda ya sametan ai. Sai kuma ga Dadah da kowa baiyi zato ba.
Yanzu kam Rayhana ce ta tashi uwawu na rawa ta bashi stool ɗin da take zaune. Amma mi ko kallo bata ishe shi ba ita da stool ɗin. Mijin Jiddah ya iso inda yake daga baki-bakin ƙofa cike da girmama yana masa barka da zuwa. Dan iya nan ya coge. Hannu Dadah ya bashi, duk da yanda Mijin Jiddahn ke noƙewa haka ya bashi shima. Dan matsayin babban yaya yake kallon Dadah sannan waliyyi dan shine ya bada auren Jiddah ɗin.
Cike da zalama Rayhana ta fara gaishe shi itama. Sai ya ɗaga mata kai kawai. Ismat da Jiddah ma suka zo har gabansa suna risinawa da gaishe shin. Hakan yasa itama Amimah tasowa tayi kamar yanda sukayi dan Dadah da yafi ƙarfin wargi. Duk botsare-botsaren Mamawo sai gata tana gaida Dadah da girmamawa. Wannan abu ya ƙonama Hasiba rai. Sai dai babu damar magana dan itama dai kwarjinin Dadahn ya gama cimmata da mamaye ta........✍️