← Book details Nur Firdaus Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 44 OF 96

Sashe 44

Nur Firdaus Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

kwanciya tayi a riginge tanata juyi da tunani har batama jin surutun yan dakin, can ta lumshe idanun ta jin wani asirtaccen sanyin dake ratsawa daga windownta harta cikin zcyarta wanda bata taba jin irin zuginsa ba wani rikitaccen yanayi ne maicike da sarkakkiya yake shigarta,a take ta dukunkune kanta tay tsammm saiga fuskar wannan mutumin acikin idanunta wanda ayanzu take kallon halittarsa zar zar zar dashi acikin kwayar idanunta tamkar ma hotonsa ta dauko da cameran idonta tana kalla ahaka har bacci yay awon gaba da ita..

*****
washe gari da safe ranar asabar da misalin karfe 9.am a cikin wani hadadden office din likita mai dauke da kayan gwajin lafiya na mata (gyneacologist) acan saman office din an rubuta Dr surayya muhammad.

mrs Haseena ce zaune akan kujera cikin wata shiga ta alfarma tanata kallon Dr. Surayya wacce ke fuskantar ta da fuskar mamaki dakuma takaici. Bayan da ta gama duba takardun gwajin da aka yi mata, tajefa mata su kan tebur sannan ta kalli Haseena kai tsaye.

"tace Haseena ke kusan ince yar uwarta ce tunda mun jima muna tare, kin san in zan baki shawara bawai a matsayina na likita zan baki ba sai dan domin zai amfane ki," Dr. Surayya ta fara magana cikin kallon reaction din haseena data wani tsime tana kallonta yayinda ta gyara zamanta da shirin jin wani karin bayani da ita kanta ba son ji takeyi

"Na san da haka Surayya shiyasa banje wajen kowa ba nazo wajenki dan kece kawai zaki iya rufa min asiri, Amma me yasa kike son ki hana ni yin wannan abun? waidama Ba ni da hakkin haihuwa ne?surry i told you this was mine and my husbands idea i just want to knw idan zaiyu...

Dr. Surayya ta numfasa Babu wanda ya ce ba ki da ryt akan haihuwa amma fa dole ne ki yi la’akari da yadda jikinki zai iya daukar nauyin ciki a wannan shekarun naki haseena. IVF yana da hadari musamman ga mace mai shekaru 46 yar gwagwarmayan siyasa irinki, dan Hakan na iya jawo miki matsaloli kamar hawar jini, ciwon zuciya, ko ma rasa rai yayin haihuwa."

Haseena ta yi shiru na wani lokaci zuciyarta cike da tantama gashi sam bata son taji ance zata mutu cikin sauke murya kasa tace" haba surayya Ke kanki kin san yadda rayuwata take wallhi Ina bukatar wannan haihuwar saboda... saboda..sai kuma tay shiruuu batace komi ba.

Dr. Surayya ta girgiza kai. "Ni Ba zan hana ki ba amma dole ne na fahimtar dake ki fahimci hadarin da ke tattare da hakan Ba wai kuma kawai batun samun haihuwr ba ne batun rayuwarki ne, Haseena Shin kin shirya fuskantar hakan?.."

Haseena ta runtse idanunta zuciyarta cike da ruɗani. Ita dai tasan cewa ba za ta iya janyewa daga wannan shawarar ba sabida tanaso taga ta faranta ma sadaat Rai batason wani abu ya rabasu har abada.

saidai maganganun Dr. Surayya sun fara bijiro mata da tunani da bata so ta yarda da su. tana shirin budan baki kenan wayarta yafara ringing nan taciro sa ajaka ahnkli ta kalli screen din sunan Hajiya Mariam Shehuri ne ke bayyana akai, nan ta kalle fuskar Dr surayya snn tace kawata can you excuse me?? Dr surayya tace sure,nan da nan haseena ta mike tsaye cikin sauri jikinta har na rawa ta dan ja gefe kadan kafin nan ta jefa wayar a kunnenta Cikin sauri zuciyarta na harbawa da fargaba da kuma sha'awar jin abin da za'a ce mata.

salam alaikum ranki shi dade.

"Haseena!" Muryar Hajiya Mariam ta fito da wani irin izza, "Albishirinki?"

Haseena ta dan lumshe ido tace goro ranki shi dade.

yanxu labari ya sameni cewa Muna da sama da kashi saba'in cikin ɗari na ƙuri’u acan fadar zabe, snn Hajiya Farida Bala ta gama shan kashi ynxu haka an tabbabtar min cewa Komai na nasarar wann kujera yana hannunmu Alhamdullhi.

Wani irin murmushi mai tattare da dadin nasara take ya bayyana a fuskar mrs Haseena tace "Masha Allah! Wannan ai babban labari ce hajiya..

"haha kibari kawai haseena ai duk karyan kada a ruwa fa take karewa Hajiya Mariam ta yi dariya cikin habaici, ke haseena Daga zarar an bayyana sakamakon zaɓen nan toh komai ya ƙare zamu maida hankli ne kan shirya auren d'ana Adnan daya nace zai auri diyar ki.

Haseena tadan jinjina kai jin ranta yay fari kal Da wannan damar da ta samu dan tasan da gaske zata iya mallakar komi inda ta rike wann damar ssai tana murmushi tace hakane ranki shi dade.. a hankali ta kuma cewa amma Gidana na Gwarimpa har yanzu yana kan mortgage ni duk shi Yafi damuna hajiya ina mai miki tuni zanso a mallaka min kafin auren nan.

"Kada ki damu haseena," Hajiya Mariam ta katse ta.

"Da zarar mun ci zaɓe, zan biya miki komai ai nariga na miki alkwarin wann, Ke dai kawai ki tabbatar da cewa ba matsala daga gefenki musmn ma akan batun yarki da adnan yace zai aura dan bana bukatar wani publicity stunt."

da farinciki aran haseena tace in sha Allah babu wata matsala hajy nan ta hau gode mata, Hajiya Mairam din ta ɗanyi shiru na ‘yan dakiku kafin ta ci gaba da magana, tace yawwa dama akwai wata yar matsala fa, malami na ma meduguri ya aiko ace min Wani yana bibiyarki. kuma yana zargin cewa ana bawa Hajiya Farida Bala wasu bayanai."

Haseena ta ɗan yatsine fuska tace toh amma Wane ne yake bina?"malamin ya kama sunanshi?

kai tsaye hajy mairam tace "Mijin ki."

Take Zuciyar Haseena ta buga da karfi tace "Me?"..mijina kuma?

"Ba mu da wani tabbaci haseena amma malam akwai hannun wani kusa da ke yi mana kutse Kuma Sadat shine wanda malam yake zargi sosai.."

nan da nan Haseena ta dan daure fuska ta harɗe hannayenta cikin jin bacin rai "Hajiya wallahi ba zai yiwu ba i knw Sadat ba zai iya cin amanata ba. yaro ne karami i make sure i study him shi babu ruwansa ma da harkan siyasata.

"Ke dai ki kula," Hajiya Mariam ta furta cikin katse ta. anan kuma zanta kkri har sai mun tabbatar da gaskiyar lamarin.

haseena tay shiru batace komi ba Bayan sun gama wayar ta ja numfashi mai nauyi Zuciyarta na raya mata cewa ba za ta iya yarda da wannan zargi akan sadat ba, sedai kuma ta san tunda aka fara hakan dolene tay wani abu aka sa ba zata iya sakaci ba, dan Idan da gaske Sadat yana aiki da makiya to komai zai iya rushewa mata.

Da wannan tunanin ta juya zuciyarta ta cika da sabon ƙuduri na jin cewa zata bincike shi da kanta kuma a ɓoye

nan ta dawo office din taja kujerarta ta zauna tay shiruuu bayan wasu mintina kadan Dr. Surayya ta kalleta cikin kulawa tareda jingina kai da kujera tana famar nazarin yadda fuskar Haseena ke nuna damuwa da ruɗani.

"Haseena, wai yaa maganan yaran ki ne?" Ta tambayeta cikin sanyin murya da son sakata magana.

Haseena ta ɗan yi murmushi maras kuzari tace "Lafiya kalau suke surayya. Nur Firdaus tana can shirye-shiryen gasar karatun Al-Qur’ani da za a yi a Kaduna sun ma tafi can, Layla kuma kamar kullum 'yar nayi na'am ne suna can tare.

Dr. Surayya ta gyara zama. "masha Allah, nur tay gadon ubanta yar albarka ce ina jin yadda ake yabawa da tarbiyanta agari nasan yanxu kam duk sun girma ko...

cikin basarwa da nuna rashin damuwa mrs haseena tace yeahh sun girma sunacan sunatayi kinsan fa ni ba yar son shiga tsabgar yara bane,

Cikin kyabe baki Dr surayya tace tbbas nasani but haseena lets talk serious, in kinje aikinki Kinadan waigowa dan tabbatar da lfyansu kuwa, Kina ma da lokacin su? Ko dai shegen siyasa da damuwar miji suka maye gurbin uwa da ke kula da ‘ya’yanta marayu?"

Haseena ta sauke numfashi tana jin nauyin zancen, kedai surayya Kin san irin rayuwar da nake yi, kinsan wahalarsa Ba abu ne mai sauƙi ba bare ince miki zan hada aikina da wani rainon yara ."

Dr. Surayya ta kalle ta ido cikin ido. tace hmmm dat is very typical of you, yanxu de mu aje maganan nan agefe., ranar talata zanje kaduna kuma ranar ne zasu rufe gasar, To me zai hana kema kiɗauki wannan damar sai mu tafi Kadunan tare? Gasar nan ba ƙaramin abu ba ce a rayuwar Nur Firdaus. haseena dan Allah na rokeki Ki jeki nuna mata cewa kina tare da ita wllh hakan zai ƙarfafa ta sosai."

kai tsaye Haseena ta girgiza kai tace Ba zan iya barin Abuja a yanzu ba surayya. kina gani dai Hajia Mariam ta kira ni yanxu tana buƙata ta, kuma kinsan mun kusa mu ci nasara Idan na bar siyasa a yanzu komai zai ruguje min..."

Dr. Surayya ta dafa hannunta da sanyin murya tace haba Haseena duk wata nasara da kike nema a duniya ba ta da amfani idan ‘ya’yan ki ba sa jin kaunarki aransu, yau Idan Nur Firdaus ta lashe gasar nan waikina so ta tsaya ne a matsayin marainiya saboda ba kizo kin nuna wa duniya ke cikakkyar uwa bace agareta? haba haseena, Kiyi tunani akai mana just this once inkinje me zai cinyeki abu na rana daya ana gamawa ma zamu dawo Abuja tare da su.

Haseena ta yi shiru, zuciyarta na dan bugawa da sauri dan Kalaman Dr. Surayya sun tsunduma ta cikin tunani mai zurfi, can kuma sai ta katse tunanin tareda daure fuska tace toh naji Allah ya kaimu ranar inkin shirya saiki neme ni amma duk tsiya dai gaskiya aranar zamuje mu dawo. Dr surayya tace in sha Allah, daga nan suka tsunduma wata hirar dake anjima ba ahadu ba har kafin nan suka rabu.

Ali akilu road kaduna state 4pm..

A dede ƙofar shiga babban mansion din jifa jifan da sukayi rakiya wa hajy mammy gidan malaminta suka tsaya domin sauketa,nan ƙananan masu aiki da suka rage suka fara tattara mata kayanta suna kaiwa ciki, hjya mamy ta sauka ahnkli da jikin tsufa tana takawa ahankli da azhkar din yamma abakinta.
Chapter 44 · 0% Book details