← Book details Nur Firdaus Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 56 OF 96

Sashe 56

Nur Firdaus Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

kasa iya daurewa yay jikinshi harna rawa ya bude text din yana gama karantawa yay wata kayattacen murmushi mai mugun taushi, miƙewa daga kwance yay ya jingine gadon bayansa da pillow sannan ya hau rubuta mata amsa
after like 2mins tana rungume da wayarta a kirjinta taji ƙarar shigowar sakonsa itama da sauri ta farga ta bude tafara karantawa sai tasha mamaki sosai dataji cewa wai "He is fine".. cikin sauke ajiyan zuciya me nauyi ta rubuta masa wani sakon, "_..just wanna let u knw dat i miss u trout the day, tunda nidai yau baka tuna dani ba ko.."_ sakon nata yana shigowa ya bude tareda kai wayar kan goshinsa ya buga kadan yarasa mesa shibai iya irin karyan nan na masoya ba, atake sai ya rubuta _"can i call u now habibty..please?_
saida tadan ja snn ta maida masa amsa aikwa saiga shigowar ƙirarsa sharply bata daga ba sanda ta dan karasa shigewa cikin bargonta ta lullube jikinta har izuwa kan ta snn ta amsa wayar a hankli cikin sanyin murya"tace salam habibi, wani irin maraitaccen ajiyar zucya ya saki snn ya lumshe idonsa sosai
yace..wasalam rabin raina, afuwan nasan nayi laifi but can i go ahead n xplain myself? "dan shiru tayi..shima bai kara cewa uffan ba,wani karamin shiru ne ya gifta tsakaninsu sunadan shakar nunfashin juna,cikin wani irin kasalliyar yanayi mai fitowa da maraitaccen shauki da son yaga ya sakata magana yace waime ya hanamin amaryata bacci ne yau?..bakinta tadan turo gaba a dan shagwbe tace "uhm aizaka tambaye ni tunda u were not picking my call, ahnkli cikin sigar damuwa tace "Adnan i was kind of worried abt you knw har na dauka ko baka da lafyane..
cikin sanyin yanayi da mairaice sautin murya yace "hey, i'm really sorry, dan Allah kiy haquri nur dama mama ne muka dan samu tsabanin fahimta da ita akan batun zuwana wajenki yau..but..

takatse shi cikin sauri...tace"no its okay... inde dan itane na haqura adnan ai basai kamin bayani ba dan she deserve all ur attention even more than i do. u knw ance an kusa bata babban kujera maybe she needs u close to her.

"murmushi mai dan sauti ya saki gameda jin dadin abunda tace har cikin zuciyarshi, cikin sauke ajiyar zucya sai yadan yi shiru, can saiya fara tambayarta abubuwan da ake shirya musu itade bata gayamai taje gidan kawunta ba, hira kawai sukayi akan gasar inda ya samu daman mata bayani cikin tausashiyar murya cewa bazai samu zuwa mata,

murynsa gwanin tausayi yanata cewa nur kiyi hkri bana son in fada miki abunda ya farune sabida kema bazaki fahimce ni ba nikuma nafiki sanin wacece mahaifyta, she doesnt really need me, my mum has this intense selfish attachment with me, kwata kwat bataso nay nesa da ita for no good reason ai tasan kina da muhimmaci awajena
kuma fa tun zuwan mu kasar nan nake tuna mata cewa i wnt to spend tmrw with u amma kiga saida na shirya zan taho kafin nan ta hanani zuwa dan Allah nur kiy hkri kinji habibtyna? daga munyi auren nan i will fly u to sumwhwer far and safe daga ni saike inda zamu spending time dinmu tare nd i promise i wll make this up to you in muka dawo Abuja kinji???

yadda yay maganan sounding soo worried and intensely in love yasaka yaƙara bata tausayi sosai, ahnkli cikim tausashi tace" Adnan pls calm down "naji na kuma fahimta kadena ban hqri i do understand ur reason wallh babu komi awajena, kuma ai mahaifiya tawuce wasa, nima bazanji dadi ba in muka taru muka bata mata ranta akan son zcyarmu kawai kabita ahnkli and dont worry abt me i will be fine..

ajiyar zcya yay me matsanancin nauyi snn yace nagode Nuri na,i just cant wait to marry you..adan kunyace tay masa murmushi, muryansa taji na ratsa maya dodon kunne "so u wanna tell me how ur day went? wani hmmm taja cikin boyayyar sautin sauƙe ajiyar zuciya dan tama rasa mezatace kawai tace"..i missed u alots today, dats all..dada kwantar da muryansa kasa yay yace wow, really?..toh lets do one thing mana, tace mene?yace how about inna dawo abuja sai kawai mufara shirin aurenmu straight away, like eveyday i take u out for our weding plans..you knw....

yar dariya ta saki cikin mamakin jin yafurta hakan duk dai tarasa mesa Adnan yake zumudin auren nan na su sosai tace"take me out for weding plan kuma? yace yeah lets build great memories toghter. lets go for photo shoots, spa day, candy shops,lets draw our marriage dreams on beach sand,lets take sooo many memorable pictures da zamu nuna ma future kids dinmu dan susan munyi soyayya me shegen dadi kuma har abada bazamu dena soyayyar ba.

dariya tayi mai dan kara dan bata san ma mezatace masa ba"
but kai ai bakason wajen hayaniya bare daukar hoto..."yana murmushi sosai yace forget about what i dont like indai hakan zai sakaki cikin farin ciki i owe u dat, i love u soo much habibity..

..ahnlkli cikin jan aji tayi ƙasa da muryanta tace i love u more, okay lets see what will happen Allah ya dawo min dakai din lfya

...kamar da wasa daganan suka tsunduma cikin hirar yar tsare tsaren abun su da zasu nayi atare
.,hirar tasu mai dadi mai sanyi da saka nishadi takaisu har wajajen ƙarfe uku na dare take Adnan ya warware kamar bashine ya wuni a daki da uban yunwa da tsananin fushi ba.

ahakan ma da kyar ta lallabashi yay bacci yau tsabar taji dadin baccin kusan kiris ya ragemata ta rasa sallahn asubahi.

Ata dayan bangaren kuwa daga cikin gidan Hajiya Mammy gabaki daya Brigdr. Javeed mufasa ya kasa samun nitsuwar bacci dan kuwa koda ya runtsa saikaga yadan firgita yafarka dan kuwa Wannan murya ta nur firdaus tana cikin zuciyarsa wacce ta fi kama masa da wani abu da ke kusa da shi fiye da yadda yake numfashi.

can cikin tsakiyar dare ya sake tashi yasauke kafafunsa kasa hankli, Sai kuma ya tsinci kansa dajin shaawar komawa gaban zanen da ya yi a daren baya,

Ya zauna akan chair yana kallon zanen wann murdadun hannunsan suna tafiya a kan layin fensirin daya kerata dashi,zucyarsace take amo da tambayar shin menene wann haukar da yake shirin faruwa dashi? shide Bai san amsar ba Amma ya san yana da bukatar ganosa cikin gaggawa dan bai taba tsintar kansa acikin wnn yanayin ba.

yajima yana zaune ahnkli har sassnyar iskan asuba ya fara ratsowa ta cikin tsadadden farin labulen windon dakin daya budeshi dan shi mutum ne da yake matukar kaunar jiyo hayaniyar tsuntsaye tareda natural iska dake kadawa ta safiya mai sanyi.

Lkcin Hannunsa na riƙe da wata charcoal pencil baki kirin, ahnkli ya kwance takardar zanen da ke manne da board din yasaka wani sabo kall akai, dan Gani kawai yake yi kamar inyana zanen yafi tunanin waccan fuskar da ya gani a makabarta.

Idonta… da bakin ta…da yadda mayafinta ya dan sauka daga goshinta lokacin da iska takada, shidai yasan karamar yarinya ce amma fa Kyakkyawa ce, tabbas. sede aransa yasan ba kyaunta bane abun burgewan, da akwai wani abu mai ƙarfi a cikin kwayar idanunta daya kasa fice masa a kansa gabaki daya shikansa bai san dalilin da yakesa hannunsa jin shaawar fara zana fuskar ba sabida ji yake kmr kwaklawar kansa ne yakeso ya fitar da ita a tunaninsa a fili.

Zanensa ya soma ayyanawa a bayyane focusing on gashin idonta mai tsayi da dogon hancinta da laushin laɓɓanta bai daga kansa ba har saida ya gama snn Ya lumshe idanunsa na ɗan lokaci ya kara duba zanen. yaga yauma the same Fuskace kallon nur firdaus ya dingayi shikansa bai san lokacin da ya sauke wata nannauyar ajiyar numfashi ba.

5:am na bugawa ya bar zanen a bude ya nufi bathrum ya watsa ruwa yay alwala ya fita can masallaci bai dawo dakin ba sai can around 7:am...

dayan zanen ya dauka akasa inda ya aje ya hadasu waje guda da sabon dayay yay pinning dinsu da pin akan board din da kyau yana dan dada gyara musu fasali, a Daidai lokacin da yake kokarin saka touch na ƙarshe akan lips din nur din yaji alamar kofarsa ta buɗu ahnkli wanda tin kafin ya farga ya juyo yaji saukar sautin murya abayansa da dan karfi...

da tsananin mamaki tace "Javeed"?

yana shako muryan simran yay tsamm ko ɗago kansa daga kan zanensa beyi ba kuma be amsata ba.

Simran ta tako ahnkli tana dan dingishi cikin doguwar red designer sleeping gown dinta, mai shegen laushi da tsada, Kansa daya kifa akan zanen take kallo sai kuma taji wani irin takaici ya gumeta tanajin kamar ma da batazo ba amma tasan babu inda zata turkesa ya kulata sai nan cikin dakin baccinsa.

wani gigimammen uhm uhnm tay gyaran murya da karfi idonta na dubansa da kyau.
shidai Javeed bai ce mata uffan ba Sai da hannunsa yaɗan matsa yasaka wani touch a saman idon zanensa snn ta iya shako sautin ajiyar zcyarsa da alama Bai taɓa nuna sha'awar wani abu kamar wann fuskan ba, bare ma tasan tunda javeed har yasamu lkci ya zauna cikin dare ya zana fuskar nan tsaf tsaf to babu makawa akwai wani boyayyen abu akasa.

Simran ta ɗan harare shi sama da kasa jikinta yana ɗaukar zafi tare da jin tsananin haushin rashin samun cikakken kulawarsa akanta.

tana tsaye harya gama gyara zanen sann ya rufe fuskar ahnkli, cikin karairaiya da sanyin jiji dakai takaraso kusa dashi
tana wani kyabe baki murya ciki ciki take kallon board din tace "wai me yasa kake bata lokacinka wajen zana wata mace naga ai kajima kana nuna ma duniya kai baka damu da mace arayuwarka ba ko, tunda dai ganinan agefenka For good 35yrs amma kaki kamaida ni mata..

dede nan Javeed ya ɗago mayun idanunsa a hankali yana kallonta dasu da irin mugun kallon nan mai sanyi da ba a gane ma maanarsa musmmn inyajefe mutum dashi.

Muryarsa kamar an sare ice. ya mata kallo daya snn yace "How can i help you doctor.,
Chapter 56 · 0% Book details