← Book details Sakar Makafi Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 85 OF 113

Sashe 85

Sakar Makafi Part 3 Complete Hausa Novel · about 7 min read

.........Tunda taji ƙugin mashin ɗin ta buɗe ido daga gyangyaɗin da take yi. Zaram ta miƙe da ɗan gudu taje jikin window ta yaye labulen. Duk da dare ne da ita kanta bata san ƙarfe nawa bane sai da ta gane shine ɗin dai. A gaban idonta ya tsallako cikin jirgin. Sai ta bar window ɗin da sauri ta koma wajen ƙofa. A rufe take dan haka ta tsaya jiran ya buɗe.
     Yana buɗewa kuwa ta daka tsalle ta ɗane sa. A bazata ya jita a jikinsa. Dan haka ya ɗan waro idanu yana mai riƙeta da ƙyau gudun kar ta sha ƙasa.
       “Oyoyo Dadah”.
   Ta faɗa da muryar mai jin barci tana zagaye hannayenta a wuyansa. Tare da sauke masa sumba a kan fuska. Ta koma kan lips ɗinsa suma ta sumbata, sai kuma ta sake rungume shi tsam-tsam.
      Dadah dai ya koma saƙago. Na farko mamakin rashin barcinta. Na biyu tarbar daya samu bayan ya barta tana rikici. Na uku ina tsoron da tace tana ji yaje?. Dan yayi tunanin zai sameta ne a takure a bedroom dan ɓuya. Da ƙyar ya fisgo numfashinsa ya ɗaga ƙafafunsa ya ƙarasa ciki da su tana ɗane a jikin nasa ƙamar ƴar biri. A haka ya ɗauka remote ya kashe television da ta saka karatun Alkur'ani. Sannan ya ɗauka wayarsa data ajiye saman table ya shige da su bedroom.
         A saman gadon ya zauna daga baki, hakan ya bama Nimrah dake naɗe da shi damar zama a saman cinyar sa. Ƙafafunta dake zagaye da ƙugunsa ta saki. Cikin dauriya ta ɗago fuskarta tana kallon tashi. Gabanta ya faɗi, sakamakon shigar idanunsa da har yanzu basu washe ba cikin nata. Nata ta rissinar, sai da ƙyar ta aro jarumtar faɗin, “Dadah kana lafiya?”.
     Shiru bai amsa mata ba. Tana kuma jin idanun nasa har yanzu a kanta.
       “Dadah dan ALLAH kamun magana”.
   Ta faɗa hawaye na silalo mata. Maimakon maganar data nema ɗin yatsan sa yasa ya dangwali hawayen nata. Ido ya zuba musu kamar mai son tantance gaskiya. Sai kuma ya murza yatsun nashi suka bushe.
       “Mi ya hana ki barci?”.
    A karo na farko ya faɗa da muryar da sai da yay yaƙi kafin control ɗin ta. Baki ta tura da sake kwantar da kanta a wuyansa tana zagayo da hannayenta bayansa. Baki a tunzure cikin shagwaɓa ta ce, “Ni bazan iya barci ba sai a jikin ka”.
       Wani murmushin gefen baki ya ɗan suɓuce masa. Baiyi magana ba ya sake miƙewa da ita a haka ya nufi bayi. Direta yayi a saman toilet sit dake rufe. Ya juya ya fara tara ruwa a bathtub madaidaici dake bayin. Daga haka ya fara zame kayan jikinsa yana hanging. Tuni Nimrah ta kauda kai Sannan ta runtse idanunta. Ƙaramin towel yaja ya ɗaura dan yana kallon duk abinda take yi. Daga haka ya sake takowa gabanta ya ɗagata tsaye. Kayan ya fara cire mata itama. Zata fara zame-zame ya dungure mata kai. Ko baiyi magana ba gargaɗinsa da ido ma dole a nutsu. Balle akai da dungure kai. Wajen ta shafa tana tura baki. Bai kulata ba ya cire kayan sai dai ta ƙi yarda a taɓa b&p. Shima bai takura ba, ya sake ɗagata cak dan bathtub ɗin ya cika ya shige da su a haka tana jikinsa. Kasancewar ruwan ɗumi ne ga shi yayi kumfa fuuu da sabulan daya zuba sai ta wani lumshe idanunta tana sauke ajiyar zuciya mai nauyi. Yayinda shi ya sauke tashi a maƙoshi...
      Yanzu kam duk yanda taso zamewa bai barta ba sai da ya cire. Duk da a cikin ruwa suke kunya mai tsanani ta mamayeta. Ba shiri ta juya ta rungume shi saboda abinda hannunsa ke aikatawa. Hajjaju Nimrah bata san sabuwar dama ta bama Dadah ba. Dan caraf ya riƙe lips ɗinta a nashi. Daga haka kuma karatun ya sauya.
        Sai da ya tabbatar bakin surutu yaji a jikinsa sannan yay musu wankan da sake ɗauraye su da ruwa mai ɗumi sosai ya kuma yi mata tsarki da wani masu ɗumin suka fito bayan sunyi alwala. Ƙin yarda tayi ta kallesa. Ga barci ya fara rinjayarta amma tasan tunda yasa sukai alwala babu zancen kwanciyar sai sunyi sallar asubahi.
      Hakan kuwa akayi. Sakasu yay suka gabatar da nafila raka'a biyu. Sai suka ɗan zauna jiran asubahi ta ƙarasa kowanne na zikiri. Sai da lokaci ya ƙarasa sannan suka miƙe yay musu jami'in. Suna idarwa ta miƙe ta cire hijjab. Da kallo ya bita, ita ko ma bata yarda ta kallesa ba ta haye gado ta kwanta. Barci take ji na tsiya, ga tsoron abinda ya faru safiyar jiya. Dan haka addu'a take ALLAH ya taimaketa kafin ya kammala azkar tayi barci. UBANGIJI kuwa ya amsa mata. Dan kafin ya gama ɗin tayi barcin mai nauyin tsiya ma kuwa....
      Lokacin daya kammala ya hawo harya zare mata abayarta bama tasan yanai ba. A haka ya sakata jikinsa kamar yanda yafi buƙata ya ja musu duvet. Addu'ar barci yay musu. Dan wannan ɗabi'arsa ce koda a barcin rana sai yayi addu'a yake kwanciya. Daga haka ya lumshe nashi idanun hankali kwance tamkar ba wani gagarumin abu ya dawo daga aikatawa ba. Zuciyar ta gama dakewa akan irin hakan. Wannan zai sake nuna maka ƙoƙari da jarumta irin ta jam'in tsaro a bayyane. Yo irinsu Madam Bily ko kaza aka yanka a gabanta walle kuka take rurus. Balle ace mutum sukutum da guda a suburbuɗa masa alburishi amma zuciya daram...

   .....★Komai ya tafi dai-dai bisa tsarin da suka shirya sai dai da amincewar UBANGIJI. Dan kuwa su Imran sun ƙetare ƙasar Dubai da Jush da taimakon jami'an ƙasar su ta reshen interpol. Sai dai bada sunansa ba, ba kuma da ƙamanin shi ba. Wannan shiri ne na tsawon watanni..
    Daga nan kuma cikin ƙasa kusan sha biyu na rana ƙwai ya fashe. Kwan kuma ya fashe ne a dalilin farkawar securitys ɗin Jush da aka bugar. Hakan kuma duk yana a cikin shirin su Dadah. Dan hatta abinda budurwar Jush ɗin ta basu suka sha sune suka bata shi.
      Sune suka kira jami'an tsaro. Cikin ƙanƙanin lokaci kuwa aka zagaye gidan. Awa ɗaya mummunan labari ya fito akan abinda ke faruwa. Ta inda zaka fahimci Jush nada ɗaurin ƙugu kafin kace mi ƙasar sa ta shirya jam'anta na musamman domin zuwa Dubai yin bincike, duk a zahiri ba'a sanar ma duniya ainahin wanda abin ya faru da shi ba sai iya su. Dan sun bada umarnin ta ƙarƙashin ƙasa ga gwamnatin ƙasar kar'a taɓa komai daya shafi case ɗin. Hakan yasa aka dakatar da jami'an dake cikin gidan suka zauna jiran masu abun dake jin duniyar ma kamar a tafin hannunsu take saboda ƙarfin iko. Duk da dai koda za'a basu dama suka dole sai anyi wasu abubuwan daya shafi ƙasa da ƙasa tunda ba lokacin mulkin mallaka muke ba yanzu ɗin ai ko....

^^^^^^^^^^^^^

     Anan kam hankali kwance Dadah da Nimrah suka sha barcin su. Dan basu tashi ba sai azhar. Bayan sunyi wanka suka fito domin karyawa da lunch ɗin da aka shirya musu. Anan ne ya kunna television dan yasan zuwa yanzu ta fashe. Ta fashe ɗin kuwa. Dan duk inda ka latso in har gidan tvn ƙasar ne da ake saka news abinda ke kai kawo kenan wannan batun kisa da ba'a game tantance waye ba. Nimrah da bata san abinda ke faruwa ba koma ace bata fahimta ba ta shiga jeroma Dadah tambaya.
        Nuna mata yay shima yanzu yake ganin labarin. Sannan bai san ma akan waye ake magana ba. Amma alamu sun nuna koma waye babba ne. Ta shiga layin ƴan jima mi da nuna mamaki. Daga haka ta saki zancen ta kama sabgarta. Dan sun fara cin abincin kenan ta ajiye spoon tace, “Yauwa Dadah ina Chocolate ɗina da kace?”.
        “Wane Chocolate?”.
     Ya faɗa batare daya kalleta ba.
Fuska ta ɓata. “Dadah harka manta. Jiya fa kace zaka saya min?”. Ta ƙare maganar idanunta na cika da ƙwalla. Sai a lokacin ya ɗan juyo ya kalleta da wani slowly look. Bakin ta sake tura masa tana matso hawayen ƙaryar. Kauda idanunsa yayi.
       “Kwaɗayayya, idan lips ɗin nan basu koma ba yanzu zasu ji a jikinsu”.
   Ya faɗa cike da basarwa yana tura mata bag ɗin daya shigo da shi jiya. Bakinta ya washe, ta ɗauka da sauri ta fara buɗewa tana dariya. Wasu haɗaɗɗun Chocolate guda biyar suka bayyana. Gashi an musu wani deco mai ɗan banzan ƙyau na masoya.
       “Thank you Dadah na”.
Ta faɗa tana kai fuskarta inda tashi take ta sumbaci kumatunsa. Kaɗan ya murmusa yana cin abincinsa da mata kallon gefen ido batare da yace komai ba. Bata sake bi takan abincin da suke ci ba ita kam ta hau buɗe Chocolate ɗin. Gutsirar farko tace, “Woow Dadah yummy”.
    Yanda tai maganar tana wani lumshe ido da ɗaga hannunta ta haɗa babban yatsarta da manuniya👌sai tai masa so cute. Zamansa ya gyara kawai yana kallonta. Sai da taci kusan rabi sannan ta ɗakko ɗaya ta miƙa masa.
        Kai ya girgiza mata.
Ta ce, “Akwai daɗi fa?”.
   “Sai dai ki bani na bakin ki”...........✍️

      101
Chapter 85 · 0% Book details