← Book details Nur Firdaus Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 32 OF 96

Sashe 32

Nur Firdaus Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

bayan sun gama bada haddan karatu suka zauna masjid din schl suna dan bubbude wrp box na gifts din dan suga meye aciki
tarkacensu candies da cholokates din kam tuni ta rabashi ma dukkan mutanenta da suke yawan zuwa wajenta, sauran ta aje ma layla. daga cikin katon wrap box din kuwa wasu tsadadun set set na arabian perfumes guda shida, watches da sets na abun wuya ne masu daukar ido sosai guda shida suma, saida wani expensive pack din colourful pure silk veils na rolling da golden pins dinsu.

tamkar an kunna jiniya haka jadidah take washe baki tana wow wow wow wow woww masha Allah kawai take furtawa tana bi daddaya tana daukar kowanne tana kalla.

akasar box din kuma sallaya ne me laushi da bakaken abaya guda biyu da turkish gown me shegen kyau dark green da diso dison baki sai sandal wedges 5inch heels guda biyu..

jadida tace masha Allah ashe dole wnn abun yay nauyi nur firdaus tay shiru tana dan murmushi...

tace koda nace masa karyana siya min wayann abubuwan duniyan sam bayaji.

jadida ta kalleta tace when a man truly loves you wallah ko kinaso ko bakiso inde yana da kudi toh akanki kudin nan zaina karewa wani abun ma ai saikin zama matarsa tukuna zaki gane ma idonki.

dan dariya sukayi atare suka hau maida kayan, nur tay tay da jadidah ta dau abunda takeso aciki amma haka taki fir saida ta mata na dole snn ta dauki silk veils guda biyu da turare guda daya.

bayan nan suka koma wajen karatu, wajajen 4:30pm na yamma suka fito hanklin nur firdaus ya mugun tashi da bataga layla ba, har sai da mai gadin schl din ya gaya mata cewa ai laylah tuni takira malam liman har yazo ya kuma dauketa sun wuce gida, sosai hakan ya bawa nur firdaus mamaki dan layla bata taba tafiya batare da ita ba, ko batare da ta mata sallama ba, amma hakanan ta basar suna kan sallama da jadidah da sauran yan matan ajinsu, kawai sai ga motar adnan ya doso ta wajen, bata ma lura ba saida taga kusan kowa awajen ya zuba mata ido yana kallon ta ana rade rade..

Adnan yana kammala parking ya fito sanye da wasu shegun kananan kaya dasuka amshe jikinsa sosai gashi ya iya tafya yana shan qamshi haka nan ya iso wajen yan matan yana dan murmushi yamusu cikakyar sallama lkcin kowacensu na masa kallo da admiration, jadidah ce ta fara kkrin sakashi dariya
tana mai cewa bazata bisu hanya akasheta da soyayya ba.

shima cikin wasan yace mata sam bazai ma yadda ta bisu ba cos he want to spend sum time da future wife dinsa.yan mata dayawa awajen na tsananin jin kishin nur wasu kuwa suna mamakin yadda soyayyarsu yay nisa.

Adnan ya bude ma nur gaban motarsa ta shiga nan da nan suka wuce suna yar musun su ta soyayya akan dalilinsa nakin daukowa harda jadidah cos she feel much safer in sun fi hakan yawa har ranta bata son yawan kebewarsu tare...

adnan yana dariya yace habibty kinga itace tafara furta hakan bani ba,kuma ai tasan nayi missing dinki ne sosai, so i dersve to have ur time nikadai ko ya??

murmushi kawai tay tace hmmm hakane toh its okay.

daga nan suka fara hirar rayuwa da abubuwan dake gabansu, sam adnan baya boye mata komi musmn gameda kansa da kuma siyasan mamansa, yah sai labari yake bata yanayin yadda ake bincike akan wasu masu ma mamanshi zagon kasa anan ne nur ta soma jin sunan hon farida bala.

ahankli yake tukin suna hira saida suka kusa daf da anguwar su saitaga ya sha wata kwana ta dan kallesa tace habibi kamanta da hanyar gidan mu ko??

murmushi yay snn ya saka mata muryan shagwaba yace na isa in manta hnyar gidanmu, swtht i just tot we shud eat out tunda kin gaji kuma inkinje gidan ma u wll be busy tolerating your kid sis layla..

ta dan hade rai shine bazaka gayamin ba kawai saika dauko hanya dani...what if i dont want..

cikin katseta yace u dont want to spend time with me? nur bakiy missing dina ba ko..ehm ehm zan yi kuka...

yadda ya fada da shagwaba sosai yasata dariya tace "we just eat and talk yeah??...

with assurity a voice nashi yace "yeah...

daga nan suka isa gaban wata hadadiyar open restaurant suka zauna a wata outdoor space, table of two yayi musu odern duk wani abun da zasu ci

tunda suka zauna suka fara hira kamar wanda sukayi shekara basuga junansu ba, ba suda hankara ba har sai wajen ana daf da kiran sallan magrib.

dan gabaki daya ya gaya mata dukkanin abunda familynsa suke ciki bai boye mata komi ba.

yace mata auren sa zaayi ne kamar taron selfish business and politcal gain domin cika wasu manyan burika na siyasa da mahaifyarsa take son cimmawa, shide bai damu ba tunda mum dinsan ta amince masa ya auretan and his dad is also okay with it.

yace mata amma tay hakuri yasan zaa kawo wasu abubuwa na publicity da cin fuska da raina arziki a cikin hidimar auren sun and he just want her to knw all this now tun yanzu sabida ya zamo suna kan hanya guda ita dashi...

sosai nur firdaus ta fahimceshi ta kuma gane cewa tabbas koda adnan ya aureta bazata taba zamowa choice din kowa a familynsa sai nasa shikadai..sann anan gaba da akwai alama cewa ba ita kadai zata kasance a matsayin matarsa ba, dole ne zaa masa auren kwarya tabi kwarya, bai fito fili ya gaya mata haka ba amma duk cikin bayaninsa ta gane hakan sosai..

saidai dayake suna matukar kaunar junansu hakan take ganin bazai zamo wata matsala ba.

ana daf za'a kira sallan magrib suka bar wajen da tulin tarkacen kayan ciye ciye daya siya mata dan ta ci anjima snn ta kaiwa kanwarta layla agida.

agaggauce ya tukasu suka iso anguwar gwarimpa lkcin waje ya dan fara duhu duhu maman sa'id ta rako mama hauwa kenan zasu shige gida suka tsaya kallon motar adnan dake tahowa.

tsayawa sukayi tsam suna binsu da ido har yay parking ya fito ya budewa nur firdaus kofa ya daukar mata jakarta da ledojin abincin ya bita da shi har bakin gate dinsu.

dede malam liman ya fito kenan ta kalleshi cikin kara yi masa godiya, yana maida mata murmushi yace mata i will call you in Few hours sai muyi maganan tafyarmu kaduna goben kinji??

ahankli tace masa toh snn ya juya ya koma motarsa yana tafiya yana lura da wani irin azababben leke da saka ido da tsananin gulman da su maman sa'id da mama hauwa suketa kallonsu dashi
..
kasa kasa yaji maman sa'id tana mika wuya tana cewa mama hauwa mama hawwa kiga kiga sai yanxu fa ya dawo da ita gida bayan yakaita hotel ya gama kwamusheta hmm aina gaya miki wallh zuwa ake ana daukarta a mota ana zuwa ana iskanci da ita ana basu ababen duniya ahayyye nanaye ayyuriri...

mama hauwa tace wann ai karuwanci ne a fili, tirrr da yayan haseena, sunyi gadon banza sun gaji watsewa awajen uwarsu, itadin haka kawai ne take cigaba a siyasar tata??? kiga haseena yarda take kyakkawa ga diri ga ilimi snn kice maza basu fi dubu wanda suke danne shegiya ba...taxo anguwa tana mana burgan banza wai ita me kudi

ba duka duka adnan yaji zancensu ba amma yatsinkayo wasu zancen nasu sosai abun be masa dadi aransa ba.

yana shiga motarsa yay ma nur waving yana kallon malam liman yatayata tattara gifts dinta suka shiga gida...

nur suna shiga gida adnan yay winding up na glass din motarsa snn ya toshe idonsa da wata muguwar bakar spec, ji yake kamar har ransa zai iya walaknta duk wani dan adam wanda ya taba mutuncin nur firdaus a duniyan nan gabaki daya.

wani irin murxa kan tayansa da wani irin gudu yay kansu maman saeed kamar bai san meyakeyi ba sai ji kake ana gudu kiti kiti kata kata kura na tashi wajen gudun ceton rai maman sa'id
ta ture mama hauwa akasa timm timm ta dabu da duwawanta akasa tay buju buju dankwalinta ya zame ya fadi kasa kwandalar kanta me kamar tsuliyar kaza ya fito sarari, birgima take cikin kura tana wayyo wayyo wayyo Allah adnan yazo da mugun gudu yay kamar zai takasu

wata iriyar kururuwa suka hauyi atare dan sun mugun tsorata adnan sanda yaga sunyi futu futu akasa snn ya sassauta tukin bayan yaci dariyarsu har ya gode ma Allah.

daga cikin motarsa cikin kyabe baki yace jisu kattin banza magulmatan banza magulmantan wofi

bai wuce ba kuwa ya karaso wajensu lkcin maman saiid ta dan dawo hayyacinta ta tashi akan mama hauwa tana kkrin dagata duk sunyi fututu saiganan adnan din ya tsaya dede kansu yay winding glass dinsa down

sede kafin suyi wata magana sukaji ya watso musu ne new new dollars note akansu zaikai kamar guda ashirin..

aikuwa nan suka sake kaurewa da kokawa kiti kiti kata kata kowacce tana ture yar uwarta wajen kkrin daukar kudi ..

karkada kansa yay yana dubansu yadda suka shagala bazata yaja musu tsaki tare da cewa bunch of hypochrites sann ya ja motarsa yawuce abunsa suka bisa da kallo gabaki daya kunya sai kuma ya lullube su.....

akabarsu da cewa kiji dan iskan yaron nan yace mana munafukai

mama hauwa tace inji de ya biyamu, Allah ya tura keya Annabi ya ja goshi...
Chapter 32 · 0% Book details