Sashe 22
Nur Firdaus Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
tun tana quest house tahau kirar sadat a waya sau da dama ta kirashin amma baya daga kiranta, can taja tsaki sanin sadaat ai yaro ne yasata dadayin tunanin nemo hanyar lallabashi ya dawo gida.
wajajen yamma bayan komi ya lafa mata ta tura masa sako mai tattare da kalamai masu tsananin taushi karshen sakon ta rubuta "Sadat, ina so mu yi wata magana Bazan iya ci gaba da wannan rayuwar batare dakai ba Don Allah ka dawo gida, mu gyara komai."
koda ta turamai seda yadauki dogon lokaci batare da ya amsa sakon ba,sai can dai daga baya ya kirata da wani boyayyar lamba cikin muryar shan qamshi tareda bayyana cewa yanakan fushi da ita kai tsaye yace Me kike so mu tattauna akai Haseena?Kin san dai lalacewar wannan lamarin badaga wajena bane daga wajenki ne keda yayanki toh ni me zan miki da kike ban hakuri in dawo???
..
cikin katsesa tareda lwangwasa murya mrs haseena tace "haba darling Sadat, kafahimce ni don Allah. Na san abinda yafaru ya taba maka zcya amma hakan ba yana nufin zaka guji nauyin da ke tare da kai ba. Iyali fa ba abu ne da zaa yi watsi da shi haka kawai ba."
Sadat yaja wata tsaki kasar wuya "..Na san Kina son in dawo in zauna miki ne don jama’arki su yi miki kallon uwa ta gari amma ba don da gaskiya kike so mu yi wata gyara ba
cikin sauri haseena da saka muryan tausayi tace haba Kadaina yin tunanin cewa ina yin wnan abun ne don jama’a. sadat Kai ne jagoran gidan nan. kuma Yaran nan suna bukatar ka kuma ni ma haka."
shide jinta yake bai kara cewa komi ba
sai can Bayan sun samu yar doguwar tattaunawa snn tayi amfani da dabara ta nuna masa cewa idan yabar gidan hakan zai kara dagula abubuwa kuma zai yi tasiri msman akan Layla Sai takuma yi masa alkawari cewa za ta gyara yanayin gidan ta tabbatar da cewa ba za a sake samun irin wannan matsalar ba. cikin magiya take rokonsa.
Duk da cewa akwai wasu manufofi a zuciyarsa amma saiya ga ya dace ya dawo din don ganin yadda zaiyi amfani da wnnan damar wajen cika babban burinsa akan yaranta.
cikin sauke numfashi mai nauyi yace "To shikann Haseena naji Zan dawo amma ki tabbatar bazamu sake samun irin wnan matsalar ba idan ba haka ba wallh saidai kawai mu rabu na har abada.
cike da farin ciki mrs haseena tace haba in sha Allah babu abunda zai sake faruwa na riga nay wa nur kaca kaca darling, Nagode sosai Sadat dinaa anjima kadan zan tura maka wani abu a acct dinka kaji baby boy dina??
wani irin shan qamshi ya dinga mata har suka kammala wayar
Bayanta lallaba Sadat yagama yarda cewa zai dawo gidan taji wani irin sanyi aranta dan ta tsani Abinda zaina dauke mata hankli dayawa musmn ma dakomi na siyasan su ya doshi kaiwa karshe dan duk mutanen da suke targeting a majalisa da votes dinsu sun soma samun kansu sosai.
nan da nan ta shirya takoma gida cike da jin sanyi aranta, Tun a hanya tariga ta shirya yadda zata jawo dikn hankalin ‘ya’yanta duk dana ta san cewa dolene ta daidaitasu domin a tabbatar da zaman lafiya a gidan dan bata son kimar ta ya zuba.
20 minutes drive ya kawo ta gidan cikin shigowar bazata nan tawuce kai tsaye zuwa ixuwa kicin din da bazata iya tuna when last ta lekashi ba,nan ta dudduba abubuwa inda tafito waje ta umarci drivernsu malam liman akan ya siyo mata abubuwan girki ita dakanta zata shirya babban abinci.
ranar gabaki daya su nur firdaus suna wajen rehearsal na gasarsu basu dawo gida akan lokaci ba gashi dama layla bata motsawa ko ina batare da nur firdaus din ba.
haka mrs haseena ta zage ta cancada wata mayyar girki da gajiya da wahala tare da sudin goshi, tuwon shinkafa da miyar egusi tay wacce Sadat ke matukar so. ta bi ta hada lemukan kayan itatuwa domin kafa teburin cin abinci,tabi tay wankarta da babban leshi dayaji stone work tafito fesss cikin wata mayyar kwalliyar zamani mai mugun kayatarwa.
wajajen hudu na yamma su nur suka dawo gidan gabaki dayansu sungaji,koda suka shigo cikin falo wani dadin qamshin abincin mrs haseena ne yasoma tarbansu tundaga kofa inda suka tsaya mamaki ya cika idanunsa ganin wai har an shirya kan dinning da abinci..
dake already malam liman yasanar musu da cewa mahaifyarsu tadawo sai basu wani girgiza ba, basu tsaya yin wata tunani ba suka wuce dakinsu dansu shirya su fito
Hanklin nur baya jikinta saboda nauyin damuwa gashi tana son taga talashe wann gasar domin mahaifinta. duk yadda layla ta nemi sanin dalilin da ya dawo da mum dinsu bata canko ba musmn ma da nur take yawan shiru shiru yanxu, after a while Bayan sunyi wanka duk sun shirya cikin dogayen riguna na atamfa layla tasaka purple colour mai desing din pattern nur firdaus ta saka blue me aiki dan kadan ata gaba, sunyi kyau bana wasa ba duk dama basu cika kwalliya ma fuskarsu ba.
sun karaso lkcin dede mrs haseena tana shirin kirarsu izuwa babban falon gidan nan Dukkaninsu suka taho suka zauna suka tsura mata idanu sai dai Nur Firdaus dake mata kallo da shakku yayinda Layla ke kamewa tana son jin menene zai faru..
babu yabo babu fallasa mrs haseena ta zuba musu ido itama tana kallon su duka sai can snn tace yawwa yan mata na toh kusaurare ni, ina kuma son ku fahimta cewa iyalinmu shine garkuwarmu, Ba za mu iya yin rayuwa ba tare da juna ba...ta danyi shiru,saikuma ta kallesu tace mijina Sadat yana hanyar dawowa nan gida,m yanxu kuma ina fatan kowannenku zai karɓe shi da hannu bibbiyu."
let what happen remain in d past kunaji na???
Nur Firdaus tayi shiru dan jin sunansa ma kawai yana saka zuciyarta tafarfasa sede batace komai ba.
Layla kuwa tayi da fuskarta kamar na wacce take jin mugun tausayin mahaifiyar sun amma a zuciyarta tajin mugun daɗin yadda mrs haseena take sake jaddada amincewa gareta fiye da ‘yar’uwarta.
mrs Haseena ta kalli Nur Firdaus kai tsaye
tace Na san akwai rashin fahimta anan amma dole ne a san cewa acikin gidana girma da daraja suna ga namiji ne, ke nur firdaus kisani Sadat babanku ne yanzu, bana son raini, bana son ganganci. kuma ina so ku duka ku nuna masa kima da daraja. i dont want to hear any funy stories frm you henceforth.
Nur Firdaus tadan runtse idanunta tana jin yadda zuciyarta ke karaya Amma kafin ta samu damar cewa wani abu Layla ta rigata cafe maganar da murya mai taushi, tay da fuska kamar ita kadai ne me hankli.
mummy ni ba ni da wata matsala da Sadat. dama kuma its all misunderstanding Ina ganin mu da muke yara ne yakamata mu gyara halin mu snn mu fahimci hakan.
Nur Firdaus ta kalli Layla da gefen idnta da tana mamakin jin yadda maganarta ke ƙara ƙuntata mata.
Tariga ta fahimci cewa Layla karamar yarinyace hala dai hayaniya ne bata so kuma bata da wayo sosai amma bata gane inda tunaninta yake dosa ba.
suna tsaka da wann maganar sukaji karar shigowar mota kirar lexus fara kal nan da nan mrs haseena tay jikin window ta dan hanye labule ta leka shi ganin shidin ne yasa tafara washe baki, Bayan yan wadu mintuna kadan ta umarce kowa ya zauna cikin nutsuwa
kafin nan Sadat ya karasa shigowa falon tadada kimtsawa ta kara qamshi wanda gabaki daya ya qamutso da qamshin turarensa me karfi daya busosu yagama rikita zucyar layla da mrs haseena
nan Haseenan ta tashi da fara’a da barin jiki taje har kofa ta tarbe shi tana murmushi ga jawo hannunsa cikin kulawa tanata kallon facial reactions dinsa dan tana son ganin komai ya koma daidai daga wajensa.
tana murmusawa ta jawosa ciki tanami nuna masa kan kujera
"ure welcome back my darling husband nida yara duk Mun shirya maka abinci mai dadi domin maraba da dawowar ka.
Sadat dake shan qamshi ya zauna cikin sigar isa da jan aji yana wani kakka kamewa yana jin yadda Haseena ke ƙoƙarin faranta masa rai sai wani babbasarwa yakeyi yana amsawa ciki ciki
Layla a gefe tana satar kallonsa da shuumar murmushin da ba a san me yake nufi ba nur kuwa ko sau daya bata daga ido ta kallesa ba dan sosai ta tsanesa musmn daya gilma mata wann sharrin awajen mahaifyarsu.
jin wajen ya dau shiru yasaka mrs Haseena ta kalli ‘ya’yan nata tace kids what is the meaning of this wai sainace muku ku gaishe shi yadda ya kamata ne?."
Nan Layla ta miƙe a hankali ta matsa kusa da Sadat tana dan murmushi da murya mai laushi tace "Barka da dawowa Baba Sadat. Muna matukar farin ciki da ganin ka a gida.
Sadat ya kyabe bakin sa jin yadda tacemai baban da gatse yana dan kallonta da idon sa baice mata uffan ba
Nur Firdaus tayi jinkirin tashi kai kamr ma bazata ce komi ba tana daga idonta sama kuwa tacikaro da idanun mrs haseena akanta curr zuciyartace ya tsaya cak da irin mugun kallon da mumynsun take mata ahnkli ta dauke kanta tay kmr bata gane me ake nufi ba. dan itade harga Allah Tana ji a jikinta cewa wann dawowar sadaat din ba Alheri bane agidan amma tasan idan tay wani magana yanxu hala mahaifiyarta za ta sake kallonta da wani laifin tada zanne tsaye
Cikin wuyarta da kyar tasako ladabi tana jan numfashi batare da ta kallesaba tace "sannu, Barka da dawowa."
Sadat bai ce komai ba amma ya jinjina kai, yana kallonta da wani irin yanayi da ita kanta bata fahimta ba ita kuwa wani irin tsanar sa takeji aranta na musmn na hudata.
Layla tana gefe haka kawai taji yadda zuciyarta ke tsananta wa da farin cikin ganin yadda Nur Firdaus ke jin mugun haushinsa.
Wannan shi ne damar da take nema zargi baya kanta, nur bazata tsareta ba, snn hanklin kowa baiya wajenta ynxu.