← Book details Sakar Makafi Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 42 OF 113

Sashe 42

Sakar Makafi Part 3 Complete Hausa Novel · about 6 min read

....★ Da asuba kamar yanda Dadah ya saba, ya fito domin tafiya massalaci. Kai tsaye sashen Nimrah ya nufa, dan yasan ita kaɗai ce ba lallai ta iya tashi ba. Sai dai bashi da tabbacin bata rufe sashen nata ba. Ya ɗan sauke ajiyar zuciya jin yana murɗa handle ɗin ƙofar ya buɗe. Ganin fitulun falon a kunne yanda ya barsu jiya bata kashe ba ya sashi ɗan girgiza kai. Bedroom ɗin ma ya sameshi a buɗe, sai dai nan kam babu haske sai da ya lalubi makunnar ya kunna. Can ya hangota a gado cikin bargo ta rufe har kanta, dan ta ƙure uban ac ɗakin yay mugun sanyi. Ya ƙarasa takawa har gaban gadon. Zama yay gab da inda yake ƙyautata zaton kanta ne, sannan ya janye bargon.
Wani irin harbawa zuciyarsa tayi a cikin ƙirji sakamakon inda idonsa ya fara sauka. Yay saurin janyesu yana maidawa kan fuskarta dan tana a kwance ne a rigingine.
Received at “Nimrah.”
Ya faɗa yana ɗan shafa fuskar tata datai masa fayau. Babu alamar zata motsa, sai ya ɗan fara bubbuga mata fuskar yana cigaba da kiran sunan ta. Karo na farko ta motsa tana yamutse fuska. Da ƙyar ta buɗe idanun da sukai wani kalar shanyewa tamkar wadda tasha wani abun maye. Tai walai da su ta maida luuu zata sake lumshe abunta. Harga ALLAH sai da Dadah yaji wani al'amari mai girman gaske. Dan hatta maƙogwaransa sai da yay wata kalar yin sama da sauri ya dawo har sau biyu. Ga shi ita kuma tama sake gyara kwanciya ne abinta.
Yanzu kam baiyi magana ba, sai kawai ya kamata cak ya tayar zaune cike da dakewa da kamewa tamkar komai bai faru ba. Nimrah da giyar barci ke ɗiba cikin ƙunƙuni ta ce. “Small Mom please ki barni zan tashi ɗan anjima. ALLAH ina jin barci”.
Ya fahimci tama manta a inda take ne, ga shi tana gama faɗa ta sake ƙoƙarin komawa zata kwanta. Dole ya tallafota sosai ya jikinsa, ita ko saita samu damar shige masa jiki, dan kanta ta kwantar a ƙirjinsa ta zagayo da duka hannyenta bayansa kawai ta cigaba da barcinta hankali kwance. Yayinda Dadah ya ɓige da riƙe numfashinsa na sakanni dan abin yazo masa a matuƙar bazata. Ya tabbatar Kiddo ta kusa ƙarasa tona masa asiri inda aka cigaba da tafiya a haka. Dan data san tarzomar da take tasarwa da tuni ta shiga hankalinta.
Shirin tada salla da ake yi ya saka tunaninsa katsewa, cikin furzar da iska ya shafa kanta dake ƙirjinsa zuwa bayanta. Sai da yay ɗan gyaran murya kafin sake kiran sunanta. Amma yarinyar nan bata da alamar sake buɗe idanun ma ko irin na ɗazun. Ya tabbatar ya riga da ya rasa raka'ar farko, gashi ya zama wajib a gareshi sake alwala.
Camak ya ɗauketa ya miƙe da su tsaye, sai dai tana jingine a jikin nasa.
“Kiddo kina son kuwa na samu salla yau?”. Yay maganar yana ƙoƙarin ɗagota daga jikinsa ya tsayar da ita akan ƙafafunta. Yanzu kam dole ta buɗe idanun, sai dai kana gani kasan barci ne taf a cikinsu. Ganin Dadah saɓanin Small Mom ya sata ware su sosai. Sai kuma duk ta nema daburcewa, ta ɗan kalla jikinta dake sanye da ƴar fingilar riga best da wandonta iya cinya, bamma tasan ta daka tsalle ta koma bayansa ba, tare da faɗin, “Naga Boni.”
Dadah da abin nata ya bashi dariya ya gimtse da ƙyar. Juyowa yay ƙoƙarin yi da nufin mata magana kawai ta rungume shi ta baya, dan da ya sake ganinta gara ai hakan. Yanzu kam sai da ya ɗan murmusa, sai kuma ya kai dubansa ga hannyenta data zagayo kan cikinsa. Nasa ya ɗora akai cikin basarwa kamar bai fahimceta ba ya furta, “Tunda kinsa na rasa salla je kiyi alwala muyi anan”.
“Ni wlhy Dadah zaka ganni”.
Ta faɗa cikin shagwaɓa tana sake ƙanƙamesa.
“Tunda baƙya so na ganki ya kike so ayi?”.
“Ka rufe idonka to”.
“Ashe ni naga Bonin ma. Shike nan na rufe”.
Sai da ta ɗanyi jimm na sakanni sannan ta sake sa, ta ɗan leƙo da kanta dan tabbatar da ya rufe ɗin. Sai suka haɗa ido. Da gudu ta nufi bayi. Kansa ya girgiza kawai yana murmurshi. Ya tabbatar zata sake ɓata masa lokaci, sai kawai ya nufi wardrobe ɗinta ya buɗe, cikin sa'a ya samu abaya a kusa. Ɗauka yay ya bita bayin, yay knocking da faɗin, “Buɗe ki ƙarɓa wannan ki saka karki sake makarar damu”.
Kaɗan ta buɗe ta miƙo hannunta da lalle yayma ƙƴau sosai. Abayar ya saka mata, cikin gargaɗi ya ce, “Kuma 3 minutes na baki”.
Mintuna ukun ma basu gama cika ba ta buɗe bayin ta leƙo. Ganin ya juya ma ƙofar bayin baya ta fito sum-sum tana sake jan ɗan kwalin abayar ya rufe mata fuska sosai. Komai baice mata ba shima ya shige bayin kawai. Bai wani jima ba ya fito yana gyara hannun jallabiyar jikinsa alamar alwala yayo. Ita kuma harta shimfiɗa abin salla guda biyu, sai dai nashi ya zama nata gaba kaɗan. Sannan ta saka hijabi yanzu. Yanda take faman sinne kai yasa baiyi magana ba kawai ya hau kan sallayar ya tada salla bayan ya juyo ya kalleta domin tabbatar da tsaiwarta tayi..
Received at 18:00
reacted with Karo na farko da Nimrah taji sautin ƙira'ar Dadah. Jitai tana neman narkewa. Daga ita har Ruƙayya suna bala'in son karatun Uncle Bilal saboda ALLAH ya bashi murya, a yau sai taji aiki gamai ƙareka. Dan jitai kamar karma su idar da sallar, sai dai babu yanda ta iya. Ya ɗaga hannu yana addu'a Nimrah kawai taji son tsokanarsa. Fuskarta da murmurshi ta ɗan matso kusa da shi, duka hannyenta biyu ta saka cikin nashi hannun tai kamar ta ɗiba abu. Da mamaki ya juyo ya kalleta, sai tai saurin matsawa baya murmushinta na ƙara faɗaɗa ta shafa addu'an a fukarta. Sosai abin nata ya bashi dariya dan ya fahimci wai addu'ansa ta kwaso. Wani mitsitsitsin murmushi yayi tare da kamo hannun nata duk biyu ya shafa a fuskarsa shima.
Dariya sosai ta sanya tana ɓoye fuskarta. Shima dai bai iya hana murmushinsa fita ba, dan abinda tai ɗin kawai ji yay ya sakashi nishaɗi. Koda tai ƙoƙarin janyewa a jikinsa bai barta ba, sai ma riƙeta yay da ƙyau yana faɗin, “Kiddo baƙya ji ko. Kin hana ni zuwa massalaci kin kuma kwashe min addu'a”.
Siririyar dariya ta saki da saka hannyenta ta rufe fuska irin na mai jin kunya. A haka tace, “Dadah ina kwana”.
Shiru yay bai amsa ba, har sai da ta janye hannunta daga kan fuskar ta ɗan kallesa, ganin ita yake kallo tai saurin sake duƙarwa. A tunaninta ko baiji bane sai ta sake maimaitawa. Yanzu ma bai amsa ba, ya dai miƙa mata tattausan hannunsa alamar suyi musabaha. Hannun ta zubama ido itama, wani abu mai nauyi da armashi na ratsa zuciyarta. A hankali ta saka nata a ciki. Sai kawai ya jawota gaba ɗaya jikinsa ya rungume.
“Haka ake gaida miji daga yau Little Shadow”.
Ba ƙaramin nauyi kalmar nan ta miji take mata ba, musamman a bakin Dadah, sai taji kamar ƙasa ta buɗe ta shige ciki. Shi kansa ya fahimci hakan, kuma yana saka shi jin nishaɗi............✍️

_Zaku sameshi a waɗan nan manhajar guda uku in sha ALLAHU._

*_NIGER🇳🇪- (500 Fcfa) (1000 CFA)_*
*_+227 98 94 12 81_*
*_My NITA_*

_Shaidar biya👇_

*_Whatsapp number_*
*_+227 98 94 12 81_*

*_TELEGRAM VIP 1000 (1K)_*

*9032345899*
*_Moniepoint MFB_*
*_BILKISU MUSA IBRAHIM_*

*_KATI MTN (1k)_*
*_09032345899_*

*_Shaidar biya: 👇_*
*_Telegram Number 09032345899_*

*_AREWABOOKS (Vvip)_*
*_Chapters & Audio_*
@BilynAbdull

*_WHATSAPP (500)_*

*1487616276*
*_Access Bank_*
*_Bilkisa Ibrahim Musa_*

*_Kati MTN:- (500)_*
*_09032345899_*

*_Shaidar biya:-_*
*_Whatsapp Number +234 805 568 7449_*

*_MASU SON A TALLATA MUSU KAYANSU SUMA_*

*_WhatsApp Number 👇_*
*+234 805 568 7449*
*_Telegram Number👇_*
*+234 903 234 5899*

*_ALLAH ya gafartama iyayenmu 😭🙏_*
Received at 18:00
reacted with 🔥58
Chapter 42 · 0% Book details