← Book details Nur Firdaus Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 54 OF 96

Sashe 54

Nur Firdaus Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Kasaitaccen sautin takun Razia din shine yadan janyo hanklinsu bisa gefenta. nur firdaus tana dage idanunta sama suka hade ido take gaban razia ya mugun fadi saita dan kafe nur da ido kamar bata taba ganin mace kyakkawa irinta a duniya ba

ahnkli nur firdaus ta sakar mata murmushi mai sanyi kafin ta dauke kanta ahnkli.

kallonta razia ta dingayi har ta karaso gefen baban nata nan itama ta nanike agefensa yarike mata hannu cikin tsantsan nuna mata soyayya da gata a fili dan ita kadaice yarsa da Allah ya bashi a duk duniya.

Kusan a shagwabe tabi ta zauna batace ma iyayenta matan uffan ba tay tsinin baki tanajin kanta a matsayin sangartacciya kuma ƴa guda awajen iyayentan wanda tasan zasu iyayin komi akanta a duniyan nan..

Tun data nemi waje ta zauna tay shiru cikin shagwaba batace uffan ba bare tay gaisuwa. kan Nur firdaus na kallon kasa tana jin yadda iyayen suka fara jajayya da razian wajen gaisuwa

sosai ta lura da cewa razian sangartacciya na kure tunani kalar wanda tsarin rayuwar turawa ya shige musu jikinsu sosai. da kyar dai suka sakata tay gaisuwar kafin nan baban nata dakansa yafara mata bayanin Dangantakarta da nur firdaus haroun ciroma

mahaifin nur firdaus Alhaj haroun ciroma shine babba same mother same father saida yar autarsu Anty safiya ciroma datake zama a saudi arabia yanxu.

itade razia kallon nur take dan a duniya bata tabajin dar dar agaban wata ƴa mace kamar yadda yaudin tahaujin faduwar gaba agaban cousin sister dintan ba, Duk wani kyanta da perfection din halittar jikintan nan datakeji dashi sai taga kamarma Nur firdaus din ta fita komi da komi nesa ba kusa ba dadin karawa wani nitsattsaen kwarjini dake tafe da ita koda batay motsi ba,ta lura kamar batayi kwalliya ba amma wani irin glowing skin din nur din yake fuskarta na baza kyalli bana wasaba,giranta a cike da gashin gira dats perfectly carved har ma giran na neman hadewa, dan space dake tsakanin two giran ma wani gashine dayay ma fuskarta kyau bana kadanba
,nur firdaus tanada dogon hanci asalin pencil nose wanda baiyi tsiriri sosai ba amma ya dace sosai da tsarin fuskartan ga kwayan idanunta grey ne kalar toka mai dan haske da maiko aciki and is as deep as an arabian coffee, taga gashin idanunta suma bakakene dogaye wara wara dasu ga lips dinta dakenan karami dan tsut dashi pinkish peach colour da yakara haskaka kyallin fuskarta da bata shafa mai komi ba. gefen fuskarta shatin dogayen sajene lub lub a kwance duk dama kanta na sanye da bakin hula, kunenta babu ko dan kunne sai wata manne kana ganin yarinyar basai amfada maka ba zakasan tana da suma, kayan jikinta da komi nata saida razia ta duba tamusu cikakken kallo dan bana tsammanin akwai wani wanda ya taba karewa nur firdaus irin kallon kwaf kwaf da razia abu ta mata acikin dan kankanin lokaci.

sede kuma tunda taji babanta yanata musu bayanin yadda mutuwar bazata yaxo ya raba nur firdaus da mahaifinta dayake matukar kaunarta sai kuma jikinta ya danyi sanyi sosai sabida akwai ababen tausayi dayawa aciki.

Razia tana da gigin miskilanci da taurinkai amma bata taba hadashi da kaskanci da walakanta jama'a ba. Snn best part of her shine tana paying attention sosai ga Addininta duk dama a kasar waje din take karatu, awajenta ta san cewa addininta nada muhimnci ba kamar yadda wasu suke kallon Addinin islam a matsayin addinin kauyanci da takurawa ba. She is ambitious abt so many things in life musamn ma film ko harkqn fashion dan arayuwanta tana son kullum taga takai wani babban matsayi a careerta a duniya da za'a na buga misali da kwatance wa mata da ita.

a fuska dai zakayi zaton Razia mace ce mai rawanin girman kai sabida tana da wann zubin miskilanci da rashin sake fuska ga kuma wnn kyantan da yanayinta da' ya kai matsayin ace tayi mulki da izza ma uban kowa dashi sai dai ita hakan duk be rufe mata ido ba dan muddin ka samu caurage din iya shiga rayuwarta zaka gane cewa she is d most wildest and kind hearted being u wll eva meet in ur life.

saidai ganin nur firdaus sosai ya dan tabata taciki duk dama tasan akwai alaqa na jini atsakanin su but she is sumhow conflicted taya ma zata jata ajiki bayan ita kanta tasan taji kishin daya kasance Nur din tanada wasu abubuwan da yazo dede da nata wasu ma yafi natan wanda datake tinkaho dasu kamarsu kyau, kyan jiki ga dogon gashi, ga wani dan uban sanyin aji da kwarjini dake fallasa kansa atattare da ita,she honestly dont knw weda to like her or not yet, sabida ganin nur yasata taji kamar her personality has meet it challenge.

haka nan har suka gama cin abincin cikin raha iyayen suka tashi suka bar wajen dan su tattauna, Razia Abu ce kawai batace ma nur firdaus uffan ba duk dama fuskarta looks normal and emotionless abt her.

komawa palor tay ta dan zauna ita daya tana latsa wayarta can saiga nur firdaus ta karaso wajen

Miskillalliyar Ajiyar zuciyar da Nur ta saki shi yasata juyowa a dan takaice Suna hade ido nur ta dan sakar mata murmushi mai sanyi snn tace "salam alaikum, Hi sis. kallo daya Razyn ta mata snn ta dauke kanta tanamai kawar da idanunta can gefe like she dont even care, dan haka ko murmushi bata iya mayar mata ba.

Nur ta dan tsaya ta rasa me xatay sai can razian ta dago kai ta kalleta cikn sanyin kyabe baki tace " Sit. zauna mana...kin xo kin tsayamin akai...

ahankli nur ta taho kafafunta harna yar hardewa tazauna a dan dofane kanta na kallon kasa tsabar yadda razian ta kafeta da wani irin bold nd piecing looks kamar wani abu na daban take kallo ajikinta.

after like 3 scnds of awkward silence tsakaninsu nan razy ta ajiye tsadadden wayarta akan cinyarta takalle sunkuyayyn kan nur snn tay karamin murmushi
ahnkli tace "Cousin sister huhn? Nur tana dago kai taga razian tamika mata hannu a sanyaye nur ta kama hannun nata ahankli sukayi musabaha nan ne razian tadanne komi aranta tay ma nur firdaus din ssnyr murmumshi snn tace " "i Am Razia Abubakar ciroma. friends call me Razzy, in law schl i am B-razzy, bt you can call me Razia Abu. calmy Nur tay nooding snn tace "got it,I am Nur firdaus haroun ciroma,i am pleased to meet you Anty razia...ahnkli razia ta kwace hannunta cikin katseta tace A'a, no tags pls waye Anty kuma?Razia abu is enuf, kidanga cemin Razia kinji..i am still in my prime u knw.. nd i love my name.

kallonta nur ta dingayi tana murmushi sabida burgeta dataji razyn tayi musmn yadda take wani irin daukaka kanta da wata iryar sanyin kasaita da tsananin wayewa.

dan shirune ya ratsa wajen sai can snn tace "so Nuriii, How old did u think you are? cikin sake ajiyan zucyan bazata nur tace "uhmm, i am 17.. i think. razy ta juyo ta mata wani irin kallo cikin dan kwalo ido.. "haa 17?, bt u look bit matured for ur young age kin wani tuttula kaya ajikinki kamar wata matar aure,bt its good sha, i bet ure a virgin ryt??

wani iri nur taji atake dan bata sn me take nufi da hakan ba dai kawai ta sauke kanta kasa tay shiruuu batace komi ba.

ita kuwa razy tafadi hakan ne sabida mamakin yanayin dataga tsantsan modesty da kuma sanyin nitsuwar nur din wanda ya balain kasance mata kamar wani sabon abu nadaban da bata saba gani a wajen yara yan 17yrs din ba dake ita a kasar waje cikin turawa take rabin rayuwarta.

dan tasan wann age din ne ma teenagers like her age sukejin kansu suke kuma fallin tashen balaga.

kafin nur ta dago kai taga wai har razia ta mike tsaye, suna hade ido ta daga wayarta ta saka a kunne snn tace "i got to go, Excuse me. daga nan bata hira tacewar nur din ba tahaura sama kan step walking calmy and majestically nur tadinga binta da ido harta bace ma ganin ta dan bata taba ganin yadda tsantsan aji, kwarjini da wayewa yake fallasa kansa ajikin mace kamar yadda yake kwaranya ajikin razia abu ba.

dan ajiyan zuciya ne yakufce mata takalle agogon hannunta ganin tara saura ta mike tsaye ta karaso wajen iyayen nasu ta samesu sunata waya da lawyernsu akan ko za'a barsu su rufa mata baya gobe a wajen gasarta amma haka fir aka hanasu.

acikin sanyin ladabi ta rusuna snn tace musu zata tafi.

saidai Daga yanayin yadda dukansu suka amsata kai zakasan sam basuji dadin tafiyar da xatayin ba, bayadda suka iya the case file againts them bai basu damar shiga rayuwarta ba harsai ta kaiga cika 18yrs old wanda lkcine da ta mallake hanklin kanta bisa tsarin kundin shariar bature sann zata iya deciding dakanta but for now haseena ce take iko da yaranta and she forbade any one daga familyn ubansu ya kusancesu sabida shaidoji data gabatar wa kotu cewa zasu cutar mata da yaranta kamr yadda suka cutar mata da mijinta.

hankalin hjy sa'adatu da na hajya bilki sosai ya tashi ganin lawyer yace musu bazasu ko samu daman halartan wajen gasar nur firdaus goben duk dama su ba jininsu bane. Alhaj Abubkar kuwa dama already ya riga ya danne xafin abun aransa dan yasan haseena tafi tsanarsa fiye da kowa a dangi kuma tana jirane yay wani abu game da yaranta ta lalata masa sunansa akoina.....

kusan duk duniya babu wanda yakaishi jiran yaga nur tacika 18yrs din,sabida ya nuna ma haseena ita bakomi bace a duniyan nan dan yasaka aransa zai kwato yaran dan uwansa ya rainesu har ya aurar dasu wanda alkwari ne daya masa tun suna yara amma haka haseena tay amfani da surkullenta na political influence ta hanashi cikawa..
Chapter 54 · 0% Book details