← Book details Nur Firdaus Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 27 OF 96

Sashe 27

Nur Firdaus Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

yau sai kusan wajajen karfe shida da rabi dede nur firdaus suka gama rehearsal ta kira
malam liman batare da bata lokci ba kuwa yazo ya dauketa ita da babban kawarta jadidah da suke da same age ya aje kowaccen su agida.

a mugun gajiye ta shigo cikin gidan jin qamshin soyayyan kaji ya mamaye ko ina gawata mayyar aroma na fried rice tana tashi daga kan dinning table dinsu she was so famished and tired gashi tawuni da tunanin jikin yar uwarta sosai ta damu.

sassanyar sallamarta ne ya ratsa falon jin ko ina shiru lokcin Haseena harta gama gyara fried rice da chicken da ta samo daga taron tawuce sama domin ta yi wanka da shiryawa.

Nur Firdaus Tana jin ƙamshin girkin cikinta yadan tsinke da azaban yunwa tana Allah Allah ta dawo ta samu ta ci itama, kai tsaye tawuce daki ta bude kofar da mamaki ta hango Layla zaune agaban madubi da alama harta watsa ruwa tana shiryawa cikin wata matsatsen jeans da top tana dan latsa wayarta time to time tana cancarawa fuskanta kwalliya.

Nur ta ɗan waro ido waje snn tace Layla?? bake ba ce kike cewa cikinki na ciwo har kin ji sauki kenan ko

Layla ta mike zumbur sannan ta kalleta da sauri tace big sis welcome back, ehmm ehmm naji jiki sosai amma ai yanzu na ɗan ji sauƙi.."

agajiye nur tace its okay i am glad ure' fine ta bude jakarta ta fidda wasu littfai gashi nan na amso miki notes daga ajinku saiki dudduba ki kwafa tunda kin ji sauki.

layla ta yi wani murmushin karya snn ta karba notes din da murna tahau dudduba wa a tsatsaye,..thank you yaa nur yanzu dai kiyi wanka kihuta nasan kin gaji ni zanje kitchen ina zuwa..nan da nan ta juya tafita cikin sauri kai tsaye tawuce hanyar dakin mahaifiyarsun.

Nur ta dan yi shiru, tare da bin bayanta da kallon shakku can ta girgiza kai ahankli kawai tafara rage uniform dinta ta ninke su tsaf tsaf akan loundry basket sann ta dora towel tanamai fadawa gidan wanka.

bayan kamar minti ashirin Nur firdaus ta kammala wanka ta shirya cikin doguwar riga baka plain jallabiya me 3qtr hands tafito tana jin yunwa sosai. Tana saukowa daga step ta ji ƙamshin abinci har yanzu yana tashi hakan yasa tayi sauri tanufi tawajen dining area domin samun abinci a nitse ta karaso ta tsaya cak

lkcin mrs taga Haseena tana zaune a dining din gefenta Layla ne da Sadat sunacin fried rice and chicken cikeda nitsuwa...

Ta ɗan ƙwalla ido ta yi sallama a hankali snn ta gaishesu ba yabo ba fallasa, ayayinda taga mrs haseena ta dauki warmer sauran last portion na abinci ta zubashi akan plate din sadaat..

nur bata saka komi aranta ba ta ja kujera ta zauna tsabar yunwa har wani jiri jiri takeji warmern ta jawo ta bubbude saidai babu wata alama da kenuna cewa an tanadar mata da nata abincin.

kamar zatay kuka ta kalle mrs haseena mummy ba a bar mini abinci ba ne? i am so famished tun safe dana karya ban sake cin komi ba.

mrs Haseena ta ɗago kai tanakan tauna nama abaki tace toh Ai ban san za ki dawo da wuri bane Kin san dai kullum kekike latti.

Nur ta haɗiye yawu tana kallon yadda Layla ke figar naman kazan cikin jin daɗi, kamar zatay kuka tace "mummy kina nufin ban da abinci? mrs haseena tace abinci fa kadan ne nur ya kare wallh, batace komi ba Sai ta ɗan sunkuyar da kai To amma ai layla tasan na dawo

Haseena ta harare ta. "and so what, ke dai Ba za ki taba daina mita arayuwarki ba yanxu so kike ace laylan dani duk mun cutar da ke akan abinci? why dont u go and cook it by urself nace miki wann kadan ne kuma ya riga ya kare wallh...

ahnkli Nur ta runtse ido zuciyarta cike da takaici ta san ba za ta taɓa samun mafita ba idan har za ta yi faɗa da mahaifiyarta a kan irin waɗannan kananan abubuwa.

mikewa tay jiki a sanyaye ta koma daki dukansu sukabita da kallo kanta na mata wani irin ciwo dan sosai ta saka ranta akan abincin.

Mrs haseena ta cigaba da mita tana cewa yar rainin hankali wai tun safe dataci bata kara ci ba yanxu saka samu taci
ta koshi wanda zamu cin ne take so itama sai taci.

sadat baice uffan ba layla ce take dan saka mata baki.

nur tana kwance akan gadon tsabar yunwa jikinta ya fara daukae zafi tunanin abunda zata dafawa kanta taci take saiga nan Layla ta bude kofa hannunta dauke da wani bowl me dauke da cornflakes tana karasowa ta ajiye bowl din corn flakes a gabanta.

yaa nur Gashi ki sha wann na hada miki" Ta furta cikin sanyin jiki.

Nur firdaus tana kallonta tace thanks layla amma Kin san ba na shan corn flakes.

Layla tayi wani irin da fuska toh ai shine kawai yarage agidan gara kisha da ace bakici komai ba...

Nur ta girgiza kai tay shiru Layla ta zauna kusa da ita tana dan murmushi kallo daya zaka mata kasan ta ƙagu ta bata labarin duk abunda ya wakana ayau.

ana daf za'a kira magrib nur na shirin mikewa layla tace yaa nur Kin san wani abu kuwa?hmm Wallahi yau ninaga bajinta

Nur ta ɗago kai kaɗan tace A'ina?"

Layla ta dan lumshe ido tana murmushi
nan da nan ta hau bata labarin fitar tasu...

yaa nur Gaskiya Adnan yana da gata. Mamansa Hajiya Mariam Shehuri, mace ce da komai na duniya ke tafin hannunta Wallahi idan kin ga yadda take tafiya, yadda take magana, yadda tayi kwalliya… ba sai an gaya miki ba itadin babbar mace ce
i also got a chance to meet all his anties wayyo big sis baki ga kaman da sukeyi da Adnan ba mum dinsa tace ma mummy wai daga taci zabe zaayi auren Adnan.

Nur firdaus ta ɗan yi murmushi kaɗan ba don komai ba sai don ganin yadda Layla ke kamkamba labarin kamar zata tashi sama, ita kuwa abun bewani darata ba dan kuwa haryanxu zuciyarta Yana cikene da wani irin nauyi da ba ta fahimcesa ba.
I WILL MAKE IT UP FOR THE FEW DAYS DAT WE LOST AYI MIN UZURI WANI ABUNE YAKE DAN SHAMIN KAI

THANKS. SURAYYAHMS
[17/02, 20:27] Anne-Aurora🦋: NUR FIRDAUS... 17

SURAYYAHMS.

toilet nur firdaus ta shiga tayi alwala ta fito tasamu layla bata dakin bowl din conflake din data kawo matan ne kawai akasa yadda ta ajiyeshi ahankli ta zare agogon hannunta ta cire snn ta shimfida abun sallah tahau kai dan taso tayine a waje inda take bitar karatu amma sabida yunwar datakeji kawai sai tayanke hukuncin yau bazata fita ba.. tada sallahn tay bayan ta idar ta gama azkar dinta, tana zaune awajen tana yan adduoi tsakanin lkcin magrib da isha kafin nan ta hada tea me kauri tasha, ta dauki cornflakes din ta aje shi agefe tahau gado tare da janyo chmistry tex book dinta tana dan duba practical din da zatayi gobe tana gamawa ta rage wutar dakin ta kwanta tay shiruuuu tanajin wani irin yanayi na tsananin kadaici da damuwa na mamayarta ta duba fuskar wayatta yafi sau biyar bataga alaman sako ko kiran adnan ba tarasa mesa rashin lkcin nasa kullum se gaba gaba yakeyi tun abun baya damunta tana masa uzuri ynxu har ya fara damunta sosai cikin raya wasu abubuwa aranta wni nannauyar ajiyan zcya yakufce mata bazata ta dan lumshe ido tanajin wani irin nauyi aranta bana wasa ba.

dagata dayan bangaren kuwa cikin sanda layla ta iso kofar dakinsu mumynta ta lafar da kunnenta ajikin kofarsun tay tsam badon komi ba saidan ta jiyo me sukeyi ata ciki

ko tunanin irin wahalar datasha akansu jiya batay ba, kawai so take yau ma ta sake jiyo wani abu
sede tun da ta saka kunnenta muryan mummynta kawai takeji da alaman tana waya da mutanen su da organisation da kuma wanda suke harkan siyasan hjya mairam dasu.

koda ga isarta wajen tafi awa uku tana labe amma mrs haseena bata gama amsa wayoyin datakeyi ba dan wann na katsewa wani zai kara shiga shikuwa sadaat na nanike da ita yana yi yana dan babbasarwa kamar babu ruwansa amma sosai yasaka kunnensa 100% yana kwasar information na abubuwan datake cewa game da hjy mairam kanem duk dama bawasu masu amfani sosai bane.

ganin wayartan bana kare bane ya jawo rigar pjymas dinsa ya saka yabar faffadar krjinsa a waje snn mike tsaye ya fita cewarsa zai je kitchen ya hada musu coffe

cikin sauri sauri da murmushi mrs Haseena ta gyada masa kai sabida tana Allah Allah ya fice ne tay wasu bayanan sirri
da mutanenta.

daga shi sai dogon wando da rigar pyjamas din daya bar gabanta abude yana dan taba jikin kofar layla tay wani irin fillewa da gudu taje ta tsuguna kadan ta boye kanta abayan katon flower vase dake aje wajen tay tsamm bata ko fidda numfashi

babu tantama yaji motsin mutum ta waje da sauri ya kutso kai wajen inda qamshin turaren ta ya datsar dashi ya tsaya cak yana dan dube dube kirjinta na bugawa ta dauke numfashinta cak tanata kallonsa jin zuciyarta na harbawa da matsanancin karfi

after like 3 mint da baiga alaman kowa ba ya karkada kai ya wuce kitchen aransa yana tsammanin ya same nur firdaus aciki tana girki tunda dazun agabansa mrs haseena tahanata abinci. shide kallon yara kanana yake musu wanda basu da wayo musmn ma nur firdaus din datake cikin rauni har wani gani yake kamar ya dau lkci dayawa yana daga musu kafa amma yanxu kam babu abunda zai hanashi samun kanta cikin sauki...

yana raya abubuwa aransa har ya isaga bakin kofar kitchen din yadan tsaya abkin kofar kadan yay tsam waiko zaiji motsinta aciki amma sai shiru

ahnkli ya turo kofar kitchen din cikin sanda yana shiga kuwa ko kammala karewa kitchen din kallo baiyi ba saiga nan layla ta billo ta bayansa kamar wacce aka jefota taja ta tsaya a dede bakin fridge...
Chapter 27 · 0% Book details