← Book details Nur Firdaus Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 67 OF 96

Sashe 67

Nur Firdaus Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

haka matar ta riko hannun Nur har cikin mota suka dau hanyar anguwrsu ta cikin gwarimpa wanda tun da suka dau hanyar nur ta kife kanta akan cinyarta ta cigaba da kuka dan ita kadai tasan abubuwan dake mata zafi..

ata bangaren su mrs haseenan kuwa tun Bayan wannan mummunan hatsarin bata sake samun wani sukuni a zcyarta ba musmn ma da sukay neman duniyan basu ga Nur awajen ba.

inkaga yadda haseena ta birkice tana neman nur firdaus awajen tanata ihun sunanta tana yawo taje nan taje nan kamar tababbiya tana kan tambayar mutane saikasha mamakinta

wanda ita kanta layla duk tagane cewa guilty conciense ne kawai yake famar damun mumynsun akan abunda tama yar cikinta ba tsantsan so na uwa ba

bayan an nemi nur angaji mrs Haseena da Layla sunkai kansu gida da kyar Sun isa Abujan bayan magriba amma laylah bata magana sai kuka duk jikinta yay sanyi dan gani take kamar hala shikenan bazata sake ganin yar uwanta ba.

duk da raunin da Haseena taji bata samu wajen zama ba suna isowa gidan ta fara neman karamin waya tana neman taimakon hukuma dan anemo mata yarta cikin wani ɗanɗano na damuwa da nauyin abunda tay.

zuciyarta cike take da tsoro da wata irin damuwar in ace yau nur ta bace yo me zatace wa dangi da kuma yan uwan ubanta da suka mugun tsanarta

Duk wanda ta kirasu sai suce mata yanzun nan zasu saka ayi wani abu akai sai can kusan bayan ishai snn taji kamar zama be kamata ba. pain killers ta sha ta cire kayan jikinta the whole mrs haseena amma ko wanka batay ba ta sauya wani kayan kawai agurguje,...

karamin wayar datake amfani dashi din ne yafara ringing ta dauka jikinta na rawa nan wani agent yake ce mata ai anga wasu masu motar haya sun dauketa akan hanya saidai ba asan inda sukay da ita ba.

hanklin haseena ya dada tashi ta bude drwarta ta kwashe kudi yakai dubu dari biyu zata wuce station dasu koma me zaay dai anemo mata motar hayan she just want her doter back home dis very night.

Nur Firdaus kuwa da ƙyar ta iya tattara nitsuwarta cikin shiru da kaɗuwa jikinta da zuciyarta yanamai ɗauke da raɗaɗin abubuwa masu yawa dake mata yawo akanta, Ba ta iya sake furta wani magana sai kallon duniyan takeyi tamkar ya sauya mata ayau din.

jingina kai tay snn ta zubawa sararin sama idanu tana tambayar zuciyarta "Shin me na yi wa Mummy da har ta iya rufe idonta ta barni cikin irin wann yanayin?

tay tsam tanata fmr ambaton sunan Allah
tanamai neman tsari daga sharrin fushi da yanke hukunci cikin hanzari abun namata shegen zafi acikin xuciyarta koda ta daure ta hadiye zafin sai taji kawai gara ta yafe ma mahaifyarta sakayya tsakaninsu naga wajen Allah.

hannunta ta saka akan fuskanta dayay fayau dan sauran hawayenta dake sauka ta shareshi tay shiru tanata memeta kalmar" la ila illahal haleemul azeem..har zuwa karshe dan sabida zucyarta ya samu sassauci daga radadi.

basu wani jima da tsayawa a gate dinsu ba sai ganan malam liman ya fito da motar cadillac red colour dauke da Haseena aciki kusan kicibis sukayi a gate din dan duk dama dare ne tuni ta gane yarta da wani irin sauri ta bude motar ta fito tare da dafe kirji tanamai cewa ohhhhh thank goodness Nagode maka ya Allah!!!!

sosai Nur ta hade rai takisam tadaga kanta matarce ta rike mata hannu tana dan janta kamar rakumi da akala, acikin mugun sauri sauri haseena ta taresu da murmushi ƙaryayye tanata ƙoƙarin danne borin kunyar da take ji taciki

da wata salon jin relieve a muryanta tace Nur,alhamdullh i tot i lost you, am glad ure back dama dai yanzu nake shirin zuwa station.

Nur kamar bata wajen haka tay mata shiru ta share furucin mrsss haseena..

jikin haseenan adan sanyaye ta kalle matar da fuskar nuna godiya nan suka gaggaisa ta yi inviting dinta har cikin gidan.

sai tambayar matar take akan abunda ya faru matar kuwa bata boye mata komi ba sede wani uban kunya ne ya kara rufe fuskar haseena dataji cewa ashe nur bata fadi asalin abunda ta mata wa kowa ba.

sai satar kallon nur din takeyi wanda tunda suka shigo bata dago kai bare tace uffan, tanaji suka gama magana haseena ta dinga ma matar godiya,har ta fito da 200k din ta bata akan tay kudin uber dana wahalar jinya amma matar taki sam...

mikewa tay tanamai cewa ai yaro na kowa ne, kedai Allah ya dada kare miki su ni kinganni shekarata 40 kenan da aure amma ban taba ko bari ba but its well yaro na kowa ne Allah ya baku lafiya ya kare na gaba.

mrs haseena tana ta mamakin kirkin matar
itakuwa ko ajikinta harsaida ta tashi tafiya snn nur ta budi baki tayita mata godiya matar sosai taji dadin kalamn nur din..

tace karki damu yan mata kisha maganinki kinji ko? ahnkli nur ta gyada mata kai.

snn matar ta kalle haseena tace toh ni zan wuce nabarku lfya

har waje haseena ta rakata tanata mata godiya dakyar ta yarje mata ta hadasu da malam liman ya wuce da ita anguwansu..

tana raka matar kafafuwanta harna hardewa tayo cikin gida, duk dama bata san me zatacewa nur ba amma she want to knw how is she is doing dan gani tay kamar ancanja mata yarta, nur da duk bata mata rai da akayi tana musu sallama agidan snn takanyi gaisuwa amma yaukam bata matayi kodaya ba kai ko kallonta batay ba.

aikuwa tana shigowa ciki taga falon wayam babu ita cikin sauri ta haura sama tay dakin su...

ahnkli ta turo kofar ta shigo ciki awani irin yananyin sanyin jiki ta samesu lokcin Layla natsaye tadan jingina kai da bango tanata wasa da yatsunta dan tarasa gane komi ganin nur tashigo dakin out of no where bata kulata ba kawai ta kwanta akan gado tay shiru batare da tace mata uffan ba..

hade ido sukayi da haseena hawayen da ke cike da idon laylan saiya zubo ahnkli

cikin wata kalar tsimewa mrs haseena ta kalli nur tace Nur
lafiya kuwa kinxo gida baki son yin magana da kowa wai kode wani abu na miki ciwo ne a kira miki likita...

nur tay shiru saidata dan jan snn muryanta ya fito a dashe batare da ta kalleta ba tace no, i am good Alhamdulillah. sai tay shiru can kuma cikin sanyin jiki ta bude lumasashun idanunta snn tace musu na gode wa Allah da kowa ya tsira.

Daga hakan ta mike ahnkli tana dingishi ta wuce ta shiga toilet ta barsu cikin wani irin salo da ya kara musu jin kunya da nauyi.

harta fito ta shirya kwanciya bacci suna tsaye suna kallonta duk sun kasa sanin me zasu ce kuma dama haseena irin mutanen nan ne da suke avoiding mistake dinsu dan sabida kawai baso san ace sune basu da gaskiya barema bazata taba iya rarrashi ko bada haquri ma yaro ba gani take kamar zai jawo yarinya ta mata rashin kunya so is better she dismiss the event with silence.

ranar kuwa ko bacci bata iya yi kwakkwara ba hakama layla abun duniya ya dameta dan bata taba ganin Nur awnn yanayin shariya da shiru shiru ba.

itakam nur tuni tay baccinta me nauyi dan babu abunda take iyayi sai ambaton Allah abakinta, harse washe gari san suka dan gaisa da layla, tanaji laylan tazo jikinta ta mannu tanata kuka da wasu kwainanenta na bada haquri amma batace mata uffan ba.

shiruntan tun yana musu kmr wasa wasa ana zaton trauma ne har ya fara basu tsoro sosai, gashi she barely eat, bare tay magana me tsayi, kowani lkci she is quite ans sober, and alone, bata kula laylan ma sosai bare kuma Haseena da wata rana ma basu haduwa...

sun dawo tun ranar wednesday da abun ya faru amma har akaci cinye wekdns din nan gabaki daya halin da suke ciki kenan agidan, wanda already hakan ya fara hatsala Mrs haseena sosai cos she expect nur ta just forget and behave normal dan wnn shiru shirun data dinga musu yafi komi rikita ma mrs haseena kwakwala da zuciya

ganin bazata taba iya rarrashinta ko dago maganan ba sai kawai tadebe kashin abun ta watsar ta tsunduma harkan siyasarta.

mutane dayawa sunxo musu jaje, within dis days har antattaro musu dan abunda aka samu amotar da basu wani kune ba luckly enuf sunyi recovering harda wayar nur da na haseena, layla kam ma sabo tall me tsada haseena ta siya mata dantaja hanklinta ta dena damuwa akan sabuwar yanayin nur amma inaa abundai nakan damun layla sosai dan tasan ba'a kyauta wa yar uwarta ba.

cikin ikon Allah kuwa kafar nur din ya fara warwarewa dan dama kwana bakwai aka bata yau gashi har sunci shida akace ta koma asibitin ranar monday a duba. ko Adnan ma bata gayamai komi ba abakin mum dinsa yaji,shine kullum zai kirata babu dare babu rana dan tunda samu aka dan gyara mata wayarta shi yake dan debe mata kewa, dan jakarta da aka samu kuma daga Id card dinta na schll sai handkyn javeed ne kawai aciki da bai kone kurmus ba.

samun hankyn nan bakaramin sanyi ya karawa zuciyarta ba dan duk lkcin data shaki qamshin turaren javeed takanji wani niitsuwa aranta gami da ratsa mata gangan jiki na ban mamaki..

but she make sure to make adnan him feel dat condition din nata is not dat serious dan bata son adinga dago mata maganan....

Dagata dayan 'bangaren kuwa tun a ranar da aka gama hidimarsu nur firdaus Dr simran ta iso garin Abuja daren ranar wednesday lkcin daf ana neman Wajajen karfe 6:30pm na yamma, babban mota kirar mesarati daga hadadden gidan hutawar Hjy zuby othman ne yazo ya dauketa daga airpot yawuce da ita gidan.
Chapter 67 · 0% Book details