← Book details Nur Firdaus Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 77 OF 96

Sashe 77

Nur Firdaus Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

tay kamar zata masa ihu dan ikon da yake nuna mata a muryan sa har yana so yafara razanata"tace i dont knw them. cikn zare mata ido yace i hate 'lies"..da har zata sharesa sai kuma ta hatsala da muryar kuka ta hau gaggaya masa komi daya faru bata boye masa komi ba, wani irin juya mata baya yayi da fuskarsa kamar ma be amice da ita ba wanda hakan ya kara bata haushi sosai..

koma mesa ta tsaya masa bayani oho wani haushin kanta ta fara ji aranta tace shidin wayene da zaina tuhumanta kaman wani ubanta haka

cikin shareta ya koma cikin motar dan yaga inda wayarta ya fadi dazun data tsaresa sai ya dauka ya aje, yana zuwa ya dauko wayar ya dawo dashi yamika mata yace unlock it, hawayenta tashare tabude masa wayar aikuwa chat dinta yana dede kan text message din da aka turo matan da hoton laylan da komi ya bude ya kalla....

yakara fixgota bada karfi ba amma yace come with me...

gaba gaba suka kara sanda suka kai gaban wani waje mai dan tudu sann ya zauna ya daga idanuwansa masu sanyi ya dallara mata tanata kallonsa taga yamika mata hannunshi dacan kamarma bazata taba kulashi ba toh bata san sanda takama hannunshin ba ahnkli yajawota tazauna kusa daf dashi..

tarasa me takeji akansa dan bata taba sakewa da mutum hakanan ba sai shi

yanzu xai bata haushi yanxu saikuma taga tana biye masa.

dan shiru sukayi na wucen gadi kafin nan yace "so, what did u think dos boys want frm you?? da rashin kunyarkin nan kin taba musu wani abune?

dan sunkyar dakai tay wani sabon hawayen taji yayanko mata ahnkli tace mishi i dont knw nifa babu wanda na sani a schl din sai kanwata da kawaye na..i just..
heard dat they are bad boys,And they rape girls.."yace really? dakyar tace mishi umm,ahnkli ya dago ya kalleta da taushin murya yace "toh sorry.
ta kallesa da sauri dan batay tsammnin zai furta mata hakan ba,ganin tana kallonsa yasa yadan lumshe ido muryansa kasa kasa yace kinaji na?
tana kallonsa tace eh,..yace "Dont ever put ur life in danger again, kanta ta sauke kasa again snn tace but i cannot leave my sister over der what if,..cikin katseta yace shushh, listen. ur sister isnt the target, u're..kiyi abunda nace miki kawai do not disobey me.

tay shiru batace masa komi ba...

ya amshi wayartan ya bude sakon ayshan ya ciro nasa wayar ya bude yay scanning din boyayyen lambar da wata application na military intelligence awayarsa aikuwa sai ga lambar aysha sata boye ya fito karara.
yace who is aysha othman? itade tunda wayarta yashiga hannunsa takejin dar dar tambayarsan ya dawo da ita dan tsillin hawayenta tashare da mamaki ayanyinta tace she is my friend..

kai tsaye yace"I dont like her. i don't want u close to her ever...

tana kallon cikin idonsa takasace masa komi sabida tadda taga yake mata magana da iko kamar wani babanta..

can ta turo masa baki gaba tace ."nide i want to go home"..

yay shiru kamar be ji ba..muryanta na rawa takallesa taga yanata famar daddana mata wayarta batama san meyakeyi ba, hawaye take ya cika mata idon tace 'please.. its late..
inason insan ko sister na ta koma gida.

saida ta fadi hakan snn yace "okay" nan
yamike tsaye zai dan jawota tay sauri ta ja jiki dashi tay gaba ya kyabe bakinsa ahankli ya biyota abaya.

tsayawa tay ya zo dakansa ya bude mata seat din gaba ta shiga ta zauna snn ya rufeta, sai da yadau like 5 more mins da wayarta awaje snn ya shigo ciki yana zama ya aje mata abunta ta dauka taga time kusan 4:30pm na asubah.

lumshe idanunta tay ta jingina kanta da jikin kujera tay shiruu
harya ya fara tukasu

tsaban tarasa menene zcyarta yake sakawa tamanta shataf bata masa kwatancen gidan na su ba, tana cikin duniyar tunani dataji sanyin A.C ya gaurayu da wann shgn qamshin turaren nasa sai kawai ta bingira da bacci.

ahnkli ya dinga tukasu time to time yakan juyo ya kalleta yana tuna yadda ta bashi labarin with all the honesty in her voice and eyes

tun ba anan yasan ba karya take masa sam
numfashinta datake saukewa a baccin is soo fragile and serene
like her kind heart harji yake da wani abu ya sameta yau din nan da baisan ya zaiyi da ransa ba.

badon yaso ba amma Dan dolensa ne kawai ya saka Security tracker dinsa a awayrta, he just cant risk it anymore ya lura kamar yarinyar tana da maqiya sosai.. even among her friends..duk da baida niyyar shiga personal life inta amma kusan dole yazame masa ya kare mutuncinta dan yasan yarinyace batay wayon da zata fahince wasu abun ba. he is going to have a spy dat will be watching her movemnt kullum daga zarar tafice daga gidansu dan tanan ne kawai yakeji hanklinsa zai kwanta.

Daga gidansun kuwa layla ta kasa bacci sai jeka ka dawo take agidan tana nadamar sakasu acikin wnn matsalar duk ta gama tsorata sosai da abunda zai iya biyo baya idanunta nakan agogo every time tana kuma kirar aysha akai akai har ayshan tazo ta dena kulata.

sai dataga hudu ya wuce sann ta yanke hukuncin kawai zata canja kaya ta fita neman nur dan bakaramin guilt takeji aranta ba, ta haura sama kenan bada jimawa ba aka kira sallah kawai tay alwala tayi sallahn

ta idar lokcin past five da hijabin sallahn ajikinta ta rarumo wayarta ta sauko kasa da sauri tana daf zata sauka waje kenan tajiyo motsin motar mrs haseena, tsayawa tay jikin flower da mugun tsoro aranta tanajin wani irin tsananin rudewa ta ciki dan batasan ma zata fara ce ma Mrs haseena ba

tay nisa cikin tunanin abun cewar kenan saicaraf haseena ta hangota, da mamaki tace "Auta?? a mugun tsorace layla ta dago kai da muryan kuka tace "mummy" sai kuma ta sauya fuska da shagwaba ta taho da mugun gudu tazo ta rungume jikin mrs haseena tafara kuka sosai

..atake hanklin mrs haseenar ya fara tashi tafara tambayarta tana cewa cmon layla what is wrong?wani abu ya farune agidan
me aka miki????

layla na kkrin budar baki zatay bayani kawai sai sukaji wata bakuwar sallama a bakin gate din gidan

malam liman ne yaje ya bude ya shigo tare da wani hukumar polisawa su biyu..

cikin katse gaisuwar su Mrs haseena tace
ahhhh ahhhh ahhhh meyafaru kuma? how can i help you officers
...

police din ya matso kusa da ita yace sorry maam, bt we have come to question ur kids.

a mugun zafafe mrs haseena tace what!?? akan me...abeg get out of my house bana son iskanci..my kids are good kids officer
..saidan in wani sharrin za'a laka min

dayan police din yace ma'am please we have permission frm head office to ask them few question please.

Da zafin kai hassena tace abt what?

yace, We have information dat ur kids are involved in night party accident wanda ya jawo aka harbe yara bakwai a hannu da wasu civilians dukan su da karaya ajikinsu...

cikin dafa kirji haseena tace hasbinallahu wa neemal wakeel and you think my children have sumting to do with party and shooting? ihun da ta musu yasaka har makota ake jin muryanta..

this must be the work of my dump enemies i am not going to let you drag my innocent girls into this nonsense baseless accusations..

"layla ko kinsan wani abu akai??

da sauri layla ta girgiza kai tace mummy nifa bansan komi ba ni sallah kawai nakeyi..sai kuma ta fashe da kuka sosai..

Haseena ta inda take shiga batanan take fita ba haka kawai zaa zo har gidana ana menan aci min mutunci dan anga mune zamu lashe kujera to wallah ba isa asaka yarana acikin wann makircin ba

you officers u better leave my house kafin yau din nan ku rasa aikin ku..my child has already admited dat she dont knw anything
..dont let me file a case againts you for child abuse and emotional black mailing..she is just 15 uban me zata muku awajen party ehhhh

dayan officer yace toh ina yayarta, ance mana su biyune..

malam liman ne ya tsoma baki yace haba officer, yarinyar data gama ciwo gasar qur'ani dana tarbiya wa Abuja kake tsamnin zaka ganta agidan party, yanxu haka zaka samu tana karatun qur'ani abaya

kallon debar albarka da mrs haseena take musu tana kan latsa wayarta agaggauce yasaka polisawan kawai suka haqura suka yanke hukuncin katse bincikensun agidanta sai bai kara ce mata komi ba dan sun santa sarai yadda tadau zafin nan yanxu zata iya kulla musu sharri ko suji sunansu na yawo a social media..

sallama suka mata akan zasu dawo in akwai bukatar hakan

ta inda mrs Haseena take shiga banan take fita ba ta rakosu har gate tana zazzaga musu buhun bala'i

mama hauwa da maman sa'id tsabar gulma koro koro suka fito waje tsegege daga ita sai mayafi ta tsaya tareda mama hauwa sunata kallo kuma sunajin me ake cewa..

kusan wuce juna motar javeed dana polisawan yay tun akan titi amma dake ahnkli yake tukin ko kallonsa basuyi ba suka bar anguwan..

maman sa'id tay sauri ta tsare haseena ita da mama hauwa nan tafara bawa haseena labari ai jiya anyi kame yara kanana yan makarantar su nur sunje sun hada party maza da mata sunata shaye shaye suna zina shine har aka harbe wasu..

maman seed cikin shan ciki tace hmm To wallahi ni na ji da kunne na tun jiya da dare aka fara case, kuma ance su 'yan makarantar nan ne na icice suka je party nan kuma faaa ana zargin an sha giya wiwi har da zina Kuma shine ace har ‘yayanki ciki?!"

cikin gallaza mata harata mrs haseena tace Allah ya kiyaye,
aniyar kowa yabishi..

mama hauwa tace uhum ni dai na ji wai akwai wata yarinya da akace ta bace ma bayan kowa ya watse
Chapter 77 · 0% Book details