Sashe 70
Luu Luu Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Hakeem yana daya daga cikin wadanda suka tsaya takara......a lokacin haisam ya shiga sahun alqalai na gasar. Tabbas a lokacin yaga matuqar qoqarin hakeem,ya kuma yaba sosai da irin hazaqarsa da yadda ya iya fadin kowacce amsar tambaya daga masu tambayar,duk da daga qarshe ya samu zuwa na biyu ne maimakon na daya,saidai a wajen yin jawabinsa abun ya qayatar da haisam,har ya sanyashi yadan murmusa kadan. Yadda Hakeem din ya bayyana shigarsa qasar kawai nasara ce basai an ayyanashi ba,ya kuma miqa kyautarsa da girmamawarsa dukka ga mahaifinsa,ya kuma ware guda daya yana sake karbar abun magana.
"Inaso a bani dama na miqa wannan kyautar guda daya data rage,zuwa ga wani mutum daya da daga yau nakejin ya zamemin wani abun kwaikwayo koda daga nan ba zamu sake haduwa ba SHEIKH MUHAMMAD HAISAM" Iya sunan da haisam din yayi amfani kawai dashi kenan,gudun bayyanuwar identity dinsa. Yana jin dadi idan ya shiga guri yayi mu'amalolinsa da rayuwarsa cikin privacy ba tare da an fahimci waye shi ba. A rayuwa yana jin ba kowanne lokaci bane......ba kuma a kowanne guri bane ya kamata asan wayeshi ba. Wannan kyautar ta Hakeem taxo masa a bazata,saidai abinda yayi masan bazai manta dashi ba.
Sosai Hakeem yaso karbar number haisam,saidai hadimansa basu bawa hakeem wannan damar ba,sun rabu yana yawan tuna haisam din,har yau daya ganshi cikin ba zata.
Sanda haisam ya kammala addu'o'insa ya shafa a nutse,hakeem ya sake miqa masa hannu cikin sakakkiyar fuskar nan tasa,cikin tataccen larabci ya soma magana da haisam din,don bazai iya tantance wanne yare yakeji ba,kasancewar ko a wancan lokacin da larabci sukayi dukka kwanakinsu da mu'amalolinsu.
"Naji dadin sake ganinka sheikh.......ban tsammaci ganinka a agadez qasarmu ba,da nasan kana kusa damu da na jima da nemanka" Murmushi yadan saki masa,baisan me ya hada jininsu haka da hakeem din ba.
"Nazo ne ganawa da d'iyar sultane,amma ban sani ba ko zan iya samun damar sake ganinka?" A nutse haisam ya daga kanshi.
"Indai baiyi sama da mintuna arba'in ba"
"In sha Allah zan qoqarta na kammala a qasa da hakan"
*AKHNAN*
A zaune take daga gaban dressing mirror din saman stool cikin shigar atamfa embellished holland golden sea blue da ratsin blue black. Wani irin colors ne a jikin atamfda masu wani irin daukan hankali da suka dace da kalar fatarta na cikakkiyar buzuwa. Wannan fatar dake da wani irin glowing da sparkle masu daukan hankali dake nuna zallar kulawa da hutu gami da jin dadi da cikakken sukunin rayuwa da take samu.
Wani irin dinki ne na buba akayi mata,kusan zata iya cewa karon farko da zata iya tuna ta sanya atamfa a rayuwarta,don itakam tafi ganewa ready made gown da exclusive abayas,sai designers materials da take bada umarnin zaba mata dinkuna ta hannun LAARA dake kula da closet dinta tana bincika me ya kamata a zuba mata,me kuma ya kamata a cire. Dinkuna dari uku da sittin da biyar duka shekara,domin kuwa sau daya tak take sanya kaya,bata kuma sake maimaita sakasu saidai a sakasu a kayan bayarwa. Shadda kam tana dasu,su dimma bawai sakasu takeyi ba,don kwata kwata iya adadin sanyawarta da shadda zata iya qididdige lokutan.
Ko wannan atamfar ma laara ce ta dinkota,ta kuma bawa birra ta gabatar mata da ita,tana ganin zata dace da shigar ta ta yau.
Ba wannan bane a kanta a yau,don tana kallon lamarin baqonta na yau shine zai zame mata matsalar qarshe,kuma namiji na qarshe da zata sake bari ya samu daman ganin xagayen fuskarta da furucin bakinta da tsadarsa yafi qarfin kowanne namiji ya jishi.
Dinkin ya zauna mata a jiki sosai,ya kuma sake fidda sigar kyanta,qirar jikinta da kuma qara mata wani irin zaunennan kwarjini. Shehnaz na kallonta tana sake gasgata da gaske suturar bahaushe na daya daga cikin suturu da tufafin dake qarawa mutum kyau da kuma kwarjini.
Birra ke taje mata doguwar sumarta tana kuma shafeta da tsadaddun mayukan da take kula dasu,saidai duk wannan abun da yake faruwa hankalinta ba'a nan yake ba.
Idanu hankali tunaninta dama nutsuwarta gaba daya ta azasu saman ipad din data kafeta saman dressing table din da yake gabanta. Wannan wasan dai......wannan tseren na Hippodrome Niamey shi take bi da kallo cikin kowanne gilmawar second.
Har a yau har kuma a kwanan gobe bata da nutsuwa akan faruwar abun. Tunda abun ya faru har zuwa yanxun yana jin sunan MARASA NASARA yana bibiyarta a duk harbawar daqiqa,bata jin kuma zata samu nutsuwar har sai ranar data lalubo WAYE SHI?....Har sai ranar data san meye manufarsa?,me yasa ya zabi ya shirya wasan,ya qirqireshi,ya kuma gabatar dashi?.
Meye dalilin bata mata LAMBARTA da ita kadai keda mallakinta tsahon shekaru?,me ya yiwa thunder data kasa controlling dinsa?,har dai shine yayi controlling dokin da kaf cikin dawakanta tafi ji dashi?,dokin da suke communicating ita dashi da tsananin sabo tamkar dan adam?.
A hankali aisa ta tura qofar tana shigowa da sallama,saidai shehnaz kadai dake kwance rub da ciki saman gado ce ta amsa,don akhnan din ko motsawa batayi ba bare tayi yunqurin amsawar. Abinda ya ja hankalin aisa din,ta taka a nutse zuwa inda take,sai tayi tsaye a bayanta tana duban abinda take kalla,wanda clip din yazo daidai inda take fadowa ya kuma tallafeta da hannunsa guda daya.
Ita da aisa din lokaci guda hannuwansu yakai kan ipad din,kaman aisan tasan niyyar akhnan nayin wurgi da ipad din ta samu nasarar rigata dauketa tana kasheta ta wurgawa shehnaz ita.
Idanunta ta aza kan akhnan,duk wani mode nata yana nuna fushi da bacin rai,wanda aisa din takejin sam baima dace ta doshi baqonta a haka ba. Muddin haka zata kasance komai zai iya faruwa.....kunyar da dukka aka tattaru ana fatan kada yau a jita zai wahala ba'a shata ba.
"Meye amfanin kallon abinda ya riga ya faru......banda yiwa kai tanadin bacin rai?" Aisa ta furta tana duban akhnan da fuskarta tayi wani irin kyau tsakanin surfanin dake wuyan atamfar bayan gama daure mata gashin da birra tayi.
Hannu ta sanya tana ture dankwalin da birra ta aza mata a kai da nufin daura mata,ta dubi aisa din tana juyo da kujerar gaba daya tana fuskantarta.
"Kina zaton wannan tarihin zai tafi ne a banza?......kina tsammanin xan qyaleshi ne?,yayimin abinda,ya kuma bace ba tare da yabar wani alama ko guda da zata bayyana wayeshi din ba......kina zaton duka hakan ya faru ne bada wani shiri ko manufa ba?......na rantse saina laluboshi a duk inda ya shiga......na kuma rantse sai na sanyashi ya kwashi kashinsa a hannu......diyar SULTANE MUHAMMAD HAMMUD NAKE FA". Idanu aisa ta janye a hankali tana sauke ajiyar zuciya. A yau ne ta sake yadda da akhnan din baudadden halinta na halitta ne......kafiyarta kuma a jininta take,bata tunanin akwai wani yanayi ko wani dan adam da zai iya canzata
"Est-ce que c'est la seule chose qui vous dérange?(wannan ce kadai damuwarki?" Ta tambayeta tana riqe da qugunta tana dubanta.
Sai data daga fararen idanunta masu surkin blue ta watsawa aisa,sannan a nutse itama tace
"Est-ce qu'il y a autre chose?(akwai wani abunne daban?)" Idanu aisa ta bita dashi,ta fuskanci da gaske idan ta biye mata zasuyi rigima ne,sai taja tsaki kawai tana matsawa inda shehnaz ke kwance.
Harara ta watsawa shehnaz din tana dubanta.
"Ba wani sauran abinda zakiyi ne?" Ta furta cikin gatse,don ta fuskanci wani lokaci plan din akhnan yana zuwa daidai dana shehnaz.
"Ques veux-tu que je fasse?(me kikeso nayi?)" Ta fada cikin rashin ko in kula. Ta sani,ita ko aisa basu isa canza ra'ayin akhnan ba.
Mayafinta ta zara wanda birra ta ajiyeshi daga gefe da nufin idan ta kammala shiryata ta bata tayi amfani dashi. Lullubawa tayi kawai saman kanta ba tare data damu da d'aura dankwali ba ta soma takawa tana fita a dakin,sai su dukka suka bita da kallo cike da mamaki.
*FALAAK*
Wata baquwar dabi'a ce a tare da ita,damuwa da duba kowanne lungu da saqo na fuskarta tanason tantancewa ko akwai wani abu daban da bai kamata ta fita dashi ba?. Ko akwai wani abu da baiyi a fuska ko kuma jikinta ba?.
Ita kanta batasan hakan yana faruwa da ita ba,har sai da taji dariyar badee'a.
Cak ta tsaya daga goga lipstick din da takeyi tana duban badi'a din.
"Lafiya?" Ta fadi a mamakance. Kai badee'a ta girgiza tana dubanta.
"Bansanki da irin wadannan sanaben ba uwar dakina......yau din da kikeyi sai abun yake bani dariya da mamaki". A hankali ta maida dubanta ga lipstick din hannunta,wanda ba wani color gareshi ba,sai ta maidashi saman madubin a hankali tana ajiyeshi.
"Dama kin qarasa,yayi miki kyau sosai" Badee'a ta fada tana duban ta. Kai falaak ta girgiza tana daukar wayarta dake gefe.
"Muje badee'a" Ta fadi tana jin wani fargaba da bugun zuciya yana qaruwar mata. Tun daga safiyar yau take lissafin adadin awannin da ya rage su shiga karatu,a duk sanda daqiqa daya ta ragu kuma sai ta samu kanta cikin wani matsanancin harbawar gudun zuciya.
Sai takejin kamar me tsoron haduwa dashi,tsoron kuma daya cakuda da zumudin zuwan awannin haduwar. Ta sani,zallar kwarjininsa ne yake dukan idanu da zuciyarta,wanda batasan dalilin hakan ba,kwarjinin da har a jiya data kwanta tana wassafashi ne cikin idanunta.
Tayi karatun addini daidai gwargwado hannun malamai kala kala a france sanda take hannun hairaan. Kusan kuma dukkaninsu babu dan africa,amma yanayin da takeji a yanxu bata taba jin makamancinsa ba.
Bata samu morsa ba,an shaida mata tana ganawa da baqi,wannan ya sanya kai tsaye suka wuce ita da badee'a wadda ke dauke da wasu daga cikin litattafan da yace zasu sauya,duk da ba duka aka samo ba. Wasu babu su a kasuwa,har sawa morsa tayi aje a duba amma an tabbatar mata babu su,sai nan gaba za'a shigo dasu daga misra.
A nutse yake takowa cikin gurin bayan Maher ya juya tun daga shingen qarshe. Wanda hakan umarni ne daga haisam din,bawai don ba za'a bar maher din ya shigo ba.