Sashe 19
Luu Luu Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
*Lambar asusu:- 6019473875*
*Safiya musa abdullahi*
*Keystone bank*
*KI TURA SHAIDAR BIYA TA NAN*
09166221261
KO
08187255862
*Al'ummar qasar nijer 🇳🇪*
*234 9166221261*
*Safiya musa abdullahi*
*MY NITA*
*CFA 500*
*SAIKU TURA SHAIDAR BIYA TA LAMBAR DAI*
09166221261
*GA WADANDA ZASU SAKA KATIN WAYA NA MTN SUMA NUMBER DUKA DAYA CE*
*MTN CREDIT 700 ZUWA GA*
09166221261
*SHAIDAR BIYA*
09166221261
*_TAFIYAR 'YAR GASKE CE........LABARIN QASAITACCIYAR MACE CE KAWAI KE IYA SIYANSA_*
*QASAITA👑*
*HUGUMANKU CE*✍🏽
💎 *L U'U L U'U*
*_(The diamond)_*💎
*H U G U M A*
PAGE 13
★★★Kamar kowane lokaci sanye take cikin wata lallausar atamfa da aka yiwa dinkin buba,irin dinkin daya sake batar da kamannin atamfar sosai,idan ka kalleta da kyau karon farko ba zaka dauka atamfa bace,zakayi tunanin wani yadi ne na musamman cikin yaduka masu daraja da tsada da takan sanya lokaci lokaci.
Ranar tana daya daga cikin ranakun da me martaba sultane yake samu ya huta a cikinsu,musamman yau daya kwana da mura jikinsa sai ya zamana babu dadi.
Musamman ta shirya masa riz kissé da soyayyar plaitain da wasu hadin vegetables na musamman. Ba wani abinci bane na daban a sunan da kuma idanu,saidai ya zama na musamman a dandano da kuma irin qamshin da yake bayarwa,qamshin kayan spices na musamman da ya sanya abincin morsa safiyya ya fita daban daga dukkan dandanon wani abinci a harshensa.
A kashingide ta sameshi cikin wata lallausar shimfida dake da tsananin taushi. Yau din ya fito a buzunsa kuma ba'adazensa sak,don kuwa riga ce 'yar shara a jikinsa ta wata dakakkiyar shadda da kum dogon wando,sai rawanin dake kansa wanda yayi masa nadi na cikakkun buzaye.
Shafukan qur'ani ne a hannunsa bugun warsh yake karantawa ciki ciki,amma shigowar safiyyan da kayan abincinta ya sakashi ajjiye qur'anin,ya kuma miqe ya zauna sosai yana murmushi.
Safiyya kenan iya rigima yake fada qasan ranshi. Ba tun yau ba yasan wannan,gwanar iya tunkarar duk wani nau'in rigima ne idan taso........idan kaso kuma komai zai wuce kamar bai faru ba.
"Marhaban lale" Ya fada yana miqa hannu zai karba mata kwandon. Janyewa tayi tana murmushi da accent dintan nan na yarensu tace.
"Bazan baka aiki ba.....kaida kake cikin lalura?". Murmushi kawai yayi. Kaman ba shekaran jiya aka gama hatsaniya da ita ba,ta birkita masa lissafi ta kuma birkitawa kowa.
Sosai ta zauna tana gaidashi cikin bashi girman da Allah ya bashin,ya amsa yana janta da tsokana,sai ta saki murmushi kawai ta jawo kwanukan abincin ta fara budewa.
"Me nassamu ni muhammadu?" Sosai maganar tasa ta sakata sakin murmushi,ta jima da sanin cewa tabbas shi din yasha banbam da sarakuna sosai......ya musu wata irin tazara me girma,yana mu'amala da iyalinsa da irin salon da zai nuna maka bai dauki kansa kowa ba a wajensu. Zakasha mamaki ida kaje ka sameshi cikin fadarsa.....ko ya fita wani taro ya cika wajen da wannan kwarjinin nasa,zaka tsinewa kanka ba shine a yanzun zaune ba.
"Tashi murmure na kawo maka". Tun bata gama zubawa ba yawunsa ya tsinke,ya sani bai taba yin matar da tasan martabar girki ba irin ta,tana da baiwa qarshe ta fannin iya abinci.......tana kuma bata lokutanta sosai wajen dafa masa abinci koda ba ko yaushe ba,girkinta a lokutanta yafi girkin hadimanta yawa.
"Wannan toshiyar baki ne halan?" Ya fada sanda yayi lomar farko,dadin abincin yana ratsashi.
Murmushi tayi tana sadda kanta qasa gami da murxa yatsunta kadan.
"Har ka gano ni?" Ta fada muryarta qasa qasa.
"Nafi kowa sanin halinki.......nafi kowa karantarki" Ya fada yana murmushi dadin abincin yana dibansa.
Kai kawai ta jinjina,bata musa ba......bata kuma yi jayayya ba. Mutum ce da bata iya boye abinda yake ranta ko yake cinta,ko yaya ne abu yake damunta sai ka fahimta,kota gaya maka,ko ka gani a fuskarta,ko ka gani a aikace. Bayan rasa imraan,bata qara tunani ko hasashen samu miji kamarsa ba,sai gashi Allah yayi mata kyauta da sultane din......wanda koda cikin mafarki bata taba kawowa zata mallakeshi ba koda wasa kuwa.
"Abincin cin hanci ne......cin hancin da na baka shine don ka tsaya ka fahimci zancan Allah da ma'aikinsa......zancan da yake da matuqar muhimmanci ba ga duniyarmu kadai ba......har lahirarmu" Tayi maganar a tausashe cikin qanqan da kai sanda ya kammala cin abincin yana miqe qafafunsa. Kallonta yakeyi sosai yana jin sautin muryarsa tana ratsashi,bazai ce ya maida gurbin safeena ba.......amma safiyya ta dabance.......daban take a zuciya da rayuwarsa.
"Wanne zance ne haka me muhimmanci har haka?".
"Batun amana ne.....magana akeyi akan amana" Ta fada yana sauke numfashinsa daga tambayarta da yayi.
"Amana?" Ya tambayeta yana jin kalmar tayi masa nauyi. Kai ta jinjina tana dubansa.
"Eh amana......amanar da safeena tabar maka......amanar da safeena tabar min.....wadda ni kam duk yadda naso ban isa na sauketa ba saida hadin kanka da goyon bayanka". Kai ya sake jinjinawa,zuwa yanzu hankalinsa yakai inda take nufa. Ganin maganar zatayi mata daidai da yadda take so ya kasance saita gyara zamanta sosai tana sake qanqan da kanta.
"Nasani ka sani......manzan rahama da kansa yana cewa......namiji me kiwo ne a gidansa......kuma zaa tambayeshi gami da abinda aka bashi kiwon.....kiwonnan kuwa ya hada da mata da 'ya'ya.......Allah yana cewa......yaku wadanda kukayi imani ku tsare kawunanku da iyalinku daga wuta......wanda wannan wutar makamashinta sune mutane da duwatsu......safeena ta tafi tabar maka amanar biftu.....shin a ranar gobe kana da kowacce amsa da zaka bata akan khadeejah idan ta tambayeka game da ita ba tare da d'ar d'ar ko tunanin ka kuskuro ta wani fannin ba?" Ta qarashe maganar da tambaya. Tambayar data masa nauyi sosai,ta kuma tilasta masa yin shuru,idanunsa akanta har lokacin.
Kanta ta girgiza sannan taci gaba da magana.
"Musulunci ya bawa iyaye daman zabawa 'ya'yansu yammata mijin aure.....hakan daidai ne,saboda ya duba cewa qila hankulansu basu nuna ba bare su zabawa kansu mijin daya dace da rayuwarsu......akwai sakin hannu me yawa game da damar daka bawa biftu.......ba zata iya ba......ba abinda zatayi wataqila saici gaba da wulaqanta masu daraja.....wanda akwai tafkeken kuskure cikin hakan.....altaab shine na tara da taqi amsa a mazaunin mijin amre......kana lissafe?". Maganar tata ta ratsashi sosai. Don sam wannan lissafin bai taba zuwa kansa ba.
"Baka tsoron wani ya cutar da ita ta wannan hanyar?.....ko bada sihiri ba qullaci idanu da baki dukka suna iya zamewa rayuwar bawa masifa".
"A'uzubillahi min kulli ainin lammah......wamin kulli shaidanin hamma" Ya furta a nutse wanda ta tabbatar yana nemawa diyarsa tsari ne daga abinda ta fada.
"Neman tsarinnan ranka ya dade ya kamata ya zama a aikace......ta hanyar taimakar diyarka ka zaba mata miji ma'abocin addini da zai saita rayuwarta" Sosai yake dubanta da maganarta ta qarshe yana fassara hakan cikin kwanyarsa.
"Eh.........namiji me addini shine kadai wanda zai iya gyara rayuwar biftu.......namiji me cike da nutsuwa da hasken addini......shi kadai ne zai cike gibin da aka bar mata cikin rayuwarta.......shi kadai ne zai iya kula da ita......ya dinke kowacce kalar baraka dake tsakaninta da ibadunta da mahaliccinta dama mutanen da take rayuwa tare dasu.......namiji me addini ne kawai zai riqe hannunta daga duhu zuwa haske......shi kadai ne fitila cikin rayuwarta......akwai tarin gyare gyaren da shi kadai ne zai mata nuni dashi......muddin kana buqatar tsiron nagartattun jikoki da zasu iya riqe masarautar AGADEZ daga fita daga hannunka.....a nan kusa muddin kanaso kaci moriyar jikokinka.....idan hakan bata kasance ba kuwa zai zamana dukkan wata dama zata qarasa subucewa daha hannunka".
Wasu irin dunqulallun maganganune da suka jima cikin zuciyarta da ruhinta......wasu irin dunqulallun maganganu masu tarin yawa da yau ta samu ta warwarewa sultane su......wata dama da taketa fama taci gaba da samunta har abada......damar da take sanyan ran da ita kadai zata iya tsaiwa gaban safeena ta gaya mata NA BAWA KHADEEJA GUDUNMAWA IYAKACIN QARFI DA IKONA.
Maganganun da suka dauki tunaninsa suka maidasu saman saitin da yakejin ya kamata su kasance.
"Na gode sosai safiyya......ina alfahari da samunki......saidai alqawari ne na yiwa kaina.....muddin raina ko yara million nawa na haifa bazan taba musu auren dole ba.....kowacce cikin yarana tana da damar farko......saidai idan ta gaza a damar farkon.....wala'alla a dama ta biyu ta rasa damarta" Dan murmushi ta saki,don iya wannan kadai daya fadi ya bata nutsuwa da tabbaci.
"Bashi da alfanu.....saidai sau tari idan har an kaucewa son rai,ita kadai ce take zamewa iyaye damar fidda yaransu zuwa turbar tsira......na aminta da alqawarin daka daukarwa kanka.......na yarda dakai kuma kan zaka canza komai.........." Kai kawai yake jinjinawa,saita rage masa tsahon tunanin daya jefa kansa ta hanyar gyara zamanta sannan tace.
"Dazun da safe munyi waya da hairaan......mun jima muna tattaunawa da ita.......daga qarshe dai ranka ya dade......raina da hankalina bai aminta da ci gaba da zaman yaran nan ba a qasar nan......mun yanke shawarar zasu dawo nan suci gaba da karatunsu......zan nema musu malamin da zai dinga koyar dasu qur'ani da litattafan addini......domin duk rayuwar da babu karatun addini a cikinta rudu ce da fagabniya zallah......ruhin da ba qur'ani a cikinsa Allah ya taimakeka fanko ne" . Kai yake jinjinawa yana sake aminta da hankali da nutsuwar morsa din. Tana da zafi da gaske ne tana da fada.......amma kusan komai tana yinsa ne bisa gaskiya da hangen nesa.
"Hakan yayi.....amma ko acan din nasan hairaan ba zata qyalesu haka ba ba karatun addini".
"Allah ya baka yawan rai ayimin afuwa.... Duk yadda zaa basu na addinin nan baikai na boko yawa ba.....har abada yaro yaro ne......akwai kuma quruciya dukkaninsu a jikinsu......suna manta shi ilimin addini tamkar dan jagora ko sandan jagora ce ga makaho......shike saita kowanne ruhi da gangar jiki.....shine yake saita ruhi rayuka da rayuwa gaba daya".
"Allah yayi miki albarka.....dawa dawa zaa taho?". Ya tambaya yana murmushi,don shi kansa kawai yana yin kara ne don kada ya shiga rayuwar yaran nasa..... Amma yan tsananin kewar jikokin nasa
"Dukkansu me martaba,falaak din......sai aafreen da aeeda,shi Aaroon nace su barshi can gurinta ya zauna da Anwar dan uwansa,kafin lokaci yakai suma na tattarosu".