← Book details Nur Firdaus Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 68 OF 96

Sashe 68

Nur Firdaus Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Acikin anguwan maitama babban gidan hutawar hajya zuby yake saidai aciki cikine can ta arean da babu wani hayaniyar gine gine sosai, Dr simran tana isowa kowani hutuwar kirki basuyi ba washe gari ranar alhamis suka fara shirinsu na zuwa wajen hamshakin bokarsu na bayan aso rock, gashi komi da sukeyi a hankare suke sabida bawani aiki me wahala bane security spys na mufasa organisation su gano manufarsu dan tun bayan rasuwar mahaifyar javeed da poison ya kasheta aka dada tsananta ma ahalin mufasa tsaro
haryau ana bincikar ahalin a kasa kasa duk wanda aka kama da hannu akisan kuma sunsan hukuncin kisa ne babu makawa.

sungama shirin su tsaf, amma gabaki daya hajy zuby ba anitse take ba, tun jiya take kirar bokan baya dagawa, a tunaninta ko zai nemeta yauda safe amma ina, kuma wann lokcin ne kawai damarsu na zuwa wajen,ta riga tasan wann kwananakin gabaki daya mijinta da dansa javeed duk zasu halacci famliy business meeting basuda lokcin kansu har sai an kammala tattauna komi.

meeting din da za'a farashine gobe ranar juma'a baza'a gama sa ba sai can ranar wata juma'ar, acikin wkends din satin ne kuma zasuyi dan karamin family dinner ne tsakaninsu wanda ya kamata ace ranar ne zata takai musu Dr simran cikinsu suganta itama tagan su shiyasa gabaki daya bakaramin daga hanklinta tay da bokar be daga kirarta ba.

tana zaune cikin wata shiga na alfarma tasaka kafurar big women berreti suit dinta baki me dogon double breasted court da faffadan wando ayayinda take latsa tsadadden wayarta for the 5th time tana famr kiran boka, can saiga personal maid dinta maimoona ta yi knocking inda saida ta dau tsawon mintina me yawa kafin nan ta bata izini ta shigo ciki

kan mai aikin na kasa cikin ladabi tabi ta durqusa agabnta kamar baiwa sann tace"Ranki shi dade angama shirya muku mota..karamin tsaki hjy zuby tay muryanta cike da izza tace"kin gaya musu cewa yau bana bukatar security persnall Driver ne kawai zai tukamu?

maimoona tace ehh na fada musu hakan ranki shi dade

dauke kai tay batace mata komi ba tamike tsaye tareda gyara zaman turban din kanta, kasaitar matar babu lefi me zafice dan duk dama tasha ruwa, amma takalmin dake kafarta me tudu na limited gucci boat na manyan mata, yau she dresses formally cikin wata iriyar tsfta da kwarewa agayu da ajinta da kullum zaka gansa kamarna wata matar shugaban kasa dan dama tariga ta saba dasaka designer suits namanyan mata itakam duk dan sabida sabo da tay da aikin office datay ma ahalin mufasa, still ynx ma yakanyi wuya kaganta da native wears face sai in suna can gida ko wani hidima ya taso.

mikewarta tsaye keda wuya nitsatsun idanunta suka sauka akan kanwarta dr simran da haryanxu take kwalliya agaban madubi, ta cakala nan ta gyara nan she is just a perfectionist

kyabe baki Hjy zuby tay dahar zata gaya mata wata baqar magana me zafi sai kuma ta tuna akwai mai aiki atsakaninsu..

wani irin juyawa tay taharare me aikin a kasaknce tace mata "Get out..mai aikin ta fita cikin mugun barin jiki tabita da kallo me cike da kyama.

tana juyowa adake tace ke simran ya isa haka ki taso mu tafi..i cant wait anymore lokci na ta tafya.

akasale simran ta juyo da soson powder a hannunta tace "yaa zuby haka zamuje batare da yasan da zuwan mu.

cikin katseta tace i dont care. kawai muje aizai iya yuwa yana can ganawa da aljanu ne tunjiya nikuma i cant wait da kudina bani da lkcin jiran uban kowa sabida chance dinmu kenan.

simran batace komi ba ta aje soson ta mike ta dan karewa kanta kallo a madubi
as usual kayan nata yamugun matseta kirjin nan ya bulloko waje kamar zaka taba ya fashe...

straight skirt da wata shirt na Dior ta saka shara shara sai ta dora puma face cap akanta ta toshe da aviator cat eye shades ta dauki yar side bag dinta na toryburch ta rataya. ahnkali suke takunsu har suka kawo waje harabar gidan aka bude musu mota me tinted suka shiga dagasu sai personal drivern hajy zubyn suka dau hanyar jejin dake daf da bayan aso rock lokcin ana neman 11 am na safe.

drivern was careful enough againts security babu me tracking dinsu har suka isa gindin aso rock din, nan hjy zuby ta sauka da mamaki tanata kallon wajen gabaki daya ya sauya mata kirjinta na wani irin bugawa taga kamr ma bokar ya jima da yin hijira, bata gama aminta da hakan ba face saida ta zaga bayan wajen tsaf ta kare masa kallo har tana haqi bata ga alaman kowa ba

wani tukukin tsaki me cike da takaici ta sauke cikin rasa abunda ke mata dadi ta dawo motar ta dau ruwan sanyi a gora tasha snn tace ma drivern kawai ya maidasu gida yanxun nan...

itakanta simran bata gane kan addan nata ba sabida bacin rai datagani a fuskarta, dama kuma ita bata wani saka abun akanta sosai ba sai selfie dinta takeyi frm time to time da wayarta ayayinda hajy zubyn ta fidda wata karamar untraceble phone ajakarta da sabon lay aciki ta danna lmabar wata babban shuumar kawarta data san kan malamai ana ce mata hajya Mansura shehi bakalori dake kuzape cikin abujan.

bugu daya kawartata tadauka kenan kowani gaisawar arziki basuyi da juna ba kawai out of no where wasu manyan bakaken motoci siffar van irin bullet proof din nan suka zagayesu da bindigogi.

wani irin luiiii hajy xuby taji ta jefar da wayar akasa simran tabi ta razana ta daga hannu sama, gashi suna tainda babu mutane sam kuma asirrince suka fito babu hali su danna alert dake jikin motar wa security na gidan mufasa bare akawo musu dauki,.

nan wasu kattin maza sanye da face mask suka fiffito suka bude motar suka kwamuso hajy zuby suka turata van din snn suka dauko simran cak itama aka sata ciki, ana aje su akay sedating dinsu da alluran gushar da hankli, drivern sun kan sumar dashi sukayi da duka da naushi sann suka kwace key din motar a hannunsa suka jawo har dashi da motar sukabar wajen agaggauce.

gaba gaba cikin jejin dake wajen suka jasu har saida suka zarce dasu cikin wata boyayyar anguwa cikin wata katafaren gida me tsayin gate da katanga aka shigar dasu, nan da nan aka wuce dasu wani babban falo direct aka watsasu akasan carpet ita da simran drivern kuma aka kaisa wani daki aka dauresa akan kujera.

basune da farkawa daga baccinsu ba sai can ana neman karfe hudu na yamma,

hajy zubyn ne ta fara bude ido after hours of shut down wani irin nauyi taji kanta na mata tarike kan tana tashi dakyar kanta a kulle dan idonunta da basu gama wrwarewa ba tadorasu akan wasu katoton hotonan mijinta abango dana dansa javeed mufasa ankunna wasu balamayen jan candle akasarsu sunkai guda bakwai sunaci da wuta snn kowani hoto an cakka masa wuka..

ahnkli hajy zuby taruntse idonta dan tasan tay mummun rashin saa yau dan batay tsammanin fitowarta witout security zai jawo ta shiga hannun daya daga cikin makiyan mufasas ba.

zaman shekara sama da arbain tay tare da mufasas dan haka tafi kowa sanin irin tarin maqiyan da suke mamaye dasu

acikin tsananin kaduwa da tsoro ta daga kai tanamai karewa wajen kallo wanda yay mata kama da shrine dan falo ne amma kuma yanayin falon is not normal,
candles, kifiyoyi, allurai, gumaka, dolls da madubi, wasu irin fake kwalaban rose water, wukake da jan kyalle,da abubuwa na sihiri sune akota ta ina..

da kyar ta dawo hayyacinta ahnkli ta mika hannu tafara tada simran wacce da kyar ta motsa tana mikewa dataga inda suke kawai tasaka wani irin tsoraccen ihu taja numfashi sama kamar zata suma, cikin yanayin panick attack tafara cewa "what the fuck? yaa zuby ina ne nan?
...ihun datay yasaka wani katon mutun ya shigo da sauri suna hade ido hajya zuby tayi wuf ta tunkaraso babu tsoro a idonta ta cakumosa tace "who is ur master,..i demand to see him ryt now..cikin daka tsawa ta karashe maganan wanda ko gama rufe baki batay ba wata murdadiyar muryan mace ya sauka acikin dodon kunnenta

,...kusan a kangare hjy zuby ta sake mutumin ta juyo in shock dan batay tsammanin wai muryan mace zataji anan din ba

juyowarta ke da wuya ta hada ido da wata ginanniyar mace tsar a tsaye, farasol kamar zaka taba fatar jikinta jini ya fito, koinanta a murje yake dukiya da hutu yagama ratsa mata gangan jiki gata dai babu yabo ba fallasa saidai kana ganin damatsunta kasan karfin doki take ji dashi..

farin bubu gown yelwatacce na leshi ta saka ajikinta haryana jan kasa, suman kanta baki kirin ta barbaza shi yazuba mata har gadon baya taci kwalliya irin na mami water tana tafiya tana swinging zuka xukan diamond nails dinta fuskarta babu alaman wasa akai...

cikin tattaro makai nitsuwa hajy xuby ta kare mata kallo san tace "who are you lady and...why am i here?
see who ever ure i am very sure you know how dangerous my husband is..

cikin katseta da wani irin mahaukaciyar dariya matar tace of couse i know,..sannu da zuwa lady zuby of the mufasas, ta kara fashewa da dariya " 'oh no ashe baki kai wann matsayin ba fa.. ure just hajiya Zuby othman the mistress whore ex-sectary of attah mufasah....
..ouchchhhhhhhh...

kamar wani saukar ruwan wuta haka maganan nan yaje ga cakke kirjin hajy zuby nan take jikinta ya fara rawa rawa kamar zata fashe dan haushi

zatay magana cikin fushi matar ta katseta tare da nuna musu wajen zama akan capert din tace su zauna, suna zaman itama ta zauna agabansu ta zuba musu ido saida tazo da kallonta dede kan simran sann tay dariya tace ohh wann ne yarinyar dakikeso ki shigar cikin ahalin mufasan?

da wani irin jiji dakai da giggiawa hjy zuby tace ke malama ni ba wann maganar ya zaunar damu ba, i demand to knw who the hell you are... wawiya, matsoraciya kawai saida kika ga babu security ne zaki iya sawa akamamu??
Chapter 68 · 0% Book details