← Book details Sakar Makafi Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 31 OF 113

Sashe 31

Sakar Makafi Part 3 Complete Hausa Novel · about 7 min read

       Sosai damuwa ke shimfiɗe a fuskar Faro dake kallon Biebah tun bayan ficewar su Dada. Sai da yaji ƙarar rufe gate alamar sun fita gaba ɗaya sannan ya sauke ajiyar zuciya. Karo na farko ya ɗaura hannuwansa duka biyu a saman kafaɗarta. Sai ta sake duƙar da kai sautin kukanta na ƙara fitowa.
         “Kukan nan bai isa haka nan ba Biebah? Nima fa yayanki ne. In sha ALLAHU zan yi ƙoƙarin maye miki gurbin su Haysam, koda ba ɗari bisa ɗari ba zan kamanta kinji”.
      Kanta kawai ta iya jinjina masa, shima bai matsawa kansa da sai tayi maganar ba ya sakata a jikinsa kawai ya rungume ta. Abinda tafi buƙata kenan a yanzu, dan haka ta lafe tana shashshekar kuka da jan ajiyar zuciya. Bayanta ya cigaba da shafawa a hankali, har sai da ya tabbatar ta rage nauyin zuciyar tata sannan ya kama hannunta suka zauna a cikin kujera. Mayafin jikinta ya yaye, dan haka ta sake sunkuyar da kanta taki yarda ta kallesa. A karo na farko yay murmurshin da har tana jin fitar sautinsa. Sai kuma ya matso sosai yana leƙen fuskarta data sunkuyar. Yanda yay ɗin ya bata kunya, tai ƙoƙarin kauda kanta gefe ya kamo fuskar cikin hannunsa.
        “Na zata kunyar ta ƙare ai kuma ko Habibiya. Kin manta yau a gidan Haydar kike? Amarya mai capacity kenan da Babban yaya da kansa ke kawota gidanta”.
      Murmurshi ta saki tare da kife kanta cikin hannunsa dake riƙe da fuskar tata. Shima ya sanya dariya yana matsota sosai jikin nasa ya sake rungumeta. Suna a haka akai kiran sallar magrib. Badan yaso katsewar yanayin ba ya kamata ya miƙar yana faɗin, “Muje na rakaki ɗaki na je massalaci”.
Received at 14:59      Babu musu ta miƙe, haka suka nufi inda bedrooms ɗin suke. Ya tsaya a farkon corridor ɗin yana kallonta. Cikin magana ƙasa-ƙasa ya ce, “Ina zan kai amarya?”.
           Kanta a ƙasa ta ce, “Koma ina”.
     Fuskar sa da murmurshi har yanzu ya ce, “Shike nan bari na kaiki ɗakina, dan yau baƙuwata ce ke”.
      Batace komai ba, shima bai sake magana ba ya kama hannunta suka nufi ƙofar dake can ciki a ƙarshen corridor ɗin. Ɗaki ne babba, an zuba masa kaya masu ƙyau, babu kuma tarkace a cikinsa sam. Ga ƙamshi da tsafta alamar yana samun gyara da kulawa. A kaikaice ta ƙare masa kallo, ya zaunar da ita a bakin gadon ya nufi bayi batare da yayi magana ba. Babu jimawa ya fito jikinsa da ruwa alamar yayi alwala.
       “Naje massalaci”.
    Ya faɗa yana nufar ƙofa. Ta amsa masa da “A dawo lafiya”.

       ★Bayan fitarsa itama alwalar ta tashi tayo. Ta gabatar da salla. Koda ta idar bata tashi a wajen ba ta zauna zugum cike da damuwa da kewar gida. Musamman ma su Ruƙayya da a koda yaushe suna nane da ita. Sai Mammah uwa abar alfaharin kowane ɗan halak. Hawaye ne suka cika mata idon, bata bari sun zubo ba ta maida su ta haɗiye. Karatun Alkur'ani ta fara dan ɗebema kanta kewa har aka kira sallar isha'i. Tashi tai ta gabatar, tayi har shafa'i da wutri. Bayan ta idar tana zaune tana addu'a ya shigo. Kyakkyawan basket ɗin hannunsa ya ajiye a gefenta shima ya nema waje ya zauna a ɗaya daga kujerun ɗakin. Tai addu'a ta juyo tana masa sannu.
         “Yauwa Baby. Ga abinci nan Hajiya ta aiko”.
    Kanta a ƙasa ta ce, “ALLAH ya saka da alkairi”. Sai kuma ta miƙe ta ɗauki Basket ɗin zuwa inda yake. Kallon da yake mata ya sakata kasa kallonsa, murya a ƙurya ta ce, “Ina kitchen yake?”.
        “Ke da gidanki kike tambayar kitchen? To na hutar dake zauna mi kike buƙata na ɗauka miki? Dan yau ke baƙuwata ce”.
      Murmushi tayi, shima ya miƙe yana nasa murmushin ya fita. Babu jimawa ya dawo da plates da cups, sai spoons. Ta zamo daga kujerar da take zaune ta buɗe abincin ta zuba masa komai. Zata miƙe ya riƙota, kusa da shi ya zaunar da ita har jikinta na gogar nasa. Abincin daya ɗiba ya kai bakinta. Zata fara nuƙu-nuƙu ya ce, “Ɗura kike so kenan?”.
      Kanta ta girgiza masa, cike da kunya ta fara amsa. Idan yaci sai ya bata a haka suka cinye abincin da gasashen naman. Ta fara gyara wajen yana tayata. Sun fito tare har kitchen ɗin da yay mata matuƙar ƙyau, dan har sai da ta tsaya tana kallo. Sai kawai jitai an ɗauketa gaba ɗayanta. Babu shiri ta kama dariya da roƙon ya sauke ta amma yaƙi sai da ya kaita har bedroom ɗinsa, a bedroom ɗin ma a cikin bathroom. Sabon brush ya buɗe mata ya saka marclen a jiki ya bata. Ita dai a kunyace ta amsa. Koda suka kammala sai yace suyi alwala...

Sun gabatar da sallolon nafila, yay musu addu'a sosai tare da dafa kanta. Sannan ya ɗora da nasiha, tare da sake maimaita mata abinda yake saurin saka shi a fushi da wanda ke saka shi a farin ciki. Itama yace ta sanar masa. Kasa magana tai, sai bai matsa mata ba ya barta. Shi ya fara miƙewa ya sake shiga bayi. Tana nan zaune kusan mintina talatin sai gashi ya fito ɗaure da towel. Da sauri ta duƙar da kanta, shi kuma dan neman magana yazo har inda take ya kamata ya miƙar. Duk yanda yaso ta kalleshi taƙi kallonsa. Sai ma jikinta dake neman fara rawa. Sai yay murmurshi kawai, cikin raɗa ya furta, “Baby sarkin kunya. Yanzu fa miji nake ba Yaya Haydar ba”.
        Ita dai batace komai ba, sai ma sake duƙe kanta da tai. Ya sake murmusawa da faɗin, “Tunda bakin ya mutu shike nan. Jeki kiyi wanka to kizo ki kwanta ki huce wannan gajiyar bikin da kuka kwasarma kanku”.
      Koda ta jinjina masa kai sai ta nufi hanyar fita. Riƙota yay. “Haba Biebalo ina zuwa kuma? Ga bathroom anan. Har kayan barci kina da su anan ɗakin, kin san duk inda Haydar yake kema kina a wajen”.        “Yaya zanje can nidai”.
     “Bazan ce a'a ba. Amma idan muka je can ɗin nine da kaina zan miki wankan kin yarda?”.
    Karo na farko ta ɗago a rikice tana kallonsa. Sai dai tama kasa furta abinda ke bakinta. Shi kuma ya fuske ya tsareta da idanunsa da ke a juye. Har sai da taji kallon na sake tsumata da ratsa mata jiki sannan tai saurin barin wajen ta nufi bathroom ɗin nashi kamar yanda ya buƙata tun farko. Sai dai babu abinda zuciyarta keyi sai dukan tara-tara, dan tunda take da shi bata taɓa ganin kalar abinda ya gani a cikin idanunsa ba yanzu........✍️

Hy Guys. Barkanmu da sake dawowa filin daga. Barkan ku da salla kuma. Fatan anyi ibada lafiya. UBANGIJI ALLAH ya karɓa mana tare da amsa addu'oin mu baki ɗaya. Ya Rabbi kasa muna cikin bayin da aka ƴanta a cikin wannan wata mai alfarma. UBANGIJI ka gafartama iyayenmu da al'ummar Musulmi da suke kwance cikin ƙasa. ALLAH kayi mana maganin dukkan matsalolinmu na zahiri da baɗini.🙏❤️❤️😘💖48

..........“Yaufa bazaka kwanar mana a gidan nan ba Zak..”
      Shiru kamar Dada baiji mi Daddy Imran yace ba. Idanunsa akan screen ɗin laptop yana aiki hankali kwance. Sarai Daddy Imran yasan ya jishi. Zancen ne baya son ayi kuma bazai barshi ba, yau zaiga ƙarshen miskilanci.
       “Haysam!”.
    Ya kira shi da sunan daya kan jima bai kirasa da shi ba. Dan haka Dadan ya ɗago idanunsa a karo na farko ya kallesa. Imran ya harare shi.
           “Kana jina kenan?”.
       Dada yay murmurshi yana kauda idanun nasa daga kallonsa. Cikin sake basarwa ya ce, “Kazo mu ƙarasa aikin nan, kasan fa gobe akwai office bamu da isasshen lokaci. Dan ba lallai ka ganni a gidan nan ba ma”.
      “Babu wani aiki da zamu cigaba da yi gida zaka wuce. Bamma san miya dawo da kai ba yanzu...”
     “Miyasa kake da rigima ne wai?”.
  Cewar Dada yana sake maida idanunsa akan screen ɗin laptop ɗin.
     Imran ya ce, “Hummm har na kai ka rigima ne. Ni yanzu ma duk ba wannan ba. Canai ka tashi muje na rakaka. Ni ban taɓa ganin ango irinka ba wlhy. Kana ganin Haydar yau ko sau ɗaya bamu ga ƙeyarsa a gidan nan ba”.
        Dada ya ɗan murmusa kawai baice komai ba. Shima Imran sai ya miƙe yazo ya ɗauke laptop ɗin jikinsa gaba ɗaya...
      Dada ya ce, “Kana lafiya kuwa?”.
  “A'a da sauƙi dai. Koka tashi ko na kira Mammah a waya”.
        “Ni ne zaka kirama Mammah?”.
     “Da gudu ma kuwa. Kana nufin zan barka ka barmin yarinya ita ɗaya tana amarya a daren ta na farko gidanka? Nima zuwa zan yau na sabunta nawa angwancin dan baza'ayi babu ni ba”.
        Dariya ta kusa kama Dada akan furucin ƙarshe na Daddy Imran. Amma baiyi ba sai dai fuskarsa ta nuna alamar murmurshi. Bai sake tankawa ba ya miƙe kawai dan yasan nacin Imran bazai taɓa barinsa yasha iska ba. Wayoyinsa kawai ya ɗiba yay hanyar fita. Imran dake kashe laptop ɗin yay murmurshi shima ya tattare komai waje ɗaya yabi bayansa....
Chapter 31 · 0% Book details