← Book details Nur Firdaus Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 46 OF 96

Sashe 46

Nur Firdaus Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

hadaddun motocin suna tsayawa Javeed din yafito daga motar cikin yanayin da ba kowane ke iya jurewa ba sabida wnn relaxed and casual looks din daya fito dashi datake karamasa wata nauin kakkarfar kwarjini data banbanta da na sauran maza., Dogon wandonsa irin tailored chinox black din nan ne baqinta yana wani irin sheqi tareda da Rolex daytona ɗinsa na gold daya makale a hannunsa na hagu tsabar laushi da farin rigarsa har zaka iya hango kwantaccen farin vest dinsa dake kwance tsamm akan faffadan kirjinsa ta ciki. tafiya yake cikin nitsuwa gurds dinsa na dan baya baya dashi dan bakowane lkci bane yakeson hayaniyar security a kusa dashi wani bin ma yafison yay yawon sa shikadai batare da taron body qurds ko security ba amma hakan sam baiyayuwa sabida babansa alhaj atta mufasah bayason barinsa haka ko kadan sabida harkan tsaro.

Matsakaicin bearded face ɗinsa yaƙara nuna ƙwazonsa, da haɗakar kamewa da kuma sassanyr izza dake tafe dashi.

Dayake harabar gidan tanada kyau da tsari nan take sanyi da kamshin furanni suka hau ratsa ilahirin gidan shi Bai tsaya ma shakar iskar da kyau ba kai tsaye ya nufi cikin gidan cikin kasaitacen takunsa mai cikeda nutsuwa.

ratsawa yay cikin doguwar falon wanda tun kafin yay sallama cikin katsesa da wata iriyar nokakkiyar sautin murya yaji sunansa na fitowa dakarfi daga can saman matakala, ya daga ido atakaice ya kalli simran is like she is freaking out, cikin kwalo ido tace oh my god Jay vee?? wani karamin tsaki yay ya dauke kansa. bata damu ba yar dariya me aji tay dan nuna jin dadin ganinsan Da wata sautin murya da ke ƙumshe da wani irin maitarso da kuma tsananin shaawa mai matsanancin yawa a kwayar idanunta ta hau saukowa.

tunda ya mata kallo daya ya dauke kansa cikin dakatawa daga tsaye batare da ya nuna alamun rashin jin daɗin ganinta dayayn a fili ba.

wani irin sauya taku tay Looking dashing acikin champaign gold skirt da rigan ta green kuma silk wanda ya fidda classy and porchy looks dinta me daukar hankali. sauke straight malaysian hair dinta ta dadayi side by side ya xuba mata har kafadunta wanda ya dada bada kim kardashian white colourn ta wani kalar kyau na ban mamaki

Masu aikin gidan dake wajen ne a tsaye cikin cool navy blue kitchen uniform suna dar dar cikin miko ma javeed din gaisuwa cikin jin tsananin shakkarsa da tsoronsa da kuma girmamawa wanda ko daga kansa sama baiyi akansu bama bare ya amsasu.

ita kuwa dr simran tunda ta kafe shi da ido wnn heavy make up Fuskan ta straight yake kallonsa tana tahowa cikin zakuwa manne da sharbeben ray ban gogles akan fuskarta, dan yau ko mayafi takasa iya yafawa don dama chan ganin idon hajya mammy yakesa in zatazo kadunan sai tana yin shigar yar mutunci irin wannan shigar, wani bin sai ta rike veil din a hannu wani lokaci kuma tayi rolling kawai akanta.

A hankali simran ke saukowa cikin catwalk mai daukar hankali tana Allah Allah javeed ya daga kai ya kalleta amma inaaa jikake kamar besan
ma wata mace tana motsi a wajen ba.

koda ta karaso cikin falon batama jira yay wata motsiba ta cigaba da kallonsa cikin tsantsan shauki kamar zata wani rungumesa amma ta kasa yin hakan sabida tanajin wani irin mugun shakkarsa

da rawan kai tace jayvee, i miss u so much jayvee, bakaji yadda naji wani farin ciki dana ganka ba, ashe zaka xo din, cos jiya i even Called you akacemun u will call me back inka tashi a bacci amma sai shiru har nayi bacci banga kirar kan ba..

wani shirun ya dada yimata har sanda ta gama far far dinta, acikin basarwa tareda yin kamr baiji metace ba yace "yaya kke?.

gyara tsayuwarta tay Cikin yanga da karairaya murya tace.. "i am good, i miss you like crazy, jayvee baka tambayeni yaushe nazo daga UK ba fa? ni inacan wata kasar inata missing dinka amma kai babu ruwanka dani ko..

kai tsaye yace yeah they told you i was busy ryt?

muryanta adan a sanyaye tace yeah amma u knw sabida kaifa nake dawowa, nd its been long i really want to spend sumtime with u, yaa zuby ce tacemin kazo kaduna shine naxo ko zamu iya samun lkci tare.

Idanunshi adan runtse yamata shiru baice komi ba. duk sai ta rasa me ke mata dadi.

...budan baki tay sede tunkan tay wani magana cikin katse mata numfashi cikin yace "kee wai ina hajiya mamy ne?

tace as usual tana can sama tanajin radio

...ƙara katse ta yay dacewa good, kai tsaye ya yunkura har zai wuce saman Simran ta wani matso kusada shi tanamai ƙoƙarin kwabe fuska kamar yar yarinya karama."Jay vee wait...bai motsa ba Ya dan tsareta da ido yana kallonta..tace hey, i dont understand u anymore, wai Me nayi maka ne kake wani shareni? i mean the way you ghosted me in UK was soo toxic. Nazo nan ma na jiraka jiya har tsakar dare, har yauma. Babu waya, babu text, ka shigo din ma amma gaisuwar ma bakaso muyi sai kace ba ni da wata muhimmanci agareka yanxu dama wajen hajiyarka kawai kazo bawajena ba haba jay vee "

Javeed ya dan dakata da latsa wayarsa dayakey cikin notsuwa fuskansa babu yabo babu fallasa yace "uhmmm i need to go upstairs simran, can you excuse me???

Simran tana kallonsa ta haɗiye wata yawu me tsananin ciwo jin yadda ya wani basar da korafinta, a take ta harde rai dan tasan Javeed tun bayau ba shi mutum ne da yake da mugun wahalar a shawo kansa, wani irin danne takaicinta tay ta ƙara matsowa kusa da shi tana ƙoƙarin dora ƙaramin murmushi dan kar yagane taji haushi

tace "Ina missing dinka ne kawai jay vee pls say sumtin nice to me.

Javeed ya yi tsaye yana kallonta dadin karin abunda yasa yakejin baisonta wann rawan kai da kuma desprate energy da Allah ya zuba mata datake ganin kamr wayewa ne, shikuma yafi son yaga mace me daukar kanta da tsada da aji sosai wanda koda bazai kulata ba he wll respect her in his hrt.

wani narke masa take kkrin yi muryanta ya fitowa da shagwaba shagwaba kamar na cikakkun karuwai ta wani langwasashi

"jayvee...pls tell me dat u came for me.. kaga yau har nasaka an maka abinci and its ur favourite, pls come with me kazo muje sama kaci abincin nd i promise you will like it.. jay..vee

cikin katseta da murya kasa kasa yace "Look, Simran," stop dis nonsense. "I am not your boyfriend, not your fiancé, and most importantly bazan taɓa zama daya daga cikinsu ba, i dont like tsilly games it looks stupid on you..

Idanunta suka firfito atake da wani irin karfi tace Dont insult mana Javeed!" i tot mun jima da gama wann maganan dakai?? you cant say that to me bayan kasan shekara ta 35 kenan ina jira na zama matarka jayveee please banason wann wasan...

saida ya dau mintina uku yana mata kallo da matsananciyar lalaci snn yace "Kiraba kanki da wannan rainin wayon da kike tunanin kece zan aura simran i havent made a choice yet. "you did. so, deal with it.

atsandare take kallon bakinsa dan ji tay kamar wani ruwan wuta yake zubawa wa naman jikinta

Bai tsaya jiran abin da zatace ba ya wuce kai tsaye zuwa sansanin Hajiya Mammy.

Simran ta tsaya cakkk tanata bin bayansa da kallo dan ita kadai tasan zafin datakeji aranta idan yana furta mata ire iren haka duk dama kawai gani take kamar aji kawai yake ja mata dan ita ta furta tana sonshi a farko dake haryau tana kulawa amma bata tabajin ance mata javeed ya kula wata mace ba.

but she cant deny the pain she is feeling, cos attitudes dinsa ma kawai na rashin nuna kulawa da ita da mugun jan ajin dayake mata ma kadai ya isa yasaka kowacce irin mace taji takaskanta bare kuma ajega kan furuncinsa dayake furtasu direct babu sakayawa babu kuma wasa aciki.

nan take Hawaye suka fara taruwa a cikin idanunta badon taji zafin abunda yay mata ba saidan saboda bakin ciki da tsananin jin haushin rashin kulata dayayi, dan inda sabo da halinsa ynxu tariga ta saba da dukkn wani yanayinsa ayanxu. cikin jan tukukin tsaki aranta tace muje zuwa nice ai zan mallake ka tunda har yaa zuby ta iya shiga gidanku ta zauna daram nima zan iya shiga wallhi.

cikin huci ta karashe furta hakan aranta snn ta juya afusace ta haura sama idanunta na cike da fushi....

isarta dakin keda wuya ta samu dayan wayarta akan madubi yana damar ringing cikin sauri ta isa gaban madubin tana dagawa tajefa a kunnenta tare da fashewa da kuka tahau gaggawa yaa zubynta yadda sukayi da javeed yanxun nan tanata zubar da hawaye sosai

cikin shahshntar da maganan hajya zubby tace "shi javeed dinne yagaggaya miki haka?

kafin simran ta amsa ta hauta da masifa
ke da Allah karyan banza karyan wofi, fada kawai yakeyi ai dama shibazai taba iya yin wani auren soyayya ba, karshe dai kece din za'a jona masa. dama aiwann mayyar tsohowarce bata sonki take cusa masa raayin karya aureki da tuni anyi an wuce wajen. amma kinsan wani abu??

simran ta girgiza kai tana share hawayenta

hajya zuby tace yi mar mar maza yanzun nan kitashi kibimin bayan sa kije kijimin mesuke tattaunawa akai shida kakan nasa saikizo nanki gayamin kinji??..

aikuwa jiki na rawa rawa simran ta katse wayar tay marmaza ta wanke fuskanta ta fito tayo hanyar sashen hajya mammy acikin sanda tanemi waje ata jikin kofar ta manne kunnenta tana jiyosu daga nan...

Javeed ya shigo cikin kayatacccen ɗakin da Hajiya Mammy ke ciki lkcin tana zaune a kan kujerar ta mai laushi tana tallafe da farin mayafinta tana kallon wani tsohon album din hotonanta masu cike da moments na dumbin tarihi wasu hotonan tana kalla tana murmushi wasu tana famar tare ruwan hawayenta akansu ahankli.

Tana ganin javeed fuskarta ya cika da annuri ta kallesa da alfahari cikin murmushi me fadi tace.... "Brigadier General sirrr, wann sabuwar matsayin naka ya fi Javeed ɗina da nake kiranka dashi tun kana ƙarami" ..
Chapter 46 · 0% Book details