← Book details Luu Luu Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 6 OF 97

Sashe 6

Luu Luu Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

FREE PAGE O4
______________________________
https://wa.link/l1gcz8
ASSALAMU ALAIKUM
Mutanen Zuzeam ventures
Ga wani sabon promo na bullo muku dashi don farin cikinku dajin dadinku
Kunsan promo na na dabanne namu ba irin nasu bane hajiya ta mai kike jira da 7500 dinki ki kwashi kayan 19k
1. Rabin kazar mallaka 4500
2. ⁠married femfresh wash 2k
3. ⁠garuka 7in1 masu wata 7 ajiki 2k
4. ⁠Gumbarmadaradanonon rakumi 1500
5. ⁠Tsimin mallaka 2500
6. ⁠maganin infection 1500
7. ⁠matsin mallaka ba aba mai kishiya 5k
Duka kayan 19k za a baki akan 7500
Kuma mutun 20 na farko sunada kyautar kayan 4k
Matsin maida tsohuwa yarinya 1k
Gumbar emergency 1k
Turaren mallaka 2k
Allah yaba mai rabo sa a Zuzeam ventures takuce 🥰👍🏼
Zuzeam ventures takawo maku ingantattun magunguna masu inganci cikin Aminci Muna da kaya kamar haka
Mallaka Maganin sanyi Maganin cire tumbiMaganin farin jini
Maganin matsiMaganin sa ni’ima da dandano Dulka Amare Set na gyran jiki
Set na amarya
Tabaje tsumin Gomba
Xuma kiba ta hips and Brest
Magungunan gyran Brest
Magungunan Karin hips
Maganin sliming
Muna da kaya masu inganci cikin sauki da rahusa
Ina wadda keneman mallaka sahihiya quaranty wlh hajiya kixo ga zuzeam ventures xakiji ddin mallaka duk fadin ran ogah duk fadansa wlh sai yyi sanyi https://wa.link/l1gcz8 gyran jiki kikeso gyran fata gyran Brest magungunan sa kiba da hips
DOMIN samunta Kai tsaye ta WhatsApp 08144015291 muna tura kayanmu ko ina cikin iKon allah 🥰👌🏻
😁😁😁 https://wa.link/l1gcz8 kedai dannan link dinnan don samun naki ki maza kiyi bucking koda kudinki saida Rabonki
________________________________

"In sha Allah,na miki alqawarin komai zaizo kamar a gabanki suka gana" Ta fada kanta a qasa. Kai momma ta jinjina tana jin yarda da armelle,ta tabbatar ba za'a samu akasi ba......tayi imanin komai zai tafi daidai indai armelle ce har fiye da yadda takeso. Tsam armelle ta miqe sannan ta rusunar da kanta.

"Na barki lafiya" Ta juya a nutse tana takawa ta fita a parlor din.

Sosai momma ta sake zuqar wani numfashin da ya cakuda da nannauyar ajiyar zuciya. Akhnan itace BARAZANARTA ta farko a rayuwa duk da ta kasance wani ruhi me tsananin daraja a wajenta fiye da diyoyin da suka fito a cikin ta. Akhnan itace barazanarta ta wani bangaren kuma itace kwanciyar hankalinta......akhnan itace matsalarta ta wata fuskar kuma nutsuwarta da kwanciyar hankalinta........shin ta yaya zata maida komai ya zamana akan saiti?,tambayar da ita kanta bata san amsarta ba.

Daya daga cikin kebantattun lambunan gidanne wanda ya zama na musamman koda a cikin masarautar. Waje ne da yake da sassa biyu masu matuqar dadin zama saboda shuke shuke na musamnan dake gurin. Kusan kowanne tsiro da aka dasashi a wajen ya fito daidai da girmansa asalin irinsa daga qasar France da Germany aka kawoshi,wannan ne ya sanya zaka ci karo da tarin tsirrai wadanda sam sam baka sansu ba baka kuma sama dasu ba. Ya zama na musamman ne saboda irin wannan tsirran da yake qunshe dasu,sai ya sake zama na daban saboda tarin nutsuwa da rashin hayaniya da gurin yake dashi.

Tun gabanin ka qarasa kaiwa ga lambun zakayi amannar cewa wani isashe ne a wajen......wani basaraken ko kuma wanda sarauta ke zagayawa a duniyarsa. Tarin dogarai dake tsaitsaye a kowanne dagin qafa da zakayi da kuma saukewa,cikin shiga da suturar masarautar TAHUO. Ba wanda ke motsi a cikinsu,suna tsaye ne qyam cikin son bawa yarimansu kariya. A nutse take karantar yanayinsu da yanayin da gurin ya sauya izuwashi cikin kowanne taku nata da zatayi,ta sani masarautar TAHUO din babbar masarauta ce kaman yadda tasu take.........girma dadewa da kuma yawan al'umma,saidai batajin ta kamo tasu ta fannin IZZA da QARFIN IKON da suke dashi.

"Eh........ Lallai ne,da gaske ne abinda ake fada game da yarima altaab" Aisa dake takawa tare da akhnan ta furta qasa qasa daidai yadda sautin zai isa ga kunnen akhnan. Da gaske take,tsarin da yanayin ya burgeta,yanayin da ya sanya cikin jikinta takejin kamar akhnan tayi miji........kamar altaab din zai dace zaiyi kuma daidai da tsarin akhnan.

Baki kadan akhnan ta tabe,saidai bata ko motsa labbanta ba ballanta tace komai da aisa. Bata jinta cikin yanayin magana,koda kuwa tana da jin cewa wani abu tasan wannan banbancin dake a tsakanin tunaninta hangenta dana sauran al'umma ya zama babbar katanga kuma hijabi daga fahimtar ma'anoninta motsinta da maganganunta.

Kamar a cikin jikinsa yake jin tahowarta......kamar a cikin jikinsa yake jin alamun fuskantowarta zuwa muhallin da akayi masa mazauni,saiya daga kansa a hankali daga duban Mac book din da yakeyi,yayi kyakkyawan gani kuwa ta hanyar zube idanunsa a kanta lokacin da take takowa d'ai d'ai da qasaitaccen takunnan nata.

Wani irin abu ne me qarfin gaske ya harba daga tsakiyar qirjinsa zuwa zuciyarsa........wata mummunar faduwa gabansa yayi,sai ya lumshe idanunsa can qasan zuciyarsa yana gayawa kansa.

"Ka nutsu altaab". Tsahon second biyar sannan ya sake bude idanunsa yana maidawa kanta da wani irin qwarin gwiwar daya samu ya arota da qarfin cin tuwo.

Ba sau daya ba,ba kuma sau biyu ba yakejin labarin kwarjinin da take dashi. Sau da dama......sau tari kuma siririyar dariya yake saki,shine fa altaab........altaab nu'uman sirreen?,har akwai dama wata halittar diya mace da zatayi masa tasiri da girma?,har akwai wata qwayar halittar KWARJINI da zata sanyashi ya gaza fuskantar diya mace ko wacece ita?,komai girma da izzarta......komai qarfin ikon masarautarsu?......kai koda hurul'eeni ce.

Daga sanda girma ya ruskeshi.......shekaru suka cillashi zuwa matakin samartaka baisan adadin matan da suka soshi ba.......baisan adadin matan da yayi soyayya dasu ba.........baisan adadin matan da ya sanya kuka a kansa ba.......sai a yanzun 'yar sarkin AGADEZ zata gagareshi?.

Bai santa ba,......bai kuma taba katarin ganin koda gilmawarta ba bare akai ga ganin hotonta.....wani abu daya fuskanci yana wahala shine.......sanin ainihin fuskarta da kuma kamanninta,duk kuwa da cewa SHUGABA ce kuma CEO ta babban kamfanin da kaf nijer babu na biyunsa. Babban kamfanin da ida kace baka taba sanin sunansa ba ko bakasan da zamansa ba kayi gawurtacciyar qarya.

Tana da wani irin dogon tsinkaye.......iya nazari da kuma karantar komai da wani irin kaifin basira dana idanu. A yanzun da take takowa tana sake fuskantarsa kwata kwata hankalinta bai tare da aisa dake fasalta mata altaab din da yadda take tsammanin samun dukka wani quality da take buqata tattare dashi.

Inda a yanayin nishadi take tabbas zata yiwa aisa murmushi ne,a yau ta yarda ta kuma sake yarda da gasken gaske ita din tasha bamban da kowa.......kamar yadda take diyar MUHAMMAD HAMMUD tallin tal! Haka dabi'unta dama zabubbukan rayuwarta sukayi nesa dana kowacce mace dama kowanne mutum.

A abinda baifi taku goma ta riskeshi ba ta gama tantance altaab.......ta kuma tabbatar cewa YA FADI bazaici ba ba kuma zai tsallake sharuddan da take neman ya cikesu kafin ya samu nasarar mallakarta ba.

Duk da cewa tana qare masa kallo ne amma koshi da ake kalla din bai fahimci shi take kalla ba......tsaiwarta a gabansa ya sanya wani abu tsarga masa tun daga qasan tafin qafarsa har zuwa tsakiyar kansa. Hakanan ya samu kansa da miqewa da dan hanzari,ya miqa hannu yana jifanta da murmushi,ya dawo da daya daga cikin kujerun dake wajen daura da tasa yana fadin.

"Barka da fitowa......marhab". Har yanzu idanunsa na a kanta yana jifanta da wani irin murmushi hadi da sanya hannunsa ya sauke nadin rawanin daya rage bayyanar fuskarsa gaba daya zuwa qasan habarsa......murmushi da ya jima da sanin cewa,yana daya daga cikin abinda yake narkar da zuciyar 'yammata.......yana daya daga cikin abinda yake qara masa kyau tare da fidda zatinsa.

Wani irin abu na daban yakeji a kanta,wani irin yanayi da bai taba tsintar kansa a ciki ba game da kowacce d'iya mace ba.......tabbas inda yasan yadda AKHANAN take.......da ya jima da nemawa kansa ita. Sai yakejin kamar daya daga cikin matan dake aljanna ce aka sauko da ita gidan duniya.

"Na tsani yawan kallo" Kalamanta suka shiga kunnensa da wani irin kaifi da sautin muryar da yanayin amonta ya tilasta masa kubcewar ajiyar zuciya.

A nutse ta taka zuwa wata kujerar ta daban da wadda ya ajiye mata,har qasan ranta tana jin tambayoyinsa shikam masu sauqi ne idan har zai iya amsasun,don bata jin kwata kwata zai iya shallake sharuddanta. Inda zata iya,zata zabi tsaiwa akan zama harta sallameshi,saidai bata jin hakan ya dace da darajarta da ikonta.......baqo ya shigo cikin masarautarta ya kuma zama dalilin tsaiwarta saman qafafunta.

"Waye kai?" Ta jefa masa tambayar bayan ta zauna sosai cikin kujerar,ta kuma aza qafarta daya saman daya da wani irin salon zama dake sake tabbatar da izza da qasaitarta.

Sauke idanunsa ya somayi akan qafafun nata,duk da ko farcenta bai samu daman gani ba amma salon zaman nata sai yaji gaba daya ya tafi dashi. Karon farko da yaji ya soma d'ari d'ari,ya kuma soma raina qarfin nasu ikon da a baya yakejin ba wata masarauta ko sultane da yakai mahaifinsa,ballantana azo Maganar 'yan'yan iko irin na nasu masarautar.

Tambayar tata ta bashi mamaki sosai,ya maida dubansa saman fuskarta yana son karantar gaskiyar tambayar tata. Abu na farko da yayi tsammanin fara ji daga bakinta shine tarba........ban gajiya sannu da hanya bisa tattakin da yayi har zuwa gareta,koda ace babu gaisuwa cikin tsarinta. To amma duka ba wannan ba........shi ALTAAB ne bata sani ba?.

"Da gaske bakisan waye altaab ba?.......altaab nu'......" Daga masa hannu tayi tana alamta dakatar dashi.

"Ka fadi matakin farko........waye kai?" Ta sake jefa masa tambayar tana ware manyan idanunta saman fuskarsa,idanun da suka sanya gabansa sake tsananta faduwa.

Yasha ganin blue eyes iri daban daban amma ba irin nata ba........yasha ganin idanuwa masu shape da launi daban daban amma banda irin nata.....natanne da gaske ko itama tana amfani da qwayar canza launin idanu?.

"Na tsani kallon qurilla" Ta furta a hankali tana ware yatsunta suka zama guda biyu.......

Motsin da tayi da yatsunta guda biyu kadai suka baiwa birra dake zaune daga qasa a gefanta alamar mataki daya ya ragewa altaab ya rasa damar ganawa da akhnan din.
Chapter 6 · 0% Book details