← Book details Nur Firdaus Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 75 OF 96

Sashe 75

Nur Firdaus Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

duk da tsoron daya gama cikata haka ta maida layla bayanta tanamai kareta basu ce musu uffan ba kuma basu motsa wajen ba..

wani tsageran gayene acikin bakonsu fahad din yataho zai kama hannun nur da karfin tsiya yajata ciki ta harzuka ta gallara masa wani uban cizo saida wajen yay jini

yana mikewa ya yunkuro zai kai mata mari Allah yaso takau da fuskartta sai marin yasauka akan layla, wani irin mugun ihu me kara laylan ta sakar musu awajen..

amugun razane tafara cewa fahad dan Allah kuyi hakuri, pls leave us alone...wallhi mu bafa wajenku muka zo na, mu gida zamu tafi pls pls pls dan Allah

nur batace komi ba tanata kallonsu tana kuma kkrin kare laylan abayanta hawaye na zubowa a idonta tana readyn wanda zaizo ta kai masa naushi a fuska sai inda karfinta ya kare ta raya aranta.

kara zagayesu gayun sukayi dayan ya fara shafa hannun layla ahankali yana jan long fingers dinta tafara razanannen kuka ta dada kankamewa nur riga ta baya...

Nur zata kai mai duka kenan wani yay wuf ya Jawota jikinsa da karfi ya shafa fuskarta lkci daya yashiga kkrin tura hannunsa rigar abayarta, Wani irin mari ta sauke masa ta fauce kwalban glass cup din dake rike a hannunsa ta buga masa akai da iya karfinta, nan gayun sukay wani kukan kura zasu mata daukar cak su shiga da ita daga ciki

ihun da bata san daga ina tafarashi ba yazo mata tafara kai musu duka ta duk inda hannunta yakai...

dede sun mata taruwar dangi suna kkrin daukarta kenan aka wani irin buga gate din da mugun karfi me razanarwa

atake gayun suka saketa ta fadi akasa tana rolling akasa layla tay gudu tazo ta dagata sunata kuka tare nan sukay gudu sukaje suka boye kansu abayan wani mota dunkule da juna...

kafin kace wani abu wasu mutane masu bakaken kaya da mask ajikinsu sun balle makullin gate din sunshigo ciki da hilux dinsu da bindigogi sai wani dau suka dallara haske a compound din..

sai ji kake ana Police, police, police, ga yan drugs, ga effcc, kan kace wani abu fahad da gangs dinsu sun bace awajen bat suka bi wani secret exit.

polisawa suna kkrin kama mazan dake haye fence aysha tazo dagudu tace ma su nur su taso akwai hanyar da zasu bi ta baya ai babu bata lkci suka bi ayshan sukabi ta secret exit din suma sai gashi kuwa sun billa waje ta baya..

wani mota suka gani cike da mutanen da suka tsira aciki suna kaiwa motar aysha tay saurin tura layla ciki itama ta shiga ciki dagangan ta ture nur akasa tay gefe, kamar kiftawar ido motar ta tashi aguje tunma basu gama rufe kofa ba suka wuce suka bar nur awajen tanata kwallara ihun kirar sunan ayshan dana laylah cikin dimuwa.

gadai wajen is safe and quiet amma daga nan kanajin hayaniyan hukumar dake guje guje da yara anata ihu ana guje guje tsoro ya cika zuciyar nur ta kama hanya kenan zata bar wajen sai taga wani mota acan cikin duhu yana dan haskata tana daga ido kuwa taga su fahad ne acike acikin wata jeep sun boye kansu suma suna jiran back up dinsu.

ashe acikin baqin da suka gayyato partyn akwai yan drugs da yan yahooo shiyasa NDLEA suka hadu da police sukazo kame

nur tana ganin sune tafara ja da baya baya kirjinta kamar zai faso waje bata sani ba ashe duk hakan shirin su da ayshane akan akawota nan yaran kam sun dage sai sun walakanta nur sun cimma burinsu akanta dan kawai suyi kaurin suna kuma dama ba wani tsoron hukumar sukeyi ba dan duk iyayensu masu kudi da power suna mugun daure musu gindi.

acikin motarsu aysha kuwa layla sai kuka take tana nadamar zuwanta nan sai ihu take ma aysha akan meyasa suka tafi suka bar nur aysha tace mata ai akwai motar da zai kawo nur din gida duk dai layla ta daga hanklinta amma haka aysha ta kira wani gaye sukayi wayan karya agaban layla suka sata ta amince cewa nur is safe and coming

wajajen 2:ocl suka kai layla gaban gidansu, aysha harda mata alkwarin cewa yanxu zasu koma su dubo nur kawai ita din ta shiga gida.

jikin layla be taba bari irinna yau ba, dan kar malam liman yasan ta fita harta dawo ta katanga ta dire ta sauka ahankli ta wuce cikin gidan luckly enuf for her mrs haseena yau ma bata kwana agidan ba..

ata fannin nur kuwa tunda taga gayun ne duka amotarsu sun takuro aciki kamar sardine suna famr haskata tay shahada tadubi gabar hanyane tarr agabanta ta wani falfala da uban gudu bata ma ganin gabnta dai tamike kan hanyar dataga motar da su aysha suka shiga yabi ta dinga gudu ba tsayawa.

ganin har tafara gudu wasu gayun suka sauko suka fara binta su kusan hudu sauran kuma suka juya da mota sukabi titi da niyyar shawo gabanta

Dan bakaramin abubuwan sharri dana walakanci suka shirya yau zasu mata ba.

tana lura da motarsu a titin tabar kan hanya tabi jeji jeji inda tasan mota bazai iyabi ba da iya karfinta take rabza gudun suna biye da ita can sai sauran ma suka parker motar sukabi sauran cikin jeji duka su bakwai din suna hunting inta

har saida suka yi nisa sosai taji ta fara kasa ci gaba da gudun.

tana haki ta fara ihu jikinta na rawa tana cewa "Help plsss...."
duk ta galaibata amma bata hakura da gudun ba, ta mugun tsorata dataji har sun kusa su kamota sai kukan fitan rai takeyi can sai taga titi daga nesa kamar wacce aka kara mata mai akafarta taruga aguje tana layi tay kan titin da mugun gudu bata ko lura da zuwan mota ba saida akay mummunan jan birki agabanta sann ta dawo hayyacinta.

wani irin tsit tayi ganin wata baqar motace ta tsaya agabanta me shegen kyau ayanayin mugun rudewa ta dan bubbuga gaban motar tana haki tace pls pls help me pleasse.

atake javeed yaji ya daskare yanata kallon ta tacikin tinted sai yana ganin kamar karyane ba nur dinshi bane gizonta kawai yake gani, haka taci ihun neman taimako baiko sauke glass dinshi ba, adan mamaknce ya daga hannunsa ya dubi time a agogonsa yaga 2.40 am na dare

He just cant believ dis..

jikinta na wani irin rawa tana kuka ganin me motar beko sauke glass dinsa bare ya kulata da sauri ta juya xata bar wajen tana daga kafarta ji kawai tay an fincikota, ihu ta fasa dai dai lkcn da su fahad dukansu suka gewayeta daya acikin su ya karaso da gun dik suna haki suka tsareta ta ko ina

javeed na zaune a mota yanata kallon ikon Allah...

nur tafara sabon kuka yaron daya rike gun din yafara mata ihu me razanarwa yana kkrin kwaco hannunta tana tuburewa lkcin ko ina a jikinta na rawa rawa ta fashe da kuka a tsorace tace Don Allah ku kyaleni..

atsawace fahad yace mu kyaleki bayan uban gudun da kika samu dan ubanki yau saikinyi yaren garinku

cewa dayay dan ubanki yasa ta hatsala basuyi zato ba ta dalla ma fahad din mari...

azuciye tace ba ubana na ba sai dai naka uban get away from me, menayi muku, what did u guys want frm me???

mamakin karfin halin ta yasaka yaran kusan haukacewa mutum na farko daya harzuka ya kawo hannunsa zai cakumota ya wanka mata mari yaji an rike hannun nasa ta baya

tsabar abuge suke da kwaya basuma san yaushe javeed din ya fito ba, wai dan rike hannun yaron dayay ya murda saida ya karya masa hannun kabas ji kawai sukai yaron yasaka ihu me kara yana furta wayyo Allahna hannuna...

yaran suka tsaya suna kallon javeed sukaga shima su yake kallo dan sosai yasha mamaki dayaga ma yarane yan kanana da basu mallaki hanklin kansu ba.

kamar wata gunki haka nur ta daga ido da kyarrr akangare tanata kallon fuskar javeed duk atunaninta ko dai imagining dinsa kawai takeyi.

tsagaren cikinsu wanda yazo da gun din ya daga gun din wai zai nuna javeed din dashi, aidashi da gun din javeed ya hadasu ya wanka musu wata gigitaccen marin da saida yaji jiri ya kwashesa atake ya yar da bindigan babu shiri.

kan kace wani abu javeed ya fidda guns harbiyu daga gefen aljihunsa yana cirewa within scnds cikeda kwarewa kai tsaye ya harbe hannun yaro dayazo da gun din wanda atake dukansu sauran suma suka zube kasa a mugun tsorace..

masu shirin gudu da sukaji wani irin tsawa da javeed yay atake suka saka gwiwonsu akasa suna rawan dari. cikin zare musu ido yace wani acikinsu yana yin tari akai zai harbesa ya kashe banza...ai atake kwayar ta warware jikin su yay la'asar

saida ya kare musu kallo fuskarsa a dore snn yace now get up and lie down flat, ur hands on ur head
...suna kan tahowa yana kai musu duka da naushi dan dama acikin sojojin ma MPs irinsu javeed mufasa bakaramin mugaye bane dan sune suke hukunta yan uwansu sojoji insunyi lefi..

He is very strong, vicious, and ruthless bazaka taba sanin haka ba face har sai wani abu ya hadaku

kan kace kobo su shidan sun shimfida kansu akan titi flat akasa hannunsu akai
na bakwai din ne daya harbe hannunsa ya rike wajen sai kuka yakeyi kamar dan akuya yana juye juye.

yana sakasu kwanciya yajuyo kan nur firdaus wani irin fixgota yyi daidai fuskarsa yana huci atake idanunsu ya sarkafe cikin na juna da wata iryar mahaukaciyar shauki

hawayenta dake kan sauka na neman yay melting dinshi amma haka ya tsime yace
ke kuma Me ya fito da ke cikin dare nan?

sai sann ta dawo cikin duniya jin gamshin turarensa mai dadin kamshi na neman ya cikata ganin wai jiran amsa yake bakinta na rawa tace"i came to look...uhmm its my sister..na fito..na fito wajen layla ne and and....sai kawai ta fara hawaye sabida yadda yake binta da wata muguwar kallon tuhuma dan bazata iya daure ma wnn wutar kishin dake yawo a kwayar idanunsan ba.
Chapter 75 · 0% Book details