← Book details Nur Firdaus Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 30 OF 96

Sashe 30

Nur Firdaus Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

ata daya bangaren tunda nur firdaus ta bar wajen cin abincin sai tafara tunani dan zucyarta sosai ya kasa samun nitsuwa da sabin dabi'un layla.
dan sai yaune da suka samu zama awaje daya dukansu uku kafin nn ta soma lura da yadda Layla take ƙoƙarin samun gindin zama awajen sadaat abun ya bala'in bata mamaki ganin wai laylace yau take yin wasu abubuwanda zai jawo hankalin Sadat akan su.

can Sai kuma taji zuciyarta ya fada cikin rudani ta kalli kanta a madubi tana mai tambayar kanta ko dama dagsken ita ce matsalar gidan kamar yadda mumynsu take fada, har cikin ranta she knew her pure intention, she just want to protect her only sister at all cost, idanunta take sukayi ja saboda rauni da damuwa gashi dama jikinta yana dauke da kasala sosai.

tana cikin wann yanayin wayarta ya fara kara ta dauka taga Adnan ne yake kira tay sauri ta dauki wayar dan tay mugun kewarsa sosai nn suka gaisa tana Allah Allah taji ya furta mata cewa zai dawo Abuja amma sai labarin aiyukansa nacan kawai yake famar bata karshe sai taji tama kasa yin magana mai tsawo dashi dan saboda tunaninta ya fara rabuwa kashi biyu.

bayan sun kammala wayar ta sanya rigar bacci wanda ya ɗan zarce idon sawunta sannan ta zauna a gefen gadonta tana jin kamar duk duniyar ne ake neman juya mata baya dan kusan kowa dake sakata farinciki ya canza, layla, adnan dama can mumynsu kam basa jituwa.

Wannan yanayi da Layla take son amfani da shi don ganin ta cimma manufarta ita sam bata fahimceshi ba dan yanxu haka a tunaninta hala layla kawai tanason a zauna lafya ne ita kuma gani take kamar sadaat din ba abun yarda bane sam.

*******
koda nur firdaus ta fito bitan karatun yau hakanan ta umarce malam liman akan daya dinga shiga gidan time to time yana duba mata laylah da sadaat..

Gashi Ranar gabaki daya Laylan ta zagene tana ƙoƙartawa domin tajawo hankalin Sadat izuwa kanta tahanyoyi daban-daban amma hakan duk ya ci tura sabida yawan shigowa da mal. liman yakeyi sai bata samun isashen dama,

gashi duk wani motsinta nayau tmkar ba ya shiga zuciyar sadat ne kamar yadda ta yi zato, da daddare can haka tasace jiki ta shigo masa har dakin mummynsu a cikin wata matsatstsiya rigar bacci mai bayyana surar jikinta

duk shuumancinta sai kuma talura da yadda Sadat din yake dan ɗauke kai yanamai yarfata cikin rashin damuwa da ita dan zuciyarsa na cike da dumbin shawarar da abokinsa Ussyn ya bashi ne game da Nur Firdaus, iya makircin layla naranar yasaka a tunaninsa yake ganin kmr kawai pretending to hate him nur firdaus takeyi amma ba har ranta take turo masa layla ita kuma take famar ignoring dinsa ba.

share layla da sadaat ya dingayi a gidan yau yasa Layla ta farajin wani irin matsananin haushin komi tanajin zucyarta ya cunkushe da haushi dan kamar hduk wani ƙoƙarinta yana tashi ne abanza.

haka ta kasance cikin zullumi da haushi har nur firdaus ta dawo daga wajen karatu ta cigaba da lura da yadda laylan take kkrin zuba masa rawan kafa shikuma yana babbasarwa.

itade batace ma layla uffan ba har sukayi bacci duk tana lura da yadda zuciyar laylan duk yabi ya cunkushe ya kuma dulmuya da damuwa.

washe gari ya zamo shine ranarsu ta karshe a Abuja gobe da sassafe ne ranar laraba shine ranar tafiyarsu wajen gasa kaduna.

yau safyar tuesday yaune nur firdaus da sauran dalibai zasuje last tilawa practice a schl dinsu kafin gobe a wuce kadunan..
kusan kowani dalibi da xai halacci wann babban gasar yana cikin tsananin zumudi da kuma farinciki amma banda ita dan lamarin layla ma kadai agidan jiya saida ya kusa hanata samun bacci.

wajajen Bayan sallar asuba Nur Firdaus ta fito ta zauna wajen data saba bita acan waje akan sallaya sanye da hijab cikin nutsuwa tana dan maimaita karatun Alkur’ani da za ta fara gabatarwa awajen gasan da aka shirya.

Muryarta mai tsananin taushi da kwarjini yanamai ratsa ilahirin gidan yana kuma jan hankalin duk wani halitatta dake saurararta Har ma da Malam Liman direbansu wanda yake ɗakinsa na mai gadi, yafito ya tsaya a kofa yanamai washe baki tsabar jin dadin sauraron yadda take zuba karatu.

Malam Liman yana murmushi yana kallon tadaga nesa cewa yake masha Allah, nur firdaus Yarinya mai nutsuwa Allah ya albarkaci wannan muryar taki, Kai! Da mutane irin ki za su yawaita a duniya da anji dadi wallh.

after some minutes Bayan nur ta kammala karatun ta taho ta sameshi tana dan murmushi cikin ladabi ta gaishesa nan ya fara zayyana mata abubuwan da ya lura dashi jiya game da layla, itade batace mishi komi ba kawai tay murmushi tareda masa godiya akan yadda yake nuna mata kulawa da goyon baya a kullum.

kanta na kallon kasa tace Malam Liman na gode sosai da tulin alherinka agaremu Allah ya saka maka da mafi alheri.

Malam Liman yana gyara hularsa cikin washe baki yace Ameen Ameen yarinyar kirki, masha Allahu na jinjina miki dan Kinyi karatu sosai domin kiyi nasara a wnn gasar, snn Ki san cewa nima nan ina alfahari da ke. nur ta kara gode masa byan haka ta koma cikin gida don shiryawa makaranta.

tana fitowa daga wanka ta ɗauko wata sabuwar rigarta na makaranta mai kyau, daya sha guga ta tsaya agaban madubi tana kkrim kama silky smooth gashinta daya zubo mata har gadon baya cikin tsari dan ita bata acuci kitsawa takeyi kadan sai ta bidashi dede. A yayin da take kan shiryawa, talura da shurun Layla yay yawa daga cewa zata yi makanta coffe bata sani ba ashe tana can tana yawone cikin gida cikin wata rigar bacci mai dan karen tsantsi wanda ya bayyana surar jikinta sosai.

comb din datake taje kanta ta ajiye akan mirron ahankli snn ta saka dogon hijab a gurguje ta fito waje domin dubata.

kitchen din tafara isa ta duba bata ganta ba aikuwa tayo hanyar falo nan ma bata ganta ba, zuciyarta taji yana tsananin harbawa cikin danne hakan tay hanyar dakin mamansu da wani irin sauri tana karyowa coner kuwa lkcin dede layla ta fito kenan daga dakin tana wani irin tafiya duk jikinta na kaduwa dauke da tray din coffe din a hannun ta babu wani abu na sirri ajikintan da baiya nunawa a sarari

Nur Firdaus ta tsaya cak jin kanta na juyawa amma dake bata son ta tsoratata ta danne hakan cikin wata nutsatstsiya da murya mai taushi tace Layla??..

take gaban layla ya tsinke dan batay tsammanin nur harta dawo cikin gidan ma

karasowa nur firdaus tay ta jawo hannunta suka bar wajen izuwa kofar kitchen kafin nan ta kalleta tace "layla me yasa kike yawo da wannan kaya a tsakar gida musman da kinsan akwai Sadat

zatay magana cikin katseta nur tace nagaji da miki fada layla wann abun fa da son ranki..nawa in tunashe ki ne Kisan cewa fa wannan abunda kikeyin ba daidai bane Don Allah ki daina irin wannan halin.

Layla ta tsaya cak a tsaye kamar wacce ji kunyar yadda nur firdaus ta mata gyara bada ihu da fada ba..

tana shirin budan baki saiga sadaat yana mai tunkarosu yana isowa yace meyake faruwa anan?

Nur firdaus ta dauke kanta kamar bada ita yake ba, caraf layla ta fara juya kan magana muryanta kamar na wanda zatay kuka tace babu komi dama Big sis ne tace na dena kawo maka coffe din.

sadaat ya kalle nur firdaus yaga bata ma kallon gefensa. salon ya sa kansa cikin maganan sai ya kalle laylan yace "i am sure bazata hanaki kawo min coffe ba, saidan in bata so kina zuwa min a haka ryt?? see, layla yanzu fa kin girma u need to listen to your big sis she knws whats best for u mm autar mamanta

layla ta sake baki tana kallonsa da mamaki ganin wai yabi bayan nur firdaus sai tay shiruuuu tanajin shi yana magana akan shigartan wanda zahiri cikata yakeyi da wata muguwan takaici da haushi, nan ta yi kamar ta fahimci abin da yake fada shima taja musu wata dogon numfashi tana dan sunkuyar dakai kasa da yanayin nadama Amma a zuciyarta, tanacike da gulluton bakin cikin yadda Nur Firdaus tasake samun karbuwa.

sadaat ne ya fara barin wajen kafin nan Nur Firdaus ta shiga kitchen ta kulle kofa dan tunda sadaat yazo ya tsoma musu baki sai bata sake cewa uffan awajen ba.

Layla ta koma ɗaki ta rufe ƙofar a zafafe sannan ta zauna dabas a kan gado ta fashe da wata muguwar kukan takaici Duk da haka zuciyarta tana cike da mummunan tunanin meyasa sadat zai yi mata haka agaban nur firdaus???

a zuciyarta ta dada kullatar yar uwarta tana mai dada rushewa da kuka sosai dan gani take kamar duk lokacin da Nur Firdaus ta yi magana sai kowa ya ɗauka ita ce mai gaskiya itace sarauniya cikin ranta da tsananin fushi tace in sha Allah zan tabbatar miki da cewa ba haka bane saina saka rayuwarki ta zama bala’i agidan nan.

tagama zanta hakan a ranta kenan sai ga nur firdaus ta shigo dakin tamata kallo daya snn ta taho ta zauna agefenta basuce ma juna komi ba nur ta kama hannunta ahkli snn tace i understand dat kinason ki gyara komi ne agidan nan amma bashine zai hanani in gaya maki gaskiya ba layla..ure my little sister, ure the best thing that cud ever happen to me, no matter what i will stand to protect u, your dignity and ur honour bazan bari ke kanki ki cutar da kanki ba.

laylah dake jin kamar xcyarta yabushe tas da mugunta ta kara fashewa da kuka tadan rungumo nur firdaus din da wata salon makrci i am sorry big sis na miki alkwari bazan sake kai masa komi ba inkince kar na sake mai magana ba bazan yi ba banason kije gasarki kina damuwa dani dan Allah kiyi haquri..
Chapter 30 · 0% Book details