← Book details Nur Firdaus Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 93 OF 96

Sashe 93

Nur Firdaus Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

anata shiri basu dawo gidan ba sai wajajen 12pm na dare tazo ta samu nur firdaus tana tattara duka important files dinta tana saka su agefe, basuce ma juna komi ba sai can layla tafara cema nur ai yanxu kam cikin shegen dake jikinta ya zuba sai ta dena guilt tripping dinsu da emotional face ta saki jiki ayi hidimar biki dan kar ace sisternta batazo bikinta ba.

aidama itace tasha gaya mata cewa bazata rabu da ita ba komin rintsi inde hakane kawai gobe tabisu wajen sakun lallen.

laylah tanata zuba maganganu yadda kasan nur bata dakin haka tay banza da ita har tagaji tay shiru.

hanklin nur sosai ya dan dawo jikinta da taji cewa ai dukan da hasina tay mata tayta zubar jini jiya yasaka cikin ya zuba atleast now she can make a move dan tagama tunani taga babu amfanin zamanta da su inba de kashe kanta takeso tayi da baqin ciki agidan ba.

washe gari da asubahi
ta dauki wani jakarta na baya, acikin wanda Adnan ya taba kawo mata dayajeshi dubai siyayyar sport wears na shi. gucci schl bag ce me kyau amma tana da dan xurfi da girma. tana kammala karatun qur'ani ta kwashe muhmmn files dinta na schl da komi data ware tunjiya da dare ta shiryasu acikin jakar da duka inne wears dinta da farin rigar javeed.

snn ta hada duk wani abu da babanta ya siya mata sai few abaya datasan kudin mrs haseena bai shiga ciki ba ta saka aciki basufi kala biyar ba,sauran duk wanda tasan idon laylah nakai tabarsu a wadrob din da dukkan wani abu data mallaka nakayan duniya da layla take saka mata ido akai tana kishinta, harma da wanda mrs hasina ta siya musu duk bata daga ko daya ba. acikin manyn hadadun hijabanta ma befi kaloli biyu kawai tadauka ba sai wanda ta'aje akan gado zata saka ajikinta.

karfe takwas ta fita basu san inda ta nufa ba, da kafa taje cikin wani 24/7 jeweries store a anguwarsu
takai tallan wani abun wuya da dan kunne na gwal da ta siya da kudinta da aka bata kyauta awani gasar makaranta..

kudinsa ya kama 400k a lalace, bata damu ba ta karbi kudi ta saka a hijabinta ta boye snn ta siya abinci da pain relievers around 9:30am tadawo gidan saida ta tabbata suna can dakin snn ta boye kudin acikin kaya tay wanka taci abincin snn tasha magani ta shirya kanta tsaf...

can ta ta fito daga ita sai jakar bayanta sai handbag dinta, kai tsaye taje dakin Mrs Haseena wanda ko sallamarta bata amsa ba,itama hakanan taqi ta gaisheta tace musu wayarta tazo abata.

nan Haseena ta mike tsaye da mamaki tace wa nur ina zataje da jaka? tafara kkrin zata kwace jakar tava meye aciki, nur ta ture hannunta da karfi
cikin tsaurin ido ta fara mata magana da wani irin busashen ido
tace karsu taba mata jakarta ita bata dauke komi nasu ba suje daki gasucan kayan duniyar datay yawon karuwanci ta samesu tabar musu su siyar suyi hidiman biki in hakan zai saisaita musu zuciya.

then she begin to tell mrs hasina everything na yadda ta samu kudaden da kayan datake zaginta akai, yau nur taki ta rufawa layla asiri, duk wani abunda ya wakana wanda Mrs haseena bata sani ba nur ta fayyace mata tace mata kuma bata damu da ko ta yadda da ita ko bata yadda da ita ba, itade kawai wayarta tazo karba zataje kaduna dan bazata iya zama da uwar da take nuna mata tsana a fili snn take tozarta ta ba.

baki bude kuma akangare mrs hasina ta dinga kallon nur ganin yadda yau ta tsaya agabanta take gaya mata magana masu zafi with no filter or ounce of respect, nur ta bushe idon ta gaggaya ma mrs hasina kalaman da inaji harta mutu wasu kalaman bazata iya mancewa dasu ba.

..sann ta dada jaddda ma mrs hasina cewa tabbas mijinta saadat shine ya aikata musu hakan kota ki, kota so wata rana zata gani.

layla duk ta rude da hayaniyarsun tana ta kuka tana karyata nur amma ko ajikinta.

kusan cacar baki sukeyi da mrs hasina
akan karda nur taje kaduna inma barinsu take so tay taje yola kawai wajen didi amma nur ta tubure tace inda taga dama zataje kuma wallh ba'a isa ahanata ba.

ganin baza'a bata wayarta bama yasa ta wuce afusace ta fara wargaza kayan mrs hasina tana watsi dasu a tsakar dakin kamar ba nur din ba har saida ta tsamo wayarta acikin wani drawar tadauki abunta batay wata wata ba ta kama hanya zata tafi

har waje Suka biyota mrs haseena tanata masifa kamar zata daga gidan...

wallh nur inkika fita agidan nan karki sake ki sake dawowa dan bazan karbeki ba...

dama can baki da kunya gashi yau halinki na boye ya fito fili, butula, duk abunda nake miki da rashin kunya saki sakamin? har nine kike cewa zakije kaduna konaki konaso to dan ubanki kije su kasheki kamar yadda suka kashe ubanki...inhar kika tafi nide wllh karki sake dawomin..

nur firdaus bata ko juyo ta kallesu ba
kuma ko hawaye bata sauke ba itakanta tasha mamakin kalar bacin ranta tun jiya kawai tasa aranta mrs hasina ta mugun tsanarta hakan bazai taba canzawa ba inta cigaba da zama da ita wata rana hala zata kasheta gara kawai ta tafi inda zata rayu.

har bakin gate layla tabiyo nur tana ririketa tana kuka tafara rokonta wai karta tafi kaduna shikenan yanxu bazata tsaya taga aurenta ba.

a fusace nur ta fincike hannunta a tsawace tace wani auren naki da kullum sai kince min ina miki baqin ciki akai layla? tou ai nice kika dauka a matsayn babbar maqiyanki kuma be kamata na kasance aranakun farincikinki ba dan haka kiyi aurenki lafya
kayan duniya kuma gasu can nabar maki
a daki, all the shoes jeweries harma da abayan dana saka a kd..take them. let them give u the happiness and love dat i cudnt give you.

tana gama blasting din layla ta fita abunta
mrs haseena ta dinga ihu tana masifa tana kwala mata kira kamar kanta zai tsage yau bakaramin mamaki nur firdaus ta bata ba dan bata taba tsammanin haqurin yarinyar nan zai kare hartay behving haka ba.

nur kuwa har saida tay nisa takai bakin titi sann ta fashe da wani irin kuka me radadi dan abunda tay kusan abune me matukar wuya ita bata iya raini da rashin kunya ma babba sai yau gashi tay ma mahaifyarta
sann ta raba kanta dasu fatan ta shine kar Allah ya kamata da lefi, saidai kuma in ta tuna cewa Allah ya baka cikaken dama raba kanka ko nisanta kanka da mutanen da suke cutar dakai sai taji wani sanyi.

ta tari mota kenan ta kunna wayarta wanda har hooking yake yi tsabar sakonnin da suka shishigo da sauri ta dudduba da bataga wanda yay kama dana javeed ba sai kawai ta maida wayar jakarta ta aje. basu ko yi nisa ba taji tafara bleeding jini na shirin wanke mata kafa duk sai taji tamugun tsorata haka tafasa tafiyar taje ta kama wani motel 20k per night ta zauna anan ta hada ruwan zafi ta shiga ciki ta wanke kanta snn tasha maganinta da tazo dasu, Rigar javeed datazo dashi ajaka shine mata kadai marar nauyi haka tacire tasaka ajikinta tasaka pad ta dan kwanta tay bacci me dan nauyi sai yamma ta farka taga jinin be dauke duka ba tasake wanka snn ta fita ta siya abinci tazo dakin ta zauna taci

ata daya bangaren kuwa tunjiya mutanen sanata farida suka samu rigar sadaat daya gama wankuwa sa jininsa ya turmushe sa datti ya bushe da kyar ma suka gane nashi ne, tun anan ka tabbatar mata cewa da wuyane in sadaat yana raye babu tantama tunda an samu rigarsa ajeji to hala har anjima da kashe sa. bakaramin baqin ciki da haukan gaske sanata farida tay ba, ji tay kamar asarar datayn ya mata yawa, ita bata ci kujera ba, bata samu ta tozarsa haseena yadda ranta ke so ba gashi kuma ta rasa shakikin yaron gidanta sadaat. zafin hakan yasa kawai ta bawa ussy oder akan duk inda akaga yaran mrs hasina abisu a akashe su karma abarsu su raye..

yau da safe ussy ya fito farautarsa saidai bai samu damar samun mrs hasina da layla ba dan tunda Nur firdaus ta rabu da su suka gama jimamin su na lkci kalilan snn suka share kashinta suka tsunduma hidimar biki dan mr haseena ta hau dokin zuciya tace sam bazata sake bata lkcinta akan ryuwar nur firdaus ba tunda tazabi taje wajen dangin ubanta in sha Allah bazata taba nemanta ba harsei tazo ta nemi gafaratta a abuja.

abun nadan sosa mata rai amma ta danne dan yau akwai kudi da abubuwan duniya a hannunta sai kawai ta tsunduma wajen harkan karya da nuna ma dangin Adnan cewa itama watace dan ta goge abun kunyar datay awajen karban kayan lefe da akaga tanata barin kudi akan layla duk sai anata mamakinta.

ussy yasan be isa yaje ta wajen hidiman ba sabida security dan haka yazo kofar gidan ya tsaya daga nesa ya samu dede maman saeid ta fito zataje gidan mama hauwa

samunta yay da magana yana son ya san ko nur firdaus haryau tana kumshe a gida koma ta mutu.

maman sa'iid tace masa ai yau din nan da safe taji suna hayaniya nur firdaus
ma ta wuce kaduna
wajen dangin ubanta
har maganan da be tanbayeta haka ta dinga zuba masa

yaji dadi sosai data masa wann barbadan harya dau dubu talatin ya bata kyauta sann ya tafi

tun ahnya ya gayama sanata farida cewa ai nur bata tare dasu mrs haseena awajen biki dan haka itace first target, nan danan kuwa tay amfani da mutanenta aka fara neman nur basu samu excat location dinta ba sai can da yamma ana daf da magrib nan da nan kuwa yazo shi gate djn motel din ya tsaya yana jiran dare ya dadayi da wata silencer ajikin bindigarsa yadda zai harbeta ta mutu basai anji karar bindinga ba.
Chapter 93 · 0% Book details