← Book details Nur Firdaus Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 53 OF 96

Sashe 53

Nur Firdaus Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

raunataccen murmushi ne ya suɓuce mata tare da gyara zaman gyalenta ta dan rusuna gabansa da ladabi tamasa sallama muryanta na rawa sann tace ni ce baba dan batayi tsammnin zai ganeta da wuri haka ba.

rikota yay ajikinshi da wani irin shaukin farinciki a muryansa yace yah Allah nagode maka, i knew dat one day u will find ur way and come my doter. wow wow look at you "Masha Allah! Nur Kin girma! dubeki Kin zama wata kyakykwar budurwa..

hawayensa dayaketa dannewa suka sauka

hannunta ya jawo jikinshi har na rawa tsabar murna Sai da suka zauna akan wata chair sannan ya fara share hawayen ya ɗaga wayarsa yahau kirar matarsa ta farko tana dagawa yace ke Hajiya Sa'adatu kifito marmaza kiga wani abu,.wacce ba jimawa ba tafito sanye da wata tsadadden riga da zani na blue shadda data sha aiki kanta a rufe da mayafi suna hade ido da nur firdaus tunkan yay magana ta taho ta gudu ta rungume Nur Firdaus din sosai tana faɗin "wayyo Allah, Masha Allah Nur firdaus??..kece yau agidan namu, A'a, kin girma sosai , masha Allah, Allah ya albarkace ki yar nan lale marhaba kai amma naji dadin ganinki. Bayan nan Nur bata kara samun wani hutu wajensu ba tsaban bada haquri da uban tambayoyi akan rayuwarta dana layla data sha. anan ne ma nur din takeji yadda mummynta tay ma yan uwan ubansun tijara snn takaisu kotu tace araba alaqarsu da ita. suna tsaka da hirar sai ga nan Hajiya Bilkisu, matarsa ta biyu da ta fito daga ɗaya ɓangaren cikin wata shigar abaya mai launin ruwan madara. itama tana zuwa ta hango tsabar kamnin nur firdaus din da na mahaifinta alhah haroun dan akwai hotonansa agidan, a ladabce suka gaisa dukkansu babu wanda bai yaba ma kokarinta na zuwa nemansu ba zuciyar nur cike yke da nuna godewa Allah da irin kyakkyawar tarbar da aka yi mata dan kusan kowa acikinsu zumudi yakeyi akanta.

musamn ma kawunta alhaj abubkar wanda duk dayana fama da baqin cikin tarkon da haseena ta kafa musu ta rabashi da yayan dan uwansa ganin nur firdaus ayaudin yasaka yadingaji kamar yasakata acikinsa dan tsabar farincikin dayaji..

oder na musamn aka kara bawa me aiki aka dada kara cikowa da abubuwan kwamulashe aka sake shirya musu dinning table din da kyau.

a tsakiya suka sakata da hirararrki kala kala har aka kira sallahb magrib alhaj abubakar din yabarsu ya fita masallaci, uwar gidan nasa hajiya saadatu ce ta jawo nur firdaus suka haura sama dakinta anan tay sallahn magrib har da isha bayan sun idar ta mammata nasiha akan rayuwa ta kuma tabbatar mata cewa su basu gujesu ba mahaifyartan ce tay duk wani abunda zatay dan ta nesanta su dasu kuma abune daya shafi siyasa, zubar da mutunci, da kuma doka me tsanani sabida haseena ta riga ta kirkiro wasu shedu masu nauyi akan yan uwan mijinta a kotu.

Nur dai batacewa komi amma already ta riga tasan halin mahaifyarta dan haka abun be wani dameta ba, kawai de yadda aka tarbetan ne cikin tsananin marmari da nuna soyayya yasataji wani iri aranta dan tasan da kawunta yana cikin rayuwarsu hala da bazatay kewar mahaifi a duniyarta sosai ba.

daga dayan ɓangaren gidan kuwa wani shantamemen dakine me matsanancin kyau wanda kallo daya zakamai kasan dakin yar gatace wanda iyayenta suke mugun ji da ita dan duk wani abuna kyale kyale akwaisa a dakin komi is Dark pink or peach hatta babban gadonta an lulluɓesane da bargo mai launin peach, wata yar matashiya ce wacce bazata wuce 24 yrs ba azaune agaban madubi wanda kallo daya zaka mata kasan takai makura wajen wayewa da kuma ilimin boko cos class and levels is screaming all over her.

zaune take agaban madubi akasaitance doguwace me wani faffadan hips gwanin shaawa, gashinta kuwa dogone har gadon baya, fatar ta is silky smooth laushi tamkar anwanketa a man zaitun.

A hankali tabuɗe manyan idanuwanta masu sheƙi tana miƙa hannuwa zuwa ga kan dumb waiter daya kawo mata abunda tafi kauna a duniyarta wato coffe. kaf duniya inka cire bacci, coffe da shopping RAZIA ABU bata damu da komi ba. cos she alwys feel like she cant live witout these 3.

acikin mugun yanayi na daukaka da cikakken kwalisa take daukar kanta aynxn tana ajinta na karshe kenan a law school England, amma wann duk be darata ba dan babban burinta a duniya shine taga tazamo wata babba kuma shaharriyar jarumar film ko fashion super model a london koma dukansu biyu. shiwann karatun law din datakeyi kusan ince na dolene kawai takeyinsa badon son ranta ba saidan ta faranta ma mahaifinta ransa sabida yaki sam ya amince mata akan nata burin na zama yar film kuma model wanda har yau ji take bazata taba hakura dashi ba.

kusan rayuwarta gabaki daya a london takeyinshi, hutune yake kawota nigeria sama sama shidinma sai an takurata sabida she alwys think her parents are too traditonal sunfiyeson abubuwan gargajiya wanda already yayi hannun riga da yadda ta tsara nata rayuwar.

Dan duk wani abu dayashafi iya daukar wanka kyau, kwalisa, iya magana, kwarjini da sarauta awajen ya mace saidai shedan yaja baya ya bawa Razia kujerar zama.

despite being a top law student in england amma daga taje hutu london inda gidanta yake bata hutawa zakaga tana shiga lungu da sako wajen gogaggya da manyan world class beauty cougars and gays da barronesses just to update her feminine power and luxurious fashion sense.

tana zaune tafi minti talatin a Gaban babban mirrornta da ya ɗauki cikakkiyar surarta da baida maraba dana Dr simran othman waziri sede ita razia nata bountiful bodyn natural babu surgery ko kadan ajiki,everything abt them is almost perfect face jarkar nono dayaso ya dan musu yawa.

kullum razia tazauna agaban madubi ta kalle kanta sai ta tuna yadda jikintan yay matukar dacewa da irin dream din ta zabar makanta, dantana mugun mugun ji da kyaun fuska da kuma tsarin dirin da Allah ya mata bana wasa ba.

kwalliya tay me mugun daukar hankli kai bazakace bacci zataje maka ahaka ba slow and majestic ta mike tsaye tana cewa "Ohh my God! I’m hot!" Ta faɗa tanadada kallon hip dinta daya kara fitowa sosai.

bayan nan ta tashi tsaye ta shiga walk in closet dinta after few mins ta dawo sanye da wata designer pink doguwar rigar bacci wacce ta mannu da dirin jikinta sosai, komawa tay tazauna akan chair din mirron tanajin kasala ajikinta sosai dan batajin tana da bukatar sauka kasa ayau bare kuma taci abincii.

bayan ta gama shafe tsadadden turarenta original tom ford me shegen qamshi Ta kara juyawa gefe da gefe guda tana kallon yadda faffadan hips ɗinta ke motsawa a cikin madubi..

dan kadan ta rausaya tay wani irin run way cat walk in two steps snn ta juyo tay wani murmushi tace Nifa super star ce!! marilyn monroe of this era, haaaaa
,..Wallahi, ni dai bazan biye wa Baba wann karon ba, Ina son yin film kuma inson na zama babban supermodel, naga na taka manyan titunan fashion a duniya just like yasmine ghauri, gigi hadid, bella hadid, kendell nd the iconic naomi campbells.

dariya me sanyi tay kafin nan taɗauki wayarta ta duba wasu hotunanta data dauka tana turawa house of liberty fashion academy london da suke famar online auditioning tana murmushi,ta san dai duk yadda akayi wata rana zasu amsata kuma daga zarar an kirata tasan babu wani abunda zai iya dakatar da ita daga zuwa london domin achieving dreams dinta face mutuwarta.

tana aje wayar tahau kimtsa doguwar bakin gashinta da ribbon ta ɗaura shi a ƙeyarta wanda Daidai lokacin ne wata ‘yar aikinsu ta leƙo..a ladabce tace "ma'am, hajiya tace ki fito wai akwai baƙuwa yau a gidan.

ahnkli razia ta juyo ta kalle me aikin acikin tattalin kai tana daddana soson powder akan fuskarta lighty tace "Baƙuwa?"
mai aiki ta gyada kai
razia Tadan ja tsaki ta ajiye soson powder toh Wacece kuma da har sai ankirani naganta?"

kallo daya tama me aiki tace me sunan bakuwar?

mai aikin tace ranki shi drankiadi naji kamar ana ce mata Nur Firdaus.

Ta ɗaga gira sama da mamaki. "Nur Firdaus? its sound familiar amma dai duk tamanta Waye hakan
"ahnkli ta lumshe ido cikin kyaɓe baki tace Toh you can leave, kijje kice ina zuwa. Tana faɗin hakan ta ɗauki wata arniyar kimono mai taushi ta saka saman rigar baccinta sannan taɗora ɗan kwali dan daidai tafito tana takawa ahnkli kamar bazata taka kasa ba.....
#SURAYYAHMS
08060712446
*oya naaa, COMENTS, AND SHARE UR constructive VIEWS LETS KEEPWAKE THE HOUSE...❤️❤️❤️*
[03/04, 19:23] Anne-Aurora🦋: *NUR FIRDAUS...26*
@surayyahms
Tafiya Razia takeyi akan steps din kamar bazatay ba domin itakanta qamshin turaren data fetsa ajikin nata tsabar dadinsu da karfin qamshinsu ji take kmr suna bugar da ita.

Daya bayan daya take dora kafafuwanta akan step cikin tattalin kai adede lokcin ranta yake gama ayyana mata tasauko kasa taga wacece nur firdaus din nan da sai an kirata daga daki ta sauko don kawai ta ganta.

tana saukowa taga iyayen nasu zaune akan wani hadadden 12 inches smooth golden luxurious dining table da aka kawatashi da ababen tabawa na zamani
masu aikin gidan ne akansu sunata aikin serving dinsu gabaki daya wajen ya gamutsu da wani irin qamshin abinci me shegen dadi da dadadan aroma na garnished soups da gasashun namar kaji.

acikin dakika razia ta kare musu kallo saidai daga nesa bata gane nur firdaus din sosai ba sabida irin yanayin shigar datayi dan kimononta is pure black witout any flashy design gashi da mugun kauri kafatta dama ba arabashi da socks hakama kanta baya rabuwa da inner cap kai kusan kominta akillace yake wanda ko angaya maka itadin karamar yarinyace da bata wuce 17yrs ba bazaka taba yarda ba.

zaune take akan chair kusa daf da kawun nata daya zuba mata cold Brew drink dake baza wani danbanzan qamshin chokolate me saka kwanciyar hankali kusan kowa awajen yana na haba haba da ita.
Chapter 53 · 0% Book details