← Book details Luu Luu Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 96 OF 97

Sashe 96

Luu Luu Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Hayaniyar ta mata kama da ire iren hayaniyar da kan motsa a gidan a duk sanda sultane yayi wasu muhimman baqi. Haka kawai taji qirjinta ya doka,wata irin fargaba tana saukar mata,fargabar data sakata miqewa a hankali tana dosar 'yar harabar dake maqalena falon wadda aka yita ta fuskar da zata iya ganin kusan duk abinda yake kai kawo cikin gidan.

"Akhnan....." Aisa ta fada da zafi,sai shehnaz ta daga mata hannu,abinda ya sanya aisa dakatawa kenan,don tasan tabbas akwai dalilin daya sanya shehnaz din yin hakan. Suna a zaune suna hangen sanda ta fita farfajiyar tana kuma aza dubanta dukka ga inda take hangowar.

★Sake duban yalwa tayi da kyau da wani irin hautsinannen kallo.

"Me kike cewa?" Ta maimaita tambayar yalwa,duk kuwa da cewa ta mata bayanin da koda baka fahimtar kowanne yare kana iya gane me yalwa ke fadi.

Kasa yalwa tayi da kanta,ta sani wannnan labarin ba kalar labarin da uwar dakin nata zataso ji bane,amma kuma labari ne me matuqar daraja da tsadar da zai ya qara daga martabarta a idanunta.

"Me martaba ne yake karbar baqi daga zinder.....wazirin qasar zinder,da shugaba limamai na zinder gaba daya wato mahaifin hakeem,wadanda sukazo da kayan neman auren gimbiya akhnan". Wannan karon ji tayi kaman ta koma ta zauna ko zata daina jin kamar ana hajijiya da ita,to amma kuma nuna rauninta a kowanne irin yanayi abune data jima da nesanta kanta dashi.

Tana da tarin rauni,yana kuma bayyana,amma a muhallin da babu wani mahaluqi da zai gani,daga ita sai ita daya qwallin qwal,domin tana ganin nuna rauni gazawa ce da zata janyo maka raini gurin wadanda ke qarqashin sarrafawarka.

"Ya akayi labari me girma irin wannan ya boyu har sai bayan ya tabbata?,labarin dani ya kamata na fara sanin da shi?" Ta yiwa yalwa tambayar. Kai yalwa ta jinjina.

"Abun akwai daure kai,don ina tabbatar miki kaf! Fadin masarautar nan,ba wanda yasan da zuwansu......banqi ko morsa safiyya ba" Tayi maganan tana juya kai cikin alhini da jimami.

"Morsa safiyya" Ta maimaita fadin sunanta kamar tana jinjina girman sunan. Kai ta jijjiga a hankali. Tunda har ya kasance sultane bai shaida mata ba.....tunda har sultane bai gaya mata ba bata zaton safiyya ma ta sani.

Ita daya ce mutumin dake sanin boyayyun abubuwan sultane wanda ba wani mahaluqi da yasan dasu........ita kadai ce wadda yake shawarwarin da ba wanda yakeyi dasu. Koda batanan sukan zama ajiyayyun shawarwari har sai randa ta dawo ta fadi nata hangen akai.

"Yaushe sultane ya fara koyon boye abubuwa?" Ta yiwa kanta tambayar da batasan ta fito sarari ba,har sai da taji yalwa tace.

"Allah masani,amma dukkan alamu sun nuna akwai giftawar magauta a ciki". Dubanta ta maida ga yalwa.

"Karbar gaisuwar sarkin zinder da mahaifin hakeem.....hakan na nuna tabbatuwar auren hakeem da akhnan?" Ta yiwa yalwa tambayar da ita kanta tasan amsarta EH ce.

Sultane baya magana ya sauyata,bama sultane kadai ba.....dabi'a ce ta dukkan wani basarake data taba sani.

Indai haka ya tabbata kenan akwai yuwuwar faruwar komai......akwai yiwuwar komai zai iya kasancewa......kasancewar da take nufin tarwatsewar abubuwa da dama.

(Don samun littafin lu'u lu'u 08187255862)

Ginannen BURI.....ajiyayyar MANUFA......tsohuwar FANSA da aka jima ana mata tanadi. Kai ta jijjiga da wani irin qarfi. Koda komai zai jagule......koda za'a rasa rayuka da lafiya na wasu mutanen ba zata bari haka ya faru ba......akwai SADAUKARWAR LAFIYA da RAYUKA da zata faru cikin masarautar agadez kenan. RASHI zai faru,koke koke zasu yaiwata,har sai ta tabbatar komai ya tafi mata yadda takeso. Ba zata damu da koma waye ZAI SAMU ko ya rasa ba.....ba zata damu da koma waye ZAI QUNTATA ko ya shiga masifa ba....FANSARTA........BURIKANTA suna gaban komai. Ba zatace Allah ya taqaita ko ya sawwaqe ba......idan ya taqaita ko ya sawwaqe tana yiwa wadanda abun zai shafa BARKA DA MURNA.

"Inason a yanzu basai wani lokaci ba,ki isar da saqon zuwan wadannan baqin ga kunnen akhnan" Ta bawa yalwa umarni. Tana kyautatawa kanta zaton samun mafita a zuwa da dawowar yalwa,tana jin motsin akhnan daga shi kadai zata tsago mafitar da zata bata haske a gaba.

"An gama" Ta furta da sauri tana miqewa daga tsugunnon da tayi a gabanta.

"TURQASHI!" Mammina ta fadi a sarari tana dunqule hannunta gami da kaiwa daya tafin hannun nata duka.

"Ki nutsu......ki nutsu zaituna" Shine abinda zuciyarta ke maimaita mata,sai tabi shawarar zuciyartata,ta zuqo iske me yawan gaske tana aikawa hunhunta,sannna ta zauna a nutse saman kujerar tana qoqarin tattaro dukka kuzarinta da kuma kowacce qofa dake cikin qwaqwalwarta dake taimaka mata wajen bada tunani me kyau.

Tana kallonsu amma tana son qaryata kanta.......tana duban sultane da baqinsa amma tana qaryata abinda zuciyarta take raya mata tattare dashi.

Kayan sarauta na masarautar zinder......kayan hadimansu dama dukka wani yanayi irin nasu ba baqon abu bane tattare da ita. Dukkan baqon da sultane zaya fito da kansa ya tarbeshi ba shakka ba qaramin muhimmanci baqon yake dashi ba a wajensa.

A hankali qafafunta da hannuwanta sukayi wani irin rauni sanda take hangen hakeem a cikinsu. Wata irin faduwar gaba ta daki qirjinta data sanyata dafe qarfen gurin da kyau. Kai ta girgiza a hankali tanason tankwabe kalar tunanin da zuciyarta ke kutso mata dashi. Daidai sanda taji birra na fadin.

"Mammina ta aiko da saqo ta hannun jakadiya yalwa". Kai kawai ta iya gyadawa birra din,wanda ta kauce kadan,abinda ya bawa yalwa daman kutsa kai farfajiyar gurin.

Tsam aisa ta miqe,tana jin hankalinta bai kwanta da tsaiwar akhnan a gurin ba. Uwa uba wanne saqone haka yalwa ke tafe dashi wanda yanayinta dukka ya nuna alamun a gaggauce take.

Taku uku aisa tayi shehnaz itama ta miqe tabi bayanta.

"Tace na gaya miki ki tattara hankalinki da nutsuwarki guri guda......baqi ne daga zinder wadanda ke dauke da dukiyar aurenki......a yaune kuma sultane zai basu tabbacin bada ke ga dansu bayarwa ta har abada da zata halasta aure a tsakaninki dashi". Kaman kunnuwanta basu jiye mata daidai ba haka taji,sai kuma ta soma jin kamar ana turata baya kafin ta dangane da jikin shehnaz da tayi tsaye a bayanta. Bata damu tasan waye ya riqeta ba,idanunta akan yalwa kamar itace sultane din.

"Bayar da aure na?,karbar dukiyar aure na?.....ga hakeem din?" Ta fada da wani sanyi a muryarta,ba kuma kalar sanyin dake cikin zuciyarta kenan ba,don wata irin kalar wuta zuciyarta ke fiddawa da adadin zafinta da zuginta ya zame mata na daban.....kalar wanda bata taba tunanin rai da zuciya zasu iya d'an d'ana su kuma jure a rayuwarta bane.

"Ba shakka.....haka abun yake". Da wani irin hanzari ta sanya dukka hannayenta biyu ta ture shehnaz dake riqe da ita,aisa tayi kan shehnaz da turwar tazo mata a bazata don kai mata dauki,gudun kada ta fada kan kujerar qarfen dake bayanta ta zame mata ciwo,wannan kuma shi ya baiwa akhnan daman ficewa daga farfajiyar da wani irin yanayi kamar name ficewar hayyaci. Da wata irin madaukakiyar murya me qarfin gaske take fadin.

zaki samu daman karanta wannan QASAITACCEN LABARIN ta hanyoyin siyan tikitinki kamar haka da naira (700) kacal*

*Lambar asusu:- 6019473875*
*Safiya musa abdullahi*
*Keystone bank*

*KI TURA SHAIDAR BIYA TA NAN*

09166221261
KO
08187255862

*Al'ummar qasar nijer 🇳🇪*

*2349166221261*
*Safiya musa abdullahi*
*NITA*
*CFA 500*

*SAIKU TURA SHAIDAR BIYA TA LAMBAR DAI*

09166221261

*GA WADANDA ZASU SAKA KATIN WAYA NA MTN SUMA NUMBER DUKA DAYA CE*

*MTN CREDIT 700 ZUWA GA*
09166221261

*SHAIDAR BIYA*
09166221261

*_TAFIYAR 'YAR GASKE CE........LABARIN QASAITACCIYAR MACE CE KAWAI KE IYA SIYANSA_*

*QASAITA👑*

*HUGUMANKU CE*✍🏽

💎 *L U'U L U'U*
*_(The diamond)_*💎

*H U G U M A*

PAGE 83
___________________________
*_Domin qulla huldar kasuwanci damu,HUGUMA CLOSET.......,siya ko siyowa wani,reposting ko sari akan farashi me rahusa da babu irinsa,maza yi joining group namu don samun ingantattun kayan da babu ha'inci a ciki da izinin Allah_*
https://chat.whatsapp.com/FrqgC0YmUWP4FPmUzYuLJX
___________________________

"Wallahi bazan aureshi ba....zanje na sake jaddadawa sultane......bazan aureshi ba!.....bana sonshi!.....a rabu dani mana haka!"

"Bita aisa......bita" Shehnaz da abun yazo mata a matuqar bazata da wani irin tarin mamaki ta fadi,sai aisa ta saketa ta kuma fita zuwa parlor din da sassarfa,inda dukka hadimanta sukayi tsaye cak cikin razana da tsoron fusataccen fushin da suke gani tattare da uwar gijiyar tasu.

Tana dab da qofar farko,amma ba wanda ya isa ya kamota a cikin su,sai zallar tashin hankalin daya bayyana a idanunsu saboda maganganun da take fadi cikin bacin rai.

Cafko hannunta aisa tayi,wadda ta qaraso gurin da gudu,sai akhnan din ta waiwayo tana dubanta gami da watsa mata wani irin kallo

"Sakeni!" Ta fada a fusace. Duban tsakiyar idanunta aisa takeyi. Wannan fusatacciyar zuciyar data jima bata yunquro ba ayau ta ballo kenan.

"Biftu?,baki da hankali?,a cikin hayyacinki kike?,sultane din zaki je ki tara gaban baqi ki gaya masa bakyason auren hakeem!"

"Eh!......haka nake shirin aiwatarwa,don suma su sani bazan auri dansu ba.....banaso!....ki sakeni aisa!" Ta fada a tsawace da lallausar muryar nan da ayau ta zama wata me kaushi.

"Bazan sakeki ba.....bazan kuma barki kije kiyi abinda xai zubda kimarki ba,ya zubda kimar masarauta,ya taba mutuncin sultane ba" Wani kallo me cike da tsananin bacin rai take jefawa aisa.

"Idan ma baki sakeni ba naje.....bazan zauna baqinciki ya kasheni ba,zanyi abinda yafi haka.....guba zansha!.....guba zan sha na mutu kowa ya huta!.....naga wanda za'a yiwa auren ko?!" Akhnan din ta furta da madaukakiyar muryar da sautinta ya karade dukka falon da wajensa.

Kasa cewa komai aisa tayi,sai idanu data zubawa akhnan a tsorace. Tasan fushinta.....wani irin fushine me girman tasiri da idan ya motsa tana yin kamar me aljanu,tanayin kamar ta rasa hankalinta ñe......amma na yau din kamar yana neman zarta hankali,yanxu qiyayyar aure a zuciyar akhnan har yakai haka?.

Batasan sanda shehnaz ta iso guri ba,sai ganinta tayi ta rungume akhnan din ta baya kuka yana balle mata.

"Ki daina irin haka biftu....meye haka?,kinsan girma da munin abinda kike fada?,da kanki kike cewa zakisha abinda zaki kashe kanki?......biftu ki dawo hayyacinki mana" Ta qarasa fada tana zagayowa gaban akhnan din gami da riqe dukka fuskarta cikin tafukan hannunta.

Wasu irin hawaye ne suka cika blue eyes dinta da suke nuna koda wanne lokaci zasu gangaro,labbanta suka motsa,motsawar da aisa ta fahimci ta furta.

"Astgafirullah ne" Wadda bata da sauti ko kadan.
Chapter 96 · 0% Book details