← Book details Sakar Makafi Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 66 OF 113

Sashe 66

Sakar Makafi Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read

.........Ganin yanda Nimrah tai sanyi tunda suka idar da sallar isha'i abin ke bama Dadah dariya. Ya dai gimtse baiyi ba, dan kuma zuciyarta ta samu nutsuwa sai ya fara shiga wanka. Koda ya fito zaune ya sameta ta zuba tagumi alamar tunani. Baiyi magana ba ya shirya cikin kayan barci masu taushi da rashin nauyi.
           Shigar ƙamshin turarensa a hancin Nimrah ya sata sauke ajiyar zuciya ta ɗago tana kallonsa. Dai-dai yana kaiwa zaune cikin kujera 1sitter. Sosai ta shagala a kallonsa, dan kayan barcin sun masa matuƙar ƙyau kamar ya saka su domin ado. Sarai yana jin idanunta a jikinsa, amma sai bai kalleta ba cikin dakewa ya ce, “Tashi kije kiyi wanka na kira miki Rukayya ku gaisa”.
         Kamar wanda yayma allurar farin ciki ta saki murmushi da miƙewa. Cike da ɗoki ta ce, “Dadah da gaske dan ALLAH?”.
     Bai ce komai ba, sai dai ya ɗago idanunsa da sukai haske da fitowa shaaa yana kallon ta. Sosai yake jin nutsuwa idan yaga farin ciki a tare da ita. Dan haka ya jinjina mata kansa kawai. Ai kai kace walƙiya fitt ta sheƙa hanyar bayi, ya girgiza kai kawai yana ɗan motsa fuska tamkar zai yi murmushi. Sai dai baiyi ɗin ba.
        Wayarsa dake a saman table ya ɗauka. Wani number da aka rubuta (Blood 1) yay dialing. Bai kaita kunne ba sai da aka ɗaga. Cikin girmamawa Ma'aruff yay sallama. Bayan ya amsa masa ya shiga gaishe shi. Dadah ya amsa tare da jeho masa tambaya.
     Ɗan jimm Ma'aruff yayi daga can. Kafin ya ce, “Dadah ban san miya faru ba har suka kai ga zuwa asibitin. Dan muma sai da safe muka sani a wajen Mammah.”
         Dadah ya jima baice komai ba. Dan har sai da Ma'aruff ya fidda ran zai ma sake magana sannan.
     “Kuna sashen Mammah ne?”.
  “Eh shigowar mu kenan”.
“Mu'azz fa?”
“Gashi yana cin abinci”.
“Yaje sashen zan kira shi”.
       Ma'aruff ya amsa da to. Sai da ya yanke kiran ya ɓata fuska. Dan wlhy shi yama fi son Dadah ya ƙyaleta. Baice komai ba dai ya sanar ma Mu'azz saƙon Dada ɗin. Ai bai ma yarda ya kai laumar abincin daya ɗibo ba ya miƙe yana ɗaukar wayarsa dake caji. Sai da ya fita Ma'aruff ke bama Ja'afar labari. Mammah na jinsu bata tanka ba. Suma sanin halinta yasa basu ja zancen ba suka kama wani....

        Koda Mu'azz ya shigo sashen babu kowa a babban falon su. Dan haka ya nufi sashen Nabeeha bayan yayi knocking. Cikin sa'a Ismat ce tazo ta buɗe masa ƙofar. Cikin ɗaure fuska ya tambaye ta “Aunty fa?”.
      Inda da ne sai ta hararesa ko gaya masa baƙa. Amma yanzu da yake akwai burin da take son cimmawa murmushi ta sakar masa. Cike da rashin damuwa da yanda ya ɗaure ɗin ta ce, “Ka shigo mana tana ciki”.
     Baiyi musu ba ya shiga falon. Ko kallon inda su Rayhana suke zaune baiyi ba. Ya ɗan dafa kujera kawai ita kuma Ismat taje kiran Nabeeha dake ɗaki. Ismat tai sallama, amma shiru ba'a amsa ba, sai ta tura ƙofar ta shiga. Shiru Nabeeha bata motsa ba, balle Ismat tasan taji shigowar tata. Cikin mamaki ta ƙaraso inda take a bakin gado zaune da kofin tea a hannu tana faman juya spoon a ciki. Itama zama tai sannan ta taɓata. Firgigit Nabeeha ta dawo hayyacinta. Dan ita ko shigowar Ismat ɗin ma bata ji ba da gaske.
        “Aunty kina lafiya kuwa?. Inata magana amma shiru”.
    Gajeren tsaki Nabeeha taja, sai kuma ta sauke numfashi tana ajiye kofin. “Sorry bamma san kin shigo ba. Hankalina ya tafi wani tunani daban”.
      “Hummm Aunty kenan. Ya kamata dai ki kwantar da hankalinki. Tunda har aka kai ga wannan gaɓar yarinyar nan ta kasance tare da shi zamanku tare babu canji. Kin dai fi kowa sanin Yaya Haysam ai.....”
         Shiru Nabeeha taƙi tankama zancen Ismat ɗin, hakan ya sata fahimtar bata son zancen. Itama sai ta barshi ta koma na farko data shigo da shi.
          “Uhm dama fa Mu'azz ne yazo yana nemanki, ina ƙyautata zaton aiko shi akai”.
     Sosai Nabeeha ta buga tsaki da yamutsa fuska, cikin ɓacin rai ta ce, “Uwar mi zan masa?”.
        “Ya kuma zan sani Aunty. Kawai yace yana nemanki. Ya kamata kizo sai kiji”.  
      “Ba inda zanje, ya faɗa miki idan yaga zai faɗa”.
     “Dan ALLAH Aunty kar kice haka. Idan kuma abinda yazo da shi mai amfani ne a gareki fa?. Dan naga waya a hannunsa ko Dadah ne yace ya kawo miki”.
       “Mtsoww!...”
Nabeeha taja tsaki, sai kuma tai shiru batace komai ba. Daga nan ma tai kamar wadda ta tafi tunani. Dan sai da Ismat ta girgiza mata hannu.
    “Aunty baki amsa ba kin sake tafiya tunanin”.
     “Mtsoww! Ƙyale ni Ismat kinji.”
   “Amma Aunty dakin duba ko wani abu ne dai dan ALLAH. Idan kuma nace ya shigo nan to?...”
    “Ismat nace ki barni!!.”
Ta faɗa cikin ƴar tsawa. Ganin kamar a hasale take yasa Ismat bata sake cewa komai ba ta miƙe ta fita rai ɓace. Itama Nabeeha ɗin sai ta rakata da harara da ƙaramin tsaki. Daga haka ta zame tai kwanciyarta....

       ......★★★.....

   Anan kam Nimrah data gama wanka cikin sanɗa ta fito. Sai dai hango Dadah zaune a cikin 3sitter yanzu ya kunna laptop taji ƴar nutsuwa. Sauri-sauri ta gyara jikinta. Ta ciro wasu turaruka masu ƙamshin tsiya dake a ƙananun kwalba da Mom tace mata na barci ne ta shafa a jikinta kamar yanda ta gaya mata. Ɗazun kayan da zata saka ta dinga fita kawai Dadah ya siya mata. Hakan na nufin kodai yau ma ta kwanta da bathrobe a jiki kota saka ɗaya daga cikin kayan Mom. Kai ina, ai har abadan ba ita babu bathrobe, dan jiya cikin sauƙi Dadah ya sule mata ita. Gara ta duba masu ɗan dama duk da bata jin akwai su ta saka ko yaya ne sai ta saka hijabi kawai ta kwanta a haka. Ita dai burinta ta koma wajensa kar ya canja shawarar kira mata Ruky.
           Kaf ta gama duba kaya babu na arziƙi, da ƙyar ta iya samun 3quarter ɗin wando coffee color ta haɗa da wata fingilar riga mai ƙaramin hannu. Tana sakawa tana waiwayen Dadah, ita dai fatanta kada ya ganta. Tana kammalawa ta sauke ajiyar zuciya, sannan ta gyara hijjab ɗinta daya kasance shi kaɗai kamar rai. A haka ta sake goga turare ta rufe akwatin ta maida shi inda yake.
     Cike da zumuɗi da ɗoki ta dawo inda Dadah yake. Azababben ƙamshin turarenta mai sanyi da sai tana a kusa da mutum zai iya jinsa sakamakon a jiki ta saka kamar yanda Mom tace mata ya shige masa hanci duk da ta saka hijjab. Sosai yaji illahirin gaɓoɓin jikinsa sun motsa. Har ta kai ya kasa haƙuri sai da ya ɗago ido ya kalleta. Ita ko da hankalinta ke kan waya kanta tsaye ta kai duƙe a ƙasa gabansa sosai har jikinta na gogar ƙafarsa ta dama take wajen.
       “Dadah na gama”.
    Ta faɗa tana leƙa fuskar screen ɗin laptop ɗin sa. Shi data gama saluɓewa ƙarfin jiki da ƙyar ya iya fisgo kalmar, “Tashi ki cire wannan hijjab ɗin”.
      “Dadah Please ka bar ni, kayan sunyi ƙarami ne fa”.
           “Idan ma babu kayan ne bana son ganin hijjab ɗin a yanzu...”
      Bata son ta cire, dan tana matuƙar jin kunya. Sai dai kwarjininsa ya gama mamayeta ta yanda bazata iya musu ba. Sannan bata son yay amfani da rashin jin maganarsa da zatayi yace ya fasa kira mata Ruky. Ita kaɗai tasan a yanda take matse da rashin jin ta a kwana biyun nan. Idanunta dake cike da hawaye ta rufe, kamar mai zare ma kanta wata jijiyar jikinta haka ta zame hijjab ɗin. Zuciyar Dadah ta harba, numfashinsa ya fita da zafi da ɗan ƙarfi. Dan kamar wanda ake sarrafa ma idanunsa da remote tana jan hijjabin sama yana binta da kallo har can sama. Tana gane kallonta yake ta juya masa baya. Bata san can ɗin ma akwai abin kallon ba.
      Sosai kayan suka mata ƙyau, ta sake koma masa tamkar wata ƴar babyn turawa. Hannunsa ya kai cikin nata, a hankali ya juyota tana fuskantar sa. Gamm ta sake yi da idanunta, shi ko daya sake binta da kallo tun daga fuskarta har yatsan ƙafarta ya wani sake shaƙar ƙamshin tare da jan ɓoyayyen numfashi mai zurfi. Sai kuma ya ɗan murza yatsun hannun nata. Tsigar jikinta ce ta tashi itama, ta motsa zata kwace. Sakin mata yayi, cike da basarwa ya furta,
        “Sit”.
    Cikin muryar umarni. Dole ta buɗe idanunta, sai kuma tai ƙasa da nufin zama inda ta fara ya katseta.
      “A nan”.
  Dole ta buɗe idanunta ta kalla inda ya nuna matan, dan furucin na sake tabbatar mata Dadah ne fa, wanda baya ɗaukar wasa ko yin wasa a mafi yawan lokuta. Sum-sum ta zagaya babu wani ja'inja ta zauna. Sai dai a ƙarshen kujerar. Bai kulata ba ya ɗauka wayarsa bayan ya ɗauƙi remote ya miƙa mata. Kiran number ɗin Mu'azz yayi, bugu ɗaya ya ɗauka..........✍️

Kuyi hakuri da jina shiru jiya rasuwa akai mana 😭🙏.
82

.........Mu'azz na yin sallama da gaida Dadah Rayhana ta zaburo. Har abin ya bama Amimah mamaki ta bita da kallo. A kuma dai-dai lokacin ne Ismat ke fitowa daga ɗakin Nabeeha rai ɓace. Mu'azz ya miƙa mata wayar kamar yanda Dadah ya bashi umarni.
       “Ga shi ki kaima Auntyn, Dadah ne”.
   Ya faɗa yana miƙama Ismat ɗin wayar. Dadah wani mutum ne da UBANGIJI ya azurta da daraja a idon mutane da yawa. Hatta maƙiyansa razani suke ji koda da kiran sunansa. Balle irin su Ismat ƙananun ƙwari dake neman fada. Jikinta har rawa yake ta amshi wayar, gudu-gudu sauri-sauri ta nufi ɗakin Nabeeha. Duk Dadah najin motse-motsenta. Sai dai baice komai ba har ya jiyo Ismat ɗin na faɗin, “Aunty gashi Dadah ne”.
       Nabeeha ta harareta, dan wayar ta manna mata a kunne kawai sannan tai furucin. Ta kuma kamo hannunta ta ɗora akai, bata jira amsarta ba ta juya ta fita...
Chapter 66 · 0% Book details