← Book details Luu Luu Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 14 OF 97

Sashe 14

Luu Luu Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Me kika ce?" Ta tambayeta tana ritsata da idanu,saita sake yin qasa da kanta.

"Kiyi haquri ranki shi dade" Akwai bacin rai sosai cikin idanunta take duban buhaina dasu. Sadakar juma'ar ta zame mata tamkar wani bangare na ayyukanta na duk sati. Sau tari ita da kanta take shirya kayan abincin cin wani kyakkyawan wando babba sosai na kaba,a fita dashi gidajen da basu da hali a ajiye maka a qofar gidanka ba tare da kasan daga ina yake ba.

Wani alqawari ne data daukarwa kanta muddin numfashinta.......wani sashe ne na abinda yake faranta mata rai a duk sanda tayi hakan,ba tare kuma da tasan abinda yake sakata wannan farincikin da nishadin ba.

"Kinsan muhimmancin aikinki kuwa?.....menene hadin kiran sultane da wannan aikin buhaina!?" Ta jefa tambayar tana dan buga cokalin hannunta kadan.

"Ki gafarceni uwar gijiyata.........nayi kuskure......"

"Ba kuskure bane wannan ganganci ne!" Ta sake fada cikin fadan da yake damfare da yadda zuciyarta ke a bace tun jiya.

"Ammm.......buhaina......a samu a maida madadin ta juma'ar da bayi ba wannan lahadin.......nan gaba kuma kome akeyi ko meye ya faru ki dinga qoqarin ganin anyin.......idan ya kama da akwai qaqqarfan dalilin da zai hana ayin saiki sanar tunda wuri". Aisa ta karbe maganar don bataso tayi tsaho,ta fuskanci idan tayi tsahon kowa ma sai ranshi ya baci.

Dogon tsaki taja ta miqe tana daukan tissue,ta tura kujerar baya tana fita daga tsakanin table din.

Jakarta birra ta dauka tabi bayanta,yayin da aisa ta girgiza kai kawai taja wata kujerar ta zauna tana cewa buhaina ta hada mata abincin dan kadan,don tasan zata samu lokacin da zata gama cin abincin harta rusketa,don tasan tabbas ne saita shiga ta yiwa sultane da mammina sallama.

Kai tsaye sultane ta fara gani,yayi mata addu'o'i sosai sannan ya rufe da cewa.

"Ina buqatar zuri'a me yawa wadda bayanta bazai yanke ba.......zuri'arta ba zata samu dogon zango da kuma dogon tarihi ba saita tsatsonki da tsatson suhaana,kece babba,kece bake da fata a kanki sama da suhaana........kece burina yafi zurfi a kanki biftu,kiyi qoqarin zama magajiyata ta wannan fannin ma......kamar yadda kika sharen hawayen rashin d'a namiji ta fannoni da bangarori da dama.....nagartaccen suruki akhnan.......nagartaccen lu'u lu'u nake buqata.......wanda zai maye min gurbin da na rasa.......kafin ki sake shiga ko ina......ki shiga wajen mommanki kiyi mata sallama". Ya qare maganar yana tuna yadda safiyya ta kasa zama,ta ratso tsananin duhun daren jiya ta iskoshi a sassansa. Sunyi maganganun da suka tsaye masa a rai,maganganun da suketa yaqi tsakanin zuciya da kwanyarsa,suna son zaqulo masa ainihin inda matsalar da damuwar suke......sunason bashi tabbacin akwai kuskure ko babu?.

Sosai maganganun sultane suke mata yawo saman kanta lokacin da take takawa zuwa sassanin morsa safiyya.

A nutse take kurbar dafaffiyar madarar dake cike da wani mug dake iya baka damar ganin abinda yake cikinsa. Cikin wannan tsaren gidan da kamalarta ta qara masa kaifi.

Daga qasan qafafunta daya daga cikin hadimanta ne ke zaune sanye da kayan aikinsu,daga gefanta wasu irin plastic robber ne guda biyu. Dayan wani ruwa ne da momma din ta cire qafafunta daga ciki me launin kore,dayan kuma wasu ganyayyaki ne shimfide a ciki masu dumi sosai,dumin da ko daga gefe kake kana iya fahimtar hakan,wani qamshi na daban suka hadu suka bayar,ruwan da kuma ganyayyakin.

Gangar jikinta ce kawai zaune a wajen,amma dukka wani hakali nata da nutsuwarta basa wajen. Tun daga daren jiya sanda take fitowa daga sassan sultane bayan ta tabbatar sunyi magana ta fahimta tsakaninta dashi,take takowa ita daya zuwa sirrintacciyar hanyar da zata dawo da ita zuwa sassanta. Gilmawar wani abu ta gani wanda inuwarsa ta gifta ta gabanta sakamakon hasken qawayayen dake a bayanta suka cillo inuwar zuwa gabanta.

"Hasbunallahu wa ni'imal wakil" Ta furta tana qoqarin danne tsoron daya taso mata. Tana da halittar tsoro a cikin zuciyarta kamar kowacce halitta ta dan adam,saidai kuma macace me wani irin dakiyar zuciya jarumta da kuma juriya ainun,wannan ya bata qarfin gwiwar juyawa don ganin meye haka me fadi ya gifta ta bayanta nesa kadan da ita.

Taku uku tayi baya tana komawa zuwa inda tafi tsammanin ta nan abun ya wuce. Sannu a hankali ta hangi rigar dake bayyana mata daya daga cikin hadiman dake aiki sassan mammina ne. Koda ta sake matsawa sosai sai idanunta suka soma dauko mata fuskar tamim wanda yake sake turata cikin hular qarfen dake saman kansa.

Cak ta tsaya tana dubansa daga tsakanin wasu shukoki da suka kerewa tsahonta sanda yake yunqurin fita daga hanyar zuwa qofar da zata sadashi da ainihin harabar sassan nasu daga nan kuma ya bulla zuwa makekiyar farfajiyar jakadunsu dama jakadun sarki.

Cak ya tsaya ya kuma waiwaya bayansa,yayi 'yan dube dubensa na wasu sakanni sannan ya sanya kansa da sassarfa yana ficewa.

Kimanin sakanni talatin cif tayi a wajen kafin ta motsa ta koma zuwa hanyar da zata sadata da ainihin sassanta.

"Me tamim yakeyi a shingen da ba wanda yake da hurumin shiga idan ba JININ sultane ba?......shiyyar data zama kebantacciya kuma mallakar iyalin sarki?.

Gabanta taji ya fadi sanda wani tunani ya yanko mata. Hankalinta taji yana neman tashi saboda tuna yadda wancan watan akayi shari'a tsakanin bayin dake aiki a sassan mammina da kuma bayi maza dake wata shiyya daban ta gidan. An samu case na alfasha tsanin baiwar mammina guda daya.....wanda har takai ga samun ciki a tsakaninsu.

Ba sultane kawai ba da baya qasar a sannan.......hatta ita hankalinta yayi mummunar tashin da sai datakai ta tara dukkan hadimanta tayi kafa musu mafi girman gargadin cewa.

"Duk wadda ke da buqatar aure a cikin ku ta sanarmin,ko a ina ta samu miji kuwa ni zan aurar da ita kamar yadda ake aurar da kowacce 'yantacciyar diya.........bazan daga qafa ba bazan kuma lamunci aikin alfasha a shiyyata ba......ina tsoron zunubin da zai jawo qin amsa addu'o'ina........duk wadda na sameta da wani abu makamancin haka.......bazanyi qasa a gwiwa ba wajen miqata kotun musulunci ta cikin gidannan ta yanke mata hukuncin da shari'a ta tana ba". Maganarta tayi amfani,don cikin watan mutum uku ta aurar,ta kuma basu daman ci gaba da aiki da ita ko tafiya?,dukkansu suka zabi suci gaba da aiki da ita,don babu abinda zaka rasa muddin kana tare da ita.

Can wani saqo dake kebance a zuciyarta kuma sai taji ta kasa gasgata haka......haka kawai taji ta gaza gamsuwa da wannan tunanin.......a jikinta takejin wani abu na daban,abinda ta kasa gane ko hasaso meye.......wannan tuna in kuma shine yaqi barinta yake bibiyarta har a wannan safiyar.

Idanunta zube saman fuskar akhnan dake shigowa da takun da sarauta da izza suka mallaka mata shi. Sanye take cikin wata irin doguwar riga da bazaka kirata baya kai tsaye ba. Don 'yar cikin tana da dogon hannu da wani irin ado daga hannun zuwa qasan rigar daga sama,yayi data saman ta kasance kamar alkyabba maras nauyi,budaddiya sosai da,wadda hannuwanta suka kasance kamar na top riga,aka cika dukka jikin rigar da wani irin ado,adon da idan ka baza fadinta sosai daga baya zai fi maka kama da adon zanen jikin dawisu,hatta da igiyar da akayi ta musamman saboda daure gaban rigar cike yake da ado da wasu irin stones masu daraja......sai wani qaramin hijab na musamman da rigar ke zuwa dashi,wanda itakacinsa wuya,wannan shi ya qarasa suturce jikinta gaba daya sai kewayayyar fuskarta data bayyana ta tsakiyar qaramin hijab din.

Idan akwai wani abu guda daya dake burge morsa safiyya akan akhnan shine SHIGAR SUTURCE jiki. Ta sani,tana suturce jikinta bawai don tasan darajar alfanu da girman abinda takeyi ba,aah.......tana suturceshi ne saboda girman kai taqama da alfahari da takeyi da jikin nata.

Tana kishi.......tana kuma alfahari da kanta...... Tana martaba jikinta tare da ganin cewa.....jikinta wata kadarace me tsada da tafi qarfin kowanne kare da doki ya samu damar ganin ta a raha haka,wannan ya sanya mafi yawan suturuntu irin rigunan ne da musamman wani kebantaccen kamfani dan qasar dubai ke fidda mata su iri daban daban,sai kuma lafiyayyu lafayu masu asalin tsada da daraja.

Tanason qananun kaya sosai......bata damu kuma da hijab ba bare dan kwali,amma dukka irin wannan shigar cikin gida takeyi. Sam momma ma bata tunanin akhnan din ta mallaki hijab,bare dankwali da yake zama aikin banza cikin dukkan kayanta.

Duk da batasan ma'anar suturta jiki ba cikin addininta........amma ta zame mata dabi'a saboda ALFAHARINTA DA IZZARTA.......wannan din yana yiwa momma dadi......tasan kuma wani abune daga Allah wanda yake iya kimsawa bawa kyakkyawar dabi'a koda shi bawan bai kalleta a mizanin komai ba.

"Barka da safiya" Akhnan din ta fada tana zama saman kilishin dake gaban momma din gami da dauke idanunta daga kan robobin da qafar momma din ke ciki.

Wani abune da tun batasan ma'anarsa da muhimmancinsa ba taga momma din tanayi,har kawo yau data mallaki hankalin kanta. Ita din wata irin mutum ce da bata bari kanta yayi murfi sam......mutum ce me yawan bincike game da duk abinda zata gani wanda batasan mene shi ba. Bata yarda da jahilci ba......bata kuma yarda da rashin sani ba,bata laminci kuma kowa ya kalleta a matsayin wadda bata sani ba.......saidai kash......tana tare da wani RASHIN SANI mafi muni da batasan dashi ba.

"Barka da asuba biftu,kin tashi lafiya?" Momma ta amsa da wani sassauqar murya. Baki akhnan ta tabe qasan ranta,tana dauko hoton abinda ya faru jiya tana kawoshi kusa da ranta.

Kamar ba itace matar nan ba data gaggaya mata maganganu mafiya muni cikin rayuwarta ba a jiyan.....tammar ba ita bace a jiyan takeyi kaman zata qonata da ruwan zafi ba......kamar ba itace ke jifanta da mummunar fata ba?,waisai gashi a safiyar yau ta juye kamar wata hawainiya?.

Sam bata jin zata ga hasken matar nan a rayuwarta kaf........kalamanta na jiya sun sake nesanta ruhinta da fatan wataqila watarana zasu fahimci inda kowannensu ya dosa.

"Na tashi lafiya......zan wuce Niamey......saina dawo" Ta fadi duka a tare da sauran maganarta tana miqewa.

*Zaki samu daman karanta wannan QASAITACCEN LABARIN ta hanyoyin siyan tikitinki kamar haka da naira (700) kacal*

*Lambar asusu:- 6019473875*
*Safiya musa abdullahi*
*Keystone bank*

*KI TURA SHAIDAR BIYA TA NAN*

09166221261
KO
08187255862

*Al'ummar qasar nijer 🇳🇪*

*2349166221261*
*Safiya musa abdullahi*
*NITA*
*CFA 500*

*SAIKU TURA SHAIDAR BIYA TA LAMBAR DAI*

09166221261

*GA WADANDA ZASU SAKA KATIN WAYA NA MTN SUMA NUMBER DUKA DAYA CE*

*MTN CREDIT 700 ZUWA GA*
09166221261
Chapter 14 · 0% Book details