← Book details Sakar Makafi Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 67 OF 113

Sashe 67

Sakar Makafi Part 3 Complete Hausa Novel · about 7 min read

      Shiru na fin mintuna biyu ya ratsa cikin wayar, ita batai magana ba Dadah ma yay shiru. Sai dai ya miƙe a inda yake zaune. Nimrah ta bishi da kallo, wani abu mai nauyi na sukar zuciyarta. A hankali zumuɗin dake kan fuskarta na kiran Ruƙayya ya shiga ɓacewa, sai kawai ta janye idanunta ta maida kan television dake aiki...

        “Baki iya sallama da gaisuwa bane?”.
    Dadah ya faɗa yana isa gaban ƙaton window ɗin glass ɗin ɗakin da ake iya ganin ƙayataccen garin na Dubai yana mai tura hannunsa ɗaya cikin aljihun pyjamas ɗinsa. Maimakon yin abinda ya faɗa sai Nabeeha ta sakar masa kuka kawai. Ya lumshe idanunsa tare da furzar da iska kaɗan a bakinsa yana sake gyara tsaiwa. Shiru kusan minti uku yana sauraren ta, kafin ya furta a hankali.
           “Kin san bana son kuka ko?”.
      “Haysam idan banyi kuka ba mi kake so nayi? Why Haysam? Why kake son tozarta ni da nunama duniya ni bamai daraja bace?”.
     “Miya kai ki asibiti batare dana sani ba?”.
  Ya tambaya maimakon amsa mata tata tambayar.
      Kukan ta sake fashe masa da shi sosai, dan har yana iya jin yanda numfashinta ke neman sarƙewa. A nan ma ya ƙara yin shiru kusan minti ɗaya..
         “Himm! Miyasa bazaki gane bana son wannan shirmen ba? Ki dinga min magana cikin natsuwa, zan baki dukkan amsar abinda kike so. Sannan na faɗa miki bana son wannan kukan”.
       “Kana son na maka magana cikin natsuwa mi yasa kake ƙuntata min? Miyasa Haysam. Kana ganin ka ƙyauta kenan ka ɗauketa ku tafi wata ƙasa batare da sanar min ba? Ko ni ba mace bace? Miyasa kake son tauye min hakki na? Da wulaƙanta ni”.
     Murmushi yayi mai kama dana takaici. Ya sake takawa jikin glass ɗin gab, maimakon kallon waje da yake sai ya jingina bayansa yanzu tare da ɗage ƙafa ɗaya a kansa, ɗayar na ajiye, hakama hannunsa na aljihu har yanzu. Inda Nimrah take ya kalla, ta zubama tv ido sosai.
        “Nabeeha ke mace ce, mai daraja ma kuwa a wajena. Kin san kuma bana komai sai da dalili. Ban tauyeki a komai ba face miki hukunci kamar yanda na faɗa miki. Gargaɗi na ƙarshe da zan miki ki daina min magana da hayaniya. Sannan mi ya kaiki asibiti?”.
      Tasan dukkan abinda ya gaya mata daga zuciyarsa ne. Dan Haysam kaifi ɗaya yake. Sannan yana cewa eh ne ko a'a da iya gaskiyarsa koda zata maka daɗi koda bazata maka ba. Ita shaida ce shi mutum ne mai tauri kuma bahago musamman akan laifin da ya masa zafi idan kai masa. Bazai maka ihu ko hargagi ba, amma zai hukuntaka da mafi tsaurin hukunci da sai kaji kama tsani kanka. Gaskiya Jiddah ta faɗa mata, maimakon zafafawa a wannan gaɓar ta lallaɓashi su shirya farko. Dan a yanzu zuciyarsa zata karkata ne kawai ga wadda ke kwantar masa da hankali a cikinsu. Sannan ita a karan kanta tana son yin amfani da wannan damar tunda har ya nemeta da kansa ta dinga ƙuntata ma Nimrah ta yanda honeymoon ɗin zai zame mata uƙubar da zai ƙi daɗi su dawo ba shiri.....
      “Wai baƙya jina ne?”.
Ya katse tunaninta. Ajiyar zuciya ta sauke mai ƙarfi, cikin dawowa hayyaci. Ta ce, “Shike nan kayi haƙuri. Amma dan ALLAH ka dinga min adalci. Idan ba haka ba zaka rasani wataran”.
     Komai bai ce ba. Ita ma sai ta fara masa bayanin daya buƙata tun farko. A zancen nata ya fahimci a gida tabar wayarta. Da kuma suka dawo batama dubata ba. Amma duk da haka sai da yay mata faɗa, sai ta shiga langaɓe masa da wai ita har yanzu bata jin daɗi, hakan kuma duk a cikin shirinta ne data fara tsara aiwatarwa. Dan ta tabbatar a duk inda yake yanzu tare yake da shegiyar yarinyar nan mai idanu kamar an soya gyaɗa marau-marau....

      Tun Nimrah na tunanin Dadah zai dawo a mintina biyar har taga an kai ashirin, kamar wasa aka kai talatin. Komai ya tsaya mata cak, takai bama ta gane abinda ta kalla. Ba bakin ciki take ya kira matarsa ba, amma tana jin wani tuƙuƙin takaici da haushi. Ta cije lips da ƙarfi, planing ɗinsu da Ruky na fara mata kai-kawo a zuciya. Dole ne fa a fara wasan tun yanzu. Dan tun a ɗazun a wayarsa da Mammah ta fahimci akwai abinda ya faru, Nabeeha ta aikata abinda ta saba ga Mammah. Ta sake tabbatar da hakan bayan magriba yana waya da Daddy Imran. Duk da tayi kamar ba jinsu take ba taji komai...
        (Rama cuta ga macuci ibada ne. Yanda ta yanke ki da wuƙa, kema ki shirya yankata da salonki wanda yafi wuƙa kaifi da zafi) Kalaman Rukayya suka shiga dawo mata. Sannan huɗubar su Mamy (Aunty Ummi) harma da su Uncle Ma'aruff na nan daram a cikin zuciyarta. Tabbas tana matuƙar jin kunya da shakkar Dadah saboda matsayinsa da kwarjinin sa. Amma tana da makami guda ɗaya a hannunta game da zama da shi da kuma yaƙar Nabeeha kamar yanda Mom (Aunty Mimi) ta faɗa.
        (Nimrah ke yarinya ce, ba lallai ki fahimci duk wannan yaƙin da muka shirya shigar miki ba a yanzu. Amma ki sani kina da dama guda ɗaya tak kuma makami akan Dadah ta yanda shi da mutanen dake gefe bazasu miki kallon rawar kai ko zaƙewa ba. Makami ki shine ƘURUCIYA. Dadah na miki kallon yarinya ƙarama kamar yanda duniya ke miki kallo, dan haka ƙuruciyarki itace takobin gina rayuwar aurenki a cikin rayuwar Dadah. Ki cigaba da zame masa yarinyar nan da yake kallon ki, tare da yin amfani da yarintar wajen mamaye duniyarsa. Sannan ki karya lagon Nabeeha da ita, ta yanda komai kika aikata hatta shi kansa zai baki kariya da kalmar KURUCIYA. Ita kuma kota gyara ku amfana tare, ko ɗayan biyu su faru da ita...)
       Murmushi tai daya tsaya mata iya lips, sakamakon tinano kalaman Mom ɗin. Dan haka ta watsar da takaicin da Nabeeha ke shirin cusa mata da makirci irin na tsohuwar mace. Tsam ta miƙe, tare da ajiye remote ɗin hannunta ta shanye dukkan damuwar fuskarta. Inda Dadah yake ta kalla. Ya sake juya mata baya, alamar hira nakai masa,
     (Dadah yanzu ne zaka fara ganin aikin ƙuruciya) Ta faɗa a zuciya tana sakin murmushi mai yalwa a zahiri. Da ɗan gudu ta nufi inda yake, a bazata kawai ta rungumo shi ta baya, tare da zagaye hannayenta akan cikinsa. Numfashi ya ɗauke ma Dadah, da ƙyar ya iya fisgo shi har yana kasa ƙarasa maganar da yake ma Nabeeha...
     Tsabar iya shege na Nimrah muryarta da ɗan ƙarfi yanda Nabeeha zata iya ji cikin shagwaɓa da diddira ƙafafu ta ce, “Wayyo Dadah ni yunwa nake ji, kazo ka bani abinci”.
       Dadah ya lumshe idanu, tare da zare hannunsa dake cikin aljihu ya ɗora akan nata dake saman cikinsa. Yayinda Nabeeha data jiyo komai da Nimrah ta faɗa nimfashinta ya tsaya cak...
       Dadah ya ɗanyi gyaran murya, tare da zagayo da Nimrah dake bayansa ta koma gabansa. Wani kalar kallon ƙasan ido ya bita da shi, batare da yay magana ba ya matsota jikinsa ya rungume. Da yake dan iya shege tayi duk da matsananciyar kunyarsa da take ji haka ta danne ta shige jikin nasa da ƙyau, har ma da kwantar da kanta a ƙirjinsa ta sake maida hannayenta duk biyu a bayansa ta zagaye..
      Dadah ya sake yin ƙaramin gyaran murya tamkar mai ƙoƙarin daidaitata. Sai kuma ya kai hannu saman gashin kan Nimrah dake ɗaure yana zare ribbon ɗin a hankali da bama Nabeeha amsar maganarta daya fara cikin dakewa.
          Da ƙyar Nabeeha ta danne daga can tai dariya cike da kissa, sai dai idanunta hawaye har sun zubo. “Humm D. Ke nan. Karka damu indai nice na maka tanadi mai girma, dan sai na tabbatar maka Nabeehanka ta zarce wadda ka sani. Zan shagwaɓa ka fiye da yanda akai maka a lokacin ƙuruciya, in taƙaice maka zance sai ka mance hanyar Kobi idan kazo hannu na...”
      Maganarta ta bashi dariya. Musamman ta ƙarshe, dan haka ya murmusa kaɗan yana tura yatsunsa cikin gashin Nimrah dake jin bugun zuciyarta na neman canjawa, jin kalaman Nabeeha da suka shiga kunnenta take tamkar saukar dalma. Ga motsin murmurshin Dadah ya sake tunzurata. Da ƙyar ta iya riƙe kanta jin amsar da yake bama Nabeeha ɗin............✍️

       83
Chapter 67 · 0% Book details