← Book details Nur Firdaus Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 17 OF 96

Sashe 17

Nur Firdaus Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

cikin idonta ya kalla yaja wata arniyar tsaki me sauti "malama wann tsawar dakike min da wa yayanki kikeyi da zaifi miki amfani, na yarda ni yaro ne agabanki amma aikinsan da tarbiyata kika auro ni bazakixo keda yaranki ku kasheni da baqin ciki tun lkcin mutuwata baiyi ba

ruwan idanunwanta ta zuba masa ganin yadau abun da zafi sosai atake sai ta sauke muryanta cikin lallami tace toh shkn please tell me exctly what happen..ina sauraranka.

wani hade rai yay dacan kamar bazai bude baki ba saiya tuna cewa haseena kamar iskace inhar ta bar nan wajen ba lallaine ya samu wani cikakken dama ba gashi bayason ya kara batawa hon farida bala ranta musmn akan wnn maganar.

nan ya fara hardahada mata labarin karya dana gaskiya ya fara gaggaya mata cewa wai har lekensa a bayin gida anayi, snn yauda safe ma anzo masa dakin naked ana seducing dinsa akan gado, yace akan gado ya tarda yarta daga ita sai breziya,kuma daga zarar zata wuce sai ta gogi jikinshi, kuma koda ya tambaya tace wai takarda ta kawo ayi mata signing zataje gasa and all the threath wanda duk baigaya mata asalin abunda ya faru ba...

amfani kawai yay da abunda layla ta masa ya yi makamashi ma sharrinsa snn ya dorasa akan nur firdaus, yy hakan ne badon komi saidan yanaso ya samu wani cikakken daman dealing da layla batare da anyi suspecting dinsa akai ba kamr dai yadda hon farida bala ta umarce sa daxu.

sosai hanklinta ya tashi sai kuma ta tuna cewa nur firdaus ce fa take nemanta akan maganan saka hannu akan takardar gasa..

ranta taji ya hargitsa ya baci amma duk da haka ta nitsu, she kept asking him to be clear with the narration, tanemi sanin wayace acikin yaranta take masa haka amma yaki sam ya furta mata kai tsaye saidai yay jam'i dan ya dada rikitata,

ta inda yake fita bata nan yake shiga ba, yace abun ya jima yana faruwa turane yakai bango, kodan yace ta haihu masa shine zata bullo masa da wann salon makarcin? ko kuma burinta na siyasa take so shima ta cimma dashi? babu irin zazzafar baqaqaen magana masu rikita xuciya da bai jefeta da su ba kuma sosai ya nuna mata yay fushi

karshe ma zatay magana cikin
katseta ya mike tsaye yana huci yana hura hanci yana cewa" look woman you have only two choices, ko ki magance wann abun ko kuma duk randa ya sake faruwa zaki nemi ni acikin rayuwarki ki rasa...i love you soo much haseena but i cant deal with bull shit i cant trust u anymore.

hakuri ta dinga bashi har kamar zata masa kuka amma ko ajikin sa saima cewa yay bazai dawo gidan ba sai ta gama magance matsalar yaranta akansa dan bazasu raina masa hankli ba

zuciyarta babu dadi suka rabu...

Bayan mintoci kadan da rabuwarsun ta iso gida cikin fushi ko amsa gaisuwar mlm liman batay ba Tana sauka daga motarta ta shige cikin gidan kai tsaye, anan ta sami Layla da Nur Firdaus a zaune a kan kujerar babban falon gidan,laylah ta saka wani plain blue dress daga cikin kayan nur firdaus,dukansu sunyi wanka sunyi kyau sun saka kananan kaya..

basu hankara da shigwoarta ba sukaji dakakkeiyar muryanta akansu..

"Nur Firdaus!"

Ta kira sunanta da karfi, tana tahowa kusa da ita daf a mugun fusace

suna hade ido tace "Menene wannan abin da nake ji akan ki? kifadi min,Me ya sa za ki bullomin da wani halin banza da zai jawo min abun kunya irin wnn? what the hell is wrong with you ehhhh.

Nur Firdaus ta mike tsaye gabanta na faduwa sosai ta girgiza kai da hanzari, hawaye suka cika idanuwanta amma be hanata yin magana cikin girmamawa ba

tace mummy har yanxu de ban fahimce me kike magana akai ba,dan ba zan taba yin wani abu makamancin abunda zai sakaki jin kunya ba kema kin sani sede in mijinki yayi wata magana da baki tantaceshi ba kuma kamata yay kigayamin dan insani..

Haseena ta kalli 'yar tata da fuskar mamaki da takaici.

"kikace bantantance ba? dont u play me for a fool...akan wane dalili zai sa ya zarge ki da wannan abu inde baki aikata ba? ko shin bakece kikai masa takardan signing na gasarki yau da safe ba, nur firdaus why are u dis disgustingly desperate

Nur Firdaus ta ja numfashi mai nauyi.
tace "mummy Bani nakai masa wata takarda ba. Amma ya kamata ki tambaye shi mena aikata masa na abun kunya daya gaya maki..

Layla, tana tsaye a gefe dede nan ta yi kokarin shiga mgnan mummy pls ki saurare big sis Ni ma na san ba ta da laifi. Sadat ne kawai yake neman...

rai abace mrs hasena tadaga ma layla hannu cikin daka tsawa tana cewa "stay out of this laylah, ke babu ruwanki da wann mganan, da wann munafukar sisternki nake magana datake neman banzatar da jikinta agaban mijina, nur yaushe kika balaga da harkinsan kiyi making moves da zai ja hanklin namiji akanki? who raise u dis way amma dai bani bako??

nur tafara jin maganan na mata nauyi hawaye suka fara sauka mata sosai

"look at you ure just seventeen, dont be a shameless pretender.
toh wallh inde asiri na kikeson tonawa a duniya toh naki ne zai tonu banawa ba. sede abun kunya ya kare akanki.. domin kuwa naji duk abunda kike ma sadaat agidan nan inbana nan kuma nasan bazai min karya ba. Nur Firdaus, idan gaskiya ne ba ki da laifi, zan binciki wannan maganar sosai. Amma idan na samu wata shaida da ke nuna akasin haka, kada ki yi tunanin zan dauki wannan abu a sauki. this is my last warning to you!!! cikin wani irin zafin rai ta furta mata haka

Nur Firdaus ta share hawayenta da suma zubo mata bazata tanata kallon mahaifiyarta cikin takaici, abubuwa dayawa na mata yawo akanta amma haka ta dannesu sabida ta karantu da ilimin qur'ani tasan cewa uwa duk yadda take tana da muhimmaci sosai dolene a girmamata

cikin danne fushinta da muryan girmamawa tace toh shikenan Ki bincika mummy ai za ki gane gaskiya idan kin yi binciken ko..

Haseena taja tsaki me yawa tajuya ba tare da wata kalma ba, zuciyarta cike da mamaki da fargabar abin dake faruwa da iyalinta wanda har yanxu kwakwalta bai gama daukawa ba

jin zancen bincike yashigo ciki layla ta mike tsaye ta dan ruko hannun nur fidaus da wani irin makrtaccen muryan kuka"Big sis dan Allah kibawa mummy hakuri kawai maganan nan ya kare anan wajen please lest not dig dis things up..
mummy fa yar siyasa ce bana son hakan ya shafi mutuncinta..

cikin katseta da mamaki nur firdaus tace Idan anbincinka akasan gaskiyan ai gaskiya bazai taba bata mata siyartaba saidai ma ya dada tsaftace shi.

kirjin layla na bugawa da guilt ta dubi mummynsu da hawaye taf a idonta cikin rawan murya tace mummy kima big sis uzuri kinji she is sorry pls mummy

mrs haseena ta kalle layla tace autata ban yarda da wani uzuri ba. nur firdaus ce sanadiyyar wnnan matsalar, ta yaya zan ci gaba da tsayawa cikin siyasa idan ta ci gaba da bata min suna?

sosai wann kalman ya hatsala Nur Firdaus
da karfi tace mummy meyena taba aikatawa dana bata miki suna?wallahi ba ni nakai masa lettar gasa ba! Sadat ya miki karya ne kawai saboda wani dalili da bazan iya fahimta ba, inda kuma kinason kiyi min adalci da zaki tambayeni meyafaru da zan iya fayyace miki komi, amma is alwys like dis baki taba saurarata ba..

"Saurararki? Me ya sa zan saurare ki? Ke da kullum kike kawo min matsala? Kece kullum kike bata tarbiyyar Layla da munanan halinki, ni be gayamin direct wacece acikin ku ba, amma ni nasan kece nur firdaus kece me taurin kan, shiyasa bazan ji wata banzan bayaninki ba, ko kin tabaji ance layla tana da samari? kece kika san wann dabiar toh wallhi karki sake ki kawomin wnn abun kunya cikin gidana kuma akan mijina nagaya miki kenan..

Nur Firdaus tagirgiza kanta cikin tsananin takaici hawayenta suna kwarara daga idanuwanta sosai..

zuciyarta na tafasa tace hakane dama i am alwys wrong a idanunki mummy amma bakince zaki bincika ki bincika..

daga nan sai bata sake cewa komi akan maganan ba, wajen ya dauka da shiru. saida ta tattara nitsuwarta tashare hawayenta snn tace abu na biyu, Layla tana fama da wasu matsaloli tun da dadewa, yanxu kuma ya fara shafar lmrin karatunta, Malamanta a makaranta sun sha neman ki amma baki responding, yau G/C unit sun kirani kan cewa laylah ta dena maida hankalinta a karatunta saboda abubuwan da ke faruwa da ita a gida, inde bazaki iya saurarar matsalata ba ai zaki saurare wann tunda ita layla kince babu ruwanta.

mrs Haseena ta katse tacikin tsawa ke yarinya Kada ki kuskura ki juya maganar nan ya dawo kan layla, dan Idan Layla na da matsala, duk kece sanadi sabida awajenki ce take koyi da dukkan wadannan halayen Ba ki taba zama misali na gari ba.

Nur Firdaus ta fusata
sosai cikin kuka tace mummy ya isa haka kamar ke kin taba zamowa wata abar misali agaremu, wai Yaushe ne ma kika taba tambayarmu halin da muke ciki? Ke kullum siyasa ce a ranki, bakisan me zan iya aikatawa da wanda bazan iya aikatawa ba shiyasa komi aka fada akaina kike amincewa, nauyin kulawa da layla akanki yake ba akaina ba, ko da yake bayau aka fara barin min nauyi ba tun da baba ya rasu nauyin kaina ma nina rike. kuma yanzu kina nufi ke kadai kike da gaskiya?

gabaki daya layla ta rude ganin yarda nur firdaus tay maganan da tsananin fusata da fushi. dan abune me tsananin cin rai ko daga yanayin yadda haseena take nuna bata amince da ita ba ko kadan. kuka take mai sanyi amma kallo daya kamata zakaji tabaka tausayi sosai.
Chapter 17 · 0% Book details