← Book details Luu Luu Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 45 OF 97

Sashe 45

Luu Luu Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Kadan kadan sautin karatun hadisai da ake karantawa daga channel din saudi sunnah daga littafin sahihul bukhari ke fita daga tafkekiyar TV din dake zaune dafa'an cikin parlor din,yayin da hannunsa ke dauke da daddadan coffee din,yana kurba yana ratsawa har cikin zuciyarsa. Ya yadda shan coffee da gahwa wani rubutaccen abune cikin jikin oromia......uwa uba ma kuma cikin jinin sarauta,nanaya yakeson kira,muryarta yakeson ji,amma koda ya kalli agogo yanzun goma na dare ne cikin agadez,a jimma kuma yasan sha biyu na dare ne. Idan ya kirata zai tada ne kawai,zai kuma lalata mata tsarin baccinta,don tana kwanciya ne akan lokaci don ta samu ta riski sallar darenta ta kuma sukwane har asuba. Dole ya haqura da kiran nata ya tattara ya wuce bedroom din nasa.

A daddade yayi shafa'i da wuturi,wanda komai tsanani baya taba bari su wuceshi,ya cire kayan jikinsa ya saka pajamas,ya tsaya gaban mirror yana feshe jikinsa da night scents dinsa masu lallausan qamshi.

Yana tsaka da feshe kyakkyawar qasumbarsa idanunsa ya sauka akan envelope din. Har ya janyesu ya ajiye kwalban turaren ya juya,sai kuma ya dawo a hankali ya dauki envelope din ya budeta ya zaro farar takardar ciki.

Rose flower ne qwara daya ta biyo bayan takardar ta fado,ya bita da kallo ba tare daya tsugunna ya dauka ba,sai ya dawo da dubansa kan takardar ya farketa a nutse,

Kwantaccen rubutune cikin yaren oromo,ya soma bin rubutun da idanu yana karantawa.

_Sallama me cike da aminci da kuma fatan alkhairi,godiya a bisa amsa gayyatar abba na zuwa cin abincin dare tun a wancan lokacin,a wannan karon ni da kaina nake roqon wannan alfarmar don sada zumunci da kuma samun lada.......Menelik ce_

Sai number wayarta har guda biyu a rubuce daga qarshen takardar. Kansa ya daga a nuts,ya cukuikuye takardar yayi cilli da ita a inda baisan inane ba,ya daga qafarsa yana qarasawa bakin gadon. Hannu ya saka ya zuge net din dake kewaye da gadon,sannan a hankali ya shige ciki yana yaba tsarin da aka yiwa gadon kansa.

"Allahumma innaka kalaqta nafsi,wa'anta tawaffaha,laka mamataha wa mahyaha,in ahyaytaha fahfazha,wa in amattaha fagfir laha,allahumma inni as'alukal afwa wal'afiyah" Lafuzzansa kuma addu'arsa ta qarshe kenan a kowanne dare idan ya kwanta,yau dinma da ita ya rufe,ya lullube idanunsa yana fatan kasancewa cikin wadanda Allah zaiwa alfarmar ganin washegari.

★★★★Sau uku tana duba tickets ko zata samu jirgin da zai tashi daga Niamey zuwa agadez koda ranar laraba ne amma sam sam babu. Wani abu daya sake quntata ta,ya kuma sake sanya ranta yayi matuqar baci.

Kamar yau dai,duk data kasance litinin ce,tana cikin ranakun da takan jima a company ba tare data dawo gida ba,amma litinin din yau din ta zama ta daban. Don tun break din da ake fita da azahar ta umarci driver dinta ya maidata gida.

A kebantaccen balcony dinta ta zauna bayan ta canza kayanta,tayi zaton zata iya sake rage wasu ayyukan a system dinta amma saita kasa,ta koma laluben ticket din da zai dace da ranakunta amma ta rasa.

Tsaye kawai tayi goye da hannayenta jikin qarfen balcony din,iskar dake kadawa daga hagu zuwa dama suna wasa da gashin kanta da muddin tana gida basu fiya shiri da dan kwali ba. Dogon wando ne a jikinta sakakke,sai shirt me gajeran hannu rounded neck data fidda qirar qirjinta da kuma shafe din shafaffen cikinta da ya bawa mazaunata suma damar fidda nasu shape din.

Banda lemo ba abinda yake dirkawa cikinta,duk wani hanya da zata samu gutsiren dalilin da ya sanya sultane mata irin wannan kiran gaggawar ta kasa samun kowanne labari,koda daga gurin mammina kuwa,don hatta mammina dinma bata da labarin kiran saida akhnan din da kanta ta gaya mata.

Bacin ran taji yana neman mata yawa,don haka ta miqa hannunta ta dauki headphone dinta dake maqale ta dora saman kanta,ta kuma lalubo waqar best artists dinta cikin mawaqan dake waqa da French wato indila.....

Waqar love story ta kunna,ta qara volume din daidai yadda zai ratsata,ta maida idanunta ta lumshe. Tanason waqar sosai,batasan kuma iya adadin sau nawa ta taba saurarenta ba,har wasu baitukan sun zauna a kanta. Amma kuma duk da haka sau daya tak ta taba kallon video din waqar.......tana against duk abinda ke cikin waqar idan ka cire waqar kawai,sautin yana mata dadi sosai,ya kuma bata nutsuwa a ranta.....amma sam video din bai mata ba. Bataga wani dalili bane......bataga kuma wacce irin qaddara ce zata sakata dakon son wanda ya mutu ba.......ko rayayyen ma bata fata qaddararta ta zana mata haka. Bata hangi komai ba cikin so sai qasqantar da mutum......ta sanya duk qarfi da izzarka kayi qasa,itakam duk wani abu da zai sanya kima da martabarta da kuma izza da ikonta su tabu to babu ita a cikinsa.

Yadda ta saka volume din ya sanya sam bataji sallamar da barratu ke yi ba,har zuwa sanda waqar ta qare,ta zare headphone din a kunnenta. Haka kawai taji yana sha'awar maimaita kallon film din the umbrella of Cherbourg.

Batayi zaton ganin barratu a gurin ba,wannan ya tsoratata sosai.

"Afuwa ranki ya dade.....inata sallama amma baki jini ba" Sosai ta shaqi iska ta kuma fesar,ta lumshe idanunta ta budesu sosai a kanta.

"Shine me?.....shine zaki tsayamin a guri?.....da izinin wa?" Qasa ta sakeyi da kanta,don ta fahimci cikin kwanakin izzar tata ce ta motsa

"Tuba nake" Ta fada a sanyaye.

"Karki kuskura ki sakemin wannan haukan.....bacemin da gani kafin raina ya qarasa baci". Da hanzari barratu ta juya tana barin gurin. Ba wani baqon abu bane a wajensu,dama kura ce tayi lafiya ai......lafiyar tata kuma sanadin dauki ba dadin da suka dinga yo ne da morsa safiyya.

A duk sanda zatayi musu wani abu na rashin martabawa ko girmamawa......muddin ya fada idanu ko kunnuwan morsa safiyyan saita dakatar da akhnan din.....tun abun yana mata zafi,tana ganin yarfata take,wulaqantata take gaban bayinta kuma hadimanta,har ta fahimci morsa safiyyan ba zata fasa mata gyara ba ko a gaban waye,dole wasu abubuwan da yawa suka ragu.

Ta gama saita system din tayi playing film din kiran mammina ya shigo. Iska sosai taja,ta yiwa birra dake tsugunne tana zuba mata lemon inibi sign na ta bata wayar,ta dakatar da zuba lemon ta dauki wayar ta miqa mata da dukka hannuwanta biyu.

Sai data janye qafafunta ta maida saman kujera sannan ta daga kiran tana rungume pillow a qirjinta.
(08187255862 luu luu paying)

"Hi..." Ta furta da siririyar muryartannan maras hayaniya ko kadan.

"Sai yaushe zaki girma ne akhnan?" Mammina tayi maganar tana gyara zamanta hadi da miqa hannu ta karbi yankakken apple daga hannun yalwa dake durqushe a gabanta.

"Mammina......indai ina dake......indai kina tare dani bazan taba girma ba" Ta fada a narke tana jin kamar ta koma cikin mammina din ta sake haifarta a matsayin d'iyar cikinta ta halali. Tabbas inda haka zata iya kasancewa lallai ba shakka da tafi kowa sa'ar samun uwa.....irin uwar da zata lullubeka da soyayyar da ba zata baka daman kokawa ba ko kadan.

"Gaskiya ne biftu na.......ina fatan kina lafiya ko?,baki sanya wannan damuwar a ranki ba?". Sosai ta sake narkewa cikin pillow din kamar wata 'yar mage.....muryarta a karye tace.

" Dole na damu mammina......banason na bata da sultane......banaso nayi masa abinda ranshi bayaso". Shuru kadan mammina tayi tana jujjuya dukka maganganunta a ranta. Akwai abubuwan da ya kamata tayi magana da akhnan akai......amma ba zatace mata komai ba,zata jira har zuwa lokacin da ta yanke gaya mata.

"Bana jin akwai wani abu da zakiwa sultane da zaiyi muni har irin yadda kike zato ko zargi ba biftu.....na jima banga soyayya tsakanin uba da 'yarsa ba irin taku.....soyayyarki da sultane daban take a zuciyarsa" Sosai maganganun mammina suka bata wani irin relief data gaza samu tunda sukayi magana da sultane. Ta sauke ajiyar zuciya me nauyi,yana daya daga cikin abubuwan da suka sanya take matuqar son mammina din,take kuma ji da ita a rayuwarta sama da kowa da ya rabeta ko ya jibanceta.

Tana bata relief qwarin gwiwa da kuma tabbaci akan duk wani abu da zai tunkareta. Tana nuna dukkanin damuwarta da kulawarta akan kome da zai shafeta...... Wannan shine cikakken banbanci da tazara me nisan gaske data yiwa morsa safiyya.......kuma irin wannan tazarar ko mafiyiyarta ta yiwa morsa safiyyan a cikin rayuwarta.

"Me yake faruwa a sahel couture?" Mammina tayi furucin cikin tausa murya.

Kiran sahel couture din da tayi ya sanya akhnan bude zara zaran idanunta gaba daya da suka rusuna a dazu.

"A sahel.......bazan iya tunawa ba mammina". Wani ajiyar zuciya me nauyi mammina ta sauke da tazarar sakanni sannan tayi magana.

" Tabbacin ba cikin nutsuwarki kike ba biftu......shin kin manta muhimmancin da kamfanin yake dashi a tare dake?.....me yasa zaki bari damuwa ta shiga cikin muhimmam al'amuranki?". Numfashi ta jawo tana gyara zamanta sosai cikin sofa din. Da jiya da shekaran jiya dama yau duka dai sunan ta shiga company dinne kawai......amma ba wani aiki da tayi daya shafeshi,ba kuma wanda ta bawa daman ganinta idan ka dauke aisa da Shehinaz,suma kuma bata bari sun mata maganar komai ba.

"Mammina.......Je ne suis pas dans le ton(bana cikin yanayin)" Tayi maganar kamar qanqanuwar yarinyar data rasa mafita.

Wani murmushi ne ya subuce mata,wanda daga ita sai zuciyarta ne kawai sukasan da fitarsa.....koda yalwa dake zaune gabanta ba zatace ta ganshi ba bare akhnan da bata tare dasu.

zaki samu daman karanta wannan QASAITACCEN LABARIN ta hanyoyin siyan tikitinki kamar haka da naira (700) kacal*

*Lambar asusu:- 6019473875*
*Safiya musa abdullahi*
*Keystone bank*

*KI TURA SHAIDAR BIYA TA NAN*

09166221261
KO
08187255862

*Al'ummar qasar nijer 🇳🇪*

*2349166221261*
*Safiya musa abdullahi*
*NITA*
*CFA 500*

*SAIKU TURA SHAIDAR BIYA TA LAMBAR DAI*

09166221261

*GA WADANDA ZASU SAKA KATIN WAYA NA MTN SUMA NUMBER DUKA DAYA CE*

*MTN CREDIT 700 ZUWA GA*
09166221261

*SHAIDAR BIYA*
09166221261

*_TAFIYAR 'YAR GASKE CE........LABARIN QASAITACCIYAR MACE CE KAWAI KE IYA SIYANSA_*

*QASAITA👑*

*HUGUMANKU CE*✍🏽

💎 *L U'U L U'U*
*_(The diamond)_*💎

*H U G U M A*

PAGE 38
_________________________
*_M&A EGYPTIAN ABAYAS_*

*Assalamualaikum*

*_Ina dandazon tawagar gayyar MATA 'YAN QWALISA?_*

*_WADANDA SUKAYI AMANNA DA ADO SUNE MUTUNCIN D'IYA MACE?_*👘🥻

*Ina masu son sari ko siyan daya na Egyptian abaya masu quality su iso garesu cikin Aminci???*

*M&A EGYPTIAN ABAYA itace zabinku NA FARKO*
Chapter 45 · 0% Book details