← Book details Nur Firdaus Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 72 OF 96

Sashe 72

Nur Firdaus Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

hakama Kawayen Malika, wacce aka kora saboda zargin ɗaukar ciki da ɗan shege badama su ganta sai sun jefeta da habaici. suna masu alaqanta nasararta da wani boyayyen sirri...

wann sati lokaci ne daya kamata ace ta samu hutu da kwanciyar hankali amma ina, hassada da baqar magana ne ta kota ina, ga sabon halin taurin kai da fushi fushi da layla ta tsira mata agida, the week was tough on nur emotionally dan zcyrta bai gama warkewa da abun da suka mata na hatsari ba gashi ta shiga wann rubibi na yan hassada, Mrs haseena kuwa dama satin karban kujerarsu ta mulki kenan dan haka bata ma zama.

Koda Firdaus bata jin abubuwan da wasu mutanen suke faɗi da kunnenta amma babu tantama tana jin nauyinsa a zuciyarta, satin gabaki daya tana fama ne da faduwar gaba, tana jin tamkar duniya na so ta jawo ta ƙasa da ƙafa.

ranar jumaar da javeed suka kammala family meeting dinsu nur sun fito daga aji kenan an tashesu a schl zasu wuce gida sai aka ji hayaniya a bakin makaranta...

wata sabuwar Motar SUV ne baƙa ta tsaya anlankaya mata red gift lane da hadadden rose bonquet ga wasu chocolate box, da gift bags. yau din adnan ya dawo daga london shi da abokansa su guda uku sukazo cikin salo me aji da nuna wayewa.

gabaki daya hanlin dalibai sai ya koma kansu wanda tuni dama dalibai matan schl din ke masa kallo a matsayin dream crush.

nur firdaus suna fitowa waje adnan yanufota da murmushinsa me taushi yakaita har gaban sabon motar snn ya ciro keys...

yana murmushi ya mika mata itade taki karba sam jadidah ce tasaka hannu ta karba...yace mata congratultions habibty my wife to be in sha Allah.

jikinta adan kame ta kallesa acikin tsantsar kunya da mamaki ta tsaya cak agaban motar dumbin Mutane na kallonsu wasu na murmushi, wasu na haɗiye kishi. adnan Ya ce, Wannan kyauta ce gare ki, badon kin riga kin zarce kowa a makarantar nanba sai dan Muryarkice ta sauya min tunani na game da mata, kuma ina fatan ki ci gaba da haskaka zuciyata dana al'umma gabaki daya. itade batace masa komi sai dai tay murmushi, duk wani kyautar daya miƙa mata a gaban kowa da kowa ko daya bata karba ba jadidah ce take karba ta musu godiya.

wasu sun dauka tsantsan tarbiya da kunyan ido ne, wasu masu nisan tunanin sungane cewa kyautar ne be zauna mata a zucyarta ba.

its like sumting has changed, gadai Adnan din datay ta zumudin yazo mata wajen gasa, yau kuma yazo amma sai bataji wann feeling din aranta ba.

tana tsoro yau inta amshi kyautar mota awajensa bata san da wani irin baqar magana da sunan kaskanci mrs haseena zata kirata dashi ba

Fahad da wasu daga cikin manyan samarin makaranta kuwa sosai abun ya razana su..SUV fa? motar millions of naira kut waye ubanta da zata samu kyautar motar da su basu ja ba.

dacan dai sun dauke ido akanta amma tunda sukaga An bata motar nan sukaji inaa dolene su sakata a tarkonsu da suka shirya.

tun ranar wann juma'a wutar Kishi, bakin ciki, da hassada suka fara doka tambura a fuskokin wasu tsirarun daliban

agaban abokansa nur tanuna masa taɗauki kyautarsan da farin ciki da nutsuwa, ta yi masa godiya. se can da suka koma gida snn ta kirashi cikin masa bayani da tattausar lafuza tace masa bazata iya karban kyautar motar sa ba kawai ya bari sai sunyi auren zaina bata irin wnn kyautar

Adnan ya fahimceta baiji wani abu aransa dakema yasan wann satin me zuwanne mamansa zata amshi sabuwar matsayi snn baifi nan da wata ba zaa kawo maganan auren su, dan haka da yammacin juma'ar yazo gidansun hira tareda driversu dan atafi masa da motar.

tun zuwansa laylah ta kasa zanne ta kasa tsaye, sai yawo take tana lekensu tana musu labe tanajin duk abunda suke cewa.

babu yadda Adnan baiyi da nur akan suje susha iska awani waje kamar yadda suka tsara hakan a waya ba amma sam taki motsi karshe ma tace masa kafarta nakan mata ciwo kawai ya bari sai tawarke kafinsu fara shirinsu na aure.

babu yadda ya iya haka ya kyaleta, ita ajikinta tanajin komi ya canza amma shikam besaka komi aransa ba face zumudin dayakey da tunanin yakusa ya mallaki abar kaunarsa.

bai bar gidan ba sai wajajen karfe 9:30 na dare dan Already drivernsa ya wuce da dayan motar, yana ficewa agidan sai ga haseena ta dawo a mugun gajiye layla na ganin haseena ta bita daki tafara gaggaya mata cewa ai Adnan ya bawa nur kyautar mota SUV me tsada kuma harta mayar masa kuma ai taji suna cewa zasuce wani waje su huta

haka dai ta harhada magana kamar yadda tay dataga kudi da turaruka da nur ta aje mata na tsaraba a jakarta da suka dawo daga kaduna, dake nur bata gaya mata cewa kawunsu bane ya basu kudin sai ta zo ta gaya ma mrs haseena gulman awani siga ta daban duk dama tay alkawari ma nur firdaus din cewa bazata fada ma kowa ba.

zancen zuwa wani wajen ayanxu shi yafi daga ma mrs haseena hankali dan sosai haseena ta kullaci wann maganangnun aranta, me nur take take samun manyan kyauta da kudade haka, amma dake Tun bayan hatsarin nan suke famar avoiding fushin juna sai ta aje maganan aranta bata cewa nur firdaus uffan ba jira take wata rana wani abu ya faru tama nur din tass tass.

laylah sai ta hada gulma sai ta dawo daki ta same nur tay tanuna mata cewa ai tana tare da ita 100% duk dama ynxu zaka ga laylan tana wasa da dariya da komi anjima kuma zakaga tafara fushi fushi da rashin kunya.

on saturday tun da asubah mrs haseena ta fita harkokinsu na siyasa anata shirya
mata, da gangami na murna dan already yanxu kam sun san sune da kujera ba sanata farida bala ba

gidan ya kasance shiru Nur ta yanke hukuncin fara shirin karatun waec inta,
layla kuma tana falo tana tik tok can da yamma saiga jadida tazo kyautukar nur da ke wajensu saiyau ta tattaro mata ta kawo matasu sukasha hira

acikin hirar tasu ne layla taji jadida tana gayawa nur cewa Ai angayyace aysha zuwa babban partyn da su fahad suke shiryawa karshen kowani sati amma wann karon ranar alhamis za'ayi sabida zasu gayyaci wasu manyan yara.

nur sosai taji baqin cikin hakan ma aysha
amma jadida kam ko ajikinta dan tasan aysha dama tana son wann kalar rayuwar holewar sosai.

abu kamar da wasa maganan partyn sai ya fara shiga ma layla zuciya, ji takey kamar she just want to go nd have fun tunda babu sadaat babu wani abu me sakata farin ciki agidan gara tabi aysha kawai ko gulma taje tay. duk hirar da jadida sukeyi da Nur tanaji amma bata saka musu baki ana partyn ba har suka cicci abinci akayi raha suka raka jadidan har anguwarsu kafin nan suka dawo gida.

ranar su biyunsu aka bari agidan dan har sai washe gari ranar sunday kafinnan suka san da cewa ashe mrs haseena batama kwana da su a gidan ba. Suna kammala breakfast, yau da murna da sakin fuska layla ta hau taya nur sorting out din dukkan kyautukanta da jadida ta kawo musu jiya.

qur'anai da littafai suka waresu waje guda suka ajesu.

certificates da duk wani abu daya shafi na karramawa nur ta tattarasu gefe zata ajesu a jakarta tana dam bude jakar kuwa caraf idon layla ya sauka kan wrapper na dollars da nur ta boye ajakar, mamaki ya cika layla sai maza ta dauke ido tay kamar bata gani ba aka cigaba da sha'ani.

suncire kudi a envolopes kala kala yakai 30, kimaninin 4 million ta samu frm indivisuals, ga 500 thousand na schl
ga cheques guda uku daga manyan baki.

anan ma nur ta raba duk wani kayan duniya da ta samu kashi biyu ta bawa laylan rabi kyauta
kudi kuma tace sai haseena tazo, kawai na kawayenta ta cire
tasaka musu rabonsu a envelope caraf layla ta amshi na aysha tace ma nur ai ita zata kai mata insun je schl gobe. subiyunsu suka zauna agidan yauma bayan sungama rarraba kyautar suka dau kudi suka siya abubuwan dadi kala kala sukaci maransu.

washe gari monday suna zuwa schl taje ta samu aysha ta bata envelope din kudin bakaramin mamakin nur aysha taji ba, daga haka laylah ta dinga takura mata akan zata kara mata wani abu inde zata samo mata gate pass na zuwa partyn su fahad ranar thursday. da kyar aysha ta amince dan remain just 2days ne partyn samun gate pass din nada wuya amma son kudi yasa tama laylan alkwari.

a fannin nur firdaus kuwa kawarta jadida ta dauka sukaje cikin gari, manyan cheques dinta data samu daga mufasa da Safeey Allah foudation da na familyn wamako ta dauka dukka takai daya wajen masu gina boreholes da rijiya a kauyuka,daya kuma ta sadaukar dan bawa yara marasa galihu ilimin Addini,daya ta raba biyu ta bada asibiti,na karshen ta siya abubuwa wa masallatai tay sadaqa dayawa fisabillah wa mahaifinta.

kwana biyu suka dauka suna aiwatar da wann abun aboye banda jadida dake rakata ko laylah bata bari tasani ba altho tasan zasu iya samun babban matsala da mrs haseena akan hakan datay amma kuma sabida Allah ya isar ma mahaifinta ladan tay gasar bawai dan kwadayin abun duniya ba dan haka bata damu da komi haseena zata gaya mata ba..

iya cheques din kawai ta taba, duk sauran cash gifts din na gida na ajiye.

******
maiduguri, Borno state. nigeria.

Ranar Alhamis da asubahin fari labari yazo ma sanata farida bala sa dumi dumin sa cewa shugaban kasa ya saka hannu an gama votes har anbuga appointmnt letter da sunan hajy mairam kanem shehuri.

tana kwance ne amma datay wani irin borataccen kukan kura tafasa wayarta fassss da jikin bango saida sadaat dake kwance tsirara haihuwar uwarsa agefenta ya farka a mugun tsorace yana haki....
Chapter 72 · 0% Book details