← Book details Luu Luu Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 3 OF 97

Sashe 3

Luu Luu Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Akhnan?......wasan kwaikwayo kikace fa?,wasan kwaikwayo?........zuwan altaab nu'uman dinne wasan kwaikwayon?". Itama zubawa aisa idanu tayi na sakanni sannan ta furzar da iska daga bakinta tana yiwa bushira,buhaina,birra da barra'u alamun su fita. Ajiye abinda yake hannuwansu dukkansu sukayi,duk kuwa da cewa basu qarasa shiryata kaman yadda mammina ta bada umarni ba......basu qarasa aikin da mammina ta basu babban gargadin su yishi yadda ya dace ba qasa da mintuna sittin kacal......saidai dukkaninsu sun sani.....umarni da maganar akhnan tana iya shafe ta mammina koda ta mammina dince daidai.

"Bansan da wanne idanu kike hange ba.....ban kuma san d wacce zuciya kike tunani ba akhnan......maganar shahinaz na gama yi miki yanzun.......saidai bakicemin komai akai ba amma kina neman sake birkita min tunani da maganganunki".

Cikin wani irin takunta na halitta tamkar macen dawisu ta qarasa zuwa ga wata Turkish sofa dake ajiye daura da ita ta zauna. Qafarta ta dora daya saman daya,sannan ta aza dukka hannuwanta guda biyu saman gwiwarta,ta kuma ware lumsassun blue eyes dinta ta zubesu saman fuskar aisa.

"Shahinaz.......bata da hankali aisa". Akhnan ta fadi karon farko......a karon farkon da tunda aisa ke bata labarin matsalar bata taba tofa komai a ciki ba koda kuwa da wasa ne.

Idanu aisa ta fidda cike da kalar wani irin mamaki.

" Akhnan?.......kin manta wace shahinaz?.....kin manta yadda yamaan yake a wajenta?". Kamar me nazartar aisa haka take kallonta,kafin ta zuqi wani qasaitaccen numfashi ta fiddashi a nutse ta tsakanin kyawawan labbanta da suka sake qawatuwa da kalar jambaki red mara damuwar haske me yawa.

"Ita ta zabawa kanta haka.......ita ta zabi rayuwa tazo mata a haka" Ta fada a taqaice da kalaman da suka sake jefa mamaki saman fuskar aisa.

Eh tana mamaki ne badon batasan wacece akhnan ba.......fitar kalaman daga bakin akhnan ba wani abu bane da zai sanyaka tsananta mamaki ba......aah......kawai ta dauka hukuncinta zai iya tsallake case din shahinaz da yamaan.

"Duk macen da d'a namiji ke wahalarwa ita taso........darajar diya mace ta zarce ta komai......musamman diya macen da tasan wacece ita,sannan kuma tasan kanta". Tayi maganar tana qarasawa gaban babban dressing mirror dinta da aka yiwa corner ta musamman cikin dakin,ta kuma dauki tissue dake cikin wani royal tissue box ta soma dauke jambakin dake saman labbanta.

"Ba zaki gane komai ba akhnan........na yarda,kinyi nisan da bazakiji kira ba........amma idan kika jarabtu da soyayyar altaab nu'umam zaki fahimci komai,basai na bata bakina da nufin yi miki bayani ba". Dif akhnan tayi,saidai hakan bai hanata goge labbanta da tissue din ba,kafin kuma murmushi ya subuce mata cikin qasa da second biyar. Wani irin lallausan qasaitaccen murmushi,wanda ba komai cikinsa sai wannan izzar dake yawo a jininta. Aisa na ankare da murmushi da ya sanyata nazartar akhnan a dabarance,tanason sanin meye ya sanyata murmushin?,don ba komai ke sakata murmushi haka ba.

"Altaab nu'umam?.......na yarda qawancanmu tun na quruciya bai gama gaya miki wacece khadeeja muhammad hummad ba.........aisa........banajin a DUNIYA akwai halitta d'a namijin data dace da KHADEEJA MUHAMMAD HUMMAD......har kuma a nade qasa bana tunanin za'a haifeshi,don har yanzun banji qamshi qamshin irin MIJIN BURI na da MAFARKINA BA.........saboda haka bani da tabbacin yin aure NAN KUSA ko a nesa" Takai qarshen maganar tana zuge zip din rigar don sam bata jin ta dace da yanayin da take jin kanta a ciki.

Idanu warwaje aisa ke kallonta,ta jima da sanin wacece akhnan........don batajin zata kasance ta biyar ko ta hudu ma cikin wadanda sukayi mata farin sanayya muddin bata tsaya ata uku ba......amma a yau din akhnan ta qarasa wanke mata kanta gaba daya.......ta sake samun tabbaci daga wasu daga kalaman shahinaz aduk sanda hirar akhnan ta taso a tsakaninsu.

"Har yau bakisan wacece ita ba......a kullum sabbin halayenta ne suke fitowa......saita rikide mata ta zame maka tamkat hawainiya a wadansu lokutan"

"Akhnan........" Ta kira sunanta a birkice tana dubanta,saidai kafin ta qarasa ta waiwayo ta zube mata manyan blue eyes dinta.....kafin kuma kowa a tsakaninsu yace wani abu an taba hannun qofar an turota kadan ta bude.

Macace wadda shekarunta na haihuwa suka fara turawa zuwa matakin girma da kadan......shekarun da duka basu wuce a sanyasu tsakanin arba'in da biyar zuwa da takwas ba.

Sanye take da wasu kayan da suke kama da suturar fulanin nigeria......saidai kuma akwai bambancin ado da kuma launin tufafin. Kanta lullube da wani babban zanin daya kasance nau'in tufafin jikinta,bawai kuma ta lullube kanta kawai bane aah....daurashi tayi saman kanta,girman zanin ya sanya daurin shima yayi girma sosai saman kanta,sai jelar kitsonta masu kauri sosai da suka biyo ta gefen kunnuwanta guda biyu. Labbanta baqiqqirin suke,har sai kayi zaton tana ta'ammali da taba sigari,saidai ko kusa bata da alaqa da wannan,saidai yanayin nata labban kenan wanda yake da tasiri a qabilarsu. Akwai wasu irin zane zane a fuskarta wanda hakan bai hana fitowar kamanninta ba.

Tafisu kenan......babbar hadimar hajiya hajja zaitun wato mammina.

"Allah shi ruhwa miki asiri.......uwargida giwa ke magana.......tace a gaya miki......dan gidan alhaji nu'uman na dab da shigowa masarauta......ki gaggauta qarasa shiryawa.......sannan ki fara biyawa ta wajenta tana son ganinki". Kyawawan idanunta masu zubin almond ta juya,sannan ta sauke wani sassanyan numfashi sannan ta gyada kanta a hankali kamar batason yin hakan,abinda ya bawa tafisu daman sakin qofar ta jata ta kulleta yadda take.

A nutse ta juya sannan ta fara takawa zuwa ga wata qawatacciyar qofa dake manne da dakin baccin,qofar da kai tsaye zata sadaka da wani mahaukacin dressing room dake shaqe da suturu na alfarma.

"Kiyi qoqari ki faranta ran sultane akhnan". Aisa dake zaune ta furta muryarta can qasa. Tsawa akhnan din tayi cak,kafin ta waiwayo a hankali,ta zube dubanta akan fuskar aisa din. Sosai taja fasali,kaman zatayi magana amma kuma sai taji babu buqatar hakan,ta dauke kanta taci gaba da takawa zuwa ciki.

Kaf kayan jikinta ta fiddasu ta zubesu a gurin,ta miqa hannu ta jawo daya daga cikin lausasan towels dake maqale a sashe guda na gurin ta daura,sannan ta matsa zuwa sashen dogayen rigunanta.

Mutum ce da ita da zabinta yasha banban dana kowa......mutum ce da ba lallai abinda yayi maka ya burgeka ko yayi daidai da tsarinka itama yayi mata ba......wata irin mutum ce da zabinta ya zama na daban kuma na musamman......tasan da hakan,tasan kuma dabi'unta fiye da yadda kowa zai gaya mata,wannan ya sanya take da wasu halaye guda uku. MISKILANCI daya gauraya da jinin sarauta dake kewaya duk wata jijiya ta jikinta yakai jinin zuwa ga zuciyarta. DAMUWA DA ABINDA YA SHAFETA ba tare da shiga shirgin kowa ba. Tana iya shafe kwanaki masu tsaho ba tare data bar kowa ya ganta ba......tana iya daukan dogon zamani tana rayuwarta ita kadai. SHAHINAZ da AISA mutum biyu rak da suke cikin rayuwarta tsahon lokaci,tun zamanin quruciya kawo yanzu......mutum biyun da har yau bata canzasu da wasu ba. Ba zasu canzu din bama Sam,don su daya ne suke iya fahimtarta a sanda tayi magana da kuma kafin ta yita,su daya ne takejin zata iya jinginasu da rayuwarta.

Ta dauki rayuwarta da matuqar muhimmanci. Ta daki rayuwarta a matsayin SIRRINTA ta dauki rayuwarta a matsayin wani rufaffen abu da bai shafi kowa ba.....bai kuma kamata kowa ya sani ko ya shiga ciki ba.

SULTANE da MAMMINA su daya ta yarjewa suyi zartarwa akan lamuran da suka shafi rayuwarta.....duk kuwa da cewa akwai MOMMA a gefe......wanda a idanu da kuma mizanin dacewa ita yafi cancanta da matsayin data bawa mammina.......saidai har cikin jijiyoyin dake tayata rayuwa tana jin matsayin MAMMINA ya shallake na kowa a gurinta......koda kuwa sultane kansa......wani lokaci tana jin sai ya jira MAMMINA.

*_uhmmm......tofa_*😟

Moroccan abaya black masu adon Golden din zare da wasu duwatsu masu qyalli ta yiwa kanta zabi. Wata irin riga ce daga sama dake da fadi yayin data cikin ta kasance daidai jikinta. Hade take da wata irin hula da take a mazaunin mayafi wanda ke maqale daga kafadar rigar daya bada yanayi na alkyabba,saidai tako ina tasha banban da alkyabbar,ta darata kyau daukan ido da kuma daraja gurin tsada. Duk da yadda ta saba da shiryata akeyi ta hanyar fidda mata kayan da zata saka,tayata daurewa da miqa mata takalmanta,bata turare powder da sauran kayan qyale qyale amma a yanzun duka taji bata buqatar wannan,ta matsa gaban madubi tana duban fuskarta.

Ta maida idanunta ta lumshe a hankali sannan ta budesu tana sake kallon fuskarta. Batasan dalilin da zai sanya sultane da mammina su dameta har haka ba,batasan me yasa suke damuwa tayi aure ba......batasan me yasa suka gaza fahimtarta ba......sun kasa gane cewa babu wani d'a namiji da zaiyi daidai da ita......ba wani d'a namiji da zaiyi daidai da muradinta......ba wani kalan namiji a duniya da zai cika dukka sharuddanta da kuma mizanin da takeso miji a gareta yakai ko ya cikashi. Bata ji a jiki da zuciyarta tana da buqatar aure.........bata kuma buqatar komai cikin rayuwarta.....rayuwarta ta dace da ita......komai yayi mata daidai yadda takeso......komai yana tafiya bisa sonta tsarinta da kuma muradinta......mene MA'NAR AURE a rayuwa irin tata?.

"Aure shine cikar mutunci kima da martabar kowacce d'iya mace......koda wacece ita.....kome ta mallaka......ko waye UBANTA!" Kalaman qarshe suka dawo mata daga bakin momma.......kalaman data gaya mata su a ranar data taqi karbar tayin auren Aaroon......tace shima baiyi mata ba kamar sauran mazan.

Idanunta ta sake lumshewa ta kuma budesu,wani zafin matar yana dawo mata sabo daga can qasar zuciyarta. A duniya ita daya ce tak take iya gaya mata duk maganar da taso........ita kadai ce take gaya mata duk maganar data fito daga bakinta.......bayan mammina da sultane.....ita daya qwallin qwal take saka idanunta cikin nata ta gaya mata abinda dukka taso.

Har yanzu zuciyarta taqi gamsuwa da matsayin matar a wajenta.......har yanzu taqi karbar wannan matsayin nata da wai sultane yake gaya mata ako da yaushe a kanta,zuciyarta ta gaza aminta da hakan harta kalleta da wannan matsayin. Ko waye......ko kuma su waye zasu bata mata rai....komai girma matsayi ko shekarun mutum indai a kanta ne sai inda qarfin mammina ya qare.......amma ta rasa ME YASA ta kasa takawa matar burki a kanta?,ta rasa wacce irin kara sultane yake mata a kanta?,batasan me yasa suka barta ita da ita ba har take yawan shige mata hanci da qudundune?. Ta fiya fada.......tana da zafin da bata ganin wanzuwarsa akan kowa sai a KANTA ita daya......ita akhnan.
Chapter 3 · 0% Book details