← Book details Luu Luu Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 63 OF 97

Sashe 63

Luu Luu Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Me kuma yanzu akayi miki?" Shehnaz ta fadi duk cikin neman hanyar da zata gusar da fadin ainihin dalilin rashin tahowarsu akan lokaci ita da aisa din.

Kaman akhnan din ba zata daina kallonta ba,sai kuma ta zare idonta daga kanta tana jin bata da lokacin bawa shehnaz amsar komai.

Duk da cewa tare suke takawa suna kuma komawa zuwa cikin gidan amma ba wanda yace da dan uwansa komai,daga qarshe suka rabu a mararraba,akhnan tana wucewa sashenta gami da bawa buhaina saqon ta aikawa nannie tace mata zata shigo.

Kafin ta gama hutawa a rest room dinta tuni barratu ta hada mata lafiyayyen ruwan wanka kaman yadda suka saba. Ruwan wankan da kullum ake shiryashi hawa biyu. Na farko ruwan ganyan gwanda ne daya zame mata abokin rayuwa dana ganyen lalle,wanda akayi packaging dinsa ake mata order dinsa tun daga qasar china. Kowacce safiya ganyen gwanda shine abu na farko da ake dafa mata ta shashi a matsayin tea(anti aging ne,indai bakison tsufa ki gwada shansa kullum da safe,yana hana tsufa da gyara fata sosai).

Mayukanta na amfani dukkaninsu organic ne daga mayuka na asali irinsu man kwakwa da sukanzo a mazubi me kyau da tsada,a kuma batar masa da kamannin da zaka kasa tantance wanne irin mai take amfani dashi?.

Wani irin kyau na musamman fatarta take dashi,kaman yadda glowing din skin dinta yasha banban dana mutane da yawa,zaka tara mutane sosai baka samu me fata me sulbi da jan hankali irin nata ba,wannan yana daya daga cikin abubuwan da yasa take alfahari da kanta,take kuma sake kula da jikinta tare da bashi wani irin tattali da muhimmanci.

Mintuna talatin ta dauka kafin ta fito,ta zarce zuwa spa room dinta,dakin da aka ware na musamman da dukkan wasu nau'ikan gyaran kayan jiki da 'ya mace zata buqata dan qarawa fuskarta da fatarta kyau dama jikinta gaba daya.

Idan ka kalli dakin zaka dauka an wareshi ne don yiwa hamshaqan mata gyaran jiki,irin tsadajjen gyaran jikinnan me aji da kuma tsada da daraja saboda yanayin kayan aikin da aka ajjiye a gurin.

Wani abu ne daya zame mata jiki duk qarshen kowanne wata,tana ware rana irin wannan ta shiga body steamer machine ta tsuma jikinta sosai da sassanyan turarukan da batasan daga ina aka samar dasu ba.
(Asalin turarukan INCENSE BY KABO DAUGHTER,masu tsananin kama jiki da muhalli da wani irin tattausan qamshi,tasted and trusted,ba tallan molanka bane +234 803 211 9803).

Wasu awanni biyun ta sake batawa wajen maintaining jikinta da gyara,bayan ta shafe kanta da kwababben lalle shima da wasu sinadarai na musamman.

Dukka wadannan din sun zame mata jiki,ta tashi dasu tun batasan darajar abun ba a gurin mammina.......asali daga wajen morsa safiyya aka fara mata,saidai rashin sakewarta da morsa safiyyan ya sanya ta miqa komai ga hadimanta da kusan dukka rayuwarta da kulawarta ta lura a hannunsu take,su kuma suna rayuwa da ita ne cikin sassan mammina din.

Sosai mammina ta riqi bada umarnin yi mata gyaran hannu bibbiyu,har ta girma yazo ya zame mata jiki. Wannan ya sanya ta zama wata ta daban........koda cikin mata dubu nawa zata shiga zaka hangeta ta fita daban a cikinsu.

Glowing dinta,qyallinta da kyan fatarta daya cakuda da wannan sirritaccen kyan na asalin buzuwa ya sake zama wani abu na daban a gurinta,kwarjinin data debo daga jinin sultane shima ya qara zama ado a komai nata.

Tsaf birra ta tayata ta shirya cikin wata sassauqar doguwar riga ta wani irin nau'in material da aka saqashi daga auduga da zare me daraja da tsada. Ko yaushe shirinta yakan zama me jan lokaci,tamkar shirin amaryar da ake kan hidimar aurar da ita,ahi yasa har yau har gobe tafiyarsu office dasu aisa bai taba zama daidai ba,har gwara ma lokacin dawowarsu.

Sha biyu saura na rana,don haka ta qarasa dining room,buhaina ta ja mata kujera ta dora mata falin yanki ta zauna,sannan ta bara'atu ta matso tana dora mata wani yankin na musamman saman jikinta don kada wani sashe na jikinta ya baci,a lokacin tana duba kiran da yake shigowa wayarta.

Daya daga cikin directors dinta na kamfani ne,saidai a yanzun bata cikin mode na wani magana daya shafi kamfanin,tana jiran ta gama settling wannan issue din dake gabanta tukunna,don haka ta maida wayar ta kife tana miqa hannu ta karbi spoon din da bara'atun keta miqo mata.

Sama sama ta taba breakfast din,so samu tayi zamanta a kebantaccen balcony dinta,to amma kuma nannie ce.......tun jiya tasan da dawowarta,ta kuma aiko still an shaida mata,amma ta gaza zuwa,wata fuskar ai tafi gaban mari.

Kawai dai bataso ta yiwa zuciyarta fami ne,tasan kuma halin nannie qwarai,bata tsoron ta mutu balle tayi rai muddin akan gaskiya ne.

Sultane yana matuqar ji da ita,ita kadai ta rage masa cikin 'yan uwanshi hudi da yake dasu,su kadai suka rage a raye a duniya......don haka dukkaninsu da idanun matsayi irin na sultane suke kallonta.

Miqewarta kawai ya gayawa birra me take nufi,don haka da sassarfa ta koma ciki,ta kuma dauko mata sassauqar alkyabbar da bata da wani nauyi ta daidaita mata ita saman kafadunta,sai tafara takawa kawai idanunta akan wayarta ba tare da tace komai kota dubi kowa ba.

Yau din a cikin jininta takejin izza da kuma miskilancinta yana motsawa,don haka duk inda zata wuce,dukkan wanda Allah yayi yaga gilmawarta zubewa yake yana kwasar gaisuwa,duk kuwa da cewa basa samun damar ganin fuskarta,bara'atu da birra dake biye da ita suke amsa musu da sautin GODIYA TAKE.

Daidai lokacin da aisa ke cikin katafaren parlour din nannie din,wani irin parlour da wanzuwarka ta farko a cikinsa zai gaya maka zallar sarautar da mamallakiyarsa take da jibi dashi.

Bai cika kayan alatu ba,amma komai na cikinsa me daraja ne da janye hankali

zaki samu daman karanta wannan QASAITACCEN LABARIN ta hanyoyin siyan tikitinki kamar haka da naira (700) kacal*

*Lambar asusu:- 6019473875*
*Safiya musa abdullahi*
*Keystone bank*

*KI TURA SHAIDAR BIYA TA NAN*

09166221261
KO
08187255862

*Al'ummar qasar nijer 🇳🇪*

*2349166221261*
*Safiya musa abdullahi*
*NITA*
*CFA 500*

*SAIKU TURA SHAIDAR BIYA TA LAMBAR DAI*

09166221261

*GA WADANDA ZASU SAKA KATIN WAYA NA MTN SUMA NUMBER DUKA DAYA CE*

*MTN CREDIT 700 ZUWA GA*
09166221261

*SHAIDAR BIYA*
09166221261

*_TAFIYAR 'YAR GASKE CE........LABARIN QASAITACCIYAR MACE CE KAWAI KE IYA SIYANSA_*

*QASAITA👑*

*HUGUMANKU CE*✍🏽

💎 *L U'U L U'U*
*_(The diamond)_*💎

*H U G U M A*

PAGE 55
___________________________
Bononza bononza https://wa.link/l1gcz8
Assalamu alaikum yan uwa mata masu albarka
Zuzeam ventures zatayi promo karshen wannan watan har zuwa cikin watan nan me kamawa insha allah
-Da 6k kachal zaa baki kaza da ciccibi da gari da tsumi da gumba pills shaki matse masu kyau da ingancin dazai sakaki dawowa ki qara harma ki kawo wani,
-Da 11k zaa baki kaza full da ciccibi da gari da tsumi da gumba, da maganin sanyi wannan promo ne akan murnar cika shekara 10 cif da fara sanaa a online Dan haka duk wadda take bukatar shiga cikin wannan promo Dan samun wannan garabasa to tayi sauri kafin ta kare
Kuma ku sani tsakani da Allah zaayi wannan promo komi me inganci ne
Kyau sosai zaa baku tsakani da Allah Idan kinada 4k ma zaa baki ciccibi kawai sai gari da tsumi masu kyau da ingancin suma,
Dan haka duk wadda take da bukata kofa a bude take
Idan kinada Yan uwa da abokan arziki zaki iya tallata masu idan kin kawo mutun goma suka shiga na 10k kinada package din 5k
Idan kin kawo mutun goma suka
Karku manta promo kwana 3 ne an kare insha Allah

Dukkaninsu suna zaune a qasan tattausan carpet din saqar hannu dake mamaye da parlour din,aisan na kashingide gefan nannie din,dankwalin kanta a qasa,yayin da waya ke riqe a hannun nannie da alama amsa wayar takeyi.

Sallamarta ta sanya dukkaninsu suka daga kai suna dubanta,aisa ce ta amsa tana tashi ta zauna sosai,suka hada idanu,sai akhnan din ta janye dubanta daga kan aisa din.

Ko batayi magana ba ta gama fahimtar abinda akhnan ke nufi......fushin takeyi da gaske,haushinta takeji,to amma a irin wannan lokacin da idan ta hau wannan qadamin fahimtar da ita yake zama abu me wahala,sai itama ta share kaman bata fahimci me take nufi ba.

A hankali ta tako zuwa gaban nannie a qasa kamar yadda ta samesu,ta zauna sosai tana tattare rigarta yadda zataji dadin zama,ta jingina da daya daga cikin kujerun alfarma da aka qawata parlour din,wanda sam sam basu ci guri ba.

Qamshin daya motsa daga jikinta bayan zamanta ya sanya aisa dubanta. Ko bata tambayeta tasan daga gyaran jikinta na wata wata ta fito,duk kuwa da cewa ita din gwanar qamshi ce,bata tunanin akwai wani company na turare da suka qware wajen fidda nau'ikan turaruka masu tsada da kama jiki da basusan da zaman akhnan din ba,amma wannan qamshin nasu khumras da lab lab din incense by kabo daughter daban yake. Wani qamshi ne da zai dinga saukar miki da nishadi,kaji zuciyarka tana wani irin sanyi da saukar da cikakken nutsuwa.

Har kullum kuma a koda yaushe,a duk kowanne wucewar daqiqa idan ta kalli akhnan mamaki take qara bata.

Da gaske ne.....kamar yadda take fada,kamar kuma yadda ta saba fadi.....bata rasa komai ba.......Allah ya bata dukkan wata cika da siffa da kowacce diya mace zataso ta mallaka......Allah ya bata wasu irin qualities da kebantattun abubuwa masu yawan gaske.....a zahiri a iya abinda idanu ke gani bata da wani sauran naqasu ko buqata........amma ta kowace fuska da kowa ke iya hange mata tana da buqatuwa zuwa AURE......abu dayan nan da har yanzu bata gamsu da cewa haka yake ba.

Har yau har kwanan gobe,har jiya da yanzu babu wani dalili guda daya da take basu ko zata basu kan haka,abinda kuma har a yanzun yake bawa aisa mamaki kenan da daure mata kai.

Wannan dalilin guda daya bai kai mizani ba.....QASAITARTA DA IZZARTA da kuma surki na GIRMAN KAI a wasu lokuta,basu gaya mata daidai din cewa......su kadai sun isa su mallake su kuma mamaye gami da ci gaba da riqe mata rayuwa ba har izuwa ga bigiren da ya dace da ita.

Hankalinta yana a kan waya,amma kunnuwanta na wajen nannie. Sai data zauna din sosai sannan ta fuskanci da HAIRAAN take wayar.
Chapter 63 · 0% Book details