← Book details Nur Firdaus Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 64 OF 96

Sashe 64

Nur Firdaus Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

ji kawai tay hjy mammy ta dada riko hannunta tana dan murmushi cikin katse mata tunani tace yan mata zaki iya daga kanki karkiji tsoro dis is my beloveth grand son..

dakyar nur tadan gyada kai sede tunkan ta daga kai javeed har yazare shades dinsa calmly ya sokata cikin aljihu...

nannauyar ruwan idanunsa yay caaa ya zubasu akanta ko ajikinsa yazuba mata ido da piercing looks insa tsaf yana mata kallon kurilla batare dayace mata uffan ba.

yanagin kamar babu wani abu gameda ita wanda baiji ajikinshi naturally ya burgesa ba, har cikin kokon zuciyarsa yake cewa
tafi ta zanensa kyau da tsari,yana kuma jin ajikinsa cewa itace missing ribs dinsa nd he cant be wrong abt this feeling dan itace mace akaro na farko dayaji hakan akanta tunda aka haifesa yazo duniya....

fuskar nan tasa a tume ba asake ba yake kan kallonta amma cikin ransa is busy scheming nd screaming fire nd passion with the kind of exciting life dayake tunanin zai iya shimfidawa da ita dan wann yarinyar tashi ce,koma waye ubanta a duniyan nan yasan de shi javeed attah mufasa shine mijinta
kuma sai ya aureta snn suyi soyayya me tsayawa arai snn ta haifa masa y'aya masu shegen kama da shi da ita...

lokcin ko yanka ka za'ayi da wuka bazakace abunda javeed yake rayawa aransa bakenan.

kasa dagowa nur tay ta dubeshi dan duk yadda zcyanta ke bugawa da mugun karfi wani abu ne taji gaba daya nabin jinin jikinta ga heartbeat din yafara aikin nashi kamar mai shirin fitowa waje, haka kawai mutumin nan na makarba ke fado mata arai aikuwa take taji idonta ya cika da ruwan hawayen tsoro tafff har saura k'iris ya zubo tabi ta dannesa da karamin murmushi

tsayawa tayi still a wajen ta kasa ko da k'wak'waren numfashi karamin shirune ya gifta awajen isowar hadiza talba da over priced smoky turarenta yasaka Nur din takara dawowa hayyancinta

Gabanta na faɗi tanata rokon Allah aranta kar ace shidin ne zcyarta na cewa
"Ya Allah... shine...? shine mutumin da na gani makabrta..."
wayyoooo Allah na shiga uku na.

karamin shirune ya gifta idanun javeed suna daure akan macen da ta tsaya masa arai snn yafi tsarawa a cikin zanensa wanda yau gata a zahiri tana numfashi haka kawai yasan Ita ce rabin ransa nd he is meant to make dis into his reality dan yasan saka mace ta soshi ba wani abu me wahala bane awajensa barema yaga nur din yar yarinyace karama.

hajy mammy ne ta dan dafata snn ta matso da ita kusa daf dashi tace Tauraruwar mu ce ita ta dauki lambar yabo fiddausi say hi to my grandson, a hankali nur ta daga ido sama kamr mai tsoro tsoro nan da nan kuwa Idanuwansu suka haɗe cikin na juna numfashinta taji ya dauke cak dataga tabbas shidin ne.

Cikin daƙiƙu dukansu sukaji duniyar tana janye musu da baya inda Babu wani motsi saina bugun zuciyarsu da bbu me jinsa sai su.

Nur ta kasa magana dogayen gashin giran idonta na rawa rawa, jikinta taji nayin sanyi.
javeed din ya hadune har batasan ya zata iya processing ko ma fassara haduwarsa acikin brain dinta ba

tun daga tsarin kyaun fuskasrsa har yakai ga hadadden dressing dinsa me aji he is giving her brain this dark Alpha sigma male vibe, maturity and elegance is all over him like a cloak.

tarasa yadda akayi ta rude kawai Saita ɗan sakar masa murmushi me taushi wanda atake ya cikeshi da jin wata sabuwar shaukin zuciya dan kodede na secnds daya be iya janye idonsa acikin nata ba. tabbas itace wacce yake zanawa cikin dare amma gani yake kamar ta canza masa ta kara masa kyau yaudin sosai

hawayen tsoro da ya boye kansa a idonta ne ya silalo tagefe daya cikin sauri tay saurin sharewa dan tsayawa yayi yanata kallon cute face dinta, dan k'aramin lips inta da idonshi ya sauk'a akai,yadda damshin hawayen ya gangaro har kan cute lips din yabi da ido yanajin duk wata sassa na gabobin jikinsa na amsawa da wata sabuwar baqon lamari dan betabajin irin shaukin shaawar mace yanamai tason masa ba sai daya dora idonsa akanta.

ita dai tana tsaye ta kasa motsi tayi ƙoƙarin sunkuyar da kai amma ina can dai tadaure muryanta ƙasa-ƙasa tace mishi "i...i..ina wun..wuuni si...r ..sir..

bai amsata ba ya ɗan jinjina kai yamaida kallonsa ta gefen kakarsa da smirks Hajiyah Mammy ta kallesa da murmushi mai cike da ma’ana she knew in her hrt javeed already liked the girl saidai kuma tasan halin shi, he is unpredictble hala tana kawo masa maganan yarinyr zaice mata a'a.

ahakli murya kasa kasa cikin raha tace mishi general wont u congratulate her she is my champion fa.

nur ta rasa yadda akayi ta harta ma shako maganansu akunnenta sai ji tay yanace ma kakartasa a tsime wai he had already congratulated her.

satar kallonsa tay duk da yadda zuciyanta ke bugawa dai tasan bai yi congratulating inta ba amma yacewa tsohuwar wai yayi.

wani irin strange feeling takeji akansa tanata kkrin dauke kanta suka kara hada ido wnn karon sauri tayi ta sauke nata dan deep grey eyes dinshi na sata taji wani iri iri sosai..

sai asann taga hadiza table dake gefenshi farinta nan dau gata siririya tawani zubo mata idanu,..cikin kwaco makanta nitsuwa tace ma hadizan "ina wuni", hadizan tay kamar baza ta amsa ba har saida suka hada ido da hajiy mmy ne tace "lafiya" a dak'ile, duk da bata san yarinyar bata taba ganinta ba amma sai da taji bata sonta sabida gani datyi Allah ya zuba mata wani irin kwarjini da kyau na musammn wanda bata taba gani ba.

batare da bata lokci ba hjy tace toh tunda kungaisa sai ayi pictures ko,javeed ya dan runtse ido ya kalle kakarsa alaman bai son hakan sede tun kan yay korafi tace is your mothers tradition ko kamanta ne muna da hotonan duka gwarzayen wann gasar agidanmu? comn lets honour dat.

nan take PAn hjya ta kirayo photographer dinsu da sukazo dashi yazo ya fara arranging yadda zasu tsaya,nur ta mannu da gefen hjy mammy javeed na daya gefen, mai hoton har ya gama jerasu sai kuma ya cewa nur din ta dawo gefen javeed ta tsaya sabida kayansu is a really nice combo, na shi cool grey ita kuma black, akace hadiza kuma takoma daga dayan gefen hjiya mmy gashi ba waya a hannunta bare ta kira Dr simran ta mata gulma dan kana kallon fuskar hadiza zakasan bataso da akayi wnn canjin ba, sai hararar nur takeyi kasa kasa aranta cewa take who is dis damn girl haka? kyau da haduwarta yasa batawani nitsu tamata kallon yar karamar yarinyar bama all she knws is tasan simran bata barin kowace irin mace kusa da javeed

nur dake jin kanta na juyawa tay kamar bata ji me hotonma yace ba haka taja ta tsaya a inda take taki motsi har sai da ya sake cewa fairy princess ki dawo nan yi hakuri kinji, sai yakara nuna mata gefen javeed. hjy mamy ta kalleta ta dan gyada mata kai a hankali ta taho tana tafiya har tazo inda yake nuna mata din ta tsaya gefen rigarta ta kam dan tsayawa tayi amma gaba dayanta ji take kamar a kan kaya take tsaye.

tsayawan da tayi a gefenshi ne ya sashi jin kmr ma zata iya karanto abunda ke gudana a ransa, shi so yake agama hoton nan gabadaya ya bar wajen dan gabaki dayanshi wani iri yakeji ajikinsa, sai da mai hoto yayi clicking guda biyu masu kyau sannan ya tsaya aka mata ita da shi da hajy mamy sukadai.

hadiza kuwa sai satar kallon javeed takeyi yadda idonsa ke yawo akan jikin yarinyar tana shan mamakin hakan har cikin ranta

nur kuwa har wani fitsari fitsari tafara ji dan bata isa ta daga ido sama ba sai taga ita mutumin nan yake kallo, ana daf angama hoto hjy mammy ta fara marairace masa tace ya tsaya suyi daga shi sai celebrant din.

lokacin dago kai kawai nur tayi ta dubeshi da tunanin zaice aa sai taga shima itan yake kallo, maza tayi ta dauke kanta ta kara rike gefen rigarta da karfi har hannunta na tara gumi dan gaba daya a tsorace take dashi.

karshede tsayuwa sukayi dukkansu biyun dan babu yadda suka iya, mai hoton ne yace javeed ya dan matsa kurkusa da nur sabida na album ne, matsawa yayi danso yake ayi a gama yabace awajen ita kuwa tana ganin ya matso tamatsa da baya nesa dashi a take kuwa yatuna abunda bata kauna caraf taji yakama hannuntan da batason ataba din yawani jawota harsaida ta kusa fadawa jikinshi..

nan take fitsarin datakeji yay kamar zai sauka ido ta wara ta bishi dashi taga bama ya kallonta ga hnunta sakale da nashi tam

ta juya ahnkli taga hankalinsu su hjya mammy kamr ma baya kansu hadizan ce kawai taga ta kura musu ido kamar wata mayya tanata kallon su, da nur tadan kalleta ne ta bita da tuwon wata muguwar harara, kanta ta dauke daga duban ta tsaya na dole har me hoto ya gama daukarsu..

yana gamawa da sauri tadan harzuka zata kwace hannunta cikin nashi saiji tay ya kara tamkewa sosai tare da matsowa daf da ita har cikin ramin kunnenta taji dirar ssnyar numfashinsa da muryansa me cike da wani yanayi na iko da nuna fin karfi yace
..."call it.."

wani tsamm tay tanajin kamar kanta zai fashe sai can ta gane me yake nufi wato yana daring inta ta sake zaginshi irin na ranan dan ya rike mata hannu.

tanaji ya dada murza damshin lallausar hannunta cikin nashi yace"..at the moque, what did u call me???

wata muguwar hadiyar yawu tay tanajin dan tsayuwar dayay daf da itan ma kamar qamshin turarensa ne gabaki daya yy tranfering mata acikin jininta dan gabaki ta dawo tana qamshi irin nasa
Chapter 64 · 0% Book details