← Book details Nur Firdaus Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 20 OF 96

Sashe 20

Nur Firdaus Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

cikin jin haushin abunda haseena ta goranta mata tace
in ma na shiga hirar maqiyarki Ai ba hirar banza ba ce, Hajiya haseena Na dai ga kamar kece kike fitowa a talabijin kina magana kan tarbiyyar yara musmmn ma yara mata. Amma inaa aimu sai mun ga abin nan da gaske awajenki, kuma Muna addu'ar 'ya'yanki su zama abin koyi, amma fa idan sun rushe ki, kar ki manta kema ki bayyana wa duniya komi kamar yadda kika bayyana maganar Ummi a idon kowa."

dede nan Haseena ta fusata tace Na san ke da sauran makwabtan nan nawa baku taba farin ciki da ganin na ci wata nasara ba. Kullum ku kuke nan zaune cikin hassada, matsiyata, yan dorin dosino a gwarimpa, jahilci ya kafe ku waje guda..kudai kuna jiran ganin na fadi kasa. Amma bari in fada miki, babu wanda zai iya rushe ni a duniyan sai ubangijin daya daukaka ni. Kuma idan kinada wani abu da za ki fada game da 'ya'yana, ki bari sai lokacin da abin ya faru, idan har zai faru kenan."

Maman Saeed ta kalli Haseena da wata irin murmushi mai cike da tsokana da tsananin haushin jin baqaqen kalaman data yafa mata.

"Ai gaskiya zata fito fili Haseena. Kuma fa sai mun ga yadda za ki kare kanki idan duniya tagane ke ma ba kida da cikakkiyar tarbiyyar da kike kokarin yada wa al'umma."

Haseena cikin zafin rai tace "Idan kika gama magana ramatu kike ko Mman Saeed, sai ki koma gida ki ci gaba da rayuwar ki ta dadiron ci. Ni baki kai nayi musayar yawu dake ba, kuma ba ki isa ki tsayar da tafiya ta ba. duk wanda yake bina da sharri dai Allah ya isa!"

Ta juya cikin fusata, ta shige mota tare da murda tayar cikin sauri tana barin wajen Maman Saeed tabi ta da kallo mai cike da cin fuska da haushi.

gidan dayan makwabcyarsu wanda tadan tsufa maman saeed ta wuce cikin huci da fushi dan taje ta barbada mata labarin komi..

dagata dayan bangaren kuwa Haseena tana tuki cikin hanzari zuciyarta cike da zafi da takaici.

"Wadannan mutane ba su da wani buri sai na ganin na fadi," ta fada a hankali tanajiin ranta na tafasa sosai.

seidei tariga taayi alkawari a zuciyarta cewa ba za ta bari su yi nasara akanta ba. Matsalolin cikin gida da waje duk ba zasu hana ta kai ga cikar burinta ba.

aikuwa nan da nan Ta sake mayar da hankali kan maganan shari'ar Ummi. tanamai tabbatar makanta da cewa wannan yarinyar zatasamu adalci kodan maqiyanta su mutu Kuma idan suna tunanin zata rushe saboda 'ya'yanta cikin karkda kai tace muje zuwa ba su san iya karfina ba....
SHARE AND COMENTS

FOLLOW ME AT SURAYYAHMS

08060712446
[10/02, 19:38] Anne-Aurora🦋: NUR FIRDAUS...13

SURAYYAHMS

bayan tafiyar haseena aiki bada jimawa Nur firdaus tashigo cikin dakinsu da hadaddn qur'aninta rungume da lallausar kirjinta tana tafiya ahankli kamar wacce bata da laka, cikin sanyin jiki ta aje qur'anin akan desk dinta tabi ta kashe wayarta snn ta zauna ahkli a gefen gado tay yar tagumi.

har cikin kokon zuciyarta takejin wani irin nauyi da damuwa dan kokadan bataji dadin yadda jiyan bacin rai yasata maida magana mezafi da kuma tsawa wa mahaifyartan ba, duk da yawan rashin adalci da tunxirata da mrs haseena tay ders dis kindest part of her heart dayake tuna aya daya tak a cikin qur'a ni daga cikin Suratul Al-Isra’ tun daga 23 da Allah yace karka daga ma iyayenka murya koda kafurta musu kalman "uff", kada kuma kamusu tsawa..

sede tafi jin nauyin ayata 24 inda Allah yake cewa “Wa khfid lahuma janaahaz zulli minar rahmati wa qur Rabbir ham huma kamaa rabbayaani sagheera.", And lower to them the wing of humility out of mercy and say, ‘My Lord, have mercy upon them as they brought me up{when I was] small.’ haka kawai inta tuna ayar ya ambace humility saita dingajin kamar bata kyauta makanta data amsa ma uwarta magana a cikin rauni da tsawa ba, duk sai tarasa ya zatay, dan bata da wani dalilin tsaurara makanta duk dama tasan kowani dan adam a duniya raunataccen halitta ne sede ita din karamar yarinyace sosai data rike ilimin addininta amtsayin madogarar rayuwarta bana wasa ba.

duk wann guilt din datakeji a xcryrta shiyasaka tadenajin radadin ciwon abunda aka mata jiya sai bata tsaya duba yawan rashin adalcin da mrs haseena tamata ba da tunanin yadda Allah zaidubi nata reaction din aranta tahau yi makanta hisabi.

dakyar ta mike tabar tunanin snn tahau shiryawa cikin gogaggen uniform dinta dayake mata wani irin kyau within 30 minutes suka fito ita da layla duk jikin nur firdaus din a sanyaye sam zucyarta baya mata dadi dan hatta layla bata gane kanta ba har suka fito waje suka samu malam liman harya fito musu da mota domin tafya mkarnta.

as usual nur firdaus ta rusuna kadan cikin girmamawa ta gaishe da drivernsu malam liman ya amsata da fara'a, nan da nan layla tadauke kanta tay kamar hanklinta baya wajensu dan bata son yawan gaisuwa.

da fara'a malam liman yabude musu mota nur firdaus ta zauna agidan gaba tare da jingina kanta akan seat tanata tilawar karatunta acikin zuciyarta har suka kai makarntr bata lura ba saida layla taja wani numfashi me shegen karfin daya kusa razata " Yaa nur kiga ikon Allah yau za'ayi emergency assembly am very sure wani abu mummunane ya faru..

nur tay saurin daga kanta sama tana mai duban windon motar
batace komi ba tana observing Duka duka abunda ke faruwa can saiga wata mata da tawagarta a tsadadden mota sun taho tana hura hanci kai tsaye sun wuce offishin shugabar makarntar.

Ayayin da Nur Firdaus da Layla suka sauka kasa tare da sauran ɗalibai sun lura cewa akwai wani irin yanayi na tashin hankali.

dan Gaba ɗaya makarantar ta cika da kananan ƙorafe-ƙorafe da kuma hayaniya wanda bai saba faruwa ba.

suna gab da shiga aji, sai wata sanarwa ta fara fitowa ana kira ga dukkan ɗalibai da malamai su hallara marmaza a filin taron asmbly da alama za'ayi wani gaggan taron gargaɗi.

nan sukaji mai gadin makaranta yana jan tsaki yana cewa Wannan abu da akeyi yau akwai matsala Allah de ya kyauta.

Nur Firdaus ta kalli Layla da dan mamaki, amma ba tace komai ba. Layla kuwa tana jin wani irin mugun nishaɗi a zuciyarta, kamar tana jin daɗin ganin tasowar rigima.

nan da nan kowani dalibi ya isa pavilion nayin asmbly aka jeru yau kowa ya hallara cikin nutsuwa dedeku daga cikin wasu ‘yan mata da samari suna tayin surutai kasa kasa suna zargin akwai wata babbar matsala data faru a ss2b..

cikin haka saiga nan shugaban makarantar gabaki daya wato Dr. Malam Ahmed Yakubu nan wajen yay wani tsiittt, ya taho cikin shigarsa ta alfarma da kamala yasha farar shadda me tsada yahau saman pavement din ya tsaya tare da duka membobin kwamitin ladabtarwa wato Disciplinary Committe ko ince DC

A gefensu wata shuumar yarinyace da aka fisani da Malika sa'id tana tsaye idonta cike da hawaye amma fuskarta na nuna taurin kai da tsaurin ido. nan Akasa ta durƙusa a gaban ɗalibai gaba ɗaya.

shugaban makarntar Malam Ahmed Yakubu dake kallon ɗaliban duka da daurarren fuska yace
"Ku saurara! A yau mun taraku ne domin mu koya muku wata darasi mai muhimmanci. ya nuna Malika, yace wann ɗalibar SS2 b ce, wacce ta kasa kiyaye martabarta kuma yanzu haka mun tabbatar cewa tana da ciki batare aure ba, wanda yazama abin kunya ga wann makaranta mai daraja da kima.

Malika ta sunkuyar dakai tana hararar kowa bakinta na motsawa kamar za ta ce wani abu muryan Malam Ahmed Yakubu ya dakatar da ita cikin jawabinsa yace "ICICE Academy ba makaranta bace da za azo mana da wasu shashanci har arena darajar tarbiyya da koyarwar Musulunci. dan haka Mun yanke shawarar korar Malika daga wann makaranta nan take, donta zama izina ga sauran yan mata. da maza, Kuma muna so mu ƙarfafa misali ga kowa kowane ɗalibi daya zama mai tarbiya da hali irin na nitsatsu daga cikinku, babban misali itace Nur Firdaus haroun please where is she, can she come up???.

jikin nur firdaus take ya dau rawa amma dake tana da karfin zuciya hakanan ta sunkuyar dakanta kasa snn ta fito tana tafiya ahankli gabanta na faduwa sosai har takai saman asemblyn cikin sanyin jiki.

lkcin ji take kamar zata nitse kasa dan fargaba, dan kuwa idon kowani dalibi da malami na akanta kirjinta yana bugawa da balain kamar zai ballo waje

shugaban makaranta ya nuna nur firdaus agaban kowa yace ita ce wacce koyaushe take zama abar koyi ga kowace ya mace a wannan makarantar.

tun daga ambatar sunan Nur Firdaus da yay sai gaba ɗaya ɗalibai suka fara surututai kasa, Malika tuni ta dago ido da sauri fuskar ta cike da ƙiyayya datake kallon nur firdaus din dashi.

Layla kuwa tana tsaye daga nesa tana kallon yadda ake yabawa tarbiyan ‘yar’uwarta a fili tanata murmushi a fili amma a zuciyarta kamar ana zuba mata garwashin wuta haka ta dingaji

daga gefe guda mahaifiyar Malika ta fito tana wani irin huci tareda tawagarta da kuma Malam ibrahim dake shugabantar guidance and counseling session na makarantar.

duk binta da case din a mutunce da sukayi taki sam sabida ita macece mai matukar ji da dukiyarta, tun tana tahowa tawajen cikin fushi takejin abunda ake fada akan nur fidaus,ga yarta malika nan akasa tay kneeling agaban kowa

jitay ranta na wani irin kuna dan Ita mace ce mai alfahari,iko da arzikinta duk dama bata da kyakkyawar tarbiyya ko kunya dan haka bata ganin aibu akan abunda yarta ta aikata. isowarta wajen asmblyn keda wuya ta fara daga murya cikin hargagi da tashin hankli tana cewa "Wannan wace irin hukunci ce? A ina aka rubuta cewa idan yarinya ta samu ciki shikenan sai a wulaƙanta ta haka? Kun ɗauki wann munafukar dalibar ta nuna Nur Firdaus da yatsa cikin zafin rai tace kunsata agaba kamar wata mala’ika kuna yabata agaban kowa,..wai har yata ce za'a yi misalin rashin tarbiya da ita tou in sha Allahu watarana za kuga abin da zai faru da naku yayan kuma munafukai mts.
Chapter 20 · 0% Book details