Sashe 73
Luu Luu Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Bakin window ta qarasa,ta saka hannu ta bude labule kamar wadda iskar dakin ta sassanyar A.c ta yiwa kadan,batakai ga ajiye hannunta ba lafuzzan da take faman jira suka sauka mata a kunnenta.
"Yalwa ce"
"Qaraso" Ta bata umarni kai tsaye ba tare da taji qarshen maganar tata ba.
Da hanzari ta baro bakin window din,ta kuma tako da dan hanzarin tana zama hannun kujera,yayin da yalwa ta zube a qasa fuskarta da murmushi.
Iya murmushin fuskar yalwa ya isa ya gaya mata kalar nasararta.......iya wannan murmushin kadai ya gama bata dukkanin amsar da takeso,amma saidai tana buqatar taji ta kuma sake samun tabbaci daga bakin yalwa din.
"Allah ya tayawa ayyukanki......komai ya tafi daidai......kamar dai kullum,kamar kuma ko yaushe,shima dai ta tankwabar da tayinsa,ta kuma watsawa sultane qasa a ido,don tozarcinsa yafi kowanne kalar tozarci da ta taba yiwa wani". Wata ajiyar zuciya me nauyin gaske ta sauke wanda take cakude da murmushi. Ta qanqance idanunta sosai tana sakin murmushi gami da hango yadda nesanta ta dawo kurkusa.......tana kuma hasashen yadda komai yake tafiya daidai,hanyoyi kuma suke gyara kansu da kansu.
"Da kyau!........" Sai ta miqe tsam tayi taku biyu.
"Duk yadda zataso ganina yanzun kada ku bari hakan ta faru,banason na zama ta farko da zata gayawa qudirinta,kaman yadda banaso ta fara haduwa dani kafin taga sultane.......ki yiwa Souleman magana,a fiddo min mota,zanje ziyarar awa daya,kafin na dawo na tabbatar komai ya kankama". Qasa yalwa tayi da kanta tana jinjinawa basirarta,sannna ta furta kalmar.
"An gama" Ta amsa mata tana miqewa da duka hanzarinta.
*FALAAK*
Haka kawai ta dinga jin hawaye suna taruwar mata a idanu,hawayen takaici hawayen kunya......hawayen mamakin yadda yaa akhnan din ke iya rufe idanu taci mutuncin masu mutunci.
Tayi tsananin mamaki a abinda ya faru jiya,ta dauka iyakar abun kenan,saiga wata sabuwa kuma akan hakeem.
Koda baqonta na jiya ba wani daraja ko martabar komai a tattare dashi......amma hakeem yakai a martabashi da darajan ilimi da alqur'anin da yake dauke dashi.
Bata taba zato ko tsammanin abun nata yakai har haka ba.......sai a yanxun,tsoro yana sake shigarta,tsoron kada Allah ya jarabceta ko ya jarabcesu da wani mummunan abu sanadin wulaqanta ma'abota alqur'ani.
Ba zata manta yadda take ganin sultane yana girmama duk wani mahaddacin qur'ani ba,tun tana mitsitsiyarta......tun tana qaramar kuma tana iya tuna sanda yake musu alqawura da dama ga duk wanda ya samu haddace qur'ani a cikinsu. Duk da bata haddace duka ba,ta haddace kusan izifi ashirin a ciki......mutuwa ce kadai zata sanyata ta manta irin shagalin da sultane ya hada cikin masarauta saboda samun izifi ashirin din da tayi,ya tabbatar mata na izu sittin dinta sai yafi haka,saidai bata samu wannan damar ba,auren hairaan ya tashi ta kuma dauketa zuwa France.
💎 *L U'U L U'U*
*_(The diamond)_*💎
*H U G U M A*
PAGE 63
Wani irin tashin hankali takeji idan ta tuna yadda taga fuskarsa. Ba wani abu daya nuna saman fuskarsa......saidai ga duk wanda yayi masa zuzzurfan kallo zaisan cewa akwai wani abu me nauyi daya sauka ya kuma nutsa can qasan zuciyarsa.
"Kiyi haquri......ranki ya dade hankula sun fara yowa kanki" Badee'a ta fadi qasa qasa tana biye da falaak. Ba wannan bane kawai burinta,burinta shine ta isa ga momma.......burinta ta ganta gaban momma.
Wani irin hali dabi'u da kuma dabi'a ce wannan tattare da yaa biftu din?.......wanne irin izza ne haka tattare da ita da takejin tana daidai da wulaqanta kowanne kalar d'a namiji?.......mutane masu mutunci......masu yakana masu kima da martaba?,amma take iya tsaiwa gabansu ta yage dukka wannan?.
Sam morsa safiyya bataji shigowarta ba,sai rungumeta ta baya da taji tayi,bugawar da zuciyarta takeyi tana ratsa gadon bayan momma din kwatankwacin mutumin da yaga wani abu me matuqar ban tsoro.
"Hasnunallahu wa ni'imal wakeel" Morsa safiyya ta fada tana sakin mayafin hannunta ta kuma juyo a hankali tana zare falaak daga jikinta tana dubanta.
Ko falaak bata ce mata ba lafiya ba ita din tasan ba wani batun lafiya sam a tattare da falaak din.
"Me ya faru?" Momma ta tambayeta bayan fa zaunar da ita ta kuma zauna kujerar dake fuskantarta.
"Ya biftu......" Ta kira sunan muryarta na karyewa,abinda ya sanya matsananciyar faduwar gaba kenan ga morsa safiyya.
"La haula wala quwwata illa billah" Ta fada can qasa tana fatan kada kunnuwanta suji cewa Akhnan din tayi abinda ta saba.
"Abinda ya saba faruwa ne ya faru?" Ta tambayi falaak a hankali kamar me tsoron furta tambayar. Kai falaak ta daga mata,hawaye na taruwa a idanunta.
"Momma.......a kunnensa jiya yaji ta mari wani......yau ma a kunnensa yaji yadda take cin mutuncin......" Sai ta kasa qarasawa saboda kukan daya qwace mata.
"Waye?" Morsa ta tambaya tana duban falaak cikin son jin abinda ya taba zuciyarta har haka.
"Sheikh mana momma......sheik muhammad" Numfashi me nauyi ta zuqa daga qofofin hancinta zuwa hunhunta,don tashin hankalin da take ji a dukka zuciyarta dama jikinta ya sanya bata tuna dashi ba. Ta fidda idanunta waje kadan.
"Farawar da gamawar dukka yana gurin dama?"
"Yana nan momma.....mun fara karatu......karatun yau ko gama shi bamuyi ba......bai nuna ba ko a fuska yaji komai ba tsakanin jiya da yau......amma nayi imanin yaji". Ta qarasa fada tana fashewa da kukan da yafi na dazu.
Shuru momma tayi tana zubawa falaak idanu. Yanayin kukan nata da yadda take yinsa da dukka zuciyarta sai ya rarraba mata hankali. Ba komai falaak kewa kuka har irin haka ba,kukan dake nuna daga ainihin zuciya yake fita ba. Wannan kukan da dukka zuciya da ruhi take yinsa......to mene yafi damunta a ciki?.
Tafi maimaita jin maganganun da yayi tsakanin jiya da yau akan abinda Akhnan ke sake shirin aikatawa.......tayi imanin a wannan karon......gagarumin tashin hankali ne ki shirin samun kowa muddin Akhnan wannan karon ta turjewa manufar sultane,batasan kuma iya wa dawa abun zai shafa ba.
Ta sani,harda ita a ciki,ita dinma zat cutu,xatafi cutuwa fiye da kowa ma,zatafi cutuwa sama da sultane.......tana cire mammina ne a dukka lissafinta saboda tasan maganar soyayya ko QAUNA tsakaninta da Akhnan wani shiryayyen abune da yake daidai da wasan kwaikwayo,wani shiryayyen abu ne da babu shi sam sam a rayuwa ta badini,sai zahirin da ya kasance idanu ne kadai suke iya ganinsa.
"Falaak" Momma ta kira sunanta jikinta da dukka muryarta suna sanyaya. Idanunta da suka kada suka sauya launi ta daga tana duban momma.
"Me yafi damunki ne haka?......"
".....momma yaji fa". Ta amsawa morsa safiyya ba tare data sauka daga tambayar ba. Idanu ta xubawa falaak din,har sai da falaak ta zargi wani abu data hanga cikin idanuwan morsa din,sai ta janye dubanta momma din tana sauke ajiyar zuciya.
"Ya zama malaminku ne bayan aminta da nutsuwa da tarin ilimin da yake dashi,cikakkiyar kamala da haibarsa da take nuna zallar kamewarsa.......ko ba dade ko ba jima,anjima yanzu gobe ko jibi dole zai iya tsintsar halayyar Akhnan......wannan din baikai ya zama wani abu me tayar da hankali sosai ba..........babban abun tashin hankalin shine bijirewa sultane da tayi a karo na qarshe......a dama ta qarshe daya bata. Biftu nada tsananin taurin kai da kafiya.......bansan wani abu da zai sanya ta janye daga tsaiwar da tayi ba akan ra'ayinta......yayin da shima sultane yake kasancewa tsayayye akan ra'ayinsa a duk sanda yazo kan mataki da gaba irin wannan" Ta qarashe maganar tana jin wani irin zugi na tasowa daga qasan zuciyarta.......wani sashe na zuciyarta kuma na gaya mata a hankali MAMMINA TAYI NASARA........TA SOMA CIKA MURADANTA kamar yadda a tsare a kuma rubuce cikin qudure qudirenta.
Saidai wani abu guda daya daya kasa wanzar da rauninsa a kanta shine.......bata yarda bata kuma taba aminta sam sam zuciyarta ta kissima mata WANI MAQIYI.....WANI ABOKIN GABA ko wani mafaraucin lamuranta wai yayi nasara a kanta......wannan yana daya daga cikin QARFINTA da har abada take dogare dashi.
".......jin da sheikh yayi bai kamata ya shiga cikin damuwoyinki ba......damuwarki shine yaya 'yar uwarki zata kubuta?,yaya zata tsira daga dukkan tarakuna......ta yaya zaku taro mutuncin mahaifinku da yake tambal tambal?" Morsa ta qarashe maganan tana duban falaak da dukkan hankalinta.
*AKHNAN*
Tun daga sanda ta iso qofar farko na sassan mammina.......dukkan wani hadimi dake numfashi cikin sashen ya shiga nutsuwarsa. Masu kaiwa da kawowa da sunan ayyuka dukkaninsu suka dakata da abinda sukeyi,suka kuma tsaya cak a inda suke kawunansu a qasa ba tare da sun iya daga kai sun kalli akhnan ba da yau muryarta ta zama wata abar ga kowa. Wannan lallausar muryar da ake tattalinta......wannan jaririyar muryar da ake yangar furta kowanne irin lafazi da ita......wannan lallausar muryar dake cike da wani irin taushi yanga yauqi da izza......muryar da ba kowa bane ya saba jinta ba......amma a yau da ita take taka kowanne gurbi na sassan mammina tana qwala mata kira.
Duk da cewa sunga fitarta,duk da cewa sunsan bata nan,amma kowa ya gaza furta mata hakan. Dukkaninsu cikin shakku da fargaba suke a tsaitsaye,harta gama duba inda ya kamata taga mammina din bata ganta ba,ta fara saukowa da sassarfa sai sukayi kacibus da aisa.
"Mammina bata nan ai.......ta fita" Aisa wadda buhaina ta rarrafa ta kirata don ita daya suke sanyan ran zata iya controlling Akhnan din ta fada tana dubanta tare da qoqarin nazartarta.
Dukka hannayenta biyu Akhnan din ta yarfar,tana jin wani abu yana mata yawo tsakiyar kanta.
"Me yasa mammina zatayimin haka?,me yasa zata fita a daidai sanda nafi buqatar ta?"
"Kina da momma ai.....morsa safiyya tana nan" Aisa ta fadi cikin bawa Akhnan qwarin gwiwa. Maganar aisan daidai take da zubawa wuta fetur,daga blue eyes dinta tayi ta zubewa aisa din su,sai kuma ta tuna dole dole akwai wanda take buqata,ko yaya tana buqatar wani on her side.
Takowa tayi ta kama hannuwan aisa duk biyun.
"Don Allah aisa.....S'ilvouse plâit........zaki rakani gurin sultane?" A mamakance aisa take kallonta.
"Gurin sultane kuma?,biftu a irin wannan lokacin......" Kai ta gyada mata tana qoqarin calming kanta.
"Dole naga sultane aisa......ina buqatar hakan". Hannunta daya aisa ta zame ta dora yatsarta a qirji.
"Ni kikeso na rakaki gurin sultane ki gaya masa kin watsar da zabinsa?......kin wofantar da zabinsa?.....zabin nannie?".