← Book details Luu Luu Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 87 OF 97

Sashe 87

Luu Luu Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Muddin kikace zaki fara narkewa da soyayyar captain obbo......na rantse nan gaba zaki koma tamkar ruwa ne.......ni nasan irin su captain sheikh..........saamee...." Sai kawai Anani ta gaza qarasawa tahau girgiza kai.

Ranar data fara duba daya daga cikin rubuce rubucensa akan soyayya,cikin wani irin tsari na a addinance yadda zaka kama zuciyar mace tabbas banda yayanta ne uwa daya uba daya tayi imanin ba abinda zai hanata fadawa soyayyarsa.

(Don samun littafin lu'u lu'u 08187255862)

Wasu irin kalamai da aka shiryasu da harshen larabci,sannan akayi translating nasu da yare biyu English da oromo,sai da tayi kwana uku tana duba littafi daya,daga qarshe data fuskanci idan batai wasa ba littafin zai iya sauketa daga karatunta daga qwallafa rai zuwa bigiren fara soyayya ba shiri,saita lallaba ta maida masa littafin sa ba tare da yasan daukowar da mayarwar ba,wanda yana dab da gama rubutunsa yayi publishing nasa aikin tafiya agadez ya tsaida komai.

Har yanzu idan ta kalleshi kalaman take gani saman fuskarsa. Wannan miskilar fuskar da babu fara'a murmushi ko sakewa a cikinta,fuskar da baki samun cikakken kallo daga gareta,da wadannan idanun masu wani irin nauyi,ashe sunsan tasirin soyayya har haka?.

Kasa cewa komai saamee tayi da tsiyar da Anani ta sakata a gaba tana mata,illa dai ta miqa mata wayar nanay kawai ta wuce dakinsu,don idan ba haka ta yiwa Anani ba tabbas zata uzzura mata ne kawai.

Saman gadonta ta fada,ta kuma jawo pillow ta rungumeshi sosai cikin qirjinta. Ba ita kadai ba,tasan akwai tarin tulin 'yammatan da suke cikin irin wannan yanayin saboda shi.

Tayi imanin a duniya ba macen da zata ganshi taji baiyi mata ba,saidai idan dama tasan ba zata samu bane. Babu wata halitta da zata kasa qaunatarsa,yana da wasu irin halaye da qualities masu tsananin tsadar da yake nasarar sace zuciyar duk wanda ya mu'amalanceshi. Hatta da qannaneshi sonshi suke,saidai su za'aci soyayya ce irin ta 'yan uwantaka,saidai duk da hakan tsakanin hussam da Aarif ba wanda ya samu irin soyayyar da dukkaninsu sukewa Muhammad haisam din.

Numfashi taja sosai cikin hunhunta. Idan tana imagination na ranar da zai kalleta yace INA SONKI SAAMEE,tana jin komai ya tsaya mata,ta kuma tashi daga wannan duniyar zuwa wata. Idan tana hasashen ranar da zata zama mallakinsa,sai taji kaman duniya gaba daya tata ce ita kadai.......to amma wanna fargabar tana nan.

Wannan alwashin yana nan,batajin kuma akwai abinda zai canza shi. Tana buqatar ya gamsu da soyayyarta da kanshi. Tana buqatar suyi exchange na soyayya,bawai ita kadai tayi dakon soyayyarsa ba. Tana babban mafarki da buri na auren namijin da duk duniya itace burinsa......itace zabinsa,itace mafarki da dukka muradansa. Koda ita batajin hakan,idan ta samu wadancan abubuwan a tare da namiji.....zata yarda zata aminta ta rayu dashi,wataqila nan gaba zuciyarta ta cika fal da soyayyarsa kamar yadda yake mata.

*MAMMINA*

Yau da kanta ta shirya kanta a daren da zuciya da qirjinta ke cike da tarin lissafe lissafe da burace burace.

Wannan zuwan,wannan tafiyar da zatayi da buqatar akhnan zuwa gaban sultane......a zahirin aiken na akhnan ne zallah.......a badininsa kuwa,wani babban buri ne......wata babbar buqata ce da take da burin cikarta fiye da girman buqatar da akhnan din keda ita.

Hannu ta sanya ta jawo jewelry organizer dinta tana laluben abun hannun da zata sanya,wanda zai dace da yanayin shigarta.

Har hannunta ya tsallake kansa,sai kuma ta dawo da baya tana sake sauke idanunta a kanshi,ta miqa hannunta ta dauka.

Wani irin bangul ne na asalin kayan gargajiya me tsananin tsadar gaske. Banguls din qwaya biyu ne rak,suna tuna mata wasu abubuwa masu nauyi da suka shude cikin rayuwarta. Suna da wani tsohon dadadden tarihin da babu ranar da zata dora idanunta a kansu ba tare da sun dawo mata da komai ba.

zaki samu daman karanta wannan QASAITACCEN LABARIN ta hanyoyin siyan tikitinki kamar haka da naira (700) kacal*

*Lambar asusu:- 6019473875*
*Safiya musa abdullahi*
*Keystone bank*

*KI TURA SHAIDAR BIYA TA NAN*

09166221261
KO
08187255862

*Al'ummar qasar nijer 🇳🇪*

*2349166221261*
*Safiya musa abdullahi*
*NITA*
*CFA 500*

*SAIKU TURA SHAIDAR BIYA TA LAMBAR DAI*

09166221261

*GA WADANDA ZASU SAKA KATIN WAYA NA MTN SUMA NUMBER DUKA DAYA CE*

*MTN CREDIT 700 ZUWA GA*
09166221261

*SHAIDAR BIYA*
09166221261

*_TAFIYAR 'YAR GASKE CE........LABARIN QASAITACCIYAR MACE CE KAWAI KE IYA SIYANSA_*

*QASAITA👑*

*HUGUMANKU CE*✍🏽

💎 *L U'U L U'U*
*_(The diamond)_*💎

*H U G U M A*

PAGE 75
___________________________
*_Domin qulla huldar kasuwanci damu,HUGUMA CLOSET.......,siya ko siyowa wani,reposting ko sari akan farashi me rahusa da babu irinsa,maza yi joining group namu don samun ingantattun kayan da babu ha'inci a ciki da izinin Allah_*
https://chat.whatsapp.com/FrqgC0YmUWP4FPmUzYuLJX
_____________________________

Sultane yana sonsu qwarai........duk kuma da son da yake musu takan jima bata sanyasu ba,amma a yau din sai taji zuciyarta ta cika da sha'awar sakasu,ta daga hannun damata ta zurasu a nutse tana sakin murmushi ganin yadda ya sake qawata hannuwan nata.

Tana maida jewelry organizer din taji an murda handle din dakin,kafin ta waiwaya kuma motsinta ya gaya mata ko wacece.

A hankali cike kuma da mamaki ta juya tana dubanta. Akhnan ce,sanye da wata farar Malaysian Avaya. An mata wani irin kyakkyawan ado da gold din zare daya sake fidda kyau da qawatuwar rigar. Maqale mayafin rigar yazo a kafadarsa,kuma iya shi kadai akhnan din ta yafawa kanta,wannna ya bawa gashinta me sulbi dake kwance a agadon bayanta daman bayyana saboda wuyanta a bude yake saboda yadda tadan dora mayafin kawai ba tare data wani daidaitashi saman kanta ba.......hakanan kana ita gabin baqar sumarta data fara daga gaban goshinta,ba wani cirewar gashi kaman dasashi akayi.

Wani irin kyau tayi,kyan daya dauki hankalin mammina ya kuma tuna mata da ranar farko data fara ganin SAFEENA a rayuwarta,ranar da har yau har kwanan gobe ba zata taba gogewa daga cikin kundin rayuwarta ba......ba kuma zata taba gogewa daga jerin sahun ranakun qaddararta ba.

Idanunta ta lumshe tana controlling emotions dinta.

"Ya akayi biftu?" Ta kirata da wani nau'un tausasawa cikin muryarta,tana duban fuskarta da tayi fayau tadan fada kadan,saidai hakan kuma sai ya zame mata kaman ado ya qawata shape din fuskarta lips dinta da hancinta gaba daya.

"Zan biki.....zanje na roqu sultane da kaina......" Ta fada da salon miskilancin nan nata da yau ya nuna muraran.

"Me yasa?,baki yarda da zan iya samun nasara a kanshi ba da kaina?" Kai ta girgizawa mammina,tana zama a sanyaye gefan sofa bed.

"Bana tunanin a duniya akwai wata halitta mafi soyuwa a ran sultane.....halitta mafi daraja,halittar da tafi qarfin yayi mata kalan kowacce alfarma kamar ni,idan zaiyimin zai iya yiwa kowa......idan bazaiyimin ba bazai iya yiwa kowa ba.....na duba littafin da mahaifiyata ta barmin yau a karon farko,a shafin farko kadai dana duba kuma na fahimci haka". Idanu mammina ta janye daga kan akhnan,tana son tuna wanne littafi ne wannan da ita ta mance dashi?,wanne littafi ne da ita bata mallakeshi ba?,wanne littafi ne haka daya halitta mata sabon tunani cikin qaramin lokaci.

Tattara komai tayi ta hadiyeshi tana sake jinjina kai.

"Gaskiyan ki ne,mu tafi tare,yana da kyau" Ta fada tana miqawa akhnan hannu,ba tare da tayi qasa a gwiwa ba ta miqawa mammina din itama cike da fatan tabbatuwar nasara.

★Cikin shigar cikakken qasaitaccen basarake yake zaune cikin parlor din nasa,sanye da tufafin zaman gida,saidai kuma duk da sun kasance na zaman gidanne,amma na dabanne dake dauke da tambarin qasaita,tun daga yauqin da yadin yakeyi zai gaya maka tsadarsa da darajarsa.

A nutse ya dauke idonsa daga saman tanqamemiyar Tv din dake aiki,wadda yake kallon labarai daga tashar France 24 dake haska labaran duniya ya maida ga bakin qofar yana amsa sallamar nutsuwarsa da kwarjininsa yana tasowa.

Wani abu ne ya sauka zuciyar mammina,ganin yadda ya zuba musu ido a nutse yana kallonsu ita da akhnan din,yayin da kwarjininsa ya daki idanu da zuciyar akhnan din,har ya sanya ta motsa kadan tana lafewa a bayan mammina.

"Barka da warhaka bajimi namijin zaki" Ta fadi tana sauke wani sassanyan murmushi saman fuskarta.

Martanin murmushin ya maida mata,yana kuma dauke idanunsa daga kan akhnan dake takowa kaman wadda ke takawa wani abu me santsi da take tsoro kada ta zame.

"Barkanki......barka da warhaka giwar agadez" Ya amsa mata cikin ransa zuciyarsa na ayyana masa komai kafin takai ga cewa ko aiwatar da komai din. Saidai har qasan zuciyarsa yana sake jaddadawa kansa,indai abinda ya shigo da ita kenan zaya basu mamaki su dukansu.

Yadda ya maida mata kirarin ya mata dadi sosai,ya kuma sake qara mata qwarin gwiwa,sai taci gaba da takowa har zuwa daura dashi. Gefen mammina ta zauna,tana rabewa sosai a jikinta,kamar qaramin yaron dake bala'in qyuya yake kuma tsoron kada a tabashi.

"Barka da wannan lokaci toron giwa......ina fatan za'ayi mana uzuri,za kuma a bamu dama,don zamu shiga lokacinka kadan". Idanunsa ya dauke daga kan mammina din,yana sauke basaraken murmushin nan nasa dake qara masa kwarjini,ya gyara zamansa sosai cikin tattausar sofa din da aka sake shimfida wani tattausan abu a samanta saboda nuna girma da martabawa ga wanda zai zauna akai din. Qaramin numfashi ya sauke dake nuna dattijantaka.

"Bawa iyali lokaci ai abune dake da matuqar tasiri da kuma alfanu,saidai kawai ina fatan lokaci ya zamana an qarar dashi akan wani abu dake da tarin muhimmanci". Ba jiya ko yau aka raini harshe da kwanyarta ba,ba kuma jiya ko yau take zaune cikin yankin agadez ba ballantana ta gaza fahimtar harshe da kuma sigar daya watso maganganunsa akai ba. Sai ta jinjina kai,tana sake lanqwasa kanta cikin yanayin da tasan yana matuqar sassauto mata dashi a duk sanda yahau wani tudun naqi din nasa. Dukkan wani siffa da yanayi da tasan yana karya mata sultane din......dukkan wani yanayi da tasan yana mata jagoran samun nasara tattare da sultane din......gaba dayansu ta aro ta lulluba saman fuskarta .

Wani yaqi ne da bawai ya shafi akhnan bane kai tsaye......a badini ma wannan yaqin.....wannan zaman nata ne....duk wani alfanu dacewa ko kuma hasara da faduwa da za'a samu NATA NE bana AKHNAN bane,akhnan ce kawai a fuskar,amma a lullube......a bayan fuskar a bayan manufar MURADANTA ne a shimfide.
Chapter 87 · 0% Book details