Sashe 93
Luu Luu Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Babu wata halitta da zata wanzu cikin masarautar,ta yaro ko babba.....mace ko namiji saida saninsa,saida cikakken sani daga gareshi,sanin kuwa daya hada da inda ka fito,me zaka shigo yi?,adadin ikon da zaka iya samu cikin gidan,wa'adin zamanka dama fitarka dukka suna tafin hannunsa qarqashin tsananin qwarewarsa wajen aiwatar da dukkan wannan abun cikin hikimar da ba damqa masa alhakin hakan akayi ba,shi ya baiwa kansa wannan girman,shi ya baiwa kansa wannan matsayin.
To amma dukka awannin daya shafe yana bincike a kansa abu guda ya samu. Malami ne da gaske,kuma dan cirani,maras wani gata ko galihu da yawan neman ilimi ya fado dashi hannun oustaz Ousmane,sukayi musanye a sanda oustaz din ya samu daman fita qaro karatu. Bashi da cikakken muhallin zama,don babu wanda yasan taqamaimen inda yake zaune,wannan ya sanya sultane bashi gidan da yake maqotaka dana gimbiya akhnan. Wadannan sune bayanan da tamim ya yiwa mammina.
Ido ta zuba masa tana jin tantama akan bayanansa. Duk kuwa da cewa ta sani,batun qwarewarsa gurin iya bincike da kuma bin diddiqi akan komai bayyananne ne,yana daya daga cikin dabi'unsa da halayensa da take matuqar so take kuma alfahari a tattare dashi,to amma wannan binciken haka kawai takejin bai kwanta mata ba. Kanta ta dauke,tayi kuma taku uku zuwa gaba tana girgiza kanta a nutse
"Bazan qaryata abinda ka binciko ba.....saidai wannan binciken ba shine ainihin abinda yake boye ba,inaji a jikina koda ba wani boyayyen al'amari a tattare dashi,to ba shakka akwai wani abu da zai iya faruwa a nan gaba,don haka inaso ka sanya ido a kanshi da dukka wani motsinsa,banaso ka bawa kowa wannan aikin,kai nakeso ka gudanar dashi da kanka,har zuwa lokacin da zan gamsu da cewa ba komai a tare dashi din........." Tayi maganan tana takawa zuwa ga hanyar da zata sadata da ciki,sai kuma ta tsaya cak.
"Akwai alamun wani motsi daga K'ASATA?" Kai ya jijjiga.
"Babu,ba wani motsi,komai ya tsaya cak,komai kuma ya lafa,al'amura suna ci gaba da gudana,a hankali sunansa da faruwar al'amarin yana bin awanni da shekaru yana salwancewa". Tsayawa tayi kaman me nazarin wani abu,murmushi kuma yana qwacewa daga kan fuskarta.
zaki samu daman karanta wannan QASAITACCEN LABARIN ta hanyoyin siyan tikitinki kamar haka da naira (700) kacal*
*Lambar asusu:- 6019473875*
*Safiya musa abdullahi*
*Keystone bank*
*KI TURA SHAIDAR BIYA TA NAN*
09166221261
KO
08187255862
*Al'ummar qasar nijer 🇳🇪*
*2349166221261*
*Safiya musa abdullahi*
*NITA*
*CFA 500*
*SAIKU TURA SHAIDAR BIYA TA LAMBAR DAI*
09166221261
*GA WADANDA ZASU SAKA KATIN WAYA NA MTN SUMA NUMBER DUKA DAYA CE*
*MTN CREDIT 700 ZUWA GA*
09166221261
*SHAIDAR BIYA*
09166221261
*_TAFIYAR 'YAR GASKE CE........LABARIN QASAITACCIYAR MACE CE KAWAI KE IYA SIYANSA_*
*QASAITA👑*
*HUGUMANKU CE*✍🏽
💎 *L U'U L U'U*
*_(The diamond)_*💎
*H U G U M A*
PAGE 80
___________________________
*_Domin qulla huldar kasuwanci damu,HUGUMA CLOSET.......,siya ko siyowa wani,reposting ko sari akan farashi me rahusa da babu irinsa,maza yi joining group namu don samun ingantattun kayan da babu ha'inci a ciki da izinin Allah_*
https://chat.whatsapp.com/FrqgC0YmUWP4FPmUzYuLJX
____________________________
"Inajin kamar lokutan sa'ata suna dab da haduwa guri daya......anya ba zamu gwada wani abu ba?,.....idan muka dace sai ya zame mana hanya mafi sauqin da bamu taba zata ba,hanya mafi sauqin da muka jima muna jiranta shekara da shekaru" Zamewa kadan tamim yayi daga saman qafafunsa,yana jin zuwa yanzun ya kamata shima ya soma motsa nasa qudurin,quduri guda daya da yakejin dukkan wahala da bautar nan ta shekara da shekaru shine kadai zai wanke masa.
"Ba laifi bane.....kuma a shirye nake na tsara hakan,a shirye kuma nake na tsara yadda komai kasance.......amma ina da wani shakku da kokwanto kadan" Ya fada fuskarsa da muryarsa suna suna muhimmancin abinda zai fada din.
"Kamar?" Mammina ta tambayeshi tana riqe da labule.
"Bazai zama matsala ko cikas ba?,bayan cikar ko kusa da cikar muradanmu idan na buqaci tukuicin farko daga gareki?". Ido ta zuba masa tana jin kamar ya raina girman izza da isarta,kamar ya raina dimbin arziqin da ta mallaka ita daya ranta.
"Tamim........kana manta wace GIWA?,kana manta wace izzatu?,sunan GIWA kana taqaitashi ne kan ma'ana guda daya tal?". Murmushi yadan saki yana kada kai.
"Wane mutum wane aikinsa.......ba daya da nake musantawa a ciki......girman tukuicin da zan buqata ne nake ganin kamar........"
".....kamar me?" Ta fadi cikin fara jin haushin maganganunsa. Qasa yayi da kansa cikin qasqantar da murya.
"Allah ya huci zuciyarki ya baki yawan rai......tukuicin DAN MUTUM nakeso......shi zan buqata giwa,ban sani ba,a sanda na buqaci hakan zaki iya daukoshi daga hannu daga kuma mallakin ko waye ki maidashi mallakina?". Murmushi ya sake subuce mata,tana jin babu wani abu me sauqi sama da haka. Sanda yake gaya mata sai lokaci yayi.......sai lokaci yayi zai gaya mata tukuicin da yake buqata,wani lokaci takan jima zaune tana hasashe da tunanin me dame tamim zai iya cewa yanaso a matsayin sakamakon bauta na shekara da shekaru?.....amma a yanzun ta samu wani irin tarin sassauci data jima bata jishi ba.
"Qarqashin mallakata akwai tarin jama'a......akwai tarin bayi nau'i nau'i,ka zabi dukka adadin dakaga dama,adadin da yayi maka.......zaka zama mutum mafi rabauta a duniya daga randa BURIKA BIYU na zaituna suka gama cika cif cif qarqashin jagorancinka,na maka alqawari zan baka duk abinda kake buqata".
★***Da kallo birra ke binsa sanda taga fitowarsa daga shiyyar mammina. Tadan sake kallon sararin sama tana qiyasce nisan dare a wannan lokacin. Ko ba'a gaya mata ba tasan cewa dare ya soma shiga sosai,kuma doka ce a dukka fadin gidan na haramtawa kowanne jinsi shiga sashen da bana jinsinsa ba,daga sanda akayi kiran sallar magariba. Abu mafi ban mamaki ya fito ne daga sassan da sukafi kowanne tsaro,sukafi kowanne dokoki tsaurara,kuma a cikin dare irin wannan?.
"Gimbiya akhnan ce take kiranka" Ta fada tana rusunar da kanta ganin irin kallon da yake binta dashi,fuskar nan mai cike da qasumba a dinke tsaf.
Sosai yaji batun yazo masa banbarakwai,saboda wannan shine karo na farko da ya soma jin hakan,sai kawai ya gyara damarar jikinsa da baya rabo da ita kulli yaumin yace.
"Muje" Tayi gaba yana biye da ita a baya.
Sanda suka isa a farfajiya ta barshi,ya soma bin gurin da kallo,don kuwa wannan shine karon farko da qafafunsa suka fara taka sassanta. Sassanta yafi kowanne sashe tsananin doka tsaro da kuma qa'idojin da SULTANE kadai aka yarjewa aga qafarsa a cikin gurin. Da idanunsa yake bin ginin da kallo da mamakin yadda aka tsarashi cike da tsaro da kuma ado da qawa.
Zubewa tayi qasa tana shaida mata isowar tamim din,sai ta miqe tana gyara lullubin after dress dinta data rufe ko ina a jikinta tana fadin.
"Muje".
Da hanzari ya sauke kanshi daga nazarin da yakeyi yana maidawa inda ya jiyo takunsu,da sauri cikin tsananin girmamawa ya sauke kanshi,sannan ya karya gwiwarsa guda daya ya kaita qasa yayin daya cake tafin qafarsa a qasa da dayar qafar yana yin qasa da kanshi.
Wani girma takeji yana ratsata a duk sanda yayi hakan a gareta. Yana cikin mutane da suke lissafinta na gaba gaba da sukafi kowa iyawa da sanin yadda zasu girmamata.
"Tashi ka zauna" Tace masa bayan ta zauna,saiya tashi din amma ya tsugunna ne saman qafafuwansa.
"Muhimmin aiki nake tafe dashi......kuma nakeso idan ka fara shi ba dawowa saida cikakken amsa da bayanai masu gamsarwa".
"Umarninki kawai nake jira" Ya fadi kai tsaye,yana jin qarin samun wani matsayi daban yana tunkaroshi,yana jin cewa shi din me nasara ne da har gimbiya akhnan zata nnemeshi cikin dare irin wannan da buqatunta.
"Basai na tsaya tambaya ko tantama ba......tabbas kana da labarin tseren dokina na qarshe a hippodrome da wani baqon mutum dan wata qasa?". Kansa ya gyada a hankali yana sadda kanshi qasa,sanin halaye da dabi'unta,da kuma dokar tsanar kallo da tayi a rayuwarta.
Numfasawa tayi kadan ta kuma gyara zamanta,tana jin kamar komai zaizo da sauqi.
"Ba wani abu me yawa kome girma nake buqata ba illa sanin wayeshi?,inason samu cikakken sunanshi da kuma qasar daya fito,kamanninsa da wani abu nashi daban da zai kaini zuwa ga inda yake.......sauran ni zan qarasa aikina da kaina". Murmushi ya saki kadan.
"Aiki ne me sauqi qwarai wannan.......ki bani kwanaki bakwai kacal idan basuyi miki yawa ba" Kai ta jinjina.
"Sun isheka?"
"Tabbas" Ya fadi yana me bata tabbaci. Kai ta jinjina.
"Yayi.......saidai akwai sharuda guda biyu cikin aikina,wanda idan ka kiyayesu nan gaba zaka iya samun damar da tafi wannan daga gurina". Wani irin dadi yaji yana ratsashi,wannan aikin aikine da zaiyishi koda babu ko sisi da zai rabauta dashi,aikine da yakejin zai iya kiyaye dukkan sharuddansa komai tsaurinsu.....wannan MATSAYIN da kusancin kawai yake buqata.
"Na farko,banason kowa yasan da aikin nan.....na biyu kuma,inason ka gabatarmin da kowacce hujja shaida da kuma sakamakon bincike,ni zan fara dubawa da kaina.....ko idanunka ban lamunce suga komai ba" Ta fadi da dukkan yanayin da yake nuna da gaske take. Ta dauki wannan hukuncin ne saboda tanason zama ta farko da zataga waye din,idan har ya zamana wani wulaqantacce ne da darajarsa batakai tata ba,zai zamana babbana abun kunya wani ya san ta tsaya bata lokutanta masu tsada wajen yin tsere da wulaqantaccen mutum irinsa. Idan ita tafara gani,zatasan yadda zata lulluba komai ta kuma dauki matakin da zai gamsar da ita a sirrance.
"An gama Allah ya qara miki daukaka" Ya fada yana dunqule hannunsa a qirji alamun dake nuna girmamawa da sallamawa.
"Jeka.......zan sa ayi maka aike a safiyar gobe".
"Godiya nake bisa wannan tarin girmamawa da karramawa da kikayimin na sakani cikin kebantattun al'amuranki" Ya fadi yana miqewa ya juya ya fice.
Ajiyar zuciya ta sauke,tana wassafa irin yadda zata ladabtar da kuma hukunta mutumin. Ita daya tasan a ukun da zata sakashi,wanda saiya qare rayuwarsa yana dana sanin jaa da ita.
★★★Akwai wani sassanyan yanayi a tattare da ita wanda hatta da badee'a ta karanci hakan.
Tana da hira wasu lokutan,duk da hirarta bata zama me tsaho da yawa,amma bata fiya zaman shuru ba musamman ga mutanen da sabo kadan ya shiga tsakaninsu irin ta da suke tare kusan mafi yawan awannin wuninta.
Numfashi taja kadan,tana rufe shafin alqur'aninta. Ta juya agogon hannunta ta kalla sannan ta dora idanunta da sukayi wani irin laushi akan badee'a
"Anya yau ma zaizo?". Dubanta badee'a tayi,yadda damuwa ke son yin tasiri cikin idanunta.